Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 64

Post

KIDA A RUWA BOOK 1 PAGE 64

.....na.... (Said to you, little brother Dada 😂💃🏼) >>><<★>><<< "Work says". That Mr Specter was laughing evilly with amusement. The others were also laughing even though Jush is a person who doesn't laugh often. Scythe put down a cup of beer, full of pride and said, "Say the game of Zak-Shadow". "Falling upon falling." Black Spider accepted, grinning. Viper continued to say, "I never thought that this illegitimate would say that easily, no lie will make it difficult for us." "I don't think so, Viper, since we've been together like that, there's already been a story about him. Ashema is like a fool, he's going around the enemy thinking he's a warrior. I'm sorry they couldn't take him to the ground a long time ago after he got into their noses already." "Hmm, don't you tell me what Garba said here. It was their general who stood up for him, and now he said that he has set up and guarded against the internal information that is being compiled so that they will not be released." "He's a troublemaker, he's done it and he's doing it from his seat. Even the Minister, we had to remove him from his seat." "This has to be done. He is the father of their invitation. We have to get rid of him.

Standalone post2,084 words

....Duk wannan bidiri da ake fa Nimrah na cikin rigar Zak-Shadow har lokacin, sai dai ta ɗan ɗaga tana kallon komai. Sai da taga su Nabeeha sun fita ta wani sauke ajiyar zuciya kamar babba tana fitowa, hawaye shaɓe-shaɓe a fuska ta kama dariya da faɗin, “Yauwa Uncle Ma'aruff kun kori ƴan daba. Ai dama kun zaneta. Kuma in ALLAH ya yarda sai ta mutu kuraye da fatalwoyi sun cinyeta ko ɗan ƙashi bazasu bar mata ba.” shirmenta ya sakasu yin murmushi gaba ɗaya. Banda Zak-Shadow dake zaune shiru har yanzu. Sai dai Nimrah na gama fita a jikinsa ya ƙarasa ajiyeta kawai ya miƙe. Da sauri Mammah ta ce, “Muhammad ina zaka?”. “Kiyi haƙuri Mammah”. Abinda kawai ya iya faɗa kenan yay waje tamkar mayunwacin zaki. Kiransa Mammah keyi, dan indai yace tayi haƙuri zai aikata ba daidai bane amma ina. Daɗi ne ya kama su Bilal, dan sun san Dada aiki ne gamai ƙare ka. Mammah na yunƙurawa zata bishi su Ma'aruff suka riƙeta cike da makirci suna bata haƙuri, nan ko so suke Dada yaje yay abinda suke so kada ta hana....

(Sai daku ƙanen Dada 😂💃🏼)

>>><<★>><<<

“Aiki ya faɗa”. Cewar Mr Specter yana wata dariyar mugunta cike da nishaɗi. Suma sauran dariyar suke har oga Jush duk da kuwa shi mutum ne bamai yawan dariya ba. Scythe ya ajiye kofin giyar daya kwankwaɗa, cike da izza ya ce, “Ka faɗi wasan Zak-Shadow”. “Faɗuwa kan faɗuwa ma kuwa”. Black Spider ya karɓe yana ƙyalƙyala dariya. Viper ya cigaba da faɗin, “Ai ban taɓa zaton shegen nan zai faɗi haka cikin sauƙi ba, babu ƙarya ya wahalar da mu.” “Ni kaina ban zato ba Viper, ashe tun da can da haka mukai da tuni labarin wani ake bashi ba. Ashema fankamar banza yake shege zagaye yake da maƙiya yana tunanin mayaƙa ne. Na rasa miyasa suka kasa kaishi ƙasa tuntuni bayan ya gama shige musu hanci tun tuni.” “Humm bakaji mi Garba nan yace ba, Janar ɗin nasu ne ya tsaya masa ai shiyyasa, dan ko yanzu yace ya kafa ya tsare akan bayanan cikin gida da ake haɗawa wai karsu fitar.” “Ɗan wahala, yayi ya gama shima ta kujerarsa yake yi. Hatta Ministan nan sai mun ɓarar da shi a kujerarsa”. “Wannan dole ne ai, shi kansa uban gayyar tasu dolene mu ɓarar da shi dan na fahimci badan wannan matakin da muka ɗauka ba bazai bamu haɗin kai ba.” “Karku wani damu kanku, duk wanda yay mana kan kara sai mun masa na itace.” Raven ya ce, “Ni bama duk wannan ba, ɗazun fa mutum nan ke sanar dani ya rasa kowane bayani daga ɓangaren cikin yaronmu. Kuma yaro mafi kwazo dake kusa da Zak-Shadow”. Cikin zabura Oga Jush ya ce, “Kana da hankali kuwa Raven, amma shine baka sanar ba?”. “Kayi haƙuri sir, nima yanzu zamu shigo nan nake ganin saƙonsa. Shiyyasa ma na ɗan dakata nai kiransa a waya kafin na shigo. Amma na bashi awanni uku akan ya tabbatar yazo da labarin da kai zai iya ɗauka”. Lokaci guda sukai ɗif, kusan mintuna biyu oga Jush ya ɗauka waya. Kai tsaye yay kiran number Garba. Aiko sai gashi ya ɗaga yana magana ƙasa-ƙasa daga can. Cikin rufewar ido Oga Jush yace, “Ina son ganinka idan ba damuwa”. A gadarance Garba ya ce, “Bazai yiwu ba dan ina kan aiki. Ka faɗi koma miye a haka ina jinka”. Duk da Oga Jush yaji haushi sai ya danne, a ransa yana tabbatar da zai yi maganin Garba ɗin, ya dai gama musu aikin nan. “Okay ba damuwa, na samu rahoto ne mai ƙarfi yanzu cewar cikin yaran Zak-Shadow babu wani, kuma makusancinmu ne.” “Miye rank ɗinsa?”. “Lieutenant.” Jimmm Garba yay alamar tunani, zuwa can ya nisa, cike da son nuna gwaninta ya ce, “Ka tura hotonsa. Duk da ina da tabbacin Ojo ne ko Rufa'i”. Oga Jush bawani yasan sunan yaron bane ba, dan haka yace, “Okay yanzun nan za'a tura maka”. Daga haka ya ajiye wayar yana kallon Raven. “Ka kira shi yanzun nan ya tura maka hotonsa a tura masa”. “Okay Sir”. Raven ya faɗa yana ƙoƙarin kiran Nanu. Bugu ɗaya kuwa ya ɗaga, cike da girmamawa daga can ya ce, “Ayi haƙuri sir ina kan bincike yanzu haka”. “Babu damuwa, zamu samu hotonsa ne?”. “Eh za'a samu sir”. “Tura min”. Cikin sakanni hoton Ojo ya shigo wayar Raven. Babu ɓata lokaci kuma aka turama Garba.....

