Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 20

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 20

..... the country owes her strength without knowing the reason. After all, that was easy for him even though he thought she was married. He knows where she is and how he is giving money to her mother, even though that is nothing to him, he already wishes for her life, so he told her how she would behave and how she would manage it. Now he is in Garmany, his business case, Hajiya Hasiba sent him the message of Nabeeha's bill, he saw that his mind was raised, he immediately called all the landing and take-off companies, so Nabeeha's chance to leave the country was closed. But even so, his mind went to bed that night and he returned to Dubai. He went straight to their house and luckily found Nabeeha sitting in the living room with her head on her knees and crying. He sits next to her and touches her with his hand and she jumps up, she pours out the water of misery to him and he just stares at her and he just looks at her... Su Ismat who is pretending to be happy. Only in this way will she achieve her dream of owning Jaafar. Full of hypocrisy, Amima pressured Hajiya Hasiba to call their mother and come to town within a week.....

Standalone post1,562 words

20

.......“Daddy ai kaine za'a baka. Amma minti biyar zatayi ka sake bani. ALLAH ji nake kamar kada na ajiyeta fa. Daddy dan ALLAH na dawo nan da zama har ayi suna?”. “To Nimrah in kin dawo makarantar fa?”. “ALLAH Daddy in ta dawo nima sai na dawo”. Ruky ta faɗa itama. Cikin girgiza kai yace, “Ai bama zan bari ku dawo ɗin ba. Daga yau ba zaku sake zuwa ba sai ranar suna.” Zasu fara magiya ya ce, “Okay nace Mammah tai zamanta kada ta dawo goben kenan?”. Ai tuni suka saki batun dawowa gidan suka fara murna jin Mammah zata dawo. Abin zai birgeka har su Auntys ɗin farin ciki suke yi. Shi dai Imran yay ma Baby addu'a sosai ya ɗan zauna suka taɓa hira sannan ya miƙe zai tafi. Dole Aunty Hafsat ta miƙe suka wuce tare. Su kuwa sai anyi sallar magriba sannan koma isha'i....

