Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 18

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 18

.....hearing in his throat, he said, "Oga, I have been accepted, but there is a real problem." "Is there a problem? Is the girl missing with them?". "She is here in the house. She has grown up to be a young woman. However, there is no sign that she has other parents besides them. It seems that what Goje once informed us that she was forgotten by her parents is true." "But this mother is truly evil. If she were still alive, she and her father would not be a small threat to us." "Even now she has slipped away from us, I don't know where I will understand Mother who I am until she gives us what we need and finally she comes back to me". "Don't worry, we have to go to the second stage, it's true. But let me talk to Oga and see what advice or plans he has for that. Since we should inform him personally that you are going to work now, don't have the kind of problem that Buba wants us to have. Are you sleeping at home now?" "No, I will not sleep here. The son of this Imran whom you despised is also his own illegitimate. Since he saw me, signs of anger appeared on his face. I must be careful with him. My son, I do not despise the enemy." "You are like me, it is the Oga who take Imran easy,

Standalone post1,653 words

18

.........Sai da sabon driver ya tabbatar su Nimrah sun gama shigewa sannan ya koma cikin mota. Wayarsa ya ciro daga aljihu ƙarama tecno, ya kashe ta ya cire murfin da batteryn ta. A mamakina rigarsa ya ɗan ɗaga ya zaro leda mara girma sosai, koda ya kwance ta tsumma ne fari ya fara bayyana da aka nannaɗe wani abu a ciki. Ya shiga warware tsumman sai ga ƙaramar bindiga ta bayyana, ƙaramar takardar dake tare da bindigar a nannaɗe itama ya ɗauka ya warware layukan waya da yawa suka bayyana. Ɗaya a ciki ya ɗauka ya saka a wayar ya maida batteryn ya kunnata. Kira yayi tare da kaita kunensa yana gyara zama. Ba'a wani jima ba aka ɗaga daga can. Kasancewar speaker ɗin wayar a buɗe take sosai yasa ake iya jin abinda nacan ke faɗa. Gaisuwa suka fara kafin nacan ya cigaba da faɗin. “Ai harna fara tunanin sakawa a bi bayanka Mole, naji har kwanaki uku babu wani bayani daga gareka. Ina fatan dai lafiya? Ka samu karɓuwar da muke so a gidan?”. Iska mai ƙarfi ya furzar cikin damuwa da ɗacin da yake ji a cikin maƙoshinsa ya furta, “Oga na samu ƙarɓuwa kam, sai dai akwai matsala gaskiya.” “Matsala kuma? Yarinyar bata tare da su ne?”. “Tana nan a gidan. Ta girma sosai ta zama budurwa. Sai dai babu wata alamar dake nuna tasan tana da wasu iyaye bayan su. Da alama abinda Goje ya taɓa sanar mana na an mantar da ita iyayenta gaskiya ne.” “Amma uwar nan tata muguwa ce gaskiya. Tabbas da ace tana raye har yanzu ba ƙaramin barazana zata zame mana ba ita da ubanta.” “Ai ko yanzu ta zame mana, dan ban san ta inda zan fahimtar da Uwa wanene ni ba har tai mana abinda muke buƙatar daga ƙarshe ta dawo hannuna”. “Karka damu dole mu tafi mataki na biyu ne kawai gaskiya. Amma ka bari zan yi magana da oga muji wace shawara ko shiri yake da shi akan hakan. Tunda dama ya kamata mu sanar da shi da kanka zakai aikin yanzu, dan kar a samu irin matsalar da Buba yaso bamu. Yanzu a gidan kake kwana?”. “A'a haba kaima kasan bazan kwana a nan ba. Dan wannan Imran ɗin da kuka raina shima shegen kansa ne. Tunda ya ganni alamun tsarguwa suka bayyana akan fuskarsa. Dole sai nayi taka tsantsan da shi. Dan ni kasan bana raina abokin gaba”. “Kamar ni kake, dama su Oga ne ke ɗaukar Imran mai sauƙi, sun kasa fahimtar irinsu sunfi illa fiye da shi wanda suka ɓoye ɗin da bai iya shanye abu. Amma ka barsu za'aje gaɓar da zasu gane shima ba abinda zasuyi wasa da shi bane. Kai kuma ka ƙara yin taka tsantsan”. “Ba damuwa sai na jika”. Daga haka sukai sallama ya sake kashe wayar ya cire layin ya maida shi inda yake tare da bindigar nan. Sannan ya tada motar yabar wajen.....