<<<<<<>>>>>>>

Dariya sosai Lt Col. Garba keyi yana kallon hoton Ojo. Lallai yanzu ne wasa zai ƙara zafi kamar yanda yake so. Domin kuwa kowa yasan Ojo yaro ne makusancin Zak-Shadow matuƙa gaya. Yaransa biyu amintattu ya saka a sirri su bincika masa ina Ojo yake daga lokacin zuwa dare. Da girmamawa suka amsa masa kuwa. Ai ko awa ɗaya basu cika ba sukazo masa da bayanin tafiyar Ojo gida. Sai dai a labari mai ƙarfi ga wani abokin Ojo shine Ojo na wani hotel ne zaune da budurwarsa bai je gida ba. Hakan yay ma Garba daɗi, da kansa ya nufi hotel ɗin neman Ojo ɗin, bayan ya saka abokin na Ojo bashi number ɗin budurwar. Dan sun gwada kiran layin Ojo a kashe. Koda ya kirata ta sanar masa inda zasu haɗu ya sameta cikin damuwa da jin haushi. Dan a amsoshin da take bashi ya fahimci haka. Jin cewar daga fita sayo mata abu a mall ɗin kusa da hotel ɗin shine bai dawo ba yay shiru yana nazari. Kafin cikin jinjina kai yace ta bashi wayarsa. “Da wayar ya fita ai”. Nan ma shiru Lt. Garba yayi, sai kuma ya miƙe ya mata sallama. Bai zame ko ina ba sai ofishin ogansa, ya labarta masa komai daya samo. Murmurshi Ogan yayi da girgiza kansa, ya ce, “Baka da dama Garba, ka dai dage da kai za'a kai Zak-Shadow ƙasa”. “Na tsaneshi ne Sir! Tun tuni da na samu dama ma da wannan hannun nawa zan kashe banza wlhy. A wannan gaɓar kam idan na bari aka ƙara masa girman da ake shirin yi zan shiga uku ne kawai, Junior ɗina ne fa a makaranta ake shirin maidawa Senior ɗina akan aiki, haba impossible nabar Haysam ya koma samana, a yanzu ma da muke mate a aiki ba ƙaramin zafin hakan nake ji ba, shiyyasa akan wannan al'amarin sai inda ƙarfina ya ƙare”. “Zan kuwa taimaka maka kodan kwatanta alkairin da kai min nima a baya. Yanzu kaje ka samu abokin shi yaron ya kai report ma ogansu kan basu san inda yake ba, kuma gidansu an kira ance baije ba zan ƙarasa sauran aikin.” “Okay Sir!”. Lt. Col. Garba ya faɗa cike da farin ciki yana miƙewa. Sai da ya ƙame ya sara masa sannan ya fita. Yana zuwa kuwa abokin Ojo ɗin ya nema, ya tsara masa komai. Shi ko aboki najin zai samu tagomashin arziƙi babu wani tunani yaje ya kaima ogansu report kamar yanda Lt Garba ya tsara masa. Oga yay shiru cikin nazari, dan kuwa Ojo yana ƙarƙashin Zak-Shadow ne, shi kuma ya kamata a kaima report ɗin rashin ganin Ojon, sai dai kuma a yanzu Zak-Shadow baya kan aiki yana hutu, a gefe kuma ga tataɓurzar da ake yi a kansa ma. Daya lissafa yaga lissafin bazai dai-daita ba sai kawai ya tura report ɗin shima sama. Tura report ɗin rashin Ojo anyi rashin sa'a ya faɗa a hannun ɗaya daga cikin membobin kwamitin bincike, wanda kuma shima sam baya ra'ayin Zak-Shadow. Aiko baiyi ƙasa a gwiwa ba ya kai ga kwamiti tare da tsatstsara zantukan da suka ja hankalinsu har suka maida hankali akan batun, tunda dama a wannan gaɓar bai kamata suyi sakaci da abu komai ƙanƙantarsa ba...

