
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 40
.....announcement..." He couldn't finish because of the blood he was doing. Explaining the violence that Major Imran Abbas is in is a waste of time. But since he is a soldier, there is no sign of trembling or physical distress. He personally took this soldier in his hand and turned their camp.... We can say that this is the beginning, the beginning of the sudden violence that the conspirators took days to prepare and adjust this part for the implementation to be sure. It is not a small damage to the three camps that were attacked. Their communication devices were cut so that they were unable to report to Zak-Shadow about the situation. At around eleven o'clock they got a chance to go out with their relatives, and six people died since the morning, four soldiers and two terrorists... Zaria where he was studying. He didn't meet their Dada until they came out for evening prayers. They loved and loved Zak-Shadow, and they saw him as a father. They only called him by the name of Dada.....
.....Gari ya ɗan fara hasken dake bayyana safiya, Major Imran daya kasa zaune ya kasa tsaye na a bakin ruwa yana zubama tsuntsayen nan dawa tamkar yanda sukeyi shi da Zak-Shadow wani irin nishi ya fara tasiri a cikin kunnen sa. Kowane yanayi soja mai ankarewa ne akan aikinsa. Cikin sauri ya ajiye robar dawar yana waige-waige da ƙara buɗe kunne saitin inda yake jin nishin. Tabbatar da wajen ya sashi zabura tare da ciro bindiga a jikinsa yaja ya ɗana, cikin sanɗa da jarumta ya tunkari wajen. Dai-dai yana isowa gab aka ƙara jan nishin da ƙarfi tare da hankaɗa ciyayin wajen. Soja ne ya bayyana jikinsa kace-kace da jini, da ƙyar yake iya ambaton, “Commandos, help us! We need you here! Where are you?.”. Ai Major Imran baima San ya zabura kansa ba. Cikin tashin hankali yakai duƙe gabansa yana mai kamashi gaba ɗaya... “Soldier! What happened? Report now! Are you okay?.”. “Sir! Hari, hari aka kai mana a kusurwar ƙofar kudanci, sun mana ɓarna, sun datse na'urar sadarwa, shiyasa muka kasa isar da sanarwa......” Ya kasa ƙarasawa saboda aman jini da yake yi. Bayyana tashin hankalin da Major Imran Abbas yake ciki ɓata lokaci ne. Sai dai da yake soja-soja ne babu alamar rawar jiki ko ɗimuwar zahiri. Da kansa ya ɗauki sojan nan a hannunsa ya juya nasu sansanin....
Zamu iya cewa wannan shine mafari, mafarin tashin hankali na bazata da masu makirci suka ɗauki kwanaki suna shiryawa da daidaita wannan gaɓar domin aiwatarwa ya tabbata. Ba ƙaramar ɓarna akaima sansani ukun nan da aka kaima hari ba. Gashi an yanke musu na'urorin sadarwa ta yanda har Headquarter sun gagara kai rahoto balle sanar da Zak-Shadow halin da ake ciki. Sai misalin ƙarfe goma sha ɗaya aka samu damar fita da waɗanda suka jikata, sai mutane shida da tun asubahin ma sun rasu, sojoji huɗu ƴan ta'addan biyu......
