Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 57

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 57

.....n the value of Mammah only made him allow it. Imran's presence was filled with sadness and hatred. Tsigit Nimrah said, "Dad, the policeman is attacking you" before someone said something, she continued to say, "And I will take revenge on you, but an eye is not better than an eye". Nabeeha's feet are very tight, including holding her waist, and the window is tight, which Nabeehan has been doing to her for a long time. Mi Imran and Uncle Nasiru would not laugh, Mammah herself had to smile a little. The father himself turned his eyes to her. Before he reached his hand and brought her close to him, she looked at him in a bit of fear, her son was going to tell Nabeehan how to help her, so she tried to erase her guilt like she does to Umma at home if she does something wrong. Suddenly, he felt her hand on his forehead. "Dad, policeman, are you still sick?". When the coldness of her hand and her warm voice passed through his ears, he only focused his eyes on her again, and failed to fight her that he intended. She was looking at him with a smile in her eyes as if she wasn't herself. He heard that he could not clean her, not to mention that he is a man who loves children very much, he

Standalone post2,089 words

...........A inda suka bar su Mammah nan Zak-Shadow daya fara fitowa riƙe da hannun Nimrah suka samesu ita da Uncle Nasiru. Kallonsa kawai Mammah keyi cike da tausayi, dan tasan ransa a matuƙar ɓace yake, yana dannewa ne saboda umarninta. A kujerar kusa da ita ya zauna. Dan wani ɗan jiri-jiri yake ji, haka yake idan ransa yakai ƙololiwar ɓaci, dan mutum ne shi mai haƙuri amma yana da fushi sosai musamman akan gaskiyarsa. Yana kaiwa zaune Nimrah ta sake matsawa kusa da shi ta manne a jikinsa saboda hararar da Nabeeha da Momynta da suka fito ke mata. Hakan kuwa sai ya ƙara ƙona ran Nabeeha, dan babban baƙin cikinta itafa ka raɓar mata miji ne, cikin ƙunƙuni ta ce, “Banda ma ana son raina hankalina Momy, jiba yanda mayar yarinyar nan ke nane masa tabbacin ta masa sani na haƙiƙ....” “Malama ya isheki haka”. Karon farko Imran da fitowarsa kenan daga office ɗin shima ya faɗa a fusace, dan shi kam ya tsani nacin magana. Haukan Nabeehan ya fara isarsa shima. Ya tabbatar shi kansa Zak-Shadow ɗin darajar Mammah kawai yasa shi ƙyaleta. Hararar Imran tayi cike da jin baƙin ciki da tsanarsa. Tsigit Nimrah ta ce, “Baba ɗan sanda tana harararka” kafin wani yace wani abu ta cigaba da faɗin, “Kuma sai na rama maka, ai ido bai fi ido ba”. Tako ballarama Nabeeha harara harda riƙe ƙugu, dan tagaji da hararar da Nabeehan ke mata tun ɗazun itama. Mi Imran da Uncle Nasiru zasuyi ba dariya ba, Mammah kanta sai da ta murmusa kaɗan. Shi kansa uban gayyar idanu ya zuba mata. Kafin ya kai hannu ya matso da ita kusa da shi, kallonsa tayi a ɗan tsorace, dan ta zata faɗan hararar da taima Nabeehan zai mata, dan haka tai ƙoƙarin son goge laifinta kamar yanda take ma Umma a gida idan tasan tayi ba daidai ba. A bazata kawai yaji saukar ɗan hannunta akan goshinsa. “Baba ɗan sanda har yanzu kanka na ciwo ne?”. Yanda sanyin hannun nata da zazzaƙar muryarta suka ratsa kunnensa sai ya sake zuba mata idanunsa kawai, yama kasa mata faɗan da yay niyya ɗin. Itama kallonsa take ƙiri cikin ido kamar ba ita ba. Ji yay bazai iya shareta ba, balle ma shi mutum ne mai son yara sosai, hannun nata kawai ya kamo ya riƙe cikin nashi, tun fitowarsu gida a karo na farko yayi magana yana gyara mata ɗan baby hijjab ɗin jikinta. “Karna ƙara jin bakin nan yayi magana, babu ƙyau rashin kunya.” ya faɗa cikin gargaɗi yana ƙoƙarin miƙewa. Da sauri ta saka hannu ta rufe bakinta, ɗayan hannun nata kuwa na riƙe a cikin nashi. Suma su Mammah miƙewa sukai ita da Uncle Nasiru suna murmushi, dan sun fahimci Nimrah zata fara sakin jikinta da su kenan, da alama kuma yarinyar akwai surutu da tsiwa.....

