Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 29

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 29

.....which only STRUGGLING MEN can face when they can see the LIGHT OF THE TRUE ONES...... ÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷ ★ONE WEEK LATER★ It has been a week since the announcement of the election results. The general and the fathers of his family and the common people who voted for him enjoyed various celebrations. If you remove the other followers, the other parties are frustrated and sad about the lack of success. But what we poor people who are in this situation do not understand. Those big ones who want to have already tied the General are happy to win. It is only in the media that they criticize and express their displeasure. Even though there are many of them in their hearts, they are unhappy, but they are suffering because in that case, the government should have given them, since the opportunity is the same in my life, in reality it is different. At the time of the fight for happiness for the new president, general Yusuf, it is not like that. Even though he did not reach the Government House, the work was done underground with Daddy Imran and Haydar Galadima (Faro). Today, General Tafida has finished his meeting with the transition committee and the meeting that since the election

Standalone post1,422 words

29

..........“Wow! Congratulations, Her Excellency General Yusuf Tafida.” Dada bai motsa ba. Bai yi murmushi ba. Bai yi mamaki ba. Sai dai zuciyarsa ta furta abu guda ɗaya dai-dai da lumshewar idanunsa a hankali (Wata rana gaskiya za ta dawo da kanta. In dai har zuciya bata manta da UBANGIJI da masu gaskiyar ba) sai kuma a hankali ya ajiye Alkur'anin ya zame zuwa sujuda. Ya jima kafin ya ɗago ya sake ɗaga hannu yana ambaton, “Subahanal-lah! Allahu-akbar!”. Akan tausasan laɓɓansa Bai ce ya damu da samuwar shugabancin Janar Tafida domin ya fita anan ba, amma tabbas ya damu da addu'ar ƙasar nan tasamu mai kishin ƙasa kamar Janar da yakema ƙyaƙyƙyawan fata akowane motsinsa, ta samu shugaba mafi alkairi, yana ji kuma a ransa ogansa kuma yaya koma uba shine zaɓin ALLAHn da suke fata da roƙa in sha ALLAHU. Sake juyawa yay yana kallon tvn a karo na biyu, dan duk da sanarwar dare ce wasu wajajen har al'umma sun fara bikin murna, sauke numfashi mai nauyi yayi, zuciyarsa tana ƙonewa irin ƙonawar da MAZAN FAMA kawai ke iya fuskanta a lokacin da suke iya hango HASKEN MASU GASKIYA......

÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷ ★ONE WEEK LATER★

Sati guda kenan da bayyana sakamakon zaɓe. Janar da ubannin gidansa dama talakawan ƙasa da suka zaɓesa sun sha shagulgulan biki tako wane ɓangare. Idan ka cire sauran mabiya sauran jam'iyyu dake cikin takaici da baƙin cikin rashin samun nasara. Sai dai abinda mu talakawa da muke a wannan yanayin basu fahimta ba. Su waɗan can manyan da suke so tuni sun ƙulle da Janar ɗin anata farin cikin samun nasara. Sai a kafafen media ne kawai suke suka da nuna rashin jin daɗi. Duk da kuwa da yawansu har cikin zuciyarsu suna jin rashin daɗin, amma suna shanyewa saboda a hakan ma dai da ai dasu za'aci gwamnatin tunda dama duk tafiyar ɗaya ce a baɗini, a zahiri ne ake daban-daban. A lokacin da nan ake faman bidirin farin ciki ga sabon shugaban ƙasa janar Yusuf ba haka bane ba. Duk da bai kai ga tarewa a gidan Gwamnati ba aikin suke ta ƙarƙashin ƙasa shi da Daddy Imran da Haydar Galadima (Faro). Dan a yanzu haka a yau Janar Tafida ya gama ganawa da kwamitin miƙa mulki da sukai zaman meeting da tunda aka ci zaɓen nan shi suketa zamanyi saboda tsare-tsare musamman ƴan jam'iyya da kowa ke ganin lokacin fanshe wahalarsa tayi za'a bashi muƙamin da yake buƙata. Suna fitowa daga meeting ɗin aka ɗaukeshi zuwa gida. Tun ma kan ya ƙarasa shigewa falon sashensa ta baya kasancewar gidan bashi cike yake da dangi sati guda kenan ya ciro wayarsa a aljihu ya fara neman layin Daddy Imran. Bugu biyu Imran ya ɗaga, dan a lokacin shima suna tare da Faro ne a wani guesthouse ɗinsa da in har zasuyi magana akan Dada can suke zuwa. A nutse Daddy Imran yay sallama tare da gaishe da Janar. Daga nan ya amsa masa sai dai Daddy Imran baya jinsa sosai sakamakon matsalar rashin network da kowa ya sani ƙasar na fuskanta. Hakan ne yasa Janar ɗin faɗin, “Ka na ji Imran?”. “I’m here, Sir.” “Yauwa ina fatan kun kammala dukkan abinda muke buƙata?”. “Yes sir! Yanzu haka ma ina tare da Haydar anan guesthouse ɗina. Ga komai daya dace a hannunmu ko abu guda bana tunanin mun bari yayi saura. Hatta da sabbin bayanai akan Ojo Dabo ya zo da su a daren jiya, sune kawai nake ganin zanyi ƙoƙarin tabbatarwa dan nima akwai wasu a hannuna”. “Babu lokaci Imran, inaga ku ajiye sabbin bayanan Ojo yanzu a hannunku, muyi amfani da tsoffin dake wajenka zasu wadatar. Dan wannan aikin shine farko da nake son na gabatar a ƙarƙashin mulkina a ranar dana taka ƙafata a gidan gwamnati in sha ALLAHU washe gari sake nazarin shari’ar Haysam Abdul-rasheed Shehu zai tabbata. Babu wani aiki da zan gabatar na tabbatar da godiyata ga ALLAH sai in fara da wannan. Dan haka ku kasance cikin shiri kawai”. Daga can Daddy Imran ya runtse ido yana sakin wani wadataccen murmushi mai faɗi da armashi, dan yana jin kamar an buɗe wata ƙofa da ta rufe a zuciyarsa da ƙwaƙwalwa a shekaru takwas da suka gabata, ƙofar dawowa, ƙofar adalci, ƙofar fansa. Cike da wata irin muryar shauƙi ya furta, “Sir! Umarninka kawai muke jira a wannan gaɓar”. Murmushi mai faɗi shima Janar ya saki, tare da faɗin, “Imran… ka shirya abinda na tambaye ka?”. “Na shirya Ranka ya daɗe. Na dawo da kowace takarda, kowace sanarwa, kwafe-kwafen shari’a, rahotanni, bincike, duk wani abu na shekaru takwas ya kammala a cikin kundi guda ɗaya. Kundin da saka hannunka kawai yake buƙata da umarni yayewar baƙin labulen daya rufe min gani da jin Zak-Shadow. KIƊA A RUWA MAI TADA HANKALIN DODONNI.” “Good Imran. Lokaci ya yi da zan sa hannu wajen dawo da gaskiya. Lokaci yayi da The two shadows zasu sake bayyana a inuwa ɗaya. Amma…” ya ɗan yi shiru, sai kuma ya cigaba da faɗin “......ba za mu je tare da kararrawa ba.” Daddy Imran ya fahimta. Aikin da aka basu ba na kan titi ba ne. Yana cikin inuwa, cikin sirri kamar yadda azzalumai ke yin wasan su. Tamkar yