
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 50
.....your work needs a rest". He just looked at him. The doctor quickly said, "I'm sorry sir". Imran smiled for the first time. Then he looked at the doctor. "Don't worry, just let him go, if he doesn't feel right, he will come back". When they were given, he went back to the state where their villages were in the hospital. He saw the damage done to them. He also went to the place where the bodies of those who lost their lives, including Captain Musa, turned their eyes on him. Captain Musa was a brave soldier. At one point, Major Imran was shot, and he died in the desert.
....Iska kaɗan Imran ya furzar yana kallon fuskar Zak-Shadow daya lumshe idanu. “Zak.. gaskiya akwai matsala, tunda har matarka ta fara nuna damuwa akan yarinyar nan”. Shiru kamar bazai tanka ba, sai kuma ya buɗe idanunsa da har sun ɗan sake kaɗewa akan Imran ɗin. “Saboda itace mai aure na?”. “Humm bazaka fahimta ba, kasan mata da kishi, bana son maimakon riƙe amanar da bani da haufi a kanka wajen riƙewa al'amarin ya koma wani abu daban. Taya kake tunanin zata riƙe yarinyar nan a wannan yanayin data fara nunawa?”. “Sai ta kasheta ai, ince dai ƙarshen kishin nasu kenan ko. Mtsoww, ni kada ka ɓata min rai ma”. Shiru Imran yay bai sake magana ba, amma tabbas shi yasan akwai rigima. Dan kishin Nabeeha ba ɓoyayye bane ga kowa. Tunda har akan ƴan uwansa da Mammah ba ɓoyewa take ba. A haka likita ya dawo ya duba Zak-Shadow ɗin, ganin ya ɗakko allurar barci ya dakatar da shi. “Ka sallame ni kawai”. Cikin girmamawa sojan likitan ya ce, “Kayi haƙuri Sir ko zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu ne, dan jikinka na buƙatar hutu sosai”. Wani kallo ya watsa masa kawai. Da sauri likitan yace, “I'm sorry Sir”. Murmurshi Imran yayi a karo na farko. Sai kuma ya kalla likitan. “Karka damu ka sallame shi kawai, idan baiji dai-dai ba sai ya dawo”. “Okay Sir”.
<<•>>°<<•>>°<<•>>
A ranar aka sallami Zak-Shadow daga asibiti. Shi mutum ne mai adalci da duba na ƙasa da shi akan komai daya dace. Dan haka maimakon tafiya gida ya samu hutun jiyya da aka basu sai ya koma jihar da ƙauyukan su Bankaura suke ƙarƙashinta ya duba sojojinsu da aka kwantar a asibiti. Ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba da ganin irin ɓarnar da akai musu. Dan sojoji da yawa sun jikkata. Hakama ya shiga har inda aka killace gawarwakin waɗan da suka rasa ransu, ciki harda Captain Musa. Lokacin daya ɗora idanunsa akan Captain Musa sai da suka sake juyewa, Captain Musa jarumin soja ne ɗan amanarsa, ya taka rawar gani matuƙa akan wannan yaƙin, babu abinda zasu masa sai addu'a. Lokaci ɗaya aka harbesu da Major Imran, shi da yake kwana ya ƙare tun a jejin ya rasu, shi kuma Imran ya suma. Bayan ya gama zagaya su kaf daga asibitin cikin barrak inda sojojin suke su, babban asibitin jihar ya nufa itama. Nan ko mutanen ƙauyukan ne da suma suka samu raunuka. Kamar yanda yay fata suna samun kulawa ta musamman daga gwamnati, akwai kuma jami'an sojinsu a tare da su, da ƴan sandan farin kaya. Suma ya dubasu. Daga nan ya wuce sansanin da aka samawa waɗan da suka tsira. Ganin yanda aka barsu a wulaƙance sai a tsakar wajen suke kwana damma zafi ne ransa ya ɓaci. Dama akwai zaman da zasuyi da Gwamnan jihar da shi da wasu manyansu a washe gari. Ai gaba ɗaya ya tattara takaicinsa ya ajiye har zuwa lokacin zaman. Daga sansanin cikin jejin da nasu sansanin yake suka koma. Komai ya lalace, sai dai anata kafa sabbin tantuna an kuma kawo wasu rundunar sojojin dan bazai yiwu abar yankin a haka babu tsaro mai ƙarfi ba. Har dare suna a cikin jejin, dan har cikin ƙauyukan Bankaura, Gangare, da Marke sai