Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 15

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 15

.....continue to strengthen the bones and muscles and the other strength is not less for him, the son in this very room he is in, he conducts his worship and exercises in his own style. The lack of stress in the heart, has protected him from modern diseases such as high blood pressure, not to mention the heart disease that the enemies are hoping for in their every move. He already believes that the LORD is the owner of everything and everyone, if you are blessed by him, the opposite is from the devil or your behavior or trials that will raise your value to another level in this world or the hereafter. He believes that's why stress is the last thing he can say he's doing. Every time he remembers his family, especially a brave mother like Mammah, he prays to her hoping to find peace of mind from the stress of his situation. Also, his brothers who look at him as the father and his wife confirm that his love is strong in her heart. Even his daughter-in-law is still in his heart, and he prays for her and hopes for a successful life today and tomorrow, but from her to Nabeeha, he is waiting for a time when it will be easier for them to go and rebuild their new life. He did not decide to

Standalone post1,760 words

15

........Shi ma'abocin ibada ne da ƙoƙarin ganin ya kiyaye dokokin UBANGIJI da kusantuwa da shi a lokacin da yake rayuwa kamar kowa. A yanzu daya ɓuya bisa faifan ƙaddararsa da jarabawa da makircin masu makirci hakan bai sauya komai ba. Sai himma da dagiya da hakan ya ƙara masa wajen sake kaɗaice UBANGIJI da bauta. Halin da yake ciki bai taɓa sakawa yaji kasawace ko tauyewa daga UBANGIJIN SA ba. Bai kuma taɓa jin nasara ce ga azzalumai ba. Bai taɓa mantawa da ƙasar da talakawan ƙasar ba. Yanda yakema kansa addu'a da zuri'arsa haka yake addu'a ga ƙasa baki ɗaya. Tabbas a siffa ta jikin ƙarfi da ALLAH ya bashi zuwa yanzu ya risina, sakamakon canjawar tsarin abincinsa zuwa zaɓin wanda ake ciyar da shi a yanzu. Shiyyasa ya zaɓi ɗaukar matakin yin azumi yau, gobe ya huta, azumi ibada ce mai girma, sannan kariya ce daga jarabawar ɗan adamtaka ta lafiya da halittun jiki da UBANGIJI ya ni'imata mu da su musamman akan abokan rayuwa. Nauyin jiki da raunanuwar ƙarfi bai sa ya gaza wajen ƙoƙarin cigaba da ƙarfafa ƙashi da tsoka da sauran ƙarfin daya rage masa ba, dan a cikin wannan nan dai tsukun ɗakin da yake ciki yakan gudanar da ibadarsa ya kuma motsa jiki da salo-salo irin nashi. Rashin ƙarfafa damuwa a zuciya, ya bashi kariya daga cututtukan zamani irin su hawan jini balle ciwon zuciyar da maƙiya ke fatar masa a kowane motsinsu. Ya riga ya amince UBANGIJI shine mai komai da kowa, idan kunga alkairi daga gareshi ne, saɓanin hakan daga shaiɗan ne ko halayenku ko jarabawar da zata sake ɗaukaka darajar ku zuwa wani mataki na duniya ko lahira. Yayi imani da hakan shiyyasa damuwa ta kasance abu na ƙarshe da zai iya cewa yana yi. A duk sanda ya tuna da ahalinsa musamman jajirtacciyar uwa irin Mammah, yakan mata addu'a da fatan samun nutsuwar zuciya daga shiga damuwar halin da yake a ciki. Hakama ƴan uwansa da suke masa kallon uban da matarsa daya tabbatar soyayyarsa mai ƙarfi ce a zuciyarta. Hatta ƴar amanarsa