Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 62

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 62

.....their part of the committee should come in. Honestly, we need evidence in our hands before we call or invite anyone. Then try to collect everything related to this attack for ten days from the beginning until they came out in the desert. We can invite Haysam in 2 to 3 days. I am warning you to be careful". Together they answered "Yes Sir". Then his ADC left and followed him.... Whose Haysam are you talking about? He married who...?" When Uncle Nasiru scolded her, he said, "It's Hausa that you don't understand anymore, do you?" Besides Haysam, your husband, is there another Haysam here? You are not a stranger, and your mother is your priest who carries you on a cart. Kinga now has it and they need to re-examine the doctor or deny it since the FATHER is not marrying HIS DAUGHTER..." "But Nasiru, are you cruel? Will your daughter join you in humiliating her?". Momyn said she spoke with a sigh and straightened up as if she was going to cover Uncle Nasiru with a blow. Then she was shaking, which made everyone stare at her except for Zak-Shadow who was pressing.....

Standalone post1,843 words

.........“Yes sir. A yanzu haka na shirya team guda uku, legal liaison, intelligence analysis, da forensics document review. Amma sir, idan har an taba goge wasu takardun fa, ba abune mai sauki ba a garemu, dan za'a iya amfani da hakan a cimmana” “No Colonel kada mu fara da zarge-zarge. Muna bukatar gaskiya. Ka kawo mini jerin sunayen waɗanda suka yi aiki tare da Shadow Recon, waɗanda suka zauna a gida da waɗanda aka tura waje. Zan fara da hira da su.” Cikin gamsuwa Colonel Haydar ya yi ƙasa da kai na girmamawa, “Sir, zan kawo jerin nan gobe in sha ALLAHU. Amma fa akwai ƴar matsala a waje, wasu daga cikin waɗanda aka rufe sun riga sun shiga harkar siyasa wasu kasuwanci. Wasu kuma sun yi murabus ne kawai dan kansu sun koma gefe.” Kai General ya jinjina kawai batare da yace komai ba, sai kuma ya ɗauki fayel ɗin dake ɗauke da hoton Zak-Shadow ya zubama hoton ido ba wasu sakanni. “Zan sanar da Ministan Tsaro cewa wannan bincike zai cigaba da tafiyar a karkashinmu har zuwa wani lokaci kafin nasu ɓangaren kwamitin su shigo ciki. Dan gaskiya muna bukatar hujja a hannuwan mu kafin mu kira ko mun gayyaci kowa. Sai kuyi ƙoƙarin tattara komai daya shafi shi wannan harin na kwanaki goma tun daga farkonsa har zuwa fitowarsu a jejin. Dan zamu iya gayyatar Haysam nan da 2 to 3 days. Ina ƙara gargaɗinku ku kula”. A tare suka amsa da “Yes Sir”. Daga haka ya fice ADC ɗinsa biye da shi.....

