
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 59
..... we don't know. Because Zak-Shadow is among them, if we move strongly he can look at us from a distance even though I know it is true." It was the other one who spoke now with a smile on his face. He said, "That's right, sir, we will do everything the right way." "This is exactly, "Prepare for me a list of those who have worked in this department for the past three years. I want to know where they are, even if some of them have resigned." "Yes, sir." <<><>>★<<><>> The night is far away, the silence is getting deeper wherever I am in the city of Abuja. On both sides of the house, tonight is a different situation. But everyone has a purpose to worry about. On Mammah's side, she focused her attention on worship, while Nimrah was sleeping alone in her bed since they came back from the hospital, she was clinging to her. There, Bilal, Yaya Ma'aruff, Yaya Ja'afar and Ammar locked themselves in a room and discussed what was going to happen in their house. Since Mammah drove them home, Aunty Ummi didn't want to go, so the discussion went back to the men and the women called them to see if there was any movement. But the fact that Mammah has her eyebrows up and down prevents anyone from
..........Cikin damuwa General ya koma office, tunda ya baro gidan gwamnati babu abinda yake maimaitawa sai sunan Zak-Shadow a fili. Zama yay a kujerar office ɗinsa tare da ɗan ja numfashi mai nauyi. Dai-dai nan mutane biyu daya buƙaci gani suka shigo office ɗin. Koda suka ƙame da sara masa alamar su zauna kawai yay musu. Cikin damuwa ya sake furzar da iska mai kauri yana kallon su. “Aikin nan ba ƙarami ba ne fa. Kuma idan rahoton da na gani gaskiya ne… to akwai wanda ya karya alkawari cikin runduna.” Cikin matsanancin tashin hankali ɗaya daga cikin hafsoshin nashi Colonel Haydar dake gefen damansa ya ce, “Sir! duk mai hankali zai fahimci hakan musamman yanda komai ya taso da zafi. Kenan za mu sake tuntuɓar sashen Recon Unit da aka rufe a baya? Akwai tsoffin bayanai da zasu taimaka nake ga.” Cikin ƙwafa General ya ce, “Ai mu ake hara kai tsaye ba Zak-Shadow kawai ba Colonel. Shiyyasa wannan binciken zai gudana a cikin inuwa ne kawai. Dan haka ko ɗaya daga cikin Recon Unit bai kamata ya san munayi ba. Saboda Zak-Shadow yana cikin su, idan muka motsa da ƙarfi zai iya kallonmu daga nesa duk da nasan ita gaskiya gaskiya ce.” Ɗayan ne yay magana a yanzu cikin jinjina kai da gamsuwa. Ya ce, “Haka ne sir, zamuyi komai a yanda ya dace.” “Wannan shine dai-dai, “Ku shirya min jerin waɗanda suka yi aiki da sashen nan a shekaru uku da suka wuce. Ina so in san inda suke, koda kuwa wasu a cikinsu sun yi murabus.” “Yes, Sir.”
<<><>>★<<><>>
Dare yayi nisa, shiru ya ƙara ratsa ko ina a garin na Abuja. A duka ɓangarori biyu na gidan daren yau yazo musu da wani yanayi ne. Sai dai kowa da manufar tasa damuwa. A ɓangaren Mammah ta maida hankalinta ne ga ibada, yayinda Nimrah ke barci ɗai-ɗai a gadon ɗakinta dan tunda suka dawo daga asibiti tana nane da ita. A can kuwa Bilal, Yaya Ma'aruff, Yaya Ja'afar da Ammar ne suka ƙule a ɗaki suna sake tattauna abinda ke shirin faruwa a gidan nasu. Tun ɗazun Mammah ta kora su Aunty Ummi gida badan sun so tafiya ba, dan haka tattaunawar ta koma a tsakaninsu su iya mazan sai kuma waya da su matan ke kiransu dan suji ko akwai wani motsi. Amma kasancewar Mammah ta haɗe girar sama data ƙasa na hana kowa damar cewa wani abu yasa su zamewa suka koma ɗakin barcinsu suna tattauna iya abinda suka ji da tunanin mi ya faru da su Mammah ɗin suka je asibiti? Sun so zungurar Nimrah ta faɗa musu tunda sunga tanada surutu amma Mammah ta kafa ta tsare ta hana yarinyar zuwa wajensu kamar tasan mi suke shiryawa.
★Anan ɓangaren ma Momyn Nabeeha da Nabeeha ɗinne a ɗakinta sun kulle kansu suna sake tattaunawa. Dan suma tunda suka dawo gidan Momyn keta sake tunzura Nabeeha, hakan ne yasa Jiddah yin fushi tabar musu gidan ko jiran zuwan mijin nata ma batai ba. Dan ta riga ta fahimci al'amarin Momynsu a wannan karon yayi babban tasiri a zuciyar ƴar uwarta Nabeeha. Tana tafiya Momyn ta koma zaginta, sai hakan ya ƙara tunzura zuciyar Nabeeha ta ƙullaci ƴar uwar tata da sake tabbatar da ba sonta da ƙaunarta take ba daman, tunda bata kishinta bata tayata baƙin cikin abinda ke faruwa da ita. Hasalima goyon bayan mijin nata take saboda neman duwawun zama. Sai hakan ya sake jagorantarta shagaltuwa da huɗubar Momy da dake jin zafin Zak-Shadow matuƙa..
