Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 11

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 11

..... he ended, and the studies that were done were not here and he put them in the front. A week went by and they went back to school, but even so, Hajiya had to set the condition that they would not give her girl, and they had to be separated from each other and the case died. It was noticed that her daughter was looking at the phone in vain just like Nimrah said...... >>>>><<<<<< Today was Friday, so they were woken up early. But there is no sign of their driver. They know that maybe he first came to pick up the Abees before he came here, even though every day he comes to pick them up before they finish their school because they are already leaving. Since they were looking at the clock until they saw it, most of the students had already passed and were taken away. The school should appoint a law and it is compulsory for every student to be picked up and the gate should not be opened for them to come out. They are tired of Ruky's pregnancy, her son is not my little granddaughter. Seeing her start to cry, Nimrah's mind was raised. She went to the Principal's office but was told that they had gone to a meeting with the teachers. She ran back to Ruky, she found that she was kneeling

Standalone post1,750 words

11

.........Kwanaki kusan biyar su Nimrah na cin ƙaniyarsu da aiki, sun jikatu matuƙa sunyi laushi, kuka da roƙo babu kalar da basuyi ba, hakama kawunansu sun bama Daddy Imran haƙuri amma yace idan suka bar aikin nan Boarding fa babu fashi. Da ga ƙarshe dai suka zagaye suka kira Aunty Ummie a waya suna mata kuka suka sanar mata. Dama kwana biyu bata leƙo gidan ba saboda aiki. Aunty Mommy kuwa basa ƙasar ita da mijinta sai a satin nan zasu dawo. Ita ko Aunty Mimi ciki gareta tsoho haihuwa ko yau ko gobe shiyyasa Mammah ta hanata zuwa gidan. Alhamdullahi zuwan Aunty Ummi da suke kira da Big Mah-mah ne ya cecesu a hannun Daddy Imran. Dan bayan an sako massalacin juma'a yazo gidan gaida Mammah ta tareshi da daɗin baki da ban haƙuri har ya haƙura masu aiki su dawo gobe. Amma duk da haka da sharaɗin daga yanzu kullum dasu za'a dinga shiga kitchen yin girki. Da wannan ALLAH ya ƙwacesu. Masu aiki suka dawo, su kuma suka samu sauƙi. A cikin satin ma suka koma zuwa islamiyya dan suspension ɗin ta ya ƙare, sai kuma karatun da akayi basa nan ya sakasu a gaba. Sati ya zagayo suka koma boko ma, amma duk da haka sai da akai zama da Hajiya ta kafa sharaɗin babu su ba yarinyar ta, dole kuma a raba musu wajen zama sannan case ɗin ya mutu. Dan an dai gane ƴarta na kalle-kallen banza a waya da gaske kamar yanda su Nimrah ɗin suka faɗa......

>>>>><<<<<<

Yau ta kasance juma'a, dan haka an tashesu da wuri. Sai dai shiru babu drivern su babu alamarsa. Sun san maybe ya fara zuwa ɗaukar su Abees kafin yazo nan, duk da kuwa a kulum su yake fara zuwa ya ɗauka kafin su ƙarasa makarantar su Abees ɗin saboda suna rigansu tashi. Tun suna kallon agogo har suka sare, ga mafi yawan ɗalibai duk sun wuce anzo an ɗaukesu. Makarantar su nada doka kuma ma tilas zuwa ake ɗaukar kowane ɗalibi bawai buɗe musu gate ake su fito ba kawai. Sun gaji ga Ruky na ciwon mara, dan ita in zatai period ba ƙaramin jikata take ba. Ganin ta fara kuka hankalin Nimrah ya tashi. Ofishin Principal ta nufa amma ta tasar baya nan wai sun shiga meeting da malamai. Da gudu ta dawo wajen Ruky, ta sameta durƙushe azaba ta isheta, bata son suje clinic ɗin cikin makaranta dan an riga an tashi. Idannunta na cika da ƙwalla itama ta kamata ta miƙar. “Tashi muje wajen security ko zai taimaka ya barmu mu fita kawai, amma shima Baba Driver bai ƙyauta mana ba”. Da ƙyar da ƙyar Ruky ta iya miƙewa suka isa gate ɗin, cikin sa'a suna isowa sai ga motar Yaya Ammar na isowa. Ajiyar zuciya Nimrah ta sauke, dai-dai Mu'azz na fitowa daga motar, ya ƙaraso inda suke da sassarfa yana faɗin, “Lafiya kuwa? Miya sami Ruƙayyan?”. “Yaya ciwon mara, muyi sauri mu tafi kasan idan ya fara tsanani sai suma. Amma Yaya driver fa?”. Sai da ya buɗe musu suka shiga yake bata amsa yana reverse. “Baba driver accident yayi, yanzu haka ma yana asibiti”. “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, badai da su Aheel ba?”. “A'a bada su ba, shi kaɗai ne yaje ɗakko motar Ummie (Aunty Lailah suke cema Ummie, Shariffa Ammie) daga wajen wanki”. “Ya rabbi, ya jikin nasa?”. “Gaskiya yaji jiki sosai, dan har yanzu ma ba'a bari an gashi ba. Motar kuwa tama tashi aiki, dan babbar mota ce ta haye shi”. Gaba ɗaya jikin Nimrah ya ƙara sanyi, ita kanta Ruky dake fama da kanta hankalinta ya sake tashi, a haka suka iso gida ciwon marar ya ƙara tsanani, dole ma sai Mu'azz ɗaukarta yayi. Gaba ɗaya hankalin ƴan gidan a tashe yake da hanlin da baba driver ke a ciki, dan mazan gidan duk suna can. Ganin hanlin da Ruky ke ciki kuma duk sai suka maida hankali a kanta. Babu bata lokaci aka kira family doctor ɗin su, da yake ya san matsalarta yana zuwa allurai yay mata....

