Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 55

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 55

..... Shehu, it is enough that he will reject this report without research. The first time he took a tissue and wiped the sweat from his forehead. In giving orders, he said to Lt. Col. Garba, "Okay you can go". Not so Lt. Col. Garba didn't want to, but he stood up and left the office. Even after he left, the Colonel was reviewing the report for more than fifteen minutes before he gave up and went to the Brigadier General's office with the documents in hand. After he was given permission to enter, he bowed and saluted all at the same time. Brigadier General Abraham Yohana stopped writing and did not show him a chair. Becoming a Colonel, he respectfully placed his file in front of the Brigadier General. "Sir, it is a big issue that needs to be reviewed urgently". For the first time, the Brigadier General looked up and looked at him, then he turned his attention to his writing and briefly said, "What are you doing Colonel Galadima?". "We received a report on Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu about this conflict led by him." One of them said, "The meeting with me has not ended yet..."

Standalone post2,267 words

.......Da mugun ƙarfi Colonel ya buga desk ɗinsa yana mai zazzaro idanu da ture takardun daya gama karantawa, cikin ƙaraji ya furta, “Lt. Col. Garba! Kana da hankali kuwa zaka kawoma mutane wannan maganar banzar. Ko gaskiya ne maganar da ake faɗa akan kana kishi da Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed ne?”. “I'm sorry sir! Wannan shati faɗi na mutane ne kawai da son haddasa fitina. Dan kawai abinda ya faru tsakanina da shi a NDA na ƙuruciya sai a kalli abu mai muhimmanci irin wannan matsayin rashin jituwa. Sir nifa soja ne, yana da ƙyau na fargar da hukumata ɓarna idan naga zata afku balle ma irin wannan. Sannan ban kawo shi gareka kai tsaye ba sai da na tabbatar, ina kuma da shaidu sosai da suma suka gani kuma akayi a gabansu a cikin yaransa”. Idanu kawai Colonel Galadima ya zubama Lt. Col Garba. Sai kuma ya sake jawo takardun yana sake dubawa ɗaya bayan ɗaya. Sosai zuciyar ke rawa, dan kuwa duk wanda ya kwana ya tashi yasan ƙwazo da gaskiyar Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu, sai dai isa cewa zai yi rejecting ɗin wannan report ɗin batare da bincike ba. Karo na farko ya zari tissue ya goge gumin daya tsatstsafo masa a goshi. Cikin bada umarni yace da Lt. Col. Garba, “Okay zaka iya tafiya”. Ba haka Lt. Col. Garba yaso ba, amma sai ya miƙe cikin nuna jimami ya fita a office ɗin. Koda ya fita Colonel yafi minti sha biyar yana sake duba report ɗin kafin ya haƙura ya miƙe da takardun a hannu zuwa office ɗin Brigadier General, dan bashi da hurumin cigaba da riƙe report ɗin a wajensa dole ya kaisa sama saboda maganar babba ce sosai. Bayan an bashi izinin shiga ya ƙame tare da salute duk a lokaci guda. Brigadier General Abraham Yohana daketa rubuce-rubuce batare daya ɗago ba yay masa nuni da kujera. Zama Colonel yayi, cike da girmamawa ya ajiye file ɗin hannunsa gaban Brigadier General. “Sir wata babbar magana ce da ake buƙatar dubata da gaggawa”. Karo na farko Brigadier General ya ɗago yana kallonsa, sai kuma ya maida kansa ga rubutunsa a taƙaice ya ce, “Mike faruwa Colonel Galadima?”. “Report ne muka samu akan Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu game da wannan rikicin daya jagoranta.” Batare daya ɗago ba ya ce, “Ba ɗazun aka gama meeting da ministan tsaro a fadar shugaban ƙasa ba akan karrama shi, shi da duk wanda akai yaƙi da bizne waɗanda aka rasa. Kuma harda kai ka sani”. “Hakane sir! Amma fa al'amarin na neman canjawa ne. Dan wannan report ɗin na nuni da Lt. Col Haysam Abdul-rasheed Shehu da hannunsa akan shirya komai daya faru, hasalima shugaban ƴan ta'addan dake hannun jami'an bincike ya tabbatar da shima yana cikin ogans......” A fusace Brigadier General ya katse Colonel. “Wace kalar banzar magana ce wannan. Haysam!? Haysam! Dai? Za'ace yana tare da ƴan ta'adda?”. “Wlhy sir nima abin ya girgizani matuƙa. Amma ka duba ka ga report ɗin dai. An kawo shi ne tun daga jihar da abin ya faru. Kuma banan kawai ba har gidan gwamnati ya isa”. File ɗin Brigadier General ya ɗauka ya shiga dubawa. Cikin ɓacin rai yay wurgi da takardar yana faɗin, “Impossible. Har abada Haysam bazai taɓa koda ɗagama ƴan ta'adda ƙafa ba balle haɗa hannu da su. Wannan ma zancen banza ne, ba kuma Haysam ake son ɓatama suna ba hukumar mu ake son ɓatama suna”. Shi kansa Colonel Galadima abinda zuciyarsa ke bashi kenan. Amma harga ALLAH zuciyarsa ta tsorata, dan ya fahimci wannan shiri ne mai ƙarfi da girma. Musamman idan akai dubi da yanda aka shirya report ɗin kansa..

