
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 19
.....LAH helped her get the rest of the meatpie, it was not finished, she answered the two women and came back since they had their own water. She had to sit down and put on her hijab. Nimrah looked at her, then she touched what she put on her lap. It was Ruky's love that filled her heart again. Her eyes filled with tears and she said, "Thank you Sweetheart". Closely. Ruky just smiled at her. She went in wearing a hijab and was eating, even though it was a rule not to eat snacks in class. But as Sayyadi Kamal made up his mind about Nimrah, even though he understood what she was doing, he did not speak. That's how she finished the water stop and came out and concentrated on her studies. He finished and went out and another teacher came in. It was like that until it was time to get up. Today, Sambarka, Mammah's children did not fight with anyone. The thing she heard when they met the driver made her resist looking at him now until they reached home. She first went out and went inside. The hunger that she was feeling stole right past the kitchen and she told Kulu to cook noodles and one fried egg for her. Before she entered their room. Ruky was lying in bed breathing tiredly, so she d
19
.........Ana fitowa sallar azhar driver ya kawo musu abinci da ɗaukar su Aheel. Babu yanda Ruky bataiba suje su amso Nimrah taƙi, dan ita kam haka kawai ganin mutumin nan tayar mata da hankali yake ta rasa dalilin haka. Tana zaune a inda Ruky ta barta ta dawo ta sameta. Tana ma buɗe abincin ta sake ɓata fuska ganin minene a ciki. Dariya Ruky tayi, dan tasan Nimrah bata damu da doya ba sam. Harararta tayi kuwa, ƙarshe ta miƙe wai ita ta ƙoshi bazata ci ba. Sanin butsutsunta yasa Ruky bata takura mata ba, anan ma ta barta ita ta koma aji. Sai da taci iya abinda zata iya ta rufe sauran ta koma ajin itama. Sun cigaba da ɗaukar darasi, Nimrah nata mutsu-mutsun yunwa, gaba ɗaya sai Ruky ta damu, har cikin ranta taji haushin su Kulu da suka aiko musu da doya bayan sun san Nimrah bata ci. Jakarta ta ɗakko ta ciri kuɗi tare da miƙewa taje gaban sayyadinsu cikin ladabi ta sanar masa zata fitsari. Bai hanata ba dan hakan normal ne. Tana fita maimakon restroom sai ta wuce shop ɗin makaranta. ALLAH ya taimaketa ta samu sauran meatpie bai ƙare ba ta amso mata biyu ta dawo tunda suna da ruwansu. Sai da ta zauna sannan ta saka mata a hijjab. Kallonta Nimrah tayi, sai kuma ta tattaɓa abinda ta ajiye mata akan cinya. Wani irin ƙaunar Ruky ce ta sake cika mata zuciya. Idanunta cike da ƙwalla ta ce, “Thanks you Sweetheart”. A hankali. Murmushi kawai Ruky tai mata. Cikin hijjab ta shige tana ci, duk da kuwa hakan doka ne ba'a ciye-ciye a aji. Amma da yake Sayyadi Kamal nada wani ƙudiri a ransa game da Nimrah ɗin duk da ya fahimci abu take ci baiyi magana ba. Haka ta kammala tasha ruwa sannan ta fito itama ta maida hankalin ta a karatun. Ya kammala ya fita wani malamin ya shigo, haka dai har lokacin tashi yayi. Yau dai sambarka ƴan caskalen Mammah basuyi faɗa da kowa ba. Abinda take ji aduk sanda suka haɗu da driver yasa tai juriyar ƙin kallonsa a yanzu har suka isa gida. Ita ta fara fita ta shige ciki. Baƙar yunwar da take ji ya sata wucewa kai tsaye kitchen tace su Kulu su dafa mata noodles da ƙwai soyayye ɗaya. Kafin ta shige ɗakin su. Ruky na kwance a gado tana maida numfashin gajiya, dan haka ita bata zauna ba sai ta wuce bathroom kawai yin wanka. Kafin ta fito kuwa an kawo mata indomie ɗinta har Ruky na ƙoƙarin ɗanɗanawa. Doke mata hannu Nimrah tai tana ƙwacewa, Ruky ta lunƙuma wadda ta ɗiba a baki tana dariya da faɗin, “Shike nan ke in kina jin yunwa sai baƙar rowa”. Cike da jin haushi ta bata amsa da, “Ai sai na musu rashin mutunci yau a gidan nan, sun san bana cin doya sukayi, maimakon su dafa min wani abun”. Ta ƙare maganar da ƙwafa idanunta na cika da ƙwalla. Dan harga ALLAH taji haushi, sai dai bata san miya hasala zuciyarta ba kuma har kamar haka. Itama Ruky ta fahimci a hasale Nimrahn take dan haka batace komai ba ta wuce bayi tana murmushi...