>>>•>•>•<•<•<<<
Tunda ya fita sallar magriba sai ƙarfe tara saura suka shigo gidan shi da Ammar dake maƙale da shi, dan shima gab da magriba ya iso daga Zaria inda yake karatu. Bai haɗu da Dadan nasu ba sai a masallaci bayan sun fito sallar magriba. Sosai suke so da ƙaunar Zak-Shadow, dan shi suka buɗe ido suka gani kuma suke kallo a matsayin uba. Ba sunan Dada da suke kiran shi ne kawai girmamawar da suke masa ba. Hatta umarni idan ya basu ko saka doka akan abu ko hanasu yin wani abu duk son da sukema abunnan sun barshi kenan har abada. Dan sunyi imanin bazai hanasu abinda zai amfane su ba, ba kuma zai sakasu yin abinda zai cutar da su ba. Komai na hidimar rayuwarsu: ci, sha, ilimi, lafiyarsu da duk wani abu da akema ɗa ɗan gata shi da Mammah ne sukai musu a rayuwa. Taya zasu gagara masa biyayya su zama butulu. Sun tabbatar soyayyar da Dada ke musu soyayya ce irin ta ƴaƴa da mahaifi. Babu abinda zasu biya shi da shi sai addu'a da fatan shima ALLAH ya bashi tashi zuri'ar, dan rashin haihuwar nan tasu na damun kowa kawai dai basa magana ne... Tunda suka baro gidan su Imran surutu kawai yake zuba masa. Shi ko Zak-Shadow nashi murmurshi, sai lokaci-lokaci yake jefa magana a taƙaice. Hakan baya damunsu, dan duk wanda yasan Dadan su yasan bamai yawan magana bane. Sam ba miskili bane, amma bai da yawan surutu ko dariya. Idan yaso hirarsa kuwa zakaji yanayi da Mammah sosai kamar bashi ba. To suma sukan ɗan samu kanshi wani lokacin ya biye musu idan yana jin nishaɗi.. Gaba ɗaya kowa na falon har matarsa da ƙannenta. Dama Aunty Ummi da Aunty Mommy da tun ɗazun suna gidan tare da shi. Aunty Mimi ce sai yanzu ta iso, ɗazun sanda Biebah ta kirata sun fita da mijinta anguwa. Suna yin sallama kuwa ta taso a guje cike da farin ciki tana faɗin, “Oyoyo Dada ta rungumeshi”. Kansa ya girgiza kawai tare da ɗan bubbuga bayanta. “Ke dai baƙya girma ko”. Ɗagowa tai tana dariya da kamo hannunsa cikin nata ta riƙe. “Dada in dai a gabanka ne ina nan ƴar yarinyata Autarka, dan ma wannan ɗan buƙulun yazo ya ragen farashin autar ne da waccan yarinyar”. Tai maganar tana hararar Ammar da Biebah. Ramawa Ammar ɗin yayi shima, “Sai ki haɗiyi ƙwallon mangwaro ki suma, dole dai a ce da mijin iya baba ai. Muma autocin nan dai ne ko Auta”. “Yes Yayana”. Biebah ta amsa masa tana ma Mimi gwalo. “Dada ka gansu ko, shiyasa idan baka nan bana son zuwa gidan nan na daɗe”. Murmushi yayi kaɗan shi dai, sai kuma ya shafa kanta da faɗin, “Ki daina lulasu, ke yanzu ai kin girmi ƙuruciyarsu. Kalleki fa da yara har biyu”. Fuskata ta ɓoye a jikin hannunsa, dan ita kunya take ji ma ace ta haihu. Shima bai sake cewa komai ba yaja hannunta suka ƙarasa cikin falon. Tashi Yaya Bilal yay ya bashi kujera da yake, ya koma kusa da Mammah, dan shi dama ɗan shagwaɓar Mammah ne, ya girma amma bai san ya girma ba. A ƙasa Ammar da Mimi suka zauna kusa da ƙafafunsa, duk sun riƙe masa hannaye kamar wasu ƙananun yara ko zai gudu ya barsu. Biebah tai ƙwaɓa-ƙwaɓa da fuska kamar zatai kuka ganin sun tsare ko ina bata samu wajen zama kusa da Dada ba. Gefensa ya nuna mata da ido, basa iya zama a kujera idan yana kan kujera har su Ja'afar kuma, amma bazata iya kuma ƙin bin umarninsa ba, dan haka ya taho saɗaf-saɗaf kamar munafuka ta zauna a hannun kujerar da yaken. Dai-dai nan Mommy ta fito a kitchen ɗauke da kofi akan tray ƙarami. “Oh ni, duk kunzo kun wani dabaibayeshi kamar ku kaɗaine da Dadan.” “Kema dai ƙya faɗa Mommy”. Cewar Aunty Ummi tana harararsu. Murmurshi Mammah tayi, yayinda matarsa dake cike fam da kishi da takaici kamar ba ƴan uwansa ba ta ɗan taɓe baki. Mugun haushin wannan soyayyar da yake nunawa ƴan uwansa take. Ta taɓa suɓutar bakin nuna masa abin yayi yawa, daya zuba mata wani mummunan kallo ai bata sake kwatantawa ba. Bilal ya ce, “Dada dan ALLAH sati biyu zakai mana ko? ALLAH muna missing ɗinka muna son muyita kallonka, idan kana nan gidan yafi daɗi”. Sai da ya amshi mug ɗin shayin da Mommy ta kawo masa ya kai baki kaɗan sannan ya amsa Bilal ɗin. “Kuyi haƙuri Bilal, lokaci na zuwa da zan zo na zauna tare da ku na baku dukkan lokaci na. Nima ina jin farin ciki a duk sanda nake tare da ku”. Sosai maganarsa ta shige su da saka su jin ƙaunarsa na ratsasu. Naneeha data ɗan zuba masa ido ya kalla, sai kuma ya kauda kansa. Falon ya ɗanbi da kallo tare da faɗin, “Ina Mu'azz!”. Biebah ta ce, “Dada yayi barci, ya gaji da jiranka ya ɓingire”. “Da wuri haka”. Ya faɗa a taƙaice. Mammah dake duba wani littafin addini ta ce, “Wannan ɗan naka ai ruwa-ruwa ne. Ina ga dai sojan zaka maidashi ko zai canja.” Dariya sukayi su duka. Banda shi daya ɗan murmusa kawai. Haka suka cigaba da hira cike da nishaɗi, duk da shi tashi maganar bamai yawa bace, sai dai sun sha murmushi dan su kam yana musu murmushi ba kamar a waje ba. Kasancewar duk anan su Aunty Ummi ma zasu kwana wannan hira bata tashi ba sai kusan ƙarfe ɗayan dare. A hakan ma sai da Mammah tace su barshi yaje ya kwanta, dan su basu ƙi a kwana ana hira suna ganin Dada ba. Tuni Nabeeha da ƙannenta dama sun koma can sashen nasu tun wajen 11. Dan haka ya fito, sai Ammar da Bilal da sukai masa rakkiya har ƙofar sashen nasa sai da ya shiga sannan suka koma...
Ganin haske alamar batai barci ba kai tsaye ɗakinta ya nufa a karo na farko tun isowarsa gidan. Zaune kuwa ya sameta tana waya, ta canja kayanta zuwa na barci da sukai mata ƙyau sosai. Idanunsa a kanta yay sallama cike da nutsuwarsa. Idanu ta ɗago a hankali ta kalleshi, sai kuma ta kawar tana yin sallama da wanda suke wayar. Dai-dai tana ajiye wayar yakai zaune kusa da ita, kasancewa a sofa take zaune. Ganin kallon daya zuba mata cike da tsarguwa ta ce, “Mummy na gaishe ka”. “Na gode”. Ya faɗa a taƙaice. Kanta ta jinjina masa itama, sai kuma ta matso kaɗan ta kwantar da kanta a kafaɗarsa, hannunsa ta kamo ta saka nata a ciki. Mintuna kusan biyu suna a haka shiru, sannin hirarsa sai ya gadama ya sata ɗaga kai tana kallon ƙyaƙyƙyawar fuskarsa, idanunsa a lumshe suke tamkar mai barci, amma tasan ba barcin yake yi ba. Dan haka ta ɗan matsa hannunsa tare da faɗin, “My Cool”. “Uhhmm”. “Kayi barci ne”. Maimakon amsa mata sai ya buɗe idon kawai yana kallonta. Kasa jurewa tai ta ɗan risinar da nata tana sauke numfashi. Cikin jin shakkar faɗar abinda ke bakinta ta cigaba da matsa yatsun hanun nasa, kafin a ɗarare ta ce, “Dan ALLAH wannan karon ka yarda muje muga likitan nan mana. Ta hakanne zamu fahimci idan wata matsala ce a tare damu mu tashi mu nema magani. Shekara goma sha fa ba kwana goma sha bace My D. Dan ALLAH kai baka jin wani abu a ranka idan ka kalla ƙannenka da yaransu? Ga su Ja'afar suma zasuyi nasu auren, nan da shekara ɗaya sai kaga duk suma da yaransu. Haka kake son suma matansu suzo a bayan bayana su haihu ina kallo....” Shiru ya mata yaƙi tankawa. Sai hakan ya ƙara ƙular mata da zuciya, dan haka yake mata a duk sanda ta kawo masa batun zuwa ganin likita. Kuka ta fashe masa da shi mai ratsa zuciya. Kafin ta yunƙura fuu ta miƙe da nufin bar masa wajen, batare daya kalleta ba shima ya riƙo hannunta, tare da fisgota ta faɗo jikinsa gaba ɗayanta. Kici-kici ta fara nason tashi tana ƙara ƙarfin kukanta, amma riƙon da yay mata da hannu ɗayan nan kawai ta gagara tashin. Ganin ba iya ƙwatar kan nata zatai ba da gaske sai kawai ta kwantar da kanta a ƙirjinsa ta cigaba da raira masa kukan.Tsawon lokaci suna a hakan idanunsa a rufe tamkar bai san tanayi ba, ganin ba dainawa zatai ba ya ɗagata a jikin nasa ya miƙe da nufin bar mata ɗakin gaba ɗaya.........✍🏼
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._