
Post
KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 60
.... This kind of excitement? Don't forget that your brother is a soldier." Zak-Shadow shouted at him again, a little angry and said, "You are putting yourself and your family in danger and taking things for granted. Imran said, "Why don't you listen to me?" I did not mean to bring him to this house, but to the new house there is no one." GOD, King Zak-Shadow, a kind of heavy heartedness dropped as he lowered his eyes and threw his head against the car. Imran smiled again, and he only felt small balls gather in his eyes. He knew that Zak-Shadow's love for him was great, that is why he also did not know how much he had in his life. They spent some time like that before they went back to where Imran grew up and lived. Soon his wife She greeted him respectfully. He also asked her about the health of the children. Soon the two women came to greet him. They both looked at him and came to him with joy.
........Imran kuwa murmushi kawai yayi daga can, sai ma ya yanke wayar yana ɗan taɓe baki. Zak-Shadow nashi kenan, shi ya yarda ya shiga kowane irin haɗari dominsa, amma idan shine ya gwada yin wani abu koyaya yanzu Zak-Shadow ɗin zai tada hankalinsa. To an taɓa rayuwa haka, shi ya sadaukar da rayuwarsa a kansa shi kuma ya gagara yin hakan saboda son tashi rayuwar, bazai yiwu ba, sai dai akan koma minene ya yarda suyi mutuwar kasko. Amma bazai yarda shima Zak-Shadow ya shiga haɗari ba duk rintsi in dai yana da damar taimakonsa... Cikakken mintuna goma ba'ai ba kuwa Zak-Shadow ya ƙarasa gidan Imran, damma sai da ya koma gida ya ɗauki mota sannan. Wata muguwar harara ya zubama Imran ɗin dake compound zaune yana jiran isowarsa, dan yasan tunda yace zai zo to zai zo ɗin. Imran yayi dariya yana tasowa, koda ya iso jikin motar da har Zak-Shadow ya fito ya bashi hannu ƙin amsa yayi. Imran ya sake murmusawa yana kamo hannun nasa sukai musabaha. Cike da tsokana ya ce, “Haba Yayan Imran ayi haƙuri. Irin wannan tada hankali haka? Kada ka manta dai ƙanin naka soja ne fa”. Harararsa Zak-Shadow ya sake yi, a ɗan fusace ya ce, “Kana saka kanka a haɗari da iyalanka kana ɗaukar abu wasa. Imran wai miyasa baka jin magana ne?...” “To bana ce ayi haƙuri ba dai, sannan baka bari na kai ƙarshen maganata bane ba fa. Ba wannan gidan nake nufin na kawo shi ba, sabon gidan can fa da babu kowa”. ALLAH sarki Zak-Shadow, wata irin ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke yana runtse idanunsa da kifa kansa jikin motar. Imran ya sake yin murmushi, sai kawai yaji ƙananun ƙwalla sun taru masa a cikin ido. Shi ya sani ƙaunar da Zak-Shadow ke masa mai girma ce, shiyasa shima bai san yawan adadin da yake masa ba a rayuwa. Sunja lokaci a haka kafin su koma inda Imran ɗin ya taso suka zauna. Ba jimawa matarsa ta kawo musu coffee. Cikin girmamawa ta gaida Zak-Shadow dan Yaya ma take kiransa. Shima ya amsa mata da kulawa yana tambayar lafiyar yara, tace suna lafiya gasu nan ma zasu zo gaisheshi. Aiko babu jimawa suka fito, su huɗu abin sha'awa mata biyu maza biyu. Dukansu kama suke da Imran ɗin. Fuskarsa da murmurshi ya buɗe musu hannayensa, suma cike da farin ciki suka zo suka shige jikin nasa. Yanda yake suna musu soyayya irin ta mahaifi haka suke masa soyayya irin ta uba da ƴaƴa. Ya tambayesu makaranta kowa yace lafiya lau, kowa kuma na ƙoƙarin bashi labarin makarantar tasa. Shi ko yana zuba murmurshi da saurarensu. Yarinya ta uku, wadda daga ita sai auta da zasu iya zama sa'anni da Nimrah ta ce, “Dada zan bika wajen Mammah”. Kanta ya shafa da faɗin, “Makarantar fa Ruƙayyan Dada?”