
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 17
.....and Afrah ran to herself, lifted her up and turned her around, they were laughing that she was the son of her housemate. Aheel and Ruky, Biebah and Mu'azz were also there. Then the noise in the hall increased, the children greeted them and they all sat down and Ruky put food in front of everyone. Biebah then reprimanded them for their noise and they quieted down and everyone concentrated on their food. The pages were finished and they came out late. The new driver will be delivered today. The one they were making eye contact with today also fell in front of Nimrah, so she turned her head to the side and greeted him like how Biebah greets him. Dan is not a child. Next Mu'azz joined him with Abees and Aheel. She, Ruky and Biebah went behind, followed by Afrah and Ayyan. It was Mu'azz who kept showing him the way until they arrived. Their Islam is very big, including security. He parked at the right place and they all went out. Karaf made eye contact with Nimrah, how her body was raised and she mentioned hasbunalahu waniimal wakil in her mind. She quickly grabbed Afrah's hand and they left. He also turned his head away, turning his eyes on Mu'azz. "Son, should I go or wait for yo
.......Gaba Biebah tayi tana musu dariya, dan in dai halayen Twins ɗin gidan nasu ne tafi kowa sabawa. Suna sakkowa dining suka nufa, Mu'azz ne kawai zaune yana kari shima sanye da uniform ɗin islamiyyar. Cike da neman magana Ruky ta ce, “Su Yaya yau kuma da yunwa aka tashi?”. Harara ya wulla mata, batare daya tanka ba ya cigaba da danna doyarsa a baki. Nimrah tai dariya tana zama a kujerar kusa da shi. “Kaga rabu da ita Yayana. Kasan ita Ruky wani lokacin uwar gulma ce. Ina kwana”. “Ai ke da ita duk sammakal. Wannan saurin gaisuwar bana ALLAH bane faɗa min nawa kike so?”. Dariya Biebah da Ruky suka sanya. Cikin ɓata fuska da tura baki Nimrah ta ce, “Kai Yaya sai kace wata mayyar kuɗi, kai shike nan bazamuyi shirin arziƙi ba sai ina son kuɗi”. “A to nasan halinki ne ai Ninah”. Tashi tai a kusa da shi ta canja kujera, ya ce, “Oho dai”. Bata kula shi ba, dan dai-dai nan ma su Abees suka shigo da gudu suma sanye da irin uniform ɗinsu. Tuni Nimrah ta miƙe tana faɗin, “Oyoyo my Afry”. Ai ko da gudu Afrah tai kanta, ta ɗagata sama tana juyi da ita suna dariya dan ƴar gidanta ce. Su Aheel kuwa wajen Ruky da Biebah da Mu'azz sukayi suma. Nan fa surutun falon ya ƙaru, dan bayan yaran sun gaishesu suma duk zama sukai Ruky ta saka ma kowa abinci a gabansa. Sai da Biebah ta tsawatar ma surutun basu sannan sukai shiru kowa ya maida hankali ga abincinsa. Shaf-shaf suka kammala suka fito karsu makara. Yau sabon driver ɗin su ne zai kaisu. Wanda suna haɗa ido da shi yau ma gaban Nimrah ya faɗi, dan haka ta kauda kanta gefe tana gaishe shi kamar yanda su Biebah ke gaishe shi. Dan ba yaro bane. Gaba Mu'azz ya shiga shi da Abees da Aheel. Su kuma ita da Ruky da Biebah suka shiga baya, sai Afrah da Ayyan tare da su. Mu'azz ne ya dinga nuna masa hanya har suka iso. Islamiyyar su babba ce sosai, dan harda securitys. A inda ya dace yay parking duk suka fita. Karaf suka haɗa ido da Nimrah, yanda tsigar jikinta ta wani tashi sai da ta ambaci hasbunalahu wani'imal wakil a zuciyarta. Da sauri ta kama hannun Afrah suka bar wajen. Shima kansa ya kauda yana maida idanunsa kan Mu'azz. “Ɗana zan tafi ne ko zan jira ku anan har ku fito?”. “A'a Baba zaka koma gida, sai ƙarfe ɗaya kuma in sha ALLAHU sannan an tashi su Ayyan kazo ka ɗaukesu mu kuma ka taho mana da abinci, sai anyi la'asar kuma ka dawo ka ɗauke mu.” “To to ba damuwa ALLAH ya nuna mana”. “Amin ya rabbi, zadai ka gane hanya ko?”. “Sosai kuwa, karka damu zan gane. Ai na taɓa aiki tanan wajen sosai dan nayi taxi”. “Oh ALLAH sarki, shike nan sai an jima ɗin to baba”. Daga haka shima Mu'azz ɗin yabi bayan su Nimrah da tuni sun shige.....