★Zak-Shadow kam tun bayan wucewar Imran daya koma sashen ɗakinsa kawai ya shige ya rufe kansa. Shi sam ba wani shirmen Nabeeha ko abinda ke faruwa a gidan ke damunsa ba. Hasalima bai ɗauki wannan serious ba dan yama gama tsara abinda zaiyi. Damuwarsa tana ga aiki ne musamman akan al'amarin Ojo da binciken da yake yi na musamman akan ainihin son sanin shuganin ƙungiyar duhu. A yanzu ma yana tsaye a bakin tagar ɗakinsa ne, yana sanye da kayan barci farare masu sauƙin nauyi, hannunsa riƙe da kofin shayi da bai gama sha ba. Sararin samaniya datai haske fayau na gangarawar ƙarewar wata ya zubama idanu kawai. A hankali tunaninsa yabar kan Ojo ya koma ga sojojin da suka barin a sansani a halin yanzu, yana jin kewar aiki, amma a lokaci guda yana jin daɗin hutunsa da ya tabbatar zai bashi damar binciken daya kafama alƙalami.. Vibration ɗin wayarsa ne ya katse tunaninsa, ya ɗan waiwaya yana kallonta a study table, kafin ya furzar da iska kaɗan tare da takawa zuwa study table ɗin. Ɗan zubama number ɗin ido yayi na sakani harta tsinke, ba suna, amma ya tabbatar duk wanda zai kira wannan layin nasa amintacce ne a garesa. Kiran ne ya sake shigowa a karo na biyu, bai jima ba yanzu kam ya ɗaga. Sallama akai daga can, ya amsa a taƙaice tare da faɗin, “Who’s this?”. Murmurshi akai mai sauti daga can, sai kuma a taƙaice aka furta, “Col. Faro”. Karo na farko Zak-Shadow ya ɗan murmusa, sai kuma ya ajiye kofin hannunsa yana kaiwa zaune a kujerar study table ɗin tare da ɗan taɓe baki cikin mamaki. “Humm kai dai bazaka taɓa canjawa ba, shi kuma wannan layin fa?”. Ƙaramar dariya Faro yayi daga can, sai kuma ya furzar da iska kaɗan shima tare da komawa serious, yace, “Zak-Shadow Ba zan iya yin wannan kiran da wata waya ta hukuma ba”. “Humm hankaka...”. Sai da yay ƴar dariyar batun Zak-Shadow ɗin da ƙarasa masa da “.....baka jewar banza ba” sai kuma cikin damuwa ya ce, “Zak... Ina cikin aiki yanzu, kuma lokaci bai ƙi min yakana ba. Amma akwai wani abu da ya kamata ka sani kafin lokaci ya ƙure.” Ɗan shiru Zak-Shadow yayi na fin sakan biyu, kafin ya sake daidaita muryarsa ya ce, “Ina saurarenka”. Ajiyar zuciya mai ƙarfi Faro ya saki, “Ka kula sosai Zak. Na ji ana motsi a sama. Sun buɗe fayil ɗin Shadow Recon Unit. Kuma sun haɗa sunanka da wani rahoto mai nauyi. Ban san gaskiyar sa ba, amma na ji suna cewa za a turo da Special Board daga Defence HQ domin bincike.” Shiru ya biyo bayan maganar, sai ɗan cizar lips da Zak-Shadow keyi kaɗan-kaɗan da ƙaramin saukar numfashin Faro. Zak-Shadow ya saki murmurshi mai bala'in ƙayatarwa a hankali yana miƙewa hannunsa ɗaya a cikin aljihu, inda ya baro jikin window ɗin nan ya koma ya sake tsayawa kamar ɗazun. Kai tsaye ya furta, “Da alama ababen farauta sun fara tsallako gaɓar ruwa domin neman ceto, sai dai idan basuyi taka tsantsan ba za suyi gudun GABA KURA NE BAYA SAYAƘI. Wane ne ke da alhakin motsin?”. “Ban sani ba, amma akwai liken tattabara a cikin runduna, Zak-Shadow naji a jikina wani na ciki ne ke aika bayanai. Ka kula sosai. Idan wani abu ya faru, kar ka bari su kama ka kai tsaye. Ka jira umarni na hukuma, amma ka sa idonka a kan mutanenka, musamman waɗanda ka fi yarda da su.” Kai tsaye ya kamo bakin zaren, dan haka ya sake sakin murmushi mai sauti, “Faro…” Zak ya kira sunansa cikin murya mai nauyi, tare da dakewa ya cigaba da faɗin, “Karka kuskura ka tona asiri da yawa. Ka tsaya a gefe, ka bar sauran wasan a kaina”. “Na riga na shiga Haysam, Imran kawai nake ji, dan yana da rauni akan ka. Kuma bana so a bar maka wannan wasan kai kaɗai, ko yin amfani da shi akan ka, dan girman filin da za'ayi shi ya wuce duk yanda kake tunani…” Daga haka Faro ya katse kiran daga can. Ji kawai Zak-Shadow yayi Beep… beep… line disconnected. Tsayawa yay kawai yana kallon wayar kamar yana son ta amsa masa sauran abin faɗar dake yawo a zuciyarsa da kanta. Sai dai yasan hakan bamai yiwu bane, yasan kuma iya batun da zai iya samu daga Faro kenan, wannan ma da yaji amintaka ce da yarda, amma duk tsanani soja baya auna wajen harbi da harsashi a gaɓar share fagen wasa. Wayar ya ajiye a hankali, yana tura labulen window ɗin da ƙyau saboda buƙatar shaƙar iska mai yawa, idanunsa ya tsayar kan sararin samaniya dake rikiɗewa zuwa duhun tsakkiyar dare. A ƙasan maƙoshi fuskarsa da murmushi mai wahalar fassara ya furta, “Da alama yanzu ne za'a dawo da wasan gaskiya. Wasan da zai rarrabe shiru da amsa kuwwar masu son a shelantawa”.