tana nan zaune daram a zuciyarsa, yana kuma mata addu'a da fatan rayuwa mai nasarori a yau da gobenta, sai dai daga ita har Nabeeha yana jiran wani lokaci ne da zai sawwaƙe musu suje suma su sake gina sabuwar rayuwar su. Bai yanke hukuncin fita a wannan wajen ba, dan bashi da wani tabbacin fitar. Sai dai yana fatan aikin daya ɓuya domin yinsa da hana Imran shiga cikin tarnaƙin su tabbata. Dan in har ALLAH ya bashi tsohon rayuwa a kurkukun nan, akwai matsayin da Imran zai kai a gidan soji da zai sa babu wanda ya isa hanashi zuwa ziyartarsa a-kai-a-kai. Idan kuma har UBANGIJI ya bashi damar cika shekarun da suka ɗiba masan ya tabbatar lokacin da zai fita koda bashi da ƙarfin jiki dana aiki, yana da zuciyar bin waɗan can azzaluman ɗaya bayan ɗaya ya hukunta su da hannunsa. Balle ma ko a yanzu ya gama shirya in har yay wasu shekaru a wajen nan sai ya nema hanyar dinga fita yana aiki yana dawowa koda a ƙarshe zai bayyana kansa a ƙarasa yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai koma kashe shi kai tsaye.... Motsin buɗe ƙofar da akai ya saka tunaninsa katsewa, dan yana duk wannan tunanin ne tare da push-up daya sabama kansa yi sama da ɗaruruwa a kowane rana koda yana azumi. Dan haka har yanzu jikinsa a bubbuɗe yake sai dai raguwar ginanniyar tsoka da bata samun sinadarin da take buƙata kamar baya. Daga yanda yake push-up ɗin kawai ya ɗan ɗago idanunsa ya kalla yaran sojin guda biyu ya janye yana cigaba da abinsa. Suma sake nutsuwa duk sukayi, dan su sun san badan zaki na keji ba basu isa ziyartar ko gefen dajin da yake farauta ba. A tare suka ƙame tare da yin salute ɗinsa, kafin na gefen damarsa ya furta, “Sir kana da vistor ne”. Cak ya ɗan tsaya na sakan, sai kuma ya cigaba da abinda yake batare da yace da su komai ba. Fin mintuna uku, dan har sai da ya cika adadin da yake buƙata kafin ya tashi da ƙyau tamkar ba shi ya gama push-up ɗin ba yaja ƙaramin towel dake jikin ƙarfen gadon kusa da sallaya ya fara goge hannunsa zuwa wuyansa. Sanye yake cikin uniform ɗin prison ɗin, amma hakan bai hana su kasancewa fes ba alamar baya barinsu da datti, sai dai sun koɗe sosai alamar tsufa da gajiya. A karo na farko ya furta, “Tsawon shekaru biyar kenan a tsarin jadawalin da doka ta sharɗanta a kaina No visitors, no communication. Miya canja hakan a yau daga dokar?”. Sake duƙar da kawuna sukai, kafin ɗayan yay magana cike da girmamawa. “Sir muma bamu sani ba. Umarni kawai aka bamu na zuwa da shi inda kake”. Idanu ya zuba musu sosai su duka biyun. Wani ɗan murmurshin gefen baki da shi kaɗai yasan yayi kayansa yayi. Ya ajiye towel ɗin a kan ƙarfen gadon ya taka a nutsensa cike kuma da tafiyar nan tasa ta nutsuwa, dattako zuwa gabansu bayan ya saka slippers a ƙafarsa. “Ku aikata aikin soja, Captains. Na fahimta.” A tare suka sara masa, zukatansu na sake jin rauni, ƙaunarsa da girmamawa. “Sir… I’m sorry.” Suka sake faɗa a tare. Bai ce da su komai ba face miƙa musu hannayesa duk biyu. Dan doka ce fita da shi sai da handcuffs. Jikin sojan har ɗan rawa-rawa yake a ƙoƙarin ɗaura masa handcuffs ɗin, haka dai ya gama suka koma gefe suka bashi hanya. Shine ya fara fita sannan suka bi bayansa har ɗakin ganawar. Vistor ɗin nasa ya juya baya, dan haka bai fahimci ko wanene ba sai da ya zauna a kujerar da aka tanada domin shi.....

