Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 63

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 63

His voice entered their noses and they all turned around, his eyes on Nimrah's feet and he responded to their greetings, and their attention was on his hand as well. With respect and caution, he greeted Mammah as well, and asked Nimrah's body to soften her cries. "Alhamdulillah, but I think we have to go to the hospital now, since the morning she is crying about her leg, I think she is in pain, but how is your hand?". He looked at his hand, and then he looked at Nimrah's feet as well. "I don't think there is anything to worry about, Mammah, even if there is a dispute". "There is no need to argue, she has a reason to do it. This pain is not a small thing for a big person, even if she is alone. The biggest worry is that she does not eat anything for this tea until she calms down and drinks." Hanu extended his hand to Biebah, who was holding a cup, but he didn't say anything. Seeing this, Mammah just stood up and said, "Well, Biebah, get up and ask the people for extra food. Mu'azz, get up, let's get ready for school." It's like he's going to cry and say, "Mamma, I'm not going, I'm going to stay with Nina". Zak-Shadow looked at him and he fell on the bed quickly, but his eyes were fil

Standalone post1,979 words

........Washe gari da fitinar Nimrah suka tashi a gidan. Dan tunda ta farka da asuba take ta kuka ƙafarta-ƙafarta. Haka suke zagaye da ita kowa na ƙoƙarin lallashinta. Yayinda Mu'azz ke tayata kukan shima. Sai kusan bakwai Zak-Shadow da bai san abinda ke faruwa ba ya shigo. Dan rashin samun isasshen barci a daren jiya shima yau makara yay ko sallar asuba a gida yayi ta. Dan haka sai yanzu yake fitowa daga sashensa, batare da ya ko kalla hanyar ɗakin Nabeeha ba, hasalima yayi zaton basa gidan, dan tunda suka dawo asibiti jiya baiga kowa ba tsakanin ita da uwar tasu da ƙannen nata, sai Jiddah ce ma da daddare ita da mijinta suka zo duba su tanata kuka da bashi haƙuri akan abinda ƴar uwar tata tayi. Tun shigowarsa falon yake jin kukan Nimrah. Kai tsaye ɗakin Mammahn ya nufa shima, inda ya tadda duk ƙannensa a ciki. Kowa kuma ƙoƙarin lallashin Nimrah dake kwance jikin Mammah yake yi, amma yarinyar nan taƙi sauraren kowa sai kwarara ihu take yi. Babu wanda yaji sallamarsa sai da ƙamshin turarensa ya shiga hancinansu da gyaran muryar da yayi sannan duk suka juyo, idonsa akan ƙafar Nimrah ya amsa gaisuwarsu, suko hankulansu na'a kan hannunsa shima. Cikin girmamawa da tsantseni ya gaida Mammah shima, tare da tambayarta jikin Nimrah data ɗan sassauta kukanta. “Alhamdulillah, sai dai inaga dole mu koma asibiti yanzu dan tunda asuba take kukan ƙafar, inaga tana mata ciwo ne, kaima yaya naka hannun?”. Hannun nasa ya ɗan kalla, sai kuma ya kalla ƙafar Nimrah ɗin itama. “Ni kam babu wani damuwa Mammah, itama harda rigima dai”. “Rigima kam ai dole ce, dan tana da hujjar yinta. Wannan ciwon ba ƙarami bane ga babba ma bare ita. Babbar damuwar ma taƙi cin komai ga tea nan har ya huce taƙi sha”. Hannu ya miƙama Biebah dake riƙe da kofin batare da yace komai ba, ganin haka sai kawai Mammah ta miƙe tana faɗin, “To Biebah tashi ki nema na mutane abincin kari. Mu'azz tashi kaima muje kai shirin makaranta.” Kamar zai yi kuka ya ce, “Mammah ni bazanje ba, zan zauna tare da Nina”. Kallon da Zak-Shadow ya watso masa ya sashi sauka a gadon da sauri, sai dai idanunsa cike da ƙwalla. Murmurshi kawai Mammah tayi ta kama hannunsa suka fice. Caraf Nimrah ta ce, “Mammah ni dai ki dawo naki nake so....” Mammah na ƙoƙarin juyowa Zak-Shadow ya watsama Nimrah harara, sai ta sake taɓe baki zatai kuka. “Kika bari wannan hawayen suka zubo zaneki zanyi. Maza karɓa kisha. Kin zauna kinama mutane kukan banza amma bakinki baya mutuwa”. “Ni dai dan ALLAH ka bita a hankali Muhammad, idan bazaka iya ba na dawo na bata”. Ƙaramin murmushi yayi. “Shike nan Mammah zan bata”. Suma su Bilal duk murmushin sukayi dan sunji daɗin ganin murmushin nashi. Shima zamansa ya gyara ya fara kai mata kofin bakinta, sai ko ta fara amsa babu musu. Sha kamar uku ta yatsine fuska tana kallonsa, ta ce, “Dada”. “Uhhhm”. Ya amsa mata a maƙoshi. “Kaima ƴar dabar ce ta jimaka ciwo a hannu?”