<<•>><<•>><<•>>

Tunda Uncle Nasiru ya fara bayanin sa jikin Nabeeha ya fara rawa, bata ma bari ya kai ƙarshe ba cikin ɗimuwa ta ce, “Abba nifa ban gane ba. Wai wane Haysam kake magana ya auri wanene...?” Sai da Uncle Nasiru ya zuba mata harara, cikin sake tsaurara harshe ya ce, “Hausar ce kika daina fahimta kenna ko? Bayan Haysam mijinki akwai wani Haysam ɗin ne anan? Ba kince ke baƙya ji ba, uwarki kuma itace limamiyarki mai ɗoraki akan keken ɓera. Kinga yanzu ke da ita bakwa buƙatar sake gwajin likita ko ƙaryatawa tunda dai UBA baya auren ƳARSA.....” “Amma Nasiru kai azzalumi ne? Ƴar taka za'a haɗa kai da kai a wulaƙanta?”. Momyn tace tai maganar cikin huci da miƙewa kamar zata rufe Uncle Nasiru da duka. Dan sai wani girgiza jiki take, hakan yasa kowa zuba mata ido banda Zak-Shadow dake danna waya kamar ma ba'a kansa ake bala'in ba. Dai-dai nan ihun Nimrah ya karaɗe kunnuwansu. Kusan lokaci guda Mammah da Zak-Shadow suka miƙe, hakama Imran da Uncle Jamilu. A tare su huɗun suka nufi kitchen inda suke jiyo ihun nata, shima Uncle Nasiru ya take musu baya. Babu wanda bai razana da ganin Nabeeha a kitchen ɗin ba da wuƙa a hannu, yayinda Nimrah ke can saman kitchen cabinet ta maƙale Nabeeha dake ƙoƙarin jawota na kuka da faɗin, “Wlhy sai na kasheki, shegiyar yarinya annoba mai kama da arnan jeji baƙa mummuna”. Nimrah dake kuka cike da ihu da cika kunne ta ce, “Niba shegiya bace ba, kuma ba arniya bace muguwa mai yanka mutane. Wayyo Ummana zata yankani kizo Umma, Kawu Tanimu na....” numfashinta ya wani jaaa alamar ɗaukewa saboda kafta da Nabeeha ta sake kai mata da wuƙar cikin rufewar idanu. Hakan kuma yayi dai-dai da isowar Zak-Shadow gabanta yay ƙoƙarin janyeta amma ina UBANGIJI ya riga ya ƙaddara sai ta sami Nimrah sai ko ta shata mata wuƙa a cinya. Ya rabbi, wani irin gigitaccen ihu da Nimrah ta saki Zak-Shadow bai ma san ya wanke fuskar Nabeeha da wani wawan mari guda biyu ba a lokaci ɗaya, wajen yin taga-taga zatai baya saboda gigita shima ta sharɓeshi a hannu, saboda kaifin wuƙar sai da ta fasa rigar shaddar jikinsa ta ratsa fatarsa. Amma bawon ALLAH bata kansa yake ba, ƙoƙarin zaro Nimrah data maƙale a lungu yake yi dan yarinyar tayi ɗif alamar ta suma. Ga jini tuni ya wanke rigarta ta dai-dai cinya inda Nabeeha ta yanke ta. Gaba ɗaya hankalin su Mammah ya gama tashi, Zak-Shadow dake rungume da Nimrah yana gama sauketa Mammah ta ɗaga rigar, ai a rikice tace, “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un” dan yanka ne babba sosai damma jini ya jiƙe ƴar cinyar tata ba'a iya ganin girmansa da zurfinsa. “Muhammad karka sauketa muje asibiti”. Mammah ta faɗa cikin tashin hankali. Suma su Uncle Jamilu gaba ɗaya sun gama rikicewa. Hatta Momyn Nabeeha rawa jikinta yake yi, tama kasa zuwa inda Nabeehar ta kife kan kitchen cabinet itama alamar taji marin maza. Sai da suka fice Uncle Nasiru da gaba ɗaya yay sumar tsaye ya tafi taga-taga zai faɗi, da ƙyar ya iya laluben bango ya dafe. A haka ya fice a kitchen ɗin shima yabar Momyn Nabeeha da jikinta ke rawa zuciyarta kamar zata fashe. Dan kasancewar a ƙarshe tazo sai idonta ke nuna mata akan ciki Nabeeha ta yanki yarinyar, kai tsaye ta kasheta... Acan compound ma su Ja'afar gaba ɗaya sun gigice saboda a yanda Dadansu ya fito da Nimrah shaddar jikinsa duk ta ɓaci da jini abinka da fara kawai sun ɗauka ta mutu ne. Hankali a tashe suke tambayar miya faru? Basu sami amsar kowa ba, sai kawai suma suka fara rige-rigen shiga mota....

★ Duk da raɗaɗin da hannunsa ke masa bata kansa yake ba, yana riƙe da Nimrah har aka gama mata ɗinki bayan an tsaida jinin da ƙyar dan anyi allura takai uku kafin aci nasara. Ya rabbi, duk mai imani dole yaji tausayin yarinyar, dan kuwa yankane bana wasa ba, gashi ya shiga sosai har ana iya ganin ƙashin ta. Su kansu asibitin da farko tsoron taɓata sukai sai da Zak-Shadow ya nema gigitasu da ihu. Dole suka dawo hayyacinsu sukai abinda ya dace. Tana sume akai komai aka gama, sannan suka farfaɗo da ita da dabarunsu. Allurar barci suka sake mata dan da ihu ta farka. Imran ya maida Zak-Shadow dake neman miƙewa ya zaunar yana ma nurse ɗin nuni da hannunsa. Ƙoƙarin nuna shi baya buƙata yayi, dan haka Imran ɗin ya ɗaure fuska ya kafa ya tsare kuma. Dole ya haƙura ya tsaya. Nashi ma da sauƙi amma fa ya yanku shima babu laifi, sai dai bai kai ko kwatar na Nimrah ba. Amma shima duk da haka sun masa ɗinki a wajen. Sun so riƙe Nimrah yace kawai a sallamesu za'a kula da ita a gida. Dole aka basu sallama da magunguna da dokar kawota ana dubawa suka wuce gida. Yanzu ɗin ma shine ya ɗauketa, ko'a mota tana riƙe a jikinsa har gida. Anan kuma suka tarar da tashin hankalin Uncle Nasiru, su Ismat da Biebah data dawo makaranta zagaye da shi suna kuka, sauƙin ma Biebah tai hankalin kiran matarsa, shine fa ta iso a rikice da likitansu datai kira a waya. Shine yaketa ƙoƙarin ganin nunfahsinsa ya daidaita sanda suke shigowa. Kai sukam dai wannan family sai dai suce Alhamdullah a wannan tsakani. Ganin al'amarin zai ƙwaɓe dole aka ɗauki Uncle Nasiru zuwa asibiti. Ga kuma Nabeeha can ta kulle kanta a ɗaki tana ihun kuka da rantsuwar idan Zak-Shadow bai saki Nimrah ba sai ta kashe kanta itama. Takaici ya saka babu wanda yabi takan haukan nata sai uwarta dake magiya da lallashinta su Amima na tayata. Da ƙyar da ƙyar dai suka samu ta buɗe. Uwar ta wani rungumeta tana kuka itama wai miyasa zatai mata haka. Miye-miye dai nan sukaita surutasu.....