(Hummm wa kuke tunani wai?)

}}}}}}}}}{{{{{{{{{ ★PRISON★

Bai san fuskar ba, bai taɓa ganinta ba. Dan haka ya zubama vistor ɗin nashi jirkitattun idanunsa masu bulale abokan gaba koda bai tanka ba har na tsayin minti ɗaya. Tabbas ALLAH ya bama Dada basira mai ƙarfi, nutsuwa, dattako da sirrin iya aiki matsayin jami'in tsaro. Zakai matuƙan shan mamaki idan akace maka a wannan kalon na minti ɗaya kacal ya fahimci fuskar bogi ce a tare da mutumin, hakan na nufin yayi amfani da facemask wajen ɓoye ainahin fuskarsa. Wani murmushin da sam bai niyyasa bane ya suɓuce masa, murmushi daya saka vistor ɗin nashi murmusawa shima, duk da bai fahimci ma'anar murmurshin Dadan ɗin ba shi. Shiru ya sake biyo baya a cikin ɗakin batare da yunƙurin tankawar kowannensu ba na tsawon lokaci. Tamkar Dada na ƙirga lokutan zamansa a wajen ne, minti biyar na cika daga agogon ɗakin da suke ya miƙe tsam batare da yace komai ba ya juya zai bar wajen. “Bai kamata ka ƙosa haka da wuri ba, domin mu mutuwa ne, ana rayuwa da mu ne dole, tun daga ranar haihuwa”. Cak Dada ya tsaya a takunsa na uku, sai dai bai juyo ba bai kuma ce komai ba har tsahon minti guda cir. Kafin a hankali cike da ƙasaitarsa mai tafiya da nutsuwar masu izza ya juyo gaba ɗayansa. Idanun nan nasa masu kaifi da zafi ya zuba masa, kafin a bazata yay wani sakaran murmurshi mai cike da ma'anoni masu ƙarfi da ya nema tarwatsa zuciyar vistor ɗin a cikin ƙarjinsa. Ya lumshe idanu ya sake buɗewa a kansa. Sai kuma ya buɗe lips kaɗan, gira a sama ya amsa masa da. “Ni kuwa kaga anan sai banga siffofin kamala irin na mutuwa mai cika umarnin UBANGIJINA ba. Siffofin akuyoyin dake gudun tsiran neman mafaka a yayin da ruwan sama ya sauka kawai na gani a gabana”. Sosai fusata ta nuna a fuskarsa vistor ɗin, duk yanda yaso danne fusatarsa hakan na neman gagara. Idanunsa sun yi ja sosai har hannunsa na rawa sai da ya dunƙuleshi a cikin juna ya matse yatsun. Dada dake kallon hannun nasa ya kauda idanunsa yana murmurshi. Ai ko sai hakan ya sake hasalashi, a kausashe ya daki tebirin yana furta, “Mune akuyoyin kenan?”. “Amsa mai ƙyau”. Dada ya bashi amsa kai tsaye yana sake takowa ya dawo wajen. Duk da hannunsa akwai handcuffs cike da salon manya ya juya kujerar ya zauna ƙafa ɗaya kan ɗaya suna kallon juna ido cikin ido. Dai-dai lokacin masu tsaronsa suka shigo saboda bugun teburi da baƙo yayi. “Sir! are you all right?”. Kansa kawai ya jinjina musu batare da ya kallesu ba balle yin magana. “Okay”. Suka faɗa suna salute ɗinsa da ɗan kallon baƙon da ya gama kaiwa wuya suka fice. Sai kuma ga wasu sun sake shigowa niƙi-niƙi da kwalaye. Su kam gaisheshi sukai kawai tare da sanar masa oga ne ya aikosu da kayan zasuyi aiki a ɗakinsa. Kamar zai ce wani abu sai kuma yay shiru da basu dama da hannu suka wuce ɗakin nasa. Ya ɗan bi kwalayen da kallo. Har sai da baƙon nasa yay wata dariyar iskanci da izgili. A wulaƙance ya ce, “Karka ji ka damu fa, mun ƙara maka matsayi ne, dan bai ƙyautu ace lokacin da mutanenka ke ihu da kururuwa kai kunnenka baya ji ba, idanunka basa gani ba. Shiyyasa muka kawo maka gift ɗin da zai baka damar ji da gani kusa da kai gab...” Tsahon sakanni bashi da niyyar tankawa daga kalamansa, sai hakan ya bama vistor damar taɓe baki da sake faɗin, “Kana jin tsoron rasa rayuwa ne? Ko faɗa ka bada amsa ne kake jima fargaba?”