★ Bincike ya tabbata akan neman Ojo ta ɓangare biyu koma muce uku. Domin kuwa ga ƴan ƙungiyar duhu, ga Lt. Garba, ga kuma kwamitin bincike. Al'amarin kamar wasa aka girmamashi ya zama babba. Inda a karo na farko Nanu ya haɗu da shugabannin ƙungiyar duhu saɓanin da da bai san kowa ba sai Raven. Yau kam sai gashi ƙuru-ƙuru zaune a tsakkiyarsu sakamakon memory card daya bayar wanda sai daga baya ya tuna Ojo ya bashi tun a washe garin fitowarsu a jeji. Oga Jush dake kallon Nanu a karo na farko yayi maga cike da izzarsa. “Nanu kake ko?”. “Eh Sir!”. “Ka tabbatar wannan memory ɗin daga hannun Ojo ya fito?”. “Kwarai da gaske. Dan kuwa a washe garin da suka fito a jeji kasancewar kasan shi bai samu wani rauni ba ya kirani ya sanarmin yayi videos sosai a wajen yaƙin, har naita mamaki shi taya ya iya yin hakan bayan suna ta ransu, shine yace shi mahaukaci ne zai shiga yaƙi, ai yana manne da Zak-Shadow dai. Dana fahimci da gaske yake sai nace mu haɗu to na amsa. Shine yace haɗuwa bazata yiwu ba na bari sai abubuwa sun lafa, idan kuma ya samu dama zai bada saƙo ta hannun budurwarsa. Ranar kuma muka haɗu da budurwar tasa ta bani saƙon da tambayata ko nasan inda yake, nace mata a'a gaskiya, shine ma dalilina na kiran oga Raven na shaida masa, dana duba saƙon kuma banga wani abu mai amfani ba sai jiya da dare dana zurfafa nazari na sake ɗakkosu na zazzage shine na samu wannan memory card ɗin”. Cikin gamsuwa oga ke jinjina kai, kafin ya bada damar a saka memoryn kowa yaga mike ciki. Dandanan kuwa aka saita komai da magiji, sai ga komai daya faru a jeji tare da su Zak-Shadow dalla-dalla, duk da ba komai aka ɗauka ba, wani gurin ma bai ɗauku da ƙyau ba amma sun samu wurare masu muhimmanci da suka sakasu a farin ciki mara misali. Musamman inda Zak-Shadow ke dawowa jejin, da inda ake kashe mahaifin Umman Nimrah, da inda ake kashe Umman kanta, da inda bomb ya tada gidansu da yara da sojoji a ciki. Harda randa Zak-Shadow kema su Baban Nimrah tambayoyi a cikin tanti. Tsabar farin ciki oga da kansa yayma Nanu ƙyauta ta musamman. A take kuma suka turama wani ƙwararren masani dake wata ƙasa yay editing videon ta yanda duk iya son gano gaskiyarka baka isa tantance abinda ke ciki ba haka yake ba. Ana dawo da videon suka kalla suka sake maidashi a sabon memory card suka kira Lt. Col. Garba suka danƙa masa, akan suna son a saka memoryn a kayan Ojo. Hakan kuwa akayi, Lt. Garba ya danƙama abokin Ojo memory card ya mayar a kayansa dake cikin barrak, sannan ya koma ya kitsama ogansa batun binciken kayan Ojo, oga kuma ya ankarar da membobin kwamitin bincike. Suko dama yanzu basa wasa da abu komai ƙanƙantarsa akan wannan case, kodan matsin lambar da suke samu daga gwamnati........✍🏼

_Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._

*_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_*

*_Zaku iya kuma tura katin Airtel na ƙasar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_*

_Shaidar biya👇_

*_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_*

*_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_*

*9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_*

*_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_*

*_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull

*_WHATSAPP (500)_*

*1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_*

*_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_*

*_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_*

*_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_*

*_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

_Chapter 65_

__________________

https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp

07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm

https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok

IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃

__________________

*_TELEGRAM GROUP_*

https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk

*_WHATSAPP CHANNEL_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F

*_TIKTOK_*

https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/

*_INSTAGRAM_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

______________________