Shaf-shaf suka kammala shirin zuwa gidan Aunty Mimi. Sunyi ƙyau cikin abaya iri ɗaya kalar brown da adon duwatsu masu haske. Daga Ruky har Nimrah akwai son kwalliyar tsiya. Ga iyayi kuma da ƴammatanci kamar ba ƙwailoli ba😝🏃🏼♀️. Koda yake sunce su ba ƙwaila bane ba😂, dan duk abinda cikakkiyar budurwa ke taƙamar da shi suna da. Fes suka fito abinsu, kai tsaye ɗakin Biebah suka shiga, itama dai ta shirya cikin nata gayun, sannin turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387 suka biyo ya sata ɗauke kwalbar tana ƴar hararsu. “Kai waɗan nan yara baƙwa mantuwa”. Dariya suka kwashe da ita a tare, Ruky ta ce, “Humm Small Mom ya zamu manta da wannan daddaɗan turaren, ai kafin a kawo mana namu muma sai su Ammy sun ɗiba mana komu sato”. “Ai dama kun saba ɓeraye”. Dariya suka sanya a tare nan ma. Ta daddagwala musu kowa ya shafa suna faman lumshe idanu. Dan ƙamshin turarrukan ba ƙaramin ratsa zukatan mai shaƙa suke ba. (Nima shaida ce masu karatu. Wlhy maza ku garzaya neman turarrukan SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Kaf turarrukanta babu na yarwa, nayi amfani da su na gani, koma nace ina kan yin amfani da su a yanzu haka. Tana kawo turarrukanta ne masu inganci da tsaftatacen ƙamshi. :Akwai Turare wuta da khumra kaloli har uku: black khumra, white khumra, brown khumra. Akwai oil perfume da kullacham ma, akwai Genine da Turare kabasa kaloli uku shima: white, black, and brown kai harma abinda ban lissafo ba. Dan tana saida kayan gyaran jiki suma na amare dama mata ƴan ƙwalisa uwargidaye masu san gyaran fata batare da kin ɓata skin ɗinki da mayukan bleaching ba. Karku ji komai ta gida ce tana nan zaune a garin Kaduna kuma tana aika kaya aduk inda kake harda kasashen ƙetare ma. Duk mai so kawai ya nemeta ta nan. Tana bada har sari ma fa masoya. +234 704 229 3387😌💃🏼🥰👍🏼). “Kai kuko wane kalar ƙamshi kukeyi haka? ya subahanallah”. Mu'azz ne mai maganar yana faman buɗe hanci. Dariya Ruky da Biebah sukayi, Nimrah kam da duk take jinta cikin rashin daɗin zuciya murmurshi kawai tayi. Ganin haka yasa Mu'azz kallonta, cike da kulawa ya ce, “Yaya dai Ninah? Ko baki da lafiya ne? Naga tunda muka baro makaranta baki da walwala”. Kai kawai ta girgiza masa alamar ba komai. Bata basu damar magana ba ta ce, “Ku muje ALLAH na ƙagara naje naga Baby”. Tana gama faɗa ta fice a falon gaba ɗaya. Duk da kallo suka bita suma fuskokinsu na nuna damuwar. Koda suka iskota a waje babu wanda yace komai, kasancewar Mu'azz ne zai jasu sai ta sauke ajiyar zuciya. Ita ta shiga gaba Ruky da Biebah na baya. Su Afrah dama suna can, dan daga makaranta can driver ya kaisu kai tsaye. Koda maigadi ya buɗe musu gate bata ganshi ba, dan haka ta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya. Suna ɗaukar