
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 13
…..at the bottom. Ammar quickly followed him and tried to help him by saying again, "I'm sorry sir". The man's face and his reply said, "Don't worry my son, it's my fault that I'm not paying attention to the documents, that's why I didn't notice your arrival. Mom, be patient..." He couldn't finish because he just raised his eyes to look at where Mammah was standing. Dan also handed him the data sheet she was sitting on the other side to speak at that time, then she paused and looked at him. Even if she is a thousand years old, she will never forget this face in her world, not to mention those who are less than thirty years old. Hearing that they were silent, Ammar turned around and looked at them. Mammah started to look at the man with her mouth open, and quickly turned to look at him as well. He quickly pulled back, rolling his eyes and saying, "O rabbi! Who is Mammah?". Mammah's head was completely dim and she couldn't say anything, except for her hand that was dancing until Ammar approached and held his body, except when his eyes were on the man who showed signs that he also had squat hair.
★EGYPT ★
“Mammah muje ki huta yau kam kin gaji fiye da kullum. Ga su Yaya Ma'aruff nata kira nasan burunsu kawai suji yanda results ɗin suke ne. Aunty Ummi ma naga ta kira video call ta WhatsApp”. Received Murmushi Mammah tayi, cikin sauke ajiyar zuciya ta ce, “Ammar yarana duk sunyi kewata ne, nima ina tsananin jin kewarsu. Dan haka ni kam ba sai sati biyun nan ya cika ba zuwa jibi tunda sunce babu wata damuwa suna bamu maganin nan kawai mu koma gida”. “Duk yanda kike so haka za'ai Mammah”. Yay maganar yana ɗan rungumota ta gefe, dama kuma suna tafiyar ne hannunta riƙe a nashi. A yanda ya ɗan rungumetan yana dariya itama yana murmurshi da kai masa rankwashi a kai yasa basa kallon gabansu balle mai tahowa. Karaf kuwa sukaci karo da wani abun da ya saka Mammah faɗin, “Subahanallahi”. Shima sai Ammar ɗin ya sake ta yana waiwayawa da ambaton, “Ya salam”. A dai-dai lokacin shima wanda sukai karon ya ambaci, “Subahanallahi” ɗin yana kaiwa duƙe da son riƙo takardun hannunsa da suka tarwatse a ƙasa. Cikin sauri Ammar ya bishi shima yana ƙoƙarin taimaka masa da sake faɗin, “I'm sorry sir”. Fuskar mutum da murmurshi ya ce, “Karka damu ɗana, nima harda nawa laifin hankalina nakan takardun ne shiyysa ban lura da tahowarku ba. Mama kiyi haƙuri kem......” Ya kasa ƙarasawa saboda dai-dai ya ɗago ne zai kalla inda Mammah ɗin take sukai ido biyu. Dan itama ta miƙo masa takardar data ɗakko ne datai gefe zatai magana a lokacin, sai ta dakata cak tana kallonsa. Ko shekara dubu tayi bazata manta wannan fuskar ba a duniyarta, balle shekarun da basu wuce talatin ba. Jin sunyi shiru Ammar daya gama tattarowa shima ya juyo yana kallon su, Mammah ya fara kallo datai tsaye ƙyam baki buɗe tana kallon mutum, da sauri ya maida kallonsa kansa shima. Ai da sauri ya wani ja baya yana waro idanu waje da faɗin, “Ya rabbi! Mammah waye shi?”. Mammah da gaba ɗaya kanta yay wani dimmm ta gagara cewa komai, sai hannunta dake ƴar rawa har sai da Ammar ya matso ya riƙota jikinsa, sai dai har lokacin idanun nasa akan mutumin da alamu ya nuna shima dai yayi sumar tsugunne ne......