Basu sami ganin Baba Driver ba sai ranar Lahadi da yamma. Gaba ɗaya gidan suka shirya suka je suka duba shi. Yaji jiki kam kwari da gaske, amma Alhamdullah yana samun dukkan kulawar data dace. Ga matarsa an ɗakko tana jiyyarsa. Komai na asibitin Kuma su Yaya Ja'afar ne suka biya. Received at 6:57 PMSosai matar ke godiya akan yanda suka bama al'amarin mijinta muhimmanci, inda wasu ne ko'a jikinsu, ƙilama suce sai an biyasu motar miliyoyin kuɗin data tashi aiki. Amma su bata motar suke ba ta lafiyarsa sukeyi. Shima Baba Driver kallonsu kawai yake yana hawaye, dan baya iya magana har yanzu. Su duka sun ɗauka yana kuka ne kawai akan halin da yake ciki. Dan haka Mammah tai masa nasihar haƙuri da tawakkali akan ƙaddara. Kusan awar su ɗaya suka koma gida suna sake jimanta al'amarin. Satin baba driver biyu ya fara samun sauƙi, zuwa yanzu kuma Mu'azz ke jigilar kai su Nimrah makaranta da ɗakkosu kullum. A haka kwanakin tafiyar Mammah da Yaya Ammar suka cika zuwa Egypt ganin likita. A tare suka mata rakiya airport cike da kewa, dan Ruky da Nimrah harda kukan su. Ƙarshe Uncles ɗin nasu suka koma lallashinsu da tabbatar musu ai sati biyu kawai zatai ta dawo. Haka suka dawo gida. Tafiyar Mammah da Yaya Ammar da kwanaki biyar al'amarin karatun Mu'azz ya taso, dole su Yaya Ma'aruff suka fara batun neman driver, dan su basu da isasshen lokaci, wani lokacin ma da ƙyar suke ƙulla sati uku a ƙasar. Ammar yana fama da aikinsa, ga Bilal ma baya ƙasar, ko yana nan aikinsa shima ya ishesa, bazasu so kuma matansu kullum na gantalin kai yara makaranta da ɗakkosu ba, balle Biebah da bata da magana yanzu sai ta project ɗinta. Sunata tunanin ina zasu samu sabon driver mai amana kamar Baba amma sun rasa makama. Shawarar kota hanyar Baban za'abi Yaya Ma'aruff ya bayar, dan haka suka amince da hakan. Bayan sun taso kasuwa suka nufi gidansa dake can wani ƙaramin ƙauye, sai dai atanan yankin babban birnin yake. Sun sameshi jikinsa Alhamdullah, sai dai ƙafa data samu nakasa sosai har yanzu anata fama. Sun sake jajanta masa da ajiye masa alkairin da basa gajiyawa wajen yi masa sannan suka sanar masa abinda ya kawosu. Cewar suna son ya sama musu wani drivern mai amana kamar shi dan sun yarda da shi. Da farko shiru yayi idanunsa na cika da ƙwalla. Sai da Ja'afar ya ce, “Baba wannan ai ba abin kuka bane. Mun yarda da kai ne da amanar ka shiyyasa muka sake biyowa ta kanka, kuma in ma ALLAH ya baka lafiya muna maraba da dawowarka cikinmu”. Hawaye Baba ya share, “Na sani ku mutanen arziƙi ne masu tarin alkairi, har abada kuma bazan manta da tarayyata da ku ba. Amma mizai hana ku cigaba da kai yaran makaranta da kanku?”