
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 14
.....yeah. When she put it on he threw his hands and went to the door which was knocked again. He stepped back a little while greeting her. "Dad, stop teasing me son of GOD. Where are you today?". The owner smiled and said, "You are great, Hajiya. The stranger came and said that the new driver was sent by Malam Buba, the old driver." She said, "Okay, let me tell Yaya Mu'azz, Uncle's are not here. Ammie and Ummie have also gone to Mom's house (Aunty Mimi they call Mom) to give birth." With a smile on his face, he said, "Allah, the king, may God live and bless what has been achieved." "Amen, Rabbi". She said as she closed the door and turned inside. "How is it that he is a new driver, and Father Driver has pushed him". Mu'azz was looking at her, then he turned his head to the television and said, "Oh, it's good to be here. GOD has limited your transportation. You always bother me with your noises and troubles. Prepare some food and take it to him while I'm eating. I finished and went out to say hello." Received When she filled her mouth with air, she went to the kitchen and said, "Why are my legs hurting today? Momma is not here, so I am having a hard time. Today, since we came back
<<>>✿<<>>✿<<
“Assalamu alaikum”. Aka kwaɗa sallama daga bakin ƙofar falon bayan anyi knocking har sau biyu. Ƙaramin tsaki Mu'azz dake zaune shi kaɗai a falon yana cin abinci yaja, ya tsani tashi yana cin abinci, dan yana tashin shike nan abincin ya fita a kansa kuma. Hanyar kitchen ya kalla inda yake jiyo surutun Nimrah da dariyar Biebah. Sai kawai ya ɗaga murya ya ce, “Ninah!”. Daga can ta ce, “Kai Yaya Mu'azz miye kuma dan ALLAH? Bana kawo maka harda ruwa ba”. “To uwar son jiki, dalla fito kiga waye ana knocking ne”. Baki a sama ta fito, tana sanye cikin shirt da riga na lass milk da furanni coffee. Tayi ƙyau sosai daka ganta kaga ƴammatan zamani masu shegen iyayi da rawar kai. Harta nufi ƙofa ya ce, “Haka zaki fita ba hijjab?”. Baki ta ƙara turawa gaba, ta dawo ta ɗauka hijjab da sukan ajiye a falon saboda irin haka, dan Mammah ta saba musu sakawa musamman idan akai baƙon ido ko suka saka ƙananun kaya, wani lokacin ma sai taga kamar anfi takura mata da sakawa fiye da Ruky da Aunty Biebah. Sai da ta saka ta zura hannayensa sannan ta nufi ƙofar da aka sake bugawar, sallamar maigadi ta amsa tana buɗe ƙofar. Ya ɗan ja baya yana gaisheta. “Baba ni dai ka daina rissina min dan ALLAH. Ina wuni?”. Murmurshi maigadin yayi da faɗin, “Ai girmanki ne Hajiya. Dama baƙone yazo yace kuma sabon driver ne Malam Buba tsohon Driver ya aikosa”. Ɗan jimm tayi sai kuma ta ce, “Okay to bari na sanarma Yaya Mu'azz, dan su Uncle's duk basa nan. Ammie da Ummie ma sun tafi gidan Mom (Aunty Mimi suke kira Mom) data haihu ɗazun”. Fuska ɗauke da murmushi ya ce, “ALLAH sarki ALLAH ya raya, ya albarkaci abinda aka samu”. “Amin ya rabbi”. Ta faɗa tana rufe ƙofar ta juya ciki. “Yaya wai sabon driver ne, kuma Baba Driver ya turoshi”. Ɗagowa Mu'azz yay yana kallonta, sai kuma ya maida kansa ga television yana faɗin, “Oh to sannunsa da zuwa. ALLAH ya iyakance min jigilarku kullum kuna damuna da surutun ku da fitina. Ki haɗa abinci ki kai masa dan abinci nake ci sai na kammala na fita mu gaisa”. Received Sai da ta cika baki da iska cikin ƙunƙuni ta nufi kitchen tana faɗin, “Ni wlhy yau ƙafafuna duk ciwo suke, dan anga Mammah bata nan sai wahala ake bani, yau tunda muka dawo school ban huta ba komai ni....” Fiiiffgg! Filon kukera da Mu'azz ya jiho ya sameta a baya. Tako dage ta ƙwalla ƙarar data saka Biebah fitowa daga kitchen da gudu tana tambayar lafiya da riƙo Nimrah ɗin. Kai Mu'azz ya girgiza cike da takaici yana nuna fillon daya jefeta da shi. “Small Mom fillo fa kawai na jefa mata dan tana min ƙunƙuni shine take wannan ihun. Wlhy Ninah kiji tsoron ALLAH. Wai uwar wa ma ya hanaki bin su Ammie ne kamar yanda Ruƙayya tayi?”. “ALLAH sai na gayaka da Uncle, kuma ai dai naji zafi. Tunda na dawo kaketa sani aiki, na maka gyaran ɗaki, kace na maka ɗan wake, duk baka gani ba sai da ka ci zalina”. “Oh gori kike min saboda kin min gyaran ɗaki da ɗan wake? Lallai ma Ninah ni ko”. Kai Biebah ta girgiza da jan ƙaramin tsaki ta koma ciki tana faɗin, “Kudai bazaku taɓa canjawa ba ALLAH ya shirye ku. Ba sai ku cinye kanku ba jarababbu. Wlhy na ƙagara Mammah ta dawo gidan dan kun isheni”..........✍️