da suka shiga. Anan dama abubuwan sukafi tsamari musamman Bankaura a ƙarshe-ƙarshe. Dan an musu ɓarna matuƙa da zasu daɗe basu maida gurbinta ba. Har a yau ana zaƙulo gawarwaki a cikin jejin da ƙauyen Bankaura irin na wanda suka ɓuya a wasu wajejajen suka kasa fita. A lokacin da suka wuce ta ƙofar gidan su Nimrah ya kwashe mintina uku yana kallon gidan da tuna abubuwan da suka faru tun daga farkon zuwan su Imran da sanda yay kiransu. Randa Nimrah tai musu zancen falawa har zaman da sukayi da Ummanta. Rayuwa kenan, cikin abinda baifi sati huɗu ba komai ya lalace, dan gidan ya rurrushe sosai sakamakon bomb da yaran Dagger suka tayar musu suma tamkar gidan iyayen Umman Nimrah. Shiyasa suma baya jin akwai wani sauran zuri'ar data rage, idan kuwa sun rage to ƙalilan za'a samu kuwa a ciki, suma yara ne ko wanda basa a garin al'amarin ya faru. Tunda suka baro jejin zuwa masaukin da aka bashi a cikin barrak na jihar wanka kawai ya iya yi ya zauna yana wasu rubuce-rubuce, bayan ya kammala kuma ya hau salloli. Bai kwanta ba sai da yay sallar asubahi. Zuwa ƙarfe goma dole ya farka dan suna da meeting da zasu zauna da Gwamna akan harkar tsaro. Amintaccen yaron nan nasa, kuma munafukinsa a bayan fage da tunda ya iso yake nane da shi ya kira a waya. Babu jimawa ya iso. Bayan miƙa gaisuwar girmamawa tamkar wani mutumin arziƙi kansa a ƙasa ya ce, “Sir! Akwai abinda kake buƙata ne?”. Batare da Zak-Shadow ya dubashi ba ya miƙa masa wata ƙaramar takarda da ATM ɗinsa. “Kaje Boutique ka sama min kayan da zanyi amfani da shi. Saura ka ɓata min lokaci”. Ya ƙarashe maganar ƙarshe cikin dakewarsa da rashin ɗaukar raini. “I'm sorry Sir, bazan daɗe ba in sha ALLAHU”. Zak-Shadow bai sake tanka masa ba, hasalima ya ɗauke kansa ya koma gaban takardun da yay ta rubutu a daren jiya.
Koda Ojo ya fito sai ya harari ɗakin da Zak-Shadow yake, kafin ya kalla ATM ɗin daya bashi da takardar mai ɗauke da pin ɗinsa ya taɓe baki. Baiyi yunƙurin komai ba sai da ya fita a barrak ɗin gaba ɗaya. Nesa sosai ya samu waje ya tsaida mai mashin ɗin daya ɗakko shi. Sauka yayi ya bashi kuɗin, ya samu ƙasan wata bishiya ya zauna. Kamar yanda ya saba kai duk wani motsi da bayanan Zak-Shadow ga iyayen gidansa yanzun ma haka yay kira ya rattafa bayani. Tun daga dawowar Zak-Shadow a jiya har komawarsu jejin nan da ƙauyukan, da takardun da yaga ya baza a ɗakin daya kwana. Daga can wanda yake gayawar ya ce, “Su kayan daya aikeka ka saya na miye?”. “Sakawa zai yi sir! Sai dai kamar akwai inda zasuje shi da wasu manyanmu dan jiya bayan mun dawo barrak ɗin sunyi wani ƙaramin meeting su uku”. “Na baka daga nan zuwa awa ɗaya, nasan ina zai je. Idan ba haka ba kada ka kirani. Sannan ka sani, dolene a yanzu sanya idonka yafi na baya, dan mun rasa yara biyu a wannan tafiyar, an kashe ɗaya, ɗaya na cikin wanda aka jima rauni a asibiti”. “Babu wata damuwa Sir, komai kuke buƙata zanyi fiye da hakan, kada ka manta na shiga rigar soja ne kawai saboda aikin ku badan zama soja ba. Shiyyasa ma a yaƙin nan ban yarda na cusa kaina a halaka ba”. “Good! Da kake tuna hakan. Yaushe zai koma Abuja?”. “Bani da cikakken bayani akan hakan shima, amma nasan bazai jima ba tunda yana ƙarƙashin hutun jiyya ne shi da aminin nashi dama sauran Captains ɗin mu. Dan shi kaɗai ma yazo jiyan alamar akwai abinda yazo yi, duk da dai nasan shi mutum ne azababbe akan aiki shiyyasa ake shan wahalar cimmas cikin sauƙi”. “Mtsoww! Zai kuwa gane kuransa a wannan karon”. Daga haka ya yanke kiran. Ojo dake dariyar mugunta zaram ya miƙe yana cire layin daya saka a wayar tasa yay kira, ya maida ainahin layinsa da kowa ya sani sannan ya sake tare mashin ya hau ya tafi aiken Zak-Shadow.