. Da mamaki ya zuba mata ido, a zuciyarsa yana ayyana (sai shegen surutu). Suko su Ja'afar dariya zancen nata ya basu, jira suke suji amsar da Dadan zai bata amma yayi shiru. Cikin kasa haƙuri Ammar ya ce, “Nimrah ƴar daba kuma?”. “Eh Uncle Ammar”. Ta faɗa kamar yanda taji Mu'azz na kiran kowansu da Uncle ɗin. Batare da jiran cewar kowa ba ta cigaba da faɗin, “Ummana tace ƴan daba ke riƙe wuƙa da yanka mutane ai. Kaga itama ta riƙe wuƙa ta yankamu ni da Dada, Dada kaima kayi kuka data yanka ka?”. Ta ƙare maganar tana tsatstsareshi da idanu. Rasama abin cewa yay, sai kawai ya samu kansa da girgiza mata kai. Idanu ta waro masa sosai, sai kuma ta yamutsa fuska alamar motsin da tai taji zafi. Amma bata haƙura ba sake cewa, “Kenan kai baka yi kuka ba? Kuma baya maka zafi kamar nawa?”. Nan ma kai kawai ya jinjina mata yana kai mata kofin shayin a baki dan ta ƙyaleshi da wannan surutun nata, gashi ta wani tsatstsareshi da idannunta. Kauda kanta tai gefe, dan in surutu nacin Nimrah itafa sai ta fetsar take jin daɗi, dan yanzu ma kai tsaye ta ce, “Dada jira na gama. Kai miyasa baka jin zafin ko kaima ɗan daba ne? Dan Lawwali yace min suna ƴan daba dake yankar mutum idan aka yanke su basa jin zafi kuma basa yin kuka”. Anya shi kam ya taɓa gamuwa da magananniyar yarinya irin wannan? A zuciyarsa yake ayyanawa, yayinda su Ma'aruff ke ƙunshe dariyar dake cinsu. Dai-dai Nimrah ta kai hannu tana taɓa hannun Zak-Shadow dake kallonta kawai Momyn Nabeeha tai sallama, kafin su amsa ta shigo Nabeeha biye da ita sai su Ismat a ƙarshe, dan ita da kanta ta tattaro su wai su duba Nimrah su bama su Mammah haƙuri. Ai a bazata Nimrah tai wani uban tsalle ta haye jikin Zak-Shadow ta ƙanƙamesa tana fasa ihu da faɗin, “Wayyo Dada ƴar daba ta sake zuwa, ɓoyeni kada ta yankamu. Wayyo Dada wayyo zata ƙara yankamu shike nan ƴar daba mai wuƙa”. Idan kunji ana sumar tsaye to ita Nabeeha da uwarta sukayi. Dan har tsakiyar kai kalmar (ƴar daba) ɗin nan ta dakesu. Yayinda su Bilal suka kasa haƙuri shi da Ammar suka shiga kwasar dariya. Suko su Amima yanda Nimrah tai uban tsalle ne da firgita ya basu dariya. Ita ko baiwar ALLAH da gaske tsorata tayi, dan tai bala'in shigewa cikin jikinsa, ƙarshe ma rigarsa ta ɗaga ta tura kanta ciki ta duƙunƙune, ALLAH ya sota ma tun a daka tsallen farko ya riƙe ƙafar tata mai ciwo a hannunsa, da ba ƙaramin fami zatayi ba kam, maybe ma ɗinkin ya farke tunda jikin ba wani ƙwari gareshi ba fatar ƙuruciya. Ihun Nimrah ya shigo da Mammah da Biebah, sai Mu'azz da har an masa shirin makaranta. A tsorace Mammah ta ce, “Wai mike faruwa?”. Da ƙarfi Nimrah dake cikin rigar Zak-Shadow ta ce, “Ƴar daba ce mai wuƙa Mammah ta dawo zata yankamu ni da Dada, ku yankata Mammah kuma ku yayyankata kamar akuya”. Duk yanda Yaya Ma'aruff da Yays Ja'afar ke dauriya a wannan gaɓar suma sai da suka dara. Sai Mu'azz ne abinka da yarinta ya hau gadon yana kamo hannunta da faɗin, “Ke Nina bafa ƴar daba bace su Aunty ne fa”. Cikin kuka Nimrah ta ce, “Ƙarya kakeyi Ƴar daba ce, ranar ita ta yankamu ni da Dada, kuma tace saita kasheni bata sona. Muguwa! Muguwa in ALLAH ya yarda sai kin mutu yau kin haɗu da fatalwar kabari da walakiri mai ƙaton sanda”. Cikin matsanancin ɓacin rai da kishin ganin yanda Nimrah ta shige rigar Dada, shi kuma ya wani zauna kamar gunki yana riƙe da ƙafarta kawai sai zuciya ta tokare ƙirjin Nabeeha. A zafafe ta ce, “Ubanki ne mugu ɗan daba shegiyar yarinya mayya, Momy ga abinda nake gaya miki nan kinƙi yarda kina wani muzo mu ganta...” tai maganar tana kai hannu zata