<<<>>><<<>>> ★EGYPT★

“Mammah dan ALLAH ki daina kukan nan ya isa haka”. Ammar ya faɗa cikin tashin hankali muryarsa na rawa idanunsa shima cike da hawaye. Sai kuma ya dubi mutumin da shima ke sharar hawaye ya ce, “Bawan ALLAH ka min bayani dan ALLAH. Minene alaƙarka da Mammah ta? Ku taimaka ku sanar min kada zuciyata ta fashe, dan kukan Mammah ba ƙaramin azabtarwa bace mai ƙuna a zuciyata”. Hawaye mutumin ya sake sharewa da handkachiff harda ɗan fyatar majina. Kafin ya kalla Ammar cikin rawar muryar alamun tahowar wani sabon kukan ya ce, “Ɗana ka kwantar da hankalinka, duk da ban san wanne a cikin ƴaƴan nawa ba ina ji a raina ko Bilalu ko Abdul-rasheed (Ammar) ne kai. Dan kune dai ƙananu da zan iya gani a wannan shekarun ba Haysam ko su Ja'afar da Ma'aruff ba”. Kafin Ammar yay magana cikin zafi Mammah ta ce, “Har kana iya cigaba da riƙe zuri'ata a cikin ƙwaƙwalwarka amma ka gagara waiwayen inda nake Tasi'u....?” “Wlhy Adda A'isha kunya ce ta hanani, tsananin kunyarki nake ji da tsoro da nadamar son zuciyata. Ina ganin bazaki sake kallo na ba a rayuwarki, bazaki sake son ji koda daga wani ne kina da ɗan uwa irina ba. Adda A'isha ni azzalumi ne butulu da ban cancanci gafara daga gareki ba balle marigayi Yaya Abdul-rasheed, dan kuwa mun kasance butulu da ga ni har Bashir da danginsa......” “Bashir bai kasance butulu a gareni ba, dan kuwa na tabbatar idan shine a raye komai girman laifin da yake ganin ya min bazai ɓoyema ganina a tsaho waɗan nan shekarun ba. Haba Tasi'u, kun maida ni mara kowa a duniya, mara gata, mara dangi gaba ɗaya. Badan Yaya Nasiru ba da nace ban san daɗin zuri'a ba a duniya. Da ƴaƴan Kawu kamar sun waiwayemu munata zumunci har bikin su Haysam duk dasu a kayi suma yanzu sun sake ɗauke min wuta gaba ɗaya saboda ƙaddarar rayuwa da muka sake shiga. Shike nan kowa ya juya bayansa a garemu dangina dana Abdul-rasheed idan ka cire Jamilu da su Khadijah saboda kawai sune ciki ɗaya da Abdul-rasheed. Wlhy idan kowa zai barni banyi tunanin harda kai ba da muke ciki ɗaya Tasi'u, kada ka manta nice na fita a cikin Inna ka kwanta, sannan nice na gama sha daga jikinta ka amsa. Miyasa zaka gujeni tsawon shekaru ashirin da shida, a talatin kaɗan ne babu rabona da kai fa Tasi'u. Miyasa? Miyasa haka?”. “Wlhy kunya ce kamar yanda na sanar miki Adda, dan ALLAH ki yafeni ki gafarce ni na tuba”. Yay maganar yana sauka ƙasa ya durƙusa a gabanta tare da riƙe ƙafafunta duk da kuwa shekarun dattijantaka sun bayyana a gare shi shima. Bata hanashi ba, sai kuka da take itama. Ga Ammar dake rungume da ita shima tuni kukan yake, dan a duniya basa ƙaumar ganin hawaye Dada da Mammah na ɗiga. Tsohon lokaci suna a haka kafin Mammah ta fara tsagaita nata kukan ta kama dattijon tana miƙarwa da faɗin, “Shike nan ya isa. Na yafe maka ka share hawayenka. ALLAH ya yafe mana gaba ɗaya. Ya jiƙan Inna da Baba da Abdul-rasheed da Bashir. Amma dan ALLAH karka sake yin nesa da ni kaji”. Tashi yay ya koma kan kujerar yana share hawayen nasa da faɗin, “In sha ALLAHU har abada bazan sake nesa dake ba Adda, na baya ma kunya ce da nadama ta sakani dole. Amma wlhy a kullum cikin begen son ganinki nake keda zuri'arki”. “ALLAH ya rufa mana asiri”. Mammah ta faɗa tana shafa kan Ammar alamar lallashi. Ɗakin ya sake ɗaukar shiru na wasu mintuna kafin ta kallesa ta ce, “Mi kake yi a Egypt? Ko nan kake aiki?”. “A'a nazo ganin likita ne kawai. Yanzu ina Paris. Sai dai kusan shekara ma biyar kenan na koma ƙasarmu, kawai dai ina zaune a kudanci ne sakamakon tsoro da fargabar tunkarar ki. Murmurshi Mammah tayi mai ƙayatarwa da faɗin, “Ja'iri ashe kana shakkata?”. “Adda wlhy ina yi dan kece madadin Inna a wajena. Ya bayan rabuwa ya iyalai?”. “To sai godiyar ALLAH, Iyalai kuma duk gasu nan sun girma sun zama magidanta. Duk da dai Bilal da Ammar da Biebah basu kai da yin aure ba. Amma Alhamdullah duk komai ya dai-daita babu abinda zamuce da UBANGIJI sai godiya”. “Alhamdullahi naji daɗi sosai wlhy Adda. Kice yanzu gida ya cika da ƴan jikoki na”. “A ya cika kam. Dan a ƙalla yanzu kana da jika goma sha bakwai zuwa sha tara nan gaba kaɗan, dan yanzu haka yau ɗin nan Mimi ma ta sake haihuwa ta huɗu. Matan Ma'aruff da Ja'afar ma duk suna da ciki a yanzu haka na uku-uku duk da ƙarami ne.” “Kai Masha ALLAH lallai zuri'a ta haɗu. Ina yaron kirki Haysam?”. Shiru Mammah tayi na sakanni, sai kuma tai murmurshi gajere da faɗin..........✍️