Cikin ƙanƙanin lokaci takardar ta gama zagaye Headquarter ɗin. Babu shiri manyan suka haɗa meeting na gaggawa. Sai dai ko farawa basuyi ba kira ya samu General na kuma gaggawa daga ministan tsaro bisa umarnin shugaban ƙasa dake son ganinsa da gaggawa a gidan gwamnati cikin sa'oi biyu kawai. Dole yabar nasu meeting ɗin akan Lieutenant General ya jagoranta. Shi kuma ya wuce amsa kiran shugaban ƙasar......

<><><><><><><>

Yanda Nabeeha ke ribzar kuka ba ƙaramin sake zafafa zuciyar Mammah take ba. Amma ta danne cikin bada umarni tace ma Ma'aruff. “Kira min Dadan ku”. Sai da ya watsama Nabeeha da Momynta harara sannan ya miƙe. Shima Ja'afar dake a wuya miƙewar yayi. Ammar kam da shigowar shi falon kenan baiji maganganun da Momyn Nabeeha ta faɗa ba tsaye yay daga bakin kofa kawai yana kallon Nabeeha ɗin. Har Ma'aruff na neman bugeshi. Kauce masa yay ya fita. Ja'afar ma ya shiga kitchen yana kai waya a kunnensa. Bayan gaisuwa ya zayyanema Uncle Nasiru daya kira komai dake shirin faruwa a gidan. Ba ƙaramin tashi hankalin Uncle Nasiru yayi ba da jin ɓacin rai, cikin sauri yace gashi nan zuwa gidan. (Shima dai Uncle Nasiru yanzu a nan Abuja yake, dan anan yake aiki, kuma anan cikin anguwar yake zaune dan da ƙoƙarin Zak-Shadow ma ya samu filin daya gina gidan, dan haka basu da nisa da su sosai). Ja'afar na yanke wayar ya kira Imran shima. Shima rai ɓace ya ce, “What! Yarinyar nan nada hankali kuwa?”. “Yaya dama ai mahaukaciyar ce kune baku fahimta ba. Wlhy badan mutuncin Uncle Nasiru ba yau sai na fasa mata baki na karyar ƙafar uwar tata”. “No. Ba wanda ya aikeka kai kuma. Gani nan zuwa gidan nima”. Daga haka ya yanke kiran...

A lokacin da can zaman meetings ya ɓarke akan Zak-Shadow da alama nan wata sabuwar ƙurar ke shirin tashi saboda baƙin kishin matarsa Nabeeha da rashin hankalin uwarta dake bata goyon baya saboda wani burinta na banza da wofi. Kasancewar Ma'aruff ya iske Dadan su na wanka sai da ya jirashi, dan haka kusan lokaci ɗaya suka shigo falon Mammah da Uncle Nasiru. Suna zama Imran na shigowa. A can kuwa Biebah dake kitchen tana aiki taji komai tuni ta fice can baya tana kuka ta kira Aunty Ummi da Aunty Mommy da ma Aunty Mimi ta gaya musu abinda ke shirin faruwa. Ai tuni suma kowa ya ɗakko hanyar zuwa gidan. Yo ubanwa ya isa taɓa musu Dada a zauna lafiya ba'atada yaƙin duniya na uku ba. Ai wlhy Mammah ce kawai keda wannan isar, itama dan uwa ce babu yanda zasuyi da ita. Duk wannan abin dake faruwa Bilal baya gidan, ya tafi saka Nimrah a islamiyyar su Mu'azz, boko ma in sha ALLAHU gobe-gobe za'a kaita. Dan tunda Mammah ta gama jin komai a wajen Zak-Shadow ta yanke shawarar a yau ɗin nan za'a saka Nimrah islamiyya gobe boko ko hakan zai sa ta saki jikinta. Dama gashi anyi sa'a cikin satin nan aka koma hutu kuma zangon farko ne.

