Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 56

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 56

...right Zak-Shadow, since he finished the first conversation with her, he went back to the dining room and sat down, he went out to fight so as not to offend Mammah. But he made sure to continue to stay where Nabeeha was so that he could start beating her for the first time in their lives, that's why he chose to go back there and stay there... When Mammah released her and Imran at the same time, he opened his eyes and looked at the hall. Seeing that Uncle Nasirun was about to faint, he quickly took the water that Mammah gave him, he just took off the lid and poured it in his hand, reaching all over and rubbing it on Uncle Nasirun's face. The deep breath brought a strong, and then there were tears.... "Innallillahi wa-inna ilaihiraji'un, son of GOD, how did you calm your mind. This is not something to worry about. Everything is easy, since GOD has brought us the times that are being tested, let's thank the LORD. And let's do it, my daughter will also find peace and tranquility." "Aisha will not go". "No, son of GOD, why don't you say that, the problem in life is that there is nothing that makes you happy and easy, let alone in life like marriage, too.....

Standalone post2,019 words

.......“Miyasa zaka mareta? Naga akan gaskiyata take dai ai? Sai a daki yarinya a hanata kuka. Idan yasan yana da gaskiyar mizai sa yaƙi yarda suje suyi gwajin?”. Cikin kuka Nabeeha ta ce, “Momy ki barshi ya kasheni, Abba ka kasheni, dama mun san ai ba son mu kake ba yanzu, shi da yay laifin ka kasa yimasa magana saboda kana tsoronsa sai ni, sai ni da nake da gaskiyata za'a tauye ni......” Wani marin ya ƙara kawo mata, dan yama kasa magana saboda abinda ya tsaya masa a maƙoshi. Da sauri Momyn tata dai ta sake tarewa. “Wlhy bazaka sake dukanta ba”. Mammah da al'amarin ya girmi kanta ma sai yanzu ta iya ɗaga baki da ƙyar tace ma Uncle Nasiru, “Dan ALLAH Yaya kayi haƙuri ya isa hakan, duka ba shine mafita ba, ku barta ta huta ta huce dan yanzu shaiɗan yayi tasiri a zuciyarta. Sannan kuma tunda gwajin take so ni zan masa magana zaije suyi, ba shike nan sai a zauna lafiya ko”. A gatsine Momynta ta ce, “Da dai yafi kam”. Taja hannunta suka nufi ƙofa. Gagara sake yin magana kowa yayi a falon, dama Zak-Shadow tunda ya gama yaɓa mata zancen farko ya koma can dining ya zauna, yaƙi fita ne dan kar ya ɓatama Mammah rai, Uncle Nasiru kuma yaga kamar ya raina shi, dan kallon uba yake masa. Amma ya tabbatar ya cigaba da zama inda Nabeeha take zai iya fara kai mata duka a karo na farko na rayuwarsu, shiyasa ya zaɓi komawa can ya zauna ɗin... Salatin da Mammah ta saki ita da Imran a lokaci guda ya sashi buɗe idanunsa ya kallo falon, ai baima San ya miƙe ba da sauri ganin Imran ya taro Uncle Nasiru alamar faɗuwa zai yi. Ganin Uncle Nasirun na neman sumewa ya ƙarɓi ruwan da Mammah ta miƙo da sauri, ɓalle murfin yay kawai ya zuba a hannu yana kaiwa duƙe shima ya shafa a fuskar Uncle Nasiru. Nannauyan numfashi ya kawo mai ƙarfi, sai kuma ga hawaye.... “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, dan ALLAH Yaya ka kwantar da hankalinka. Wannan fa ba wani abun tashin hankali bane ba. Komai mai sauƙi ne, tunda ma ALLAH ya kawomu zamanin da ake gwaje-gwajen sai a godema UBANGIJI ko. A kuma je ayi dan itama ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali.” “A'isha bazai je ba”. “A'a dan ALLAH Yaya kada kace haka, ita masalaha a rayuwa babu abinda ya kaita daɗi da sauƙi balle ma a rayuwa irin ta aure, itama yana da ƙyau a bata hakkinta kodan cire zargi, kasan bazan iya bijirema umarninka ba, amma dan ALLAH ko sau ɗaya ne ka bani damar nan na roƙe ka”. Yunƙurawa yay zai tashi, Zak-Shadow da Imran suka taimaka masa. A kujera suka maida shi, yay shiru tsawon lokaci, wata irin nadamar auren Momyn Nabeeha yake ji da zama da ita ba tsawon shekaru, wlhy badan ƴar uwarsa bace jininsa mafi kusa da har nadamar haɗa zuri'a yayi da ita. Matar nan itace babban ƙalubalensa na rayuwa, yasha wahala a hannunta a zamansu na turai, dan gaba ɗaya ta fanɗare masa ta saka yaransu fanɗare masa. Shiyasa ma ya yanke shawarar dawowa gida Nigeria. Ko batun saƙo da yake turama su Mammah ɗin da bai zuwa daga baya abokin nashi yazo ya gaya masa gaskiyar itace ta hana, ta dinga amsa tana rabawa uku ta bashi kaso ɗaya ta ɗauki biyu... Imran ne ya katse masa tunani da faɗin, “Uncle kayi haƙuri nima ina bayan Mammah, ka bari aje ai gwajin kawai kodan samun zaman lafiya da cire zargi, itama yarinyar kaga zata rayu cikin salama”. “Imrana.....” “Dan ALLAH Uncle”. Imran ya sake katsesa. Kallon Zak-Shadow Uncle Nasiru ya ɗanyi, sai tausayinsa ya sake kama shi da kunyarsa mai tsanani, dan tabbas ya cutar da shi da har ya bari aka aura masa Nabeeha bayan yasan bata da isashiyar tarbiyya. Tabbas Haysam magajin Abdul-rasheed ne tako ina, dan ko a halayya da dattako da sanin ya kamata bai bar komai na mahaifinsa ba, kawai dai shi Abdul-rasheed mutum ne mai faranfaran da yawan magana, saɓanin Haysam mai shiru-shiru da ƙarancin fara'a a fuska idan ba shi yaso ba. Amma kowa ya shaida mutum ne mai haƙuri da kawaici.....