<<>><<>><<>><<>>

“Wannan shine gidan Sir!”. Matashin ya faɗa cikin karyayyen harshensa fuska cike da murmushi. Shima Dabo murmurshin yayi masa, tare da zaro kuɗi da zasu iya kaiwa dubu biyu ya bashi. “Nagode sosai, amma ko zaka bani number ɗinka, dan in na kammala abinda nake na kiraka ka fita dani koda nayi dare”. Ɗan jimm matashin yayi yana gyara zamansa akan mashin ɗinsa, dan haka Dabo yay murmushi a karo na biyu. “Karka ji tsoron komai, ni bamai cutarwa bane ba”. “Kayi haƙuri sir, kasan yankin namu ne sai a hankali, ana mana ƙwacen mashina musamman da dare a hanyar tamu shiyasa kaga nayi shiru, amma badan ina tunanin zaka cutar dani ba”. “Ayya na fahimta. Shike nan ba damuwa nagode sosai kaje kawai”. “A'a bara na baka number ɗin, sai dai idan dare yayi sosai sai dai na baka haƙuri dan ina jin tsoro bazan iya fita da kai ba”. “Na gode”. Bayan Dabo ya amshi lambar mai okada ya ɗan tsaya a ƙofar gidan yana waige-waigen da ƙarema wajen kallo. Garin ƙauye ne sosai, dan gidaje ma ɗai-ɗai suke. Gidajen duk babu wata katanga irin dai gini ne na yankin. Sai da ya ɗan furzar da iska kafin ya taka steps ɗin barandar ya haye kanta, dai-dai ƙofar dake rufe ya tsaya tare da fara knocking. Yayi fin sau uku sannan akazo aka buɗe. Cikin masa kallon rashin sani tsohuwar data buɗe ƙofar ta ce, “Waye kai? Wa kake nema?”. Tsaiwa Dabo ya gyara, cikin girmamawa ya sanar mata shi baƙo ne, kuma ma'aikacin soja, yazo wajensu ne akan wani Ojo”. Dan danan yaga fuskarta ta canja, jikinta har rawa ya ke ta kamo hannunsa tana faɗin, “Ojo! Kai soja ne?, kasan inda yarona Ojo yake? Da gaske kaga Ojo na? Shigo-shigo maza shigo ciki”. Ciki ta turashi, ta maida ƙofar ta rufe. Falo ne madaidaici da wasu ruɓaɓɓun kujeru a ciki, sai ƙaramar tv akan katakon tv stand. Sai da ta jawo wani ƙyalle ta saka masa a kujerar sannan ta sake jan hannunsa alamar ya zauna. Baiyi musu ba ya zauna, jikinta har rawa yake ta nufi wata ƙofar tana cigaba da maimaita masa kalmar sannu da zuwa data kasa daina faɗa. Karo na farko yabi falon da kallo, har idanunsa suka sauka akan hotunan dake saman tv ɗin falon manne a bango. Guda kusan huɗu ne, ɗaya mata da miji ne suna da ƙuruciya, kamaninta yasa ya gane itace duk da ta tsufa a yanzu. Sai na biyu mutumin kusa da ita ɗinne dai shi kaɗai da kayan sojoji, sai uku yara biyu matasa masu kammani da juna matuƙa, wanda kai tsaye yaga kamanin Ojo a tare da yaran duk da sanda akai hoton suna ƙananu sosai. Sai na ƙarshe zai iya cewa Ojo ɗin ne da kayan soja.... Dawowar tsohuwar ya katse masa tunani da nazartar hotunan. Ruwa ta ajiye masa da faɗin, “Fara shan wannan bari naje na kawo maka lemo nan kusa”. Hannunta ya kamo da murmushi dan harta yunƙura zata bar wajen. “A'a Mama ruwan ma ya isheni, yi haƙuri ki zauna magana zamuyi ne”. Cikin damuwa ta ce, “Ko kaima kana tsoron cin abun hannuna ne? Kaima ance maka ni mayya ce ko....” Hawaye suka shiga sakko mata. Da sauri ya shiga bata haƙuri da lallashinta, da ƙyar ta tsagaita kukan bayan ya tabbatar mata shi babu wanda ya sanar masa komai a kanta. “Ka tabbatar?”. “Yes Mama”. “To kasha ruwan”. Danta samu kwanciyar hankali ya ɗauki ruwan yasha sosai tare da mata godiya. Sannan ya fara magana cike da nutsuwa da kulawa. “Mama kamar yanda na faɗa miki ni soja ne, nazo garin nan ne kuma takanas saboda ke. Sai dai kafin na faɗa miki dalilin zuwana ina son nasan wanene Ojo a wajenki?”. Cikin jinjina kai da sauke tagwayen ajiyar zuciya ta ce, “Ojo ɗana ne, shi ɗin twins ne shi da ɗan uwansa, suna kamanni da juna sosai ta yanda koni wani lokacin suna ruɗani bana gane su. Su biyu kawai muka haifa, babansu soja ne, an kashe shi shekaru masu yawa, lokacin su Ojo nada shekara goma-goma. Bayan mutuwarsa nasha wahala akan rainon su Ojo, dan babu mai taimaka min, haka na dinga noman Togo da doya ni kaɗai ina biya musu kuɗin makaranta. Bayan sun gama Secondary Ojo yace yana son zama soja kamar mahaifinsu. Na tsorata sosai da hakan saboda a aikin aka kashe babansu, duk yanda na lallaɓa Ojo yaƙi saurarena yace shi dai yana so, dole na barshi. Shiko ɗan uwansa Jeo baice yana son komai ba, dama na masa maganar komawa karatu sai yace ba yanzu ba. Ban matsa masa ba na barshi. Bayan tafiyar Ojo saina fahimci Jeo ya fara rashin ji da yawo da abokan banza suna bin yaran ƙauyen nan. Na zaunar da shi nai masa faɗa amma bai saurareni ba, sai ma ya koma ba kullum yake kwana a gida ba sai randa yaso, canjawar halayensa na damuna sai dai babu mai taimakona ya masa faɗa sai na haƙura. A haka Ojo ya dawo gida cike da farin cikin zama soja bayan wani lokaci, nima duk da bana so na tayashi farin ciki, yayi kwanakinsa ya sake komawa, a lokacin shima Jeo ya shirya yabar ƙauyen nan wai zai yi karatu. Tun daga nan ban sake ganinsu ba su duka sai bayan shekara biyu Ojo yazo min da wata yarinya wai da zai aura. A lokacin ne ya gyara min gidan nan ya zuba min wannan kujerun da komai masu ƙyau ya ajiye min kayan abinci da kuɗi. Kwanansa goma sai ga Jeo shima yazo, gaba ɗaya Jeo ya canja min a yanda na sanshi, ya zama wani iri da shi, babu tarbiyyar dana basu ko ɗaya a tare da shi. Ni da Ojo mukai masa faɗa sosai, yay mana alƙawarin duk zai daina abinda yake yi Ojo ya ɗauki kuɗi ya bashi shima. Daga nan ya ɗauki budurwarsa suka tafi yace min sai nan da wata uku zai sake zuwa dan yanzu an masa canjin wajen aiki ne ma, na musu addu'a suka tafi suka bar Jeo anan, sai da ya ƙara kwana biyu ya lallaɓa ni ya amshi abinda Ojo ya bani sannan shima ya koma......” ta fashe da kuka sosai, da ƙyar Dabo ya lallasheta ta cigaba da faɗin, “Tun daga lokacin ban sake ganinsu ba su duka biyun. Nayi kuka nayi nema harna gaji, nayi addu'a an tayani amma babu wanda ya dawo. Tun mutane na tausayina har suka daina suka fara kirana mayya, wai na sayar da jinin ƴaƴana ne dan ni nayi rayuwa mai yawa”. Ba ƙaramin tausayin tsohuwar nan bane ya sake mamaye Dabo ba. Haka ya dinga lallashinta harta tsagaita kafin ya cigaba da mata tambayoyi. “Amma Mama kafin Ojo ya tafi bai gaya miki inda aka mai dashi aiki ba?”. “Bai gaya min ba, kawai yace min arewa ne”. “Shima Jeo babu wanda ya sake sanar miki ya ganshi?”. “Wani abokinsa ya taɓa gaya min wai sunje har inda Ojo ke aiki shi da Joe, amma basu ganshi ba akace yana kan aiki, daga nan suka dawo, shi sai ya samu hanyar barin ƙasa zuwa turai, akan shima Jeo zai biyoshi daga baya, sai dai Joe bai bishi ba daya tambayi wanda yayi musu hanyar sai yace shi tun ranar bai sake ganin Joe ba ma”. “Yanzu ina abokin nashi?”. “Ya koma turai, dama yazo tafiya da Mamansa ne. Ga gidansu anan bayana kaɗan harma ya rushe saboda babu kowa”. “Mama kince kamanin Joe da Ojo mai tsanani ne har mutane basa banbance su, kema wani lokacin suna ruɗar dake. Amma da wane irin banbanci kike banbance su a sauran lokaci?”. Ɗan shiru tayi na wani lokaci, kafin ta nisa tana jinjina kai.........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 58_