. “Ni na gaji da zuwa dama”. Murmurshi yayi har haƙoransa na bayyana, ya ce, “Babbar magana, dama ana gajiya da neman ilimi Baby na. Kinga yanzu dai kije school, na miki alƙawarin weekend zan zo da kaina na ɗaukeki dama na kawo miki ƙawa”. Wani tsalle Ruƙayya ta saka cike da farin ciki tana ma sauran ƴan uwanta gwalo. Suma sai suka fara ƙorafi, sai da Imran ya ga zasu damesu yace su wuce su ƙarasa shiri lokaci zai ƙure ga driver na jiransu. Badan sun so ba suka wuce ciki. Shi kuma suka cigaba da tattauna abinda ya dace. Sun tsayar da shawarar bazasu kula Ojo ba sai nan da kwana uku, zuwa lokacin ya jigata yayi laushi. Dole anan Zak-Shadow yay breakfast, dan basu baro gidan ba sai 11:30, suna zuwa ya wuce sashensa yin wanka. Shi kuma Imran ya shiga wajen Mammah, in da ya samu Uncle Nasiru da Uncle Jamilu da yazo daga Bauchi, kasancewar kuɗin jirgi Zak-Shadow ya tura masa shine ya iso da wuri. Itama Mammah ganinsa kawai tayi, har ma abin ya bata mamaki, bata samu damar tambayarsa komai ba bayan gaisuwa sai ga Uncle Nasiru yazo. Suna zaune suna hira harda su Yaya Ma'aruff da ganin Uncle Jamilu ya hanasu fita kasuwa, dan sammakon nasa da zuwan bazata ya tabbatar musu akwai dalili. Suna nan zaunen Dada ya shigo, basu ba hatta Mammah sai da ta zuba masa ido. Shi ko kamar baiga kallon da suke masan ba ya sake fiskewa abinsa. Ja'afar daya kasa haƙuri cikin ɗan sosa ƙeya ya ce, “Humm wlhy Dada manyan kaya na maka ƙyau, ka ganka kuwa kamar sabon ango...” ya ƙarasa faɗar angon a hankali. Hararar da Dadan ya watso masa ta saka Ma'aruff rufe baki yana danne dariya, Ja'afar kam sai yay saurin haɗe hannayensa alamar ban haƙuri, su ko su Mammah duk murmurshi sukayi. Mammah ya fara gaidawa, sannan cikin girmamawa ya gaida Uncle Nasiru da Uncle Jamilu, suma su Ja'afar suka gaisheshi. Dai-dai nan kira ke shigowa a wayar Imran, ganin likitan jiya ne mai kiran yasa shi ɗagawa a wajen batare daya tashi ba, sun gaisa yay masa bayanin ga result ya fito ya za'ayi? Sai yace masa ya jirashi gashi nan zai zo ya amsa. Yana yanke wayar ya sanar musu doctor ne. Uncle Nasiru yace, “Ai sai muje kenan?”. “A'a Uncle bara kawai naje na amso kuyi zamanku”. Su Ma'aruff najin haka suka miƙe wai bari su rakashi, shi ko yace suje. Daɗi ne ya kamasu, tunda dama neman hanyar jin komai sukeyi. Bayan fitarsu ne Mammah da Uncle Nasiru da Uncle Jamilu suka sake tattauna abinda ke faruwar, dan shi dama Zak-Shadow bai ma Uncle Jamilu bayanin komai ba. Sosai Uncle Jamilu ya girgiza, tare da jin tausayin yarinyar, dan yanzun kam Mammah ta buɗema Uncle Nasiru da Uncle Jamilu komai game da mahaifin Nimrah ɗin matsayinsu na iyaye. Sai lokacin ma Zak-Shadow ke tambayar tana ina?. Mammah ta ce, “Bilal ya tafi kaita makarantar su Mu'azz, nayi mamakin ma har yanzu bai dawo ba dan tun goma suka tafi”. Shima agogon hannunsa ya kalla dan gab ake da kiran sallar azhar, sha biyu kusan da ashirin ne. Zai yi magana sallamar su Imran ta katseshi, kowa juyawa yay yana kallonsu banda shi. Imran ya zauna, Mammah tace Ja'afar yay kiran su Momyn Nabeeha daga nan su wuce kasuwa ta sallamesu. Baki suka tura gaba su duka alamar basu so hakan ba, dan su so suke ai komai a gabansu. Amma an koresu bayan daga Dadan sai su a gidan. Babu yanda zasuyi suka fitan, shi Ja'afar yaje ya sanar ma da su Nabeeha batun kira. Dan suna falo suna breakfast da sai yanzu suke yinsa. Daga ƙofa ya tsaya ya sanar musu, bai jira amsarsu ba ya juya abinsa. Harara Momyn tasu da Nabeehar suka rakashi da ita, yayinda Ismat ke jin kamar taje ta rungumeshi, tana matuƙar son Ja'afar, amma shi ko kallo bata isheshi ba, randa aka saka ranar aurensu tasha kuka, amma sai ta ƙara ƙarfafa kanta akan kota biyu taje. Sai da suka gama abinda suke fin minti ashirin sannan suka