★Kai sojan da Zak-Shadow ya saka ya biyo bayansa ke ɗawa tamkar ƙadangare, sai da ya ga mashin ɗin da Ojo ya hau yayi ɗan nisa sannan ya tare wani shima ya hau. Bayan Ojon yasa suka bi, sai dai bai sauka a mashin ɗin ba lokacin da suka iso inda ya sauka a nashi mashin ɗin ya shige wani Boutique. Har yace mashin ɗin ya juya sai kuma yace ya dakata, suna nan kusan mintuna ashirin Ojo ya fito cikin sauri yana kallon agogon hannunsa. Mashin ya sake tarewa ya haye. Yanzun ma sakawa sojan yay suka cigaba da bin bayansa, sai dai ganin ya sauka a ƙofar gate ɗin barrak ɗin shi kuma sai ya sauka can nesa ya biya mai mashin ɗin ya ƙaraso da kafa. Bai nufi masaukin Zak-Shadow ba har sai da ya tabbatar Ojo ya kai masa kayan ya baro ɗakin sannan. Cike da girmamawa yayi knocking, Zak-Shadow ya bashi izinin shiga. Cikin ƙamewa da sarawa ya ce, “Sir! Duk inda yaje tare mukaje da shi ina biye......” tsaf ya labarta masa komai da ya gani ya kuma ji daga Ojo. Wani kalar zuba masa ido Zak-Shadow yayi, dan tabbas zuciyarsa ta girgiza. Saboda daga jiya zuwa yau ne kawai ya ɗarsa zarginsa akan Ojo, zargi kuma ba irin wanda ya samu bayani ba a yanzu. Dan kuwa shi zargin ma da yakema Ojon daban, abinda yaji a yanzu daban. A take wata ƴar zufa ta taru masa a goshi, idanun nan suka shiga juyewa. Da wata irin tsatstsaurar murya ya furta, “Ka tabbatar da abinda ka faɗa?”. “Yes sir! Duk abinda na faɗa maka shine gaskiya, zaka iya saka wani binciken bayan ni ma domin tabbatar wa”. Wani irin amsa kuwwa sunan Ojo ya shiga yi a kunnen Zak-Shadow da brain ɗinsa, har yana ma jin kamar wata juwa-juwa na neman ɗibarsa. Ojo fa, yaron daya bama yarda mai girma bayan Imran, dan ko sauran amintattun yaransa basu kai Ojo ɗin ba ciki kuwa harda shi wannan Yusuf ɗin daya kawo masa bayani akan Ojo ɗin yanzu. Lallai babbar magana, ashe kamar yanda yayi hasashen yaƙin nasa biyu ne na cikin gida dana waje hakan take.
>>•<>•<<>•<<>•<<
Har Zak-Shadow suka isa gidan gwamnati al'amarin yaronsa Ojo na masa kai-kawo a zuciya. Da ƙyar ya iya dannewa suka tattauna sosai akan abinda ya dace. Bai gusaba kuwa sai da ya sakko zancen ƴan gudun hijira da aka bari a wulaƙance. Babu wani tsoro ko shakka kuma ya nuna ma gwamna idan fa akai sakacin barinsu a wulaƙance to za'a iya fuskantar ƙalubale mai girma da yafi wanda ake kai a yanzu. Amma basu muhallin zama da tattara yaransu a saka a makarantu a samawa matan sana'ar yi da sauran mazan da suka rage shine babban gata garesu dama al'umma baki ɗaya.........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 51_
__________________
https://vm.tiktok.com/ZSHcfQFhUuBVU-MpLRV/https://www.instagram.com/dijas_delicacy_?igsh=MWp3MThqcXlsZXB2eg==Wa.me/+2348140002981
https://www.instagram.com/dijas_delicacy_?igsh=MWp3MThqcXlsZXB2eg==
Assalamu alaykum mutanen Sokoto Da kewaye Shin Ko kunsan cewa DIJAS DELICACY ashirye take Domin faranta ranku a bukukuna Da kowani irin even? Kama Daga samosa, doghnut, spring rolls meat pie, birthday cakes Da sauransu Bata tsaya anan ba tana amsar orders koda yaushe. Inda samosa kike nema frozen Ko fried duka tana dasu akan 3k 10pcs and she bakes daily🥰 Bata tsaya anan ba GA masu son gyaran jikinsu wata skin care tana siyarda best skin care products Kama Daga face wash, face cream,body butter, shower gel dadae sauransu tana aeka Kaya a kowani gari cikin aminci Da yardar allah GA no. Dinta kiyi saving Domin samun naki was.me/+2348140002981 __________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________