((★))<>((★))
WASHE GARI....
A yau rana ce a gurin kowa kamar sauran ranaku da suka shuɗe. Sai dai ga Zak-Shadow rana ce da tazo da abubuwa kashi-kashi. Masu ban tsoro da ban mamaki har ma da ruɗani musamman ga ahalinsa dama duk wani masoyinsa. Rashin samun isasshen barci da daddare baisa ya kwanta da safe domin yin ramuwarsa ba. Dan ana idar da sallar asubahi ya fito a masallacin kenan su Ammar zagaye da shi kiran Imran ya shigo wayarsa. Dama ya fito da wayar ne shima dan nemansa, sai kuma akai sa'a shi ya fara kiransa. Barin inda ƙanen nasa suke yay ya koma gefe, duk suka bishi da kallo rayukansu babu daɗi, dan sun kwana da damuwa. Yanzu ma sun yanke shawarar tunkararshi da batun da aketa ɓoye musun duk da sunji komai, sai dai shakkarsa ta sakasu inda-inda har Imran ya kirashi. A tare suka saki ajiyar zuciya, sai kuma suka kalla juna....
“Na kama yaron nan a daren jiya da kaina dan na kasa haƙuri”. “Oh shittt! Imran miyasa kai hakan?”. Zak-Shadow ya faɗa cikin runtse ido. Cikin rashin damuwa Imran ya ce, “Zak.. wannan abun dole muyisa da gaggawa, dan jiya Dabo ya sake kirana sakamakon abubuwan daya sake samu a gidan su Ojo. Shiyasa na fahimci jira har sai gobe yabar barrak mu kamashi zai iya zama matsala. Shiyasa kawai na tarfashi a wani hotel da ya je”. “Hakan da kayi shine dai-dai, amma matsala zata iya biyo bayan hakan nayi da kanka da kayi”. “Miyasa?”. “Ba maganar waya bace. Yanzu dai ina ka ajiye shi?”. “Yana cikin gidana, dan hakan ne kawai zai k.......” “Imran!!!!! A are you madd!!!!”. A yanda yay maganar ba Imran ba hatta su Ma'aruff sai da suka firgita. Kafin Imran ya iya cewa wani abu Zak-Shadow ya cigaba da magana cikin kaushin murya da zafafawa. “Maza ka kimtsa shi gani nan zuwa zan fiddashi. Wane irin mugun tunani da ganganci ne wannan zaka kaishi cikin gidanka? Wlhy idan ka bari wani abu ya biyo hakan da zai taɓaka sai na HUKUNTAKA Imran. Sai na HUKUNTAKA tabbas sai na HUKUNTAKA....” Kai da kaji yanda yake magana kasan tabbas Imran yana cikin babban lagonsa da yake matuƙar tsoro da gudun abinda zai iya taɓa rayuwarsu.........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_Chapter 60_
__________________
https://chat.whatsapp.com/J92XqvWDRch1EJPdGDBa41?mode=wwt
https://vm.tiktok.com/ZSHWHk4ULWbMN-geqJz/ This post is shared via TikTok Lite. Download TikTok Lite to enjoy more posts: https://www.tiktok.com/tiktoklite
https://chat.whatsapp.com/KfkKd9vD8MrAst8i8CQDsj?mode=wwt Assalamu alaikum, Mutanen arziki Ina musu capacity😍🥰 kuna Neman Inda zaku Samu ingantattun Kaya masu kyau da quality sosai 💝 Kamar Kayan Yara Zannuwan Gado Kayan kitchen Shoes and bags Jewellery Laces, atamfa,shadda Dadai sauransu. To nesa tazo kusa, Maza Danna wannan link din domin Samun Kaya masu inganci da ƙayatarwa da idan kika saka ko ina kika shiga sai an kalleki an ƙara kallo.
Ko ku nememu ta wannan number 08165751018 ❤️❤️❤️😘 __________________
*_TELEGRAM GROUP_*
https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk
*_WHATSAPP CHANNEL_*
https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F
*_TIKTOK_*
https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/
*_INSTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
______________________