
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 16
..... you see the bottom of something beautiful that she is looking at. Just then, Ruky opened the servant's door and came out, tied with a towel as a sign of bathing. Seeing how Nimrah was choosing to kiss her mouth, she moved closer to her and allowed the dew of the water to follow her white skin. Nimrahn picked her up quickly as if she was scared, then Ruky giggled. In anger, she reached out to wipe the water and asked her, "You shameless girl, why did you give me water?". Ruky was still laughing and said, "I see, you are fighting to rob me like an advertising girl, are you still struggling to look at the picture of the baby?". "Humm, don't you understand, Ruky ALLAH, babies are so beautiful, I love a baby so much, why do you see all the people who have given birth to Ammie and I'm blocking them in their department. Even if I get married, every year I'll keep giving birth." "Kambu, Ninah, but you are not smart, what about every year?". "Yes wlhy, you're a couple too". Sitting next to her, Ruky had oil in her hand and said, "Oh my God. When you talk about having a baby, you remind me of Sayyadi Kamal. Hmmm, oh my God, it's really like the way our classmates are gossiping about yo
16
..........“Yana lafiya shima Alhamdullah. Kai fa ina fatan dai ƙanwata ta koma ko ka sake sabon aure?”. Kansa ya ɗan shafa yana murmurshi, sai kuma ya ce, “Ta koma bayan taga na koma da kuɗin gidan nan, dan har mun sake haihuwar yara biyu ma. Amma ta rasu shekara kusan bakwai data wuce. Sai yaran yanzu kawai.” ya ƙare maganar idanunsa na tara ƙwalla. A take tausayinsa ya sake kamata. Ta shiga jajantawa da masa ta'aziyya. Shima Ammar yay masa ta'azziya. Dan har yanzu bai san ainahin wanene shi ba, tunda sanda wacan abun ya faru suna yara sosai musamman shi da Mimi ma da basu wuce shida zuwa bakwai ba maybe, sai dai ya fahimci ɗan uwan Mammah ne na jini koda kamanni da yanayin tattaunawar tasu. Cikin share sabbin hawaye Tasi'u yake amsa musu. Mammah dai ta babbashi haƙuri daga haka ta koma jansa da hira harya saki jiki shima yana jan Ammar a jikinsa......
%><%><%><%><%>
Kwance take a madaidaicin gadon ɗakin daya kasance guda biyu iri ɗaya hannunta da waya tanata faman zabga murmushi, kai da gani kasan wani abu dake ƙayatar da ita take kallo. Dai-dai nan Ruky ta buɗe ƙofar bayinsu ta fito, ɗaure take da towel alamar wanka tayo, ganin yanda Nimrah ke zabga uban murmurshi bakinta har kunne yasa ta matsawa kusa da ita ta yarfa mata raɓar ruwankan dake ta bin farar fatarta. Ɗagowa Nimrahn tai da sauri irin na firgita, dan haka Ruky ta ƙyalƙyale da dariya. Cikin harara ta kai hannu ya goge ruwan data yarfo mata ɗin ta ce, “Ƴar wulaƙanci miye na yarfa min ruwa?”. Ruky na ƴar dariyarta har yanzu ta ce, “Gani nai kinata faman washe baki kamar ƴar tallar makilin, wai har yanzu hoton jaririyar kike faman kallo?”