}}}{{{{}}}}{{{{
“Alhamdulillah Sir! Yanzu kam komai ya kammala kenan, sai jiran umarnin fara campaign”. “Haka ne Imran, amma ni duk ma jikina yayi sanyi. Badan al'amarin Haysam ba banga abinda zai kai ni shiga siyasa ba. Dan siyasar ƙasar nan sirrikan cikinta basu da daɗin tonawa. ALLAH dai ya rufa mana asiri ya ƙara kare mana imaninmu”. “Amin ya rabbi Sir. Amma abubuwan dama ko ba'ace komai ba duk mai hankali yasan akwai ɗunbin kwamacala a ciki kam. ALLAH dai ya kare mana ku, ya azurtamu da shugabanni na gari.” “Iyakarta kenan kam. Mu dai ku cigaba da mana addu'a, ku dinga saka yara na mana.” “In sha ALLAHU Sir za'a ƙara dagewa, dama anayi a koda yaushe. Sir nace yanzu bazaka sake sama mana damar ganawa da Haysam ba. Wlhy ina cikin matsanancin matsin zuciya na kewarsa matuƙa. Shekara biyar ba kwana biyar ba”. Sosai tausayin Imran ya sake cika zuciyar Janar, dan har idanun Imran ɗin sun cika da ruwan hawaye. Cikin kwantar da murya ya ce, “Kayi haƙuri Imran, na san kai da zuri'ar Haysam da iyalinsa dole ne ku kasance cikin bege da kewarsa. Kuma hatta muma muna cikin wannan yanayin. Amma ina sha ALLAHU aski ne yazo gaban goshi, kasan kuma masu iya magana sunce daman yafi zafi. Dole ne mu cigaba da daurema zukatanmu, dan wannan gaɓar da muke da babban shiri a kansa tafi kowace gaɓa nauyi da haɗari, idan mutanen nan suka fahimci muna da wani shiri wlhy zasu iya kashe Haysam ta guba da hanyoyi masu sauƙi dan a yanzu sun fimu kusanci da shi. Mu cigaba da masa addu'a kamar yanda muka saba, tunda muna samu labari mai daɗi akan kasancewar sa cikin koshin lafiya daga yaron nan Captain Ibrahim, na yarda da yaron bazai kawo mana zancen daba haka yake ba, muma shaida ne tunda ya kawo mana wasiƙa da muka tabbatar daga Haysam take. In sha ALLAH ko ban samu mulkin nan ba a wannan karon zan ƙara ƙaimi Imran”. “Maganarka haka take Sir, kayi haƙuri nima kewa ce da damuwa harta sani faɗar hakan. ALLAH ya saka maka da alkairi ya bada ladan zuminci.” “Karka damu Imran, wlhy har cikin zuciyata nake jinku kai da Haysam da Haydar, dan naji matuƙar daɗin aiki da ku fiye da yanda kuke tunani. Shiyyasa nake jinku tamkar ƙannena da muka fito uwa ɗaya uba ɗaya. Zan iya bada rayuwata akan ganin Haysam ya fita, dan ya yimin abubuwa da bazasu ƙirgu ba. Sau biyu Haysam na tarar harsashi a wajen bani garkuwa, kuma duka biyun a jikinsa suka ƙare har yay jiyya. Taya zan manta da irin wannan ƙanin a duniyata in dai ina numfashi.” Hawaye Imran ya share yana ɗan murmurshi, ya ce, “Ka cancanci fiye da haka a wajenmu Sir. ALLAH dai ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, ya kuma cika burin alkairi”. Sun cigaba da hira da duk ta shafi batun Dada da siyasa. Kafin Imran yay masa sallama ya fito. Da yake cikin ɓadda kama yake maimakon gida sai ya ɗauki hanyar kasuwa, dan jiya Mimi ke sanar masa haihuwar ta, yanzu haka ma ya bari Aunty Hafsat zata je can barka. Wani shago ya fara shiga, sai da ya tabbatar babu mai bin bayansa daga gidan Janar sannan ya fito ya nufi babban