>>>><<<<★★>>>><<<< ★DUBAI★

Cikin zafin rai take magana kuma da harshen turanci. Shi ko yayi sabale yana kallonta dan komai tayi birgeshi take. Shi kaɗai yasan irin wutar masifar sha'awarta da yake ji tsahon shekaru. Ya kuma kasa binta ta ƙarfi batare da yasan dalili ba. Bayan kuma hakan abu ne mai sauƙi a garesa duk da kuwa yasan tana da aure. Yasan inda wata ce ba ita ba yanda yake narkama uwarta kuɗi duk da hakan ba komai bane a garesa da tuni ya mata fata-fata ta yanda ko rayuwarta sai ya ce ga yanda zatayi sannan zata gudanar da ita. Yanzu haka yana ƙasar Garmany ne harka business ɗinsa Hajiya Hasiba ta tura masa saƙon kudirin Nabeeha, yana gani hankalinsa ya tashi, a take ya kira duk wani Companyn sauka da tashin jirage yasa aka rufe damar Nabeeha na barin ƙasar. Amma duk da haka hankalinsa yaƙi kwanciya a daren ya baro ya dawo dubai ɗin. Kai tsaye gidan nasu yayo, cikin sa'a kuma ya sami Nabeeha a falo zaune ta haɗa kai da gwiwa tana kuka. Zama yay kusa da ita da kai hannu zai taɓata ta zabura, shine take zazzaga masa ruwan masifa data sakashi zuba mata ido kawai yana kallonta... Su Ismat dake laɓe farin ciki ya kamata, dan itama wlhy ta tsani guy ɗin nan, dan bata da wani burin daya wuce Nabeeha ta koma ɗakin aurenta. Ta haka ne kawai itama zata samu cikar nata burin na mallakar Ja'afar. Cike da munafunci Amima ta dannama Hajiya Hasiba kira da mahaifiyarsu data shigo gari tun cikin satin daya gabata. Aiko cikin mintinan ƙalilan suka iso dan duk suna kusa da gida ne dama. Wata tsawa Hajiya Hasiba ta dakama Nabeeha. Cikin zafin rai ta ɗaga hannu zata mareta caraf Adeel ya riƙe hannun. Cike da gadara ya ce, “Karma ki fara dan ina ganin mutuncinki na haihuwarta da kikayi, amma da a maimakon riƙe hannun nan naki sai dai ki jisa a ƙasa yana lilo”. Maimakon jin zafin abinda yay mata murmushi Hajiya Hasiba tayi daga ita har ƙanwarta Mamawo. Cike da girmamawa suka shiga faɗin, “ALLAH ya huci zuciyar babba ɗan manya jinin alkairi. Nayi kuskure ayi haƙuri raina ne ya ɓaci. Taya zata zauna tana gaya maka irin wannan shirmen..” “Karki damu ta isa ne ai, girmanta ne. Ni zan koma kawai, amma zan dawo anjima anan zanyi dinner”. “An gama ranka ya daɗe”. Hajiya Hasiba ta faɗa cike da girmamawa. Yayinda Mamawo ke wani shegen murmushi tana binsa da wani kallo zuciyarta cike da abubuwa. Amma a zahiri baka isa karantar abinda ke ranta ba dan cikakkiyar ƴar bariki ce data iya takunta. Yana ficewa suka koma yima Nabeeha faɗa da nuna mata karfa ta dawo tana dana sani da wannan damar da ALLAH ya bata. Wai miye akai akayi wani Haysam can da bata da tabbacin yana ma raye ko an jima da kashe shi ne. Kuka ta saka musu cike da bori da rashin kunya tabar wajen. Dole sukai shiru bayan duk sun ja tsaki. Bayanta itama Ismat tabi zuciyarta na zafi. Koda ta shiga ɗakin taga Nabeeha ta kwanta tana kuka zaman lallashinta tayi, ganin taƙi yin shiru ta ɗauka wayarta a karo na farko ta danna kiran Jiddah, abinda sai ta jima batayi ba saboda duk haushinta suke ji akan gaskiya da take gaya musu. Batai zaton zata ɗaga mata ba ma, amma sai gashi ta ɗaga cikin tsaftatacciyar sallama. Da ɗan rawar murya Ismat ta amsa mata, sai kuma ta fara gaisheta. Ɗan jimmm Jiddah tayi kafin ta amsa tana kallon Abban su dan taje barka gidan Aunty Mimi ne shine ta biyo gidan gaishe su. Kukan da Ismat ɗin ta fashe da shi ne ya saka Jiddah faɗin, “Ismat lafiya kuwa? Ko wani ne ya rasu?”. “Aunty babu wanda ya rasu, kawai abubuwa ne suka mana yawa. Mom ta takura dole sai Aunty Nabeeha ta kashe aurenta ta auri wannan mayen mutumin. Jiya mukai shirin gudowa kawai ta sace passport ɗinmu ta ɓoye. Yau kuma sai gashi yazo. Aunty ki taimakemu ki sanar da Abba yazo ya tafi damu. Wlhy gida muke son dawowa, aunty Nabeeha na son komawa gidan mijinta”. Jiddah dake jin jikinta ma na rawa ta ɗan saci kallon Abbansu. Ai ko yayi kicin-kicin da fuska yama maida hankalinsa a television inda ake hira da ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyar SGP, wato tsohon janar ɗin soja kuma ɗan majalisan tarayya mai ci Janar Yusuf Shu'aibu Tafida. Yawu masu kauri ta haɗe, cikin damuwa ta maida kallonta ga Hajiya Zuwaira da suke kira Ummu a gidan. Idan ka cire Nabeeha da Ismat da har yanzu basa ko gaisheta. Kai Ummu ɗin ta girgiza mata alamar ta kwantar da hankalinta, dan taji komai itama kasancewar hansfree ta saka wayar. Cikin dauriya Jiddah ta ce, “Wannan shi nake nuna muku tun farko amma kuka kasa ganewa Ismat daga ke har Aunty Nabeeha. Yanzu dan ALLAH yaushe rabonku da kiran wani a cikinmu har Abban, aƙalla shekara uku kenan fa. Ni kuma kun saka ni a black list kona nemeku bata shiga harta WhatsApp. Ni yanzu a wannan gaɓar mizan iya yi, wane tabbaci ne dani akan baku biye ma Momy ɗin ba akan ƙudirinta.....” “Wlhy aunty bamu taɓa aikata wani abu saɓanin abinda kike tunani ba mu kammu balle Aunty Nabeeha”. Duk da Jiddah bata da tabbaci sai da ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, duk da tasan wacece mahaifiyarsu akan son duniya babu abinda bazata aikata ba. Itafa ko uwarmi zasuyi suyi ba ruwanta tunma suna ƙananunsu indai kuɗi zai shigo fine. Hawayen da suka cika mata ido ta haɗiye, ta ce. “Shike nan Ismat ki bani zuwa gobe, yanzu haka ma bana gida naje barkar Aunty Mimi ne data haihu. Amma zan yi magana da Abban”. “To aunty dan ALLAH ki taimaka mana, ke kaɗai ce hope ɗinmu a yanzu wlhy”. “Karki damu in sha ALLAH duk yanda muke zan taɓoki, ni dai fatana ku cigaba da riƙe mutuncinku kada ku biyema Mom”. “In sha ALLAHU Aunty ki mana addu'a”. “Ita nake muku kullum”. Daga haka ta sauke wayar. Tun kafin ma tai magana Uncle Nasiru ya dakatar da ita da faɗin, “Tashi ki wuce gida dare yayi? ALLAH ya bamu alheri”. Yanzu kam sosai idonta ya tara hawayen, ta waiwaya tana kallon Ummu. Kai ta jinjina mata alamar taje, tabar komai a hannunta kawai. Sai kawai ta miƙe tai musu sallama ta fita. Dama ita ta tuƙo kanta. Aiko tana shiga motar ta kife kanta a sitiyari kawai ya fashe da kuka. Ta jima tana kuka har sai da maigadi yazo yana mata knocking glass sannan ta haƙura ta share hawayenta taima motar key......