__________________

Ina mata ma'abota ado da kwalliya maryam's all-in-one emporium ta tanadar muku Mayafai masu kyau da aminci kama daga plain chiffon veils masu kyau kamar daga Egypt suka sauko🥰 jersey scarfs , beaded and stoning veils, Chantilly, 2D to 10D Turkish veils Dubai d.s Kuma abun farinciki muna bada sari da siyan dai dai ina Kano Ina tura kaya ko'ina cikin Aminci da yardar Allah ga number ta 09064960666

https://chat.whatsapp.com/FfaJ30ZOz8NHazD2ZwtzAd?mode=wwt

A cikin duniya ta gayu da burgewa mayafi shine ya ke daukaka ado da aji

Maryam's all-in-one emporium 09064960666 Kano Anan ne gayu yake tarar da qawa.

Ki more hadaddun Mayafan mu da suka hada da Plain chiffon veils (soft & flowy) Italian Chantilly veils (pure elegance Jersey Veils (comfort meets class) Lafaya and many more.

Each piece tells a story of grace, crafted for women who understand beautyin simplicity.🤍

🖤 Premium quality 💛 Affordable luxury 🖤 Available in elegant shades 💛 Delivery 🚚 duk inda kike a fadin duniya

Ba mayafi kawaii kike bukata ba you deserve a statement of class.👑

Wholesale group https://chat.whatsapp.com/FfaJ30ZOz8NHazD2ZwtzAd?mode=wwt

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________