shagon su Ma'aruff da yafi kowane shago girma da cikar kaya a kasuwar. Dan kuwa ƙaton waje ne da zaka iya samu abubuwa da yawa da duk ya shafi kwalliyar jiki. Ɓangare-ɓangare ne, akwai atamfofi, abayas, lesuka, shadda, materials, kayan yara tun daga kan jarirai har zuwa samari. English wears na mata dana maza, mayafai. Kai duk wani abinda ya shafi sutura ta maza da mata, yara da manya akwai ta. Sai bangaren kayan kwalliya, akwatina, cosmetics komai har zinari suna sayarwa. Kai shagon nan dai sai Alhmdllh, dan ko yara masu aiki sunfi ashirin a ciki. Suko manyan gwasake na office abinsu. Ga camaras tako ina da suke kallon shiga da fitar kowa daga ofisoshin nasu... A tare ma ya taddasu a office ɗin Ja'afar, dan sakatariyansu batama yi yunƙurin fara zuwa neman masa izinin shiga ba sanin wanene shi a wajensu. Sai ma gaisheshi data shiga yi cike da girmamawa. Ya amsa mata a taƙaice yana wucewarsa yay knocking direct, sannan yay sallama ya shiga. Cike da farin cikin ganinsa da girmamawa suke masa barka da zuwa. Ma'aruff ya ajiye kofin tea ɗin hannunsa da yake sha yana miƙewa ya gyara masa kujera, dan basuyi breakfast a gida ba saboda sun makara aka haɗa musu suka taho da shi. “Cin abinci a office sai kace tuzurai?”. Imran ya faɗa cike da tsokana. Dariya sukayi a tare. Ja'afar ya ce, “Yaya makara mukayi wlhy, kasan kuma twiny da wutar ciki ya azalzalan dole muka taho da shi. A haɗo shayi ko coffee ko kunu?”. “Haba sai kace wani ku, sai da Auntynku ta cika min ciki na fito nikam. Bani ruwa mara sanyi kawai it's okay”. Ja'afar na dariya ya kawo masa ruwan, da kansa ya zuba masa a kofi sannan ya zauna suna gaishe shi a tare. Da kulawa ya amsa musu, da faɗin, “Gobe su Mammah zasu dawo ko?”. “In sha ALLAHU Yaya, wlhy duk kewarta ta ishemu gidan ba daɗi. Autocinta ma duk sunyi sanyi ko ƙiriniyar basa yi da ƙyau kwana biyu”. “Ai ni kaina kewar tata nake. Jiya da safe dana leƙa gidan duk sai yay min wani iri. Dan itama Ammah ta maƙale a ƙauye taƙi ta dawo Abbah nata ƙorafi”. Received at 2:05 PMReactions Cikin dariya har suna haɗa baki wajen faɗin, “Ai jiya da muka je da daddare yanata faɗa, wai yau tunda safe zai aika driver a ɗakkota, shi ya gaji su Mabruka nata bashi kwamacalar abinci, tuwon ma jiƙaƙƙe suke masa”. Yanzu kam dariya suke harda Imran. Dan rikicin Abba sai Hajjo ke iya masa. Itama idan ya rikice mata wani lokacin sai ta haɗa shi da Mammah da yake ɗauka tamkar babbar ƴarsa ake samun lafiya. Sun cigaba da hirarsu har suka gangaro kan batun Bilal da shima dai watan gobe zai dawo gida in sha ALLAHU. Sai magana auren Biebah data dage ita bazatai aure ba sai Dada ya fito, in ba haka ba ita da aure har abada. Imran da yasan ga shirin da suke yace su barta kawai in sha ALLAHU komai zai warware. Bai bari shagon ba sai bayan sallar azhar. Ya haɗo shopping na kayan babys da turamen atamfa har akwati biyu aka kai masa mota. Gida ya wuce kai tsaye, zaije ya ɗan samu ya huta bayan la'asar sai ya leƙa gidan Mimi yaga baby dan dama siyayyar duka tata ce......✍️