. “Baba bazai yiwu ba, kasan yanda uziriri sukai mana yawa dai, idan muka ce mune zamu kaisu za'aita samun matsala. Ga boko ga islamiyya, ga cefanen gida kai Mammah anguwa da iyalanmu”. Baba yay shiru zuciyarsa na kai-kawo, dan yasan bazasu fahimci mi yake nufi ba daman kai tsaye, shi kuma tsoro bazai barshi fitowa ya buɗe musu komai ba kai tsaye, sai kawai yace to su bashi lokaci zai kira a waya. Cikin gamsuwa sukai musu sallama suka tafi. Cikin damuwa matarsa ta ce, “Wai miyasa kake ta musu kwana-kwana malam? Mutanen nan mutanen kirki ne, banyi zaton zasu zo da damuwa kanada damar musu maganinta ka kasa ba”. “Ba kasawa nai ba Tabawa, kawai ina duba al'amarin ne dai kawai, kin san yanda rayuwa ta lalace yanzu ba kowa ke raɓarka da ƙyaƙyƙyawar zuciya ba. Ko ni ɗin ma alkairin su da hukuncin UBANGIJI ne ya sauya ni daga dalilin raɓarsu”. Cikin rashin fahimta ta ce, “Kamar ya? Ban gane ba malam!”. Murmushi kawai yayi bai sake cewa komai ba ya barta da wasi-wasi. Awa ɗaya ba'ayi da tafiyar su Yaya Ma'aruff ba Baba Driver yayi baƙo. Kasancewar matarsa tasan mutum ya saba zuwa wajensa bata kawo komai a ranta ba ta shiga ciki gida ayyukanta ta basu waje. Dan yana jiyyar a ɗakin soro ne... “Rabe! Kana ganin taurin kanka zai cigaba da baka nasara ko? Halin da kake ciki bai zame maka aya ba kenan?”. Murmurshi Baba Driver yayi mai ciwo, idanunsa cike da ƙwalla ya ce, “Ba darasi ne ban ɗauka ba Ari, ina tausayin bayin ALLAHn nan ne. Wlhy mutanen nan munanen kirki ne su da mahaifiyarsu. Sannan ya kamata mu yarda ba laifinsu bane akan abinda ya faru baya, shima kansa wanda ake son azabtar da su ta dalilinsa mufa sani rayukanmu ya jajirce wajen karewa, ALLAH ne ya ƙaddara za'a tarwatsa mu a ƙauyukanmu har mu watse irin haka. Hasalima mutanen nan dake munana shi a garemu sune silar faruwar komai akan waɗan can abubuw......” “Rabe! Kana nufin wuyanka yayi kaurin bijirema su Oga Dagger ko? Amma kasan minene hukuncin yin hakan a gareka ko? Karka manta kana cikin ƴantattun da aka bama damar zuwa su rayu a cikin mutane har suyi aure su hayyafa cikin ƴanci. Baku san wahala da azabar da mu dake cikin jeji kullum a ɓoye muke sha ba. Mutanen nan da kake ƙoƙarin karewa ance maka kaje kai musu wani abu ne? Information ɗin abinda ke gudana a rayuwarsu kawai akace ka dinga kawowa. Musamman ita wannan yarinyar Nimrah, amma taurin kai yasa ka zauna kana kawowa mutane ƙauli da ba'adi, gashi nan har sai da ka jama kanka zaman guri ɗaya, da da ƙarar kwana ma yanzu wani labarin ake ba naka ba. Ni dai yanzu ga saƙo, Oga Mole da Oga Dagger sunce gobe zasu turo sabon driver ka turashi ga mutanen nan ya maye gurbin ka, zaɓi ya rage naka kayi koka kuskure kai ne zakai kuka, dan a yanzu ba kai za'a hara ba ƴaƴanka ne ko matarka”... Yana gama faɗa ya miƙa batare da ya saurari magiya da roƙon Baba Driver ba.....

★>><<<<★>>>><<★ ★DUBAI★

Ganin yanda Nabeeha ke faman haɗa kaya ya bama Ismat data kawo mata breakfast har ɗaki tsoro. Duk yanda taso daurewa saita kasa. Cikin damuwa ta ajiye tray ɗin da take ɗauke da shi ta nufeta. Hannunta ta riƙe cikin rauni da damuwa ta ce, “Aunty wai mi kike yi haka ne? Ina zaki kike haɗa kaya?”. Hannun nata ta fisge, kukan da take faman riƙewa tun daren jiya saboda taurin zuciya a karo na farko ta fashe da shi..........✍️