titi kowa ya fara mata tambaya, saita wayance tace kewar Mammah ce. Duk sun gamsu, dan sun san Nimrah da Mammah sai ALLAH. Nimrah akwai ƙulagucin iyaye, dan haka tai bala'in sakin jiki da Mammah duk da har yanzu bata manta da Ummanta ba, sai dai bata iya tuna fuskarta sosai saboda ƙarancin shekaru na wancan lokacin. Tunda ta fara hankali da wayo cikin hikima Mammah ta koyar da ita yima mahaifanta addu'a kwanciyar kabari cikin aminci. Kulawa da take samu yasa bata jin maraici, ba kuma ta taɓa zaman yin kukan rashinsu ba sakamakon babu wani abu na labarinsu data sani ko take ji a yanzu balle ya tuna mata abubuwa a kansu. Garama Ummanta wasu ƴan abubuwan kan mata flash ɗin baya game da ita a cikin zuciya musamman idan Mammah ko su Aunty Ummi da zasu iya zama sa'annin Umman ita da Ammie (Aunty Hafsat mahaifiyar su Ruky kenan Matar Imran) takanji kamar Ummanta. Suna isowa tun Mu'azz bai gama kashe motar ba ta fita da gudu tai cikin gidan. Dariya kawai sukai mata. Aunty Biebah na addu'ar ALLAH ya cika musu burinsu na fitowar Dada sarari wataran Nimrah ta haifa musu Baby gudan jinin sa. Ita kanta bata san yanda zata misalta irin farin cikin da wannan ranar zatazo musu da shi ba balle Mammah....
“Oh ya ALLAHU ka shirya min Ninah jama'a ke da wa?”. Zama Nimrah tai kusa da Aunty Mommy dake rungume da Baby tana saka masa kaya an mata wanka tana murmushi, sai da ta shafa kan babyn sannan cikin shagwaɓa ta bama Aunty Momyn amsa. “Mum ba kowa fa, kawai ina gudu na fara ganin Baby ne. Jiya fa dan mugunta Ruky ina barci taƙi tada ni suka taho”. Aunty Mimi data kasa haƙuri ta ce, “Ai Dada zai sha fama a wajen nan dai kam. ALLAH yasa sanda zai dawo kinyi hankali Ninah”. “Mamy shi Dada ina ruwansa da hankalina koda ya dawo? Kuma ALLAH inada hankali”. Kasa haƙuri sukai kowa sai da ya dara. Ita kam ko'a jikinta tunda ta samu ta amshi Babyn gaisuwa ma sama-sama tai musu ta koma gefe. A haka su Biebah suka shigo niƙi-niƙi da kaya suna sanar da zuwan Daddy Imran. Dai-dai lokacin kuma Aunty Hafsat ta fito daga bedroom ɗin Aunty Mimi da alama salla tayi. Ai ko zaram Nimrah ta miƙe ta nufeta tana faɗin, “Ammie na dan ALLAH Babyn nan kalleta da ƙyau dawa take kama?”. Dariya Aunty Hafsat tayi ta ce, “Da ke. Sai dai ALLAH yasa kada tayo ƙiriniyar taku ke da hassanar ki”. Aunty Lailah dake fitowa a kitchen ita da Aunty Shariffa sai ƙanwar mijin Aunty Mimi ta ce, “A'a gara dai ta biyo komai da komai zaifi armashi Aunty”. Nan ma dariyar aka shiga yi, a haka Imran ya shigo ya samesu. Sai da ya zauna kowa ya gaisheshi cike da girmamawa sannan ya dubi Nimrah data ƙanƙame Baby bata da niyyar bayarwa. “Daughter baza'a bani Babyn bane?”. Murmushi tayi har haƙoranta na bayyana, sai kuma ta miƙe ta je gabansa tana faɗin.........✍️