<%>°<%>°<%> PRISON

Wani zuba masa kaifafan idanunsa yay a hankali, tare da sakin wani murmushi mai zafi da izza, mai tabbatar da cikakken izgili da raini fiye da nashi. Dan a ƙarshe da wani salo irin na maida mutum banza sakarai Dada ya taɓe baki. Sannan cikin son tunzurawa ya ɗan karkatar da kansa, fuskar sa ta cika da izza mai nutsuwa. Like yana magana da wani shasha can ya furta, “Tofa! kaga fa kana ƙoƙarin bani mamaki.” Ya yi murmushi mai ɗan kaifi, ba na farin ciki ba, na jarumin da ya saba da iya riƙe nauyin abu a zuciya da ƙwaƙwalwa batare daya bari abokin gaba ya fahimci lagonsa ba. Cikin halin ko in kula ya cigaba da da ɗin, “Ka zo nan kana min barazana da dorinar ƙarya, ka ce ku ne ƙasa, ku ne haske, ku ne gwamnati. Amma duk da wannan ƙarfin ikon naku kuma kuka zaɓi ɓoye fuska kamar masu tsoron haske a gaban ZAKIN dake ɓoye cikin keji?. Gaskiya ban yarda da wannan ƙarfin ikon naku mai kama dana ƴan wasan kwaikwayo ba, ya kamata ku koma ku canja shiri.” Ya ɗan sake matsawa gaban tebirin sosai yana sassauta murya kamar mai son yin raɗa idanunsa na sake shiga cikin na baƙon, sai dai muryar tasa ta cika da nauyin, da ƙarfi irin na masu izzar ƙarfin zuciya da jarumtar ƙwarai dake jinsu ko a ɗaure su ba masu risinawa wawaye bane. “Ɗan aike!. Ka manta da abu ɗaya.” Shiru ya mamaye ɗakin. Baƙon ya tsaya tamkar an dasa shi a wajen yana kallon Zak-Shadow da jin ƙaguwar son barin wajen dan wani irin firgitashi al'amarinsa keyi, dauriya kawai yake da dannewa saboda sanin akwai camara a jikinsa dake ɗaukar komai. Kai tsaye kuma duk abinda suke tattaunawa ƴan ƙungiya ma na kallonsu........✍️