. “Humm bazaki gane ba Ruky ALLAH jarirai nada ƙyan kallo, ina son jariri sosai, shiyyasa kike ganin duk sanda su Ammie suka haihu nake tarewa a sashensu. Ke nifa ko aure nayi duk shekara zan dinga hauhuwa”. “Kambu, Ninah amma baki da hankali, duk shekara fa?”. “Eh wlhy, ke ni ƴan bibbiyu ma”. Zama kusa da ita Ruky tai da mai a hannu ta ce, “To ALLAH ya baki. Ni sai da kikai maganar haihuwa ma kika tuna min da sayyadi Kamal. Hummm bawan ALLAHn nan fa da gaske kamar yanda ƴan ajinmu ke gulma ya mutu a kanki Ninah, idan yana karatu hankalinsa duk a kanki. Ga kuma Teacher Khalil, yanda ya wani dage yana karemu randa muka suburbuɗi Hibba Abubakar na sake tabbatar da zancen Maimoon Qasim fa”. Baki Nimrah ta taɓe tana gyara zama. “Ruky rabani da wannan shashancin kinji, ni wlhy duk basu min ba.” “Kai Ninah kiji tsoron ALLAH, wlhy duk ɗinsu sun haɗu, dama dai kawai kice ba yanzu ba ne sai na yarda, dan mukace mun kawo samari yanzu ai ƙaniyarmu Uncle's zasu ci, musamman Uncle Bilal da akoda yaushe yake mana gargaɗin nan. Amma ALLAH nidai ina son soyayya, kinga idan naga Seniors ɗin mu na lobewar nan da boyfriends ɗinsu, ko mazan da ƴan mate ɗin mu sai naji kamar na bama Anwar ko Uncle Haneef ɗin gidan Mamy dama”. “Lallai Ruky baki da hankali, yo ALLAH na tuba ko soyayya zanyi mi zan wani yi da ƴan tamatsitsin yaran school ɗin mu. Yo yaushe suma aka gama aikarsu kiran yayunsu gida. To ALLAH bari kiji, ko dariya naga kimma wannan Anwar ɗin sai na ci masa mutunci. Karki maida mu marasa aji mana, ƴan yara da su inama laifin kamar Yaya Ammar haka. Amma kosu Teacher Khalil nawa suke”. “Hhhh shegiya Ninah, wato marasa aji? To yaushe ma muka gama tafasar balle mu ƙone har kike batun wani aji. Shekara sha biyar fa muke. Ga aunty Biebah nan harta kammala master ɗinta bata ma zancen aure, ta dage sai Dada ya dawo gida zatai aure. Hakama Aunty Ma'u dake ƙoƙarin kammala Secondary ita da Aunty Halimatu, balle azo kammu haihuwar jiya inji Yaya Mu'azz. Da kike kiran su Teacher Khalil yara kuma, ai bana jin Yaya Ammar zai girmesa. In baki so kamarsu ba tsoho kike so kamar su Daddy ko mi?”. “Ƴar wulaƙanci, kamar su Daddy kuma? Kamar shekarun Uncle Ammar dai, amma kamar su Daddy ai da kunya ƴar soyayyar nan bazaka samu ka bajeta ba, kin san kuma nifa ina son harkar nan ta love ba wasa” tai maganar tana kashema Ruky ido ɗaya, bata jira cewar ta ba ta cigaba da faɗin, “Ya Mu'azz kam bar ɗan rainin hankali, shima sai kace ba haihuwar jiyan ba. Ya gama mana rashin m ɗinsa dai sai mun riga shi aure. Dan mu yanzu idan Daddy yace rana ɗaya za'a haɗa auren da Small Mom da su Aunty Ma'u mune next. Shifa, sai ya jira Uncle Bilal, Uncle Ammar da Yaya Khalifa ma ƙila, to ko Yaya Imam ya girmesa. “A'a wlhy kar ki masa baki, duka shekara nawa Yaya Khalifa ɗin ya bashi, sai dai ayi musu tare, gara Yaya Imam to, kuma shima tare suke tafi a school ai”. Cike da dariyar mugunta Nimrah ta ce, “Oho dai, ko haka ɗin mun more masa. Ke muyi gulma mana. Dan ALLAH baki ga wai kamar Uncle Bilal da Aunty Ma'u akwai wata a ƙasa bane?”