Tunda Zak-Shadow ya shigo falon yaji zuciyarsa ta sake zuwa wuya. Da ƙyar ya iya daurewa ya gaida Uncle Nasiru ya samu kujera ya zauna, tare da jingina bayansa ya lumshe idanunsa kawai yana sauraren zagin da Uncle Nasiru kema Nabeeha da ke neman komawa faɗa tsakaninsa da Momynta data saka baki. Sai da Mammah ta basu haƙuri da nuna musu kuskuren abin kunyar da suke neman yi agaban yara sannan sukai shiru kowa na huci. Dai-dai nan Imran ya shigo da sallama shima. Kai tsaye ya ƙaraso falon dan shima ɗan gida ne, har bedroom ɗin Mammah shiga yake. Yanzu ma sai da ya gaida su ita da Uncle Nasiru da Momyn Nabeeha su Ma'aruff suka gaisheshi shima. Da ido Mammah taima su Ma'aruff ɗin umarnin fita a falon. Badan sun so hakan ba suka fita. Amma sun san duk rintsi Mammah bata maganar data shafi Dada a gabansu in har bata farin ciki bace, amma a ganinsu wannan tasha banban ai, sai dai duk da haka an kora su waje. Bayan gama fitarsu da rufe ƙofa suka koma jikin windows suka maƙe, dan sun fi son jin komai yanda zasu ci ƙaniyar Nabeeha da lasisi. Mammah da bata san suna laɓe ba kai tsaye ta maida kallonta ga Zak-Shadow. “Muhammad”. Ta kira sunansa kamar yanda ta saba. Idanunsa da suka rine ya buɗe, sai kuma ya gyara zamansa cike da girmamawa ya amsa mata. “Miya haɗaka da matarka haka da zafi har kake zaginta da korota daga ɗakinka cewar zaka daketa”. A karo na biyu ya ɗan juya ya kalli sashen da Nabeeha take manne da Momynta, sai kuma ya dawo da kallonsa ga Mammah. Ƙaramin murmurshin takaici yayi, mamakin wannan ƙarya ta Nabeeha na cizonsa, amma sai ya danne, cike da girmamawa ya ce, “Tazo min da wata maganar banza ne akan yarinyar nan da kuka taho da ita daga asibiti Mammah”. “A gani na ai bayani ya kamata kai mata ba kakkausan lafazi ba.....” “Miye wani kakkausan lafazi zagi dai.” Momyn Nabeeha ta katse Mammah a hasale. “ALLAH kika ƙara magana sai kin bar falon nan”. Cewar Uncle Nasiru yana nuna Momyn Nabeeha. Itama a hasale ta ce, “To ubana”. “Dan ALLAH kuyi haƙuri Yaya”. Mammah ta faɗa cikin tausasawa, sai kuma ta cigaba da faɗin, “Muhammad ita yarinyar wacece a wajenka? Ƴar waye? Miyasa kazo da ita nan?”. Ta jera masa tambayoyin duk da kuwa ita ya mata bayanin komai ɗazun.. Iska ya furzar mai ɗacin gaske, dan haka Imran yay saurin faɗin, “Mammah bara nai muku bayanin komai”. “Ai bakai aka tambaya ba”. Momyn Nabeeha ta faɗa tana hararar Imran. A hasale Uncle Nasiru ya ce, “Shine kuma zai bada amsa, kai Imrana faɗi muna jinka. Kai Imran ya jinjina ma Uncle Nasiru yana gyara zama. Yayin da a jikin Windows su Ja'afar kejin kamar su tsallako falon su daki bakin Momyn Nabeeha, dan zuwa yanzu suma su Aunty Ummi sun iso, tuni kuma su Ma'aruff sun musu bayanin komai dan haka suka nema wajen maƙewa suma ayi komai da su. “Wannan yarinya sunanta Naja'atu, amma iyayenta na kiranta Nimrah saboda sunan kakarta