••><••><••><••

Da ƙyar Mammah da Imran suka ci ƙarfin Uncle Nasiru ya yarda da batun gwaji, shi dai gogan bai sake tankawa ba. Yayinda can ƙanensa ke cike tab a waje. Dan sanda Momyn Nabeeha ta fita da ita yanda suka zuba musu idanu a fusace sai da sukaji hantar cikunnansu ta motsa, shiyasa da sauri suka wuce su zuwa sashen su Nabeehan. Bayan sallar Magriba da aka kira Mammah tasa Biebah zuwa ta sanar musu su fito za'a asibitin. Koda suka fito a tsakar gida suka iske Mammah ta fito, Uncle Nasiru dama bai shiga ciki ba bayan dawowarsu massalacin. Hakama Imran da Zak-Shadow dake can gefe Imran ɗin na lallashinsa. Cike da gadara Momyn Nabeeha tace kuma sune zasu zaɓi asibitin da za'aje. Nan ma Uncle Nasiru zai yi magana Mammah tai saurin cewa sun amince ayi hakan. Takaici kamar zai kashe Uncle Nasiru da Zak-Shadow, amma dole sukai shiru aka tafi asibiti. Ita da ƴarta motar ta suka shiga. Su ko suka shiga mota ɗaya. Imran ke tuƙi, Uncle Nasiru a gefensa. Mammah da Zak-Shadow suka shiga baya Nimrah da Bilal ya dawo da ita tana barci a cinyarta, dan har yanzu barcin takeyi. Motar ta ce gaba tasu a baya. Cike da kulawa da lallashi Mammah ta kamo hanun Zak-Shadow a cikin nata, dan ta tabbatar zuciyar ƴan mazan na nan na tafasa a ƙirji, saboda umarninta ne kawai zai je gwajin nan. Aiko tabbacin a zuciyen yake ko motsi baiyi ba koda ta riƙe hannun nashi. Idanunsa kuma a rufe har suka iso asibitin daya kasance privete ne, babban asibiti ne kuma da akeji da shi a Abuja. Abinka da maganar kuɗi ko zaman mintina goma basuyi ba likitan da zasu gani ta basu izinin shiga. Nimrah da tun zamansu wajen ta farka tana lafe jikin Mammah Imran ya miƙama hannu. Mammah ta kalla, sai ta mata murmushi da faɗin, “Jeki kinji, ai yanzu zaku dawo ina nan ina jiranki”. Kai ta jinjina Mammah, sannan ta miƙama Imran ɗin hannu ya sakko da ita. Da ƙafafunta ta taka har ƙofar Office ɗin, sai a lokacin kuma uban gayyar ya miƙe saboda maganar da Mammah tai masa. Nabeeha da itama sai yanzu uwarta ta kamata ta miƙar ta harari bayansa tana murguɗa baki, hakama Momynta da harara ta rakashi. Suna zuwa ƙofar ɗakin inda Imran ke tsaye tsagal Nimrah mai bakin magana da barci ya fara sakinta ta ce, “Baba ɗan sanda kanka ke ciwo ne?”. Yanda tai maganar idonta akan Zak-Shadow ya saka Imran yin ƙaramin murmushi, shiko idanu kawai ya zuba mata ya ƙi magana. Yayinda Mammah da Uncle Nasiru ke murmurshin maganar tata, nan kuma Nabeeha da Momynta ji suke kamar su shaƙe shegiyar yarinyar. Nimrah bata haƙura ba ta matso kusa da Zak-Shadow, kamar zatai kuka tana kallon fuskar tasa dai ta kama hannunsa, “Baba ɗan sanda akwai zafi sosai ko? Kada kayi kuka kaj.....” “Ke dan ubanki yima mutane shiru!!!”