. “Humm wlhy na gani, ranar graduation ɗin su Small Mom sai wani kallon ƙasan ido yake mata.” dariya suka kwashe da ita harda tafawa. Nimrah ta ce, “Wlhy soyayya tayi Besty, idan ban samu ɗan soyayya ba na rako mata duniya”. Cikin dariya Ruky tace, “Muna son soyayya zaki ce, ai duk wanda yazo sai mun tantance shi walle karki damu, love ai duniya ce”. “A wlhy love duniya ce, shiyyasa nake son maƙalewa a sashen su Mamy, dan in ana bajakoli su da su Uncle's nasha kallona”. “Muguwa, wlhy Ninah kiji tsoron ALLAH, tun baki tafasa ba zaki ƙone. ALLAH yasa su ganoki suci ƙaniyarki, kinga sai ai miki auren ai”. “Shegiya ni da ke ai duk sammakal ne, zatace ta tadda muje mu”. Dariya suka sake fashewa da ita suna tafawa..... Buɗe ƙofar ɗakin nasu ya saka su yin shiru, sai kuma duk suka rufe bakunan nasu da hannu. Biebah ta hararesu. “Anya kuna duba agogo kuwa? Kuke mana irin wannan ihun dariyar haka kamar sabbin kammu”. “Kai Mom ALLAH hira ce kawai tai daɗi”. “Kuma da ihu haka? Na sake jin wannan dariyar kamar ba mata ba sai na ɓata muku rai. Dalla ku bani wayata kuyi shirin barci ku kwanta” tana gama faɗa ta amshi wayar tata da Nimrah ke kallon hoton baby, Dan su basu da waya Uncles nasu sunce ba yanzu ba. Juyawa tai ta fita tana mai rufe musu ƙofar. Gwalo sukai ma bayanta a tare, kafin Nimrah ta miƙe zuwa bayin itama dan yin wanka. Bata wani jima ba ta fito, lokacin har Ruky ta gama nata shirin barcin ta haye gadonta, dan kowa da nashi. Ƙasa-ƙasa suka cigaba da hirar a haka kuma duk ta sanari har Nimrah ta shirya itama ta haye nata gadon.
WASHE GARI da wuri suka ta shi, babban burinsu tafiya gidan Aunty Mimi ganin baby musamman ma Nimrah da jiya ba'aje da ita ba. Dan tana barci su Aunty Shariffa suka wuce da Ruky, sai yau Biebah tace zasu je tare tunda itama bataje ba taje Tahafiz, amma tace mata yau ma sai sunje sun dawo daga Tahafiz suma sannan. Rashin sabon barcin safe saboda makaranta yasa suna kammala salla sukai bitar karatun Alkur'ani dan sun san yau sayyadinsu zai amshi hadda sukai azkar kowa ya miƙe. Ruky ta fara gyara ɗakinsu ita kuma Ninah ta wuce gyaran ɗakin Biebah. Koda ta shiga ɗakin Biebah harta sauka ƙasa taya masu aiki haɗa breakfast ita kuma. Sun kammala gyara ɗakuna har bedroom ɗin Mammah duk da bata nan basa gajiya da gyarawa sannan suka shiga wanka. Dama bedrooms suke gyarawa da sama ɗakin su Yaya Ammar, sauran wajaje kuma masu aiki. Shirin sukai cikin uniform ɗin islamiyya su ash color na wando da hijjab har ƙasa tsahon hijjab ɗin yasa da yawansu basa yin rigar suke saka t-shirt a ciki. Fitowarsu dai-dai da fitowar Biebah daga nata ɗakin tana wani kalar sassanyan ƙamshin turare. Su duka kasa haƙuri sukai sai da suka tanka. “Woow Small Mom kin sayi sabon turare ne? Wlhy wani ƙamshin bala'i mai kassara jiki”. Murmushi tayi tana ɗan girgiza kanta. “Yan biyun Mammah kenan iyayen iyayi ƴammatan gobe. To wannan ƙamshin da kuke ji ba turaren kanti bane, haɗaɗen turaren gida ne dan khumra ce ma kawai na ɗan shafa sai kabasa da nayi a kaya na, nima a sashen Aunty Lailah na samoshi.