. Da wani irin salon luuu Zak-Dada ya ɗago idanunsa yana kallonsa cike da izza da nutsuwarsa da ALLAH ya mallaka masa a kowane hali. Sai kuma ya ɗan matso kaɗan ya dafe duka hannayensa dake sanye da handcuffs a saman table ɗin, idanunsa ya sake ajiyewa kai tsaye cikin nasa tamkar zai soke ruhinsa da su. Da golden voice ɗin nan tasa mai razanasu ya furta, “Jarumin gaske sulƙen yaƙi da linzamin dokinsa ne kawai GUZIRINSA. Duk lokacin da kaji abokin faɗa ya zagaye kansa da MAKAMI ni Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi na faɗa maka tsoro ne ya saka shi”. “Tsoro!?”. Baƙo ya faɗa cike da son aro jarumta da ƙarfafa kai na dole. Sai kuma ya murmusa yana ɗan buga yatsunsa akan tebur. “Kana da yawan cika baki a magana. Amma ka sani mu ba da suna muke aiki ba. Idan suna ya bayyana, haske zai shigo. Idan haske ya shigo, tsarin ya lalace. Mu mune mazaunan ƙasa a ɓoye. Mu ne masu murɗa jijiyoyin gwamnati. Mu ne masu rubuta dokar da gwamnati ke karantawa.” Ya sake matsawa kusa kusa sosai. “Yau shekaru takwas kenan muna kallonka daga nesa. Kana tunanin wannan gadarar taka ce ta baka wannan filin? Ko har yanzu gurɓataccen tunaninka na cigaba da baka wancan ƙarfin ikon da kake gadara da shi a baya har yanzu yana da tasiri? Ka manta cewa ƙasar nan tun kafin ka yi tunanin kare ta, mun riga da mun shafe shekaru muna sarrafa zuciyar manyan da kake kira shugabannin cikinta. Kalli kanka mana, har yau baka ɗauki darasi daga ikonmu bane?. Mu muka bar ka a nan. Mu muka hana a kashe ka. Mu muka hana a sake buɗe shafin ka. Ba wai saboda kana da muhimmanci a garemu bane. A’a…” Ya yi kakkarfan numfashi yana wani murmushi, ya cigaba da faɗin, “…saboda muna son ka zauna ka kalli yadda ƙasar da ka ɓata shekarun ƙuruciyarka a kareta ta koma filin WASAN ƘWALLON ƙafarmu. Da jinin abokanka, zuri'arka, ƴan ƙasar taka zata zame mana mai danshin da zamu ji daɗin gudu a kanta. Kaɗan da zamu rage a cikinsu ka kalli yadda suke bauta mana. Ka kalli yadda za mu rusa duk tsarin da ka kare rayuwar taka a karewa. Ka bar gudanar da tunanin cewa kai ka san makircin ƙasa. Kai ɗan wasa ne a wani katafaren wasan da muka fara shekaru masu yawa da suka wuce tun kan haihuwarka, kaga hakan yayi kama dana masu TSORO?”. Ya ƙare dogon sharhin nashi yana gyara zama da jifan Dada da kallon raini yana wani dariyar iskanci da izgili. Sai dai maimakon yaga Dadan ya firgita ko nuna tsorata da matsanancin tashin hankali kamar yanda sukai tsammani sai yaga saɓanin hakan a bayyane. Domin kuwa da wata nutsuwa da baƙon bai taɓa gani ba, ya ɗaga kansa ya kalle shi da idanun da suka saba ganin bala’i ba tare da girgiza ba.........✍️

A gaya masa gaskiya ko a barshi da Dadan kai?. To bari dai mu gaya masa ko kaɗan ne 😂💃.

😝Kai kam baƙo duk wanda ya baka shawarar zuwa wajen nan ba sonka yake ba, yo ubanwa ke zuwa gaban zaki yay wasa ya kwashe kayan wasan salin alin ya koma gidansu yay barcin hutu.🥱. Amma dai bari muji amsar da MAZAN FAMA zasu baka🤣.

Barkanmu da dawowa, ya weekend?😎