tafi, a zatonsu wai haƙuri Zak-Shadow zai bada ya faɗi gaskiya tunda su basu san likita ya kira ba, duk kuma Kusancinsa da Momyn bai kirata ya sanar mata komai ba saboda hargaɗin Imran. Yanda Momy ke cika da batsewa haka Nabeeha keyi, da ƙyar ta gaida Ubanta da Mammah. Momy kam babu wanda ta gaisar, sai Mammah ita ta gaidata, ta amsa kuma da ƙyar. Shima Uncle Jamilu da yake bamai damuwa bane sai ya gaisheta. Imran da Zak-Shadow kam yi sukai kamar ma basu san da shigowarsu ba, sai hakan kuma ya ƙona mata rai, a ganinta ko Imran bazai gaisheta ba ai shi ya dace Zak-Shadow ya gaisheta kodan ƴarta da yake aure. Cikin danne takaici Uncle Nasiru yay gyaran murya tare da yin sallama. Kowa ya amsa sannan ya amshi takardar da Imran ya miƙo masa. “Ga result ya fita, doctor ya kira Imran yaje ya amso. Zamu duba sai muga mike cik.....” A wani irin zabure Momyn Nabeeha ta ce, “Kamar ya result ya fito anje an amsa? Ke nan wani abun aka ƙulla daban, yo inba wani abu aka ƙulla ba ai banga dalilin zuwa a amso result bada saninmu ba, kuma ai can ya kamata muje asibitin shi likitan ya mana bayani idan ba wani munafunci bane kuma ko an siyesa ne banda labari”. Babu wanda ya tanka mata, shima Uncle Nasiru baki kawai ya ɗan taɓe yana girgiza kansa. Ya kuma buɗe takarda ya fara bayanin da kowa zai gane, sannan ya ajiyeta a kan table yace duk mai buƙata zai iya ɗauka ya sake dubawa. Caraf Nabeeha ta ɗauki takardar ta duba kuwa, tunkan takai ƙarshe ta fashe da kuka wai ita wlhy bata yarda ba, sai dai in anje ansayi likitan nan ne, dan haka sai dai a sake zuwa wani asibitin a sake sabon gwaji. Yanda Momynta ke sake zugata da faɗan maganganu sai zuciyar Uncle Nasiru data Zak-Shadow ta sake hasala. Hatta Mammah dannewa kawai take tana murmushin mamaki, shi kansa Imran sai faman cizar lips yake. Sai Uncle Jamilu ne ke magana cikin lallashi da son fahimtar da Nabeeha da uwarta. Amma da alama ma ko saurarensa ma basayi. Gani sukai kawai Zak-Shadow ya miƙe abinsa yana kallon agogo, sai kuma ya kalla Mammah da girmamawa ya ce, “Kiyi haƙuri da hukuncin dazan yanke”. Cikin matuƙar tsoro Mammah ke kallonsa. “Wane irin hukunci kuma Muhammad? Kar ma kayi tunanin abinda zuciyata ke hasaso min”. “Mammah wanda ya dace ne, na san kuma kema zai gamsar dake in sha ALLAHU. In dai abinda nake tunanin zakiyi hasashe ne kuma bashi bane”. Daga haka ya kalla su Uncle's ɗin. “Lokacin salla yayi Uncle's”. Uncle Nasiru daya gama kaiwa wuya yana kallon Nabeeha data cika kunnen mutane da ihu kawai ya fisgi flowers base dake saman Centre table ya wurga kanta. Da hannu ɗaya Zak-Shadow ya cafe, yayinda kowa a falon ya waro idon tsorata, dan gilas ne flowers base ɗin, sun tabbatar idan ya sauka akan Nabeeha sai taji ciwo in ma bai fasa mata kan gaba ɗaya ba. Haƙuri Mammah da Uncle Jamilu suka hau bashi, yayinda Momyn Nabeeha ta kacame da tsiya Nabeehar na tayata da ihun kukan iskanci..........✍🏼
_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._
*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*
*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*
_Shaidar biya👇_
*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*
*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*
*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*
*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*
*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull
*_WHATSAPP (500)_*
*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*
*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*
*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*
*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*
*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._