damƙo ƙafar Nimrah dake hannun Dada. Abinda kuwa bata taɓa zato bane ya faru, dan kuwa caraf aka riƙe hannun nata, tana ƙoƙarin fisgewa cikin rufewar idanu Mammah ta ɗauke fuskarta da mari. Lokaci guda ɗakin yay tsitt, dan bama ita data ɗago a birkice taga Mammah ce mai marin ba hatta Zak-Shadow kansa ya girgiza, dan kowa yasan wacece Mammah akan kawaici.... Katse tunaninsu Mammah tayi, cikin faɗa ta ce, “Shin haka kike dama Nabeeha ko yanzu ne wannan halayyar banzar take neman shigarki? Wane shirme ne wannan kike yi akan yarinya ƙarama ƴar cikin ki, wadda da ALLAH ya baku haihuwa kin haifi wadda ma ta fita......” Hannun Nabeeha Momynta ta kwace daga wajen Mammah, itama a fusace ta ce, “Haba Hajiya A'isha yada haka da girmanki? Bakiga laifin Haysam shi da ya auri ƴar cikinsa ba sai laifinta, kishiya ko jaririyace ai yin kishinta ba haramun bane balle wannan hatsabibiyar yarinyar mai kama da an haifeta a tsakiyar tasha.....” “K! Ya isheki haka Malama!!”. Ma'aruff ya faɗa a zafafe tamkar zai kaima Momy duka. Cikin zazzaro idanu dan shima akwai zuciya kamar Dada ya cigaba da faɗin. “K har kina da bakin cema wata ƴar tasha bayan ga ƴar tasha nan kin haifa mai yankar mutane da wuƙa, ai gaskiya Nimrah ta faɗa ƴar daba kika haifa, sannan Wlhy mahaifiyarmu ta fita cikin idanunki idan ba haka ba kuma zaki sha mamaki, dan akan Mammah da Dada komai zamu iya yi ciki harda koya muku tarbiyya dan naga tayi ƙaranci anan. Ku mi yasa baku san kawaici bane ba, idan badan Mammah ɗin ba wlhy da tun jiya mun yagalgala ku sai buzinku.”. “Iyeee!!! Ma'aruff ni zakama rashin kunya?”. “Anyi miki ɗin, in har zaki taɓa mana uwa duka ma zaki iya ci a hannunmu. Anata muku kawaici amma bakwa ganewa, damma kin samu ana gayawa ƴar taki gaskiya da gyara tarbiyyarta tunda ke kin kasa. Nimrah kuma ta zama matar Dada sai dai duk mai mutuwa ya mutu da baƙin ciki babu canji, wani wasan ma sai nan da shekarun girma.....” Hannun Ma'aruff Mammah ta riƙo dan yi yake kamar zai kwashe Momyn Nabeeha da mari. “Ya isa haka”. Cewar Mammah tana janye Ma'aruff baya. Kafin ta maida dubanta gasu Nabeeha, babu alamar wasa ko sassauci a tare da ita ta nuna musu hanyar fita, “Ga hanya Hajiya Hasiba, idan kuma kuka kaini bango to zan barku da Muhammad, kun san kuma abin bazaiyi ƙyau ba. Dan na fara gajiya da tausarsa akan wannan haukar na Nabeeha. Dan ALLAH ku barmu muji da abinda ya dame mu.” Cikin ɓacin rai itama Momyn ta buɗe baki zatai magana Mammah ta sake ɗaga mata hannu tana girgiza kanta.... “Idan bazasu fita da arziƙi ba Mammah ki barmu mu fitar da su, dan mu nan munma ishesu Dada yafi ƙarfinsu, su ɗin banza ya tanka haukarsu”. Yanzun kam Ja'afar ne mai maganar. Jiki a sanyaye Ismat tazo ta kama hannun Momynsu dana Nabeeha, shiyyasa tacema Momy kada aje bada haƙurin nan yanzu dan tasan nacin Nabeeha da mitar tsiya, sun kuma san wanene Dada a gidan. To gashi nan shi baima ko kallesu ba su Yaya Ma'aruff na neman lakaɗa musu duka. Duk haƙurin Mammah yau an sakata tayi abinda ko da kwatance basu taɓa gani ba a tsawon rayuwar zamansu gidan kusan shekara uku..........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 64_

__________________

https://chat.whatsapp.com/L3BXH7JYlBRHIkFRiOjeW3?mode=ems_copy_t

UMMU KHALIFA COLLECTION

Ina Mata Yan kwalisa ina mata masu san kayan ado kamar Egyptian abaya sleeping drees kids were shos bags musk dahara original.

To kukanku yazo karshe domin ummu khalifa sun zo muku da duk wadannnan kayan dierct suke order dinsu daga Egypt zuwa gida Nigeria kaidai kawai kashiga link dinsu domin gani ya kori jiii..

Ba nan ummuh khalifa suka tsaya ba suna nemawq mutane visa masu shaawar shugowa kasar ta Egypt karatu ko yawon bude ido ko kasuwanci ku tuntubeta a number dinta +201017018846/07048811474/

KO kuma shafinta na tiktok https://vt.tiktok.com/ZSU1FEkjc/

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________