. Nabeeha ta daka mata tsawa. A mamakinsu ko irin ma ta tsorata nan sai ma ƙuri datai mata da idanu ba shakka ba girgiza. Aiko ji Nabeeha tai ta sake hasala, ta fige hannunta tayi kan Nimrah zata daka, sai lokacin ta sake matsawa jikin Zak-Shadow sosai ta rungume ƙafafunsa tana ɓoye fuskata. “Wayyo Baba ɗan sanda kace Kada ta dakeni, bana son duka bana so....” Jin shiru ba'a daketan ba tai shiru, sai kuma ta ɗan leƙo fuskarta taga miya faru. Nabeeha ta gani tsaye cak tana huci kamar zakanya. Sai dai bata san miya tsaidata ba. Abinda kuwa bata sani ba wani shegen kallo Zak-Shadow kema Nabeeha ɗin daya sakata dakatawar. Imran shi ya katse yanayin da faɗin, “Bismillah ku shiga”. Ƙwafa Nabeeha tayi da watsama Nimrah harara, ƙasa-ƙasa ta ce, “Sai na kasheki shegiyar yarinya ƴar zin....”. Bata ƙarasaba Momynta taja hannunta suka shige. Shima cikin lallashi Imran yay masa magana da ido, bai tanka ba ya kama hannun Nimrah suka shiga, Imran biye da su. Da Imran kawai doctor ya gaisa, koda ya miƙama Zak-Shadow hannu yi yay kamar bai ma gansa ba. Shima doctor ɗin sai ya sake nutsuwa dan ya fahimci waɗan nan mazan bana wasan yara bane ba. A ɗarare ya juya ga Momyn Nabeeha yana tambayarta mike tafe da su. Ganin Momyn Nabeeha zata fara wani ƙalƙale-ƙalƙalen magana da iyayin ƴan bariki Imran ya katseta kai tsaye yay ma likitan bayanin abinda suke buƙata. Doctor yaga ba wajen wasa bane dandanan ya ɗauka waya yay kiran wani. Kafin kace mi an musu dukkan abinda ya dace anan cikin office ɗin nashi batare da sunje lab ba. Dukkan abinda ya kamata anyi musu, duk da dai ansha badaƙala da ihu lokacin yima hajja Nimrah nata gwaje-gwajen. Bayan an kammala komai doctor yace results sai nan da kwana biyu. “Bazai yiwu mu sameshi a gobe ba doctor. Abin na gaggawa ne Please”. Momyn Nabeeha ce mai maganar, doctor yay ɗan jimm, sai kuma ya jinjina kai. “Okay ba damuwa hajjaju ai kece. Zuwa yamma zan kira ki”. “Ai ni da zai yiwu ma zuwa 12 nake so, dan goben zuwa 1 inada meeting da first lady, kuma sai dare zamu fito”. Bakin doctor a washe ya ce, “Shike nan yanda kike so haka za'ayi, zan yi ƙoƙarin hakan”. “Na gode”. Ta faɗa tana kama hannun Nabeeha suka fito, dama Zak-Shadow tuni ya fice da Nimrah. Sai Imran ne kawai aka bari, gama nazartar alaƙar dake tsakanin doctor da Momyn Nabeeha ya sashi tsayawar kuma. Sai da suka fice sannan doctor ya kallesa. “Ranka ya daɗe akwai sauran wani abu ne?”. “Mai muhimmanci ma kuwa. Naga akwai alaƙa tsakaninka da su, to ka sani idan ɗigo ya canja a cikin result ɗin da muke buƙatar gani kayi kuka da kanka. Suna Major Imran Abbas.” Daga haka Imran yay ficewarsa a office ɗin shima yabar likita da baki buɗe na firgici da mamaki. Dan a kwanakin nan babu sunayen dake amsa kuwwa a kafafen yaɗa labarai dana sada zumunta kamar Major Imran Abbas da Zak-Shadow da sauran Captains ɗin da akasha wancan gumurzun..........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 57_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp

07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃 __________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________