“Tunda barci take kaje ka raba kayan nan da jikinka Muhammad, sam basu da ƙyan gani duk jini abinka da farin abu ƙara tada hankali yake”. Mammah ce mai maganar cikin damuwa da sanyi, dan kuwa babu abinda ke mata kai-kawo idan ta kallesa sai lokacin da Abdul-rasheed ke shinfiɗe a ƙasa an lulluɓa masa babbar rigar shaddarsa data jiƙe da jini. Dama su kaɗai ne a ɗakin nata, daga ita sai shi sai Nimrah daya shinfiɗar a gado. Kansa ya jinjina yana miƙewa. Har ya fara tafiya ta sake dakatar da shi. “Dan ALLAH na roƙeka kada kace musu komai?”. A karo na farko ya zubama Mammah hargitsatstsun idanunsa da suka mugun kaɗewa kamar wanda ya busa cocaine. Ita kanta Mammah sai da taji zuciyarta ta motsa saboda yanda idanun nasa suka koma. Magana yake son yi amma zuciyar ƴan maza tazo wuya ya ma kasa, sai kawai ta ce, “Dawo ka zauna”.. Bata jira amsawarsa ba ta taso ta kama hannunsa ta maidoshi inda ya tashi. Baya iya bijire umarninta, dan haka ya koma ya zauna kawai kamar yanda ta buƙata. Itama sai ta sauke ajiyar zuciya ita ta fita a ɗakin. Babu jimawa Ma'aruff yay sallama a ƙofar ɗakin cikin rawar murya alamar shima tsoron shigowa yake, dan sun san wanene Dadansu idan yana fushi, ya subahanallah abin babu ƙyau sam. Sum-sum ya shigo kansa a ƙasa kamar munafuki, kaɗan ya saci kallonsa yaga idanunsa a rufe suke, ƙaramar ajiyar zuciya ya sauke tare da ajiye kayan a kusa da shi kaɗan. Idanunsa cike da hawaye miryarsa na rawa kamar wani ƙaramin yaro, ba komai ya kawo hakan ba kuma sai tausayin Dada, dan duniya basa ƙaunar abinda zai taɓa musu shi. “Kayi haƙuri Dada, ga kaya ka canja inji Mammah”.. sanin ya jishi, yasan bazaiyi magana ba kuma yasa shi fita yana share hawayen da suka sakko masa. Wlhy badan Mammah ta hana su ba yau sai sunma Nabeeha dukan mutuwa a gidan nan, kuma da bazata kwanar musu a gida ba. Amma babu yanda suka iya Mammah ta kafa ta tsare. A falo ma sauran ƴan uwansa na zaune jigum-jigum, dan har su Ummi ma sun zo gidan tuni..........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 63_

__________________

https://chat.whatsapp.com/J92XqvWDRch1EJPdGDBa41?mode=wwt

https://vm.tiktok.com/ZSHWHk4ULWbMN-geqJz/ This post is shared via TikTok Lite. Download TikTok Lite to enjoy more posts: https://www.tiktok.com/tiktoklite

https://chat.whatsapp.com/KfkKd9vD8MrAst8i8CQDsj?mode=wwt Assalamu alaikum, Mutanen arziki Ina musu capacity😍🥰 kuna Neman Inda zaku Samu ingantattun Kaya masu kyau da quality sosai 💝 Kamar Kayan Yara Zannuwan Gado Kayan kitchen Shoes and bags Jewellery Laces, atamfa,shadda Dadai sauransu. To nesa tazo kusa, Maza Danna wannan link din domin Samun Kaya masu inganci da ƙayatarwa da idan kika saka ko ina kika shiga sai an kalleki an ƙara kallo.

Ko ku nememu ta wannan number 08165751018 ❤️❤️❤️😘

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________