taci...........” tsaf Imran ya zayyane musu komai, sai dai banda ainahin halin da mahaifinta ke ciki, hasalima kamar yanda Umma ta roƙa sai ya sanar musu mahaifinta ya rasu a rikicin kamar mahaifiyar tata. Ba ƙaramin daɗin hakan da yayi Zak-Shadow da Mammah sukaji ba. Dan ita Mammah komai sai da Dadan ya sanar mata bai ɓoye ba. Cikin damuwa sosai Uncle Nasiru ke jimanta al'amarin, da tsakanin jin tausayin Nimrah a ransa. Amma a mamakin kowa sai ji sukai Nabeeha ta ce, “Wlhy ban yarda ba, Imran kai dama ai munafuki ne nasani, tun ba yau ba nasan ba ƙaunata kake yi ba. Banda ma rainin hankali in har da gaskene abinda ka faɗa ɗin ai ba ita kaɗai bace aka kashewa iyaye, miyasa su sauran yaran kuka barsu can ita kuka taho da ita nan. Ba sai ku barta acan camp ɗin ba kamar sauran. Ni wannan labarin ƙanzon kuregen bazan taɓa yarda da shi ba, dan dama na jima ina zargin ana cin amanata, idan har ana son na yarda ba ƴarsa bace sai dai muje asibiti ai musu gwaji shi da ita.....” A matuƙar fusace Zak-Shadow ya miƙe, cikin buɗaɗɗiyar muryarsa dake fita da kaushi da ɗaci ya nuna Nabeeha, “Baki isa ba, kinyi kaɗan wlhy. Kije labarin ƙaryar aka baki, kuma ana cin amanar taki kiyi duk abinda zakiyi, dan ke baki isa sakani yin abinda banyi niyya ba wawiya kawai”. A fusacen itama ta miƙe tana kuka, kai da ka ganta kasan kishi ne da zuga suka rufe idannunta, itama cikin ƙaraji ta ce, “To wlhy kuwa sai dai mu rabu, dan nima baka isa na cigaba da zama da kai ba. Jaka ka ɗauke ni ko dabba?, shekara da shekaru ina fama da kai muje muga likita akan matsalar haihuwa amma kaƙi saboda kasan mi kake shiryawa, kaje ka ajiye wata ƴar iska a jeji kana dadiro da ita ku haihu dan yanzu an kasheta ka ɗakko ƴar ka kawo gida mu shaƙi iska ɗaya da ita, mu kwanta muhalli ɗaya da it.....” Tasss! Tasss!!! Kake jin saukar mari har biyu a kan fuskarta irin mai gigitarwar nan, ai ko ƙara ta ƙwalla, dai-dai da miƙewar Momyn ta ta riƙeta tana shiga tsakkaninta da Uncle Nasiru mai marin........✍🏼

Gaskiya ƙawata Nabeeha baki ƙyauta ba, ya zaki mana haka kuma😳😏.

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 56_

__________________

https://chat.whatsapp.com/L3BXH7JYlBRHIkFRiOjeW3?mode=ems_copy_t

UMMU KHALIFA COLLECTION

Ina Mata Yan kwalisa ina mata masu san kayan ado kamar Egyptian abaya sleeping drees kids were shos bags musk dahara original.

To kukanku yazo karshe domin ummu khalifa sun zo muku da duk wadannnan kayan dierct suke order dinsu daga Egypt zuwa gida Nigeria kaidai kawai kashiga link dinsu domin gani ya kori jiii..

Ba nan ummuh khalifa suka tsaya ba suna nemawq mutane visa masu shaawar shugowa kasar ta Egypt karatu ko yawon bude ido ko kasuwanci ku tuntubeta a number dinta +201017018846/07048811474/

KO kuma shafinta na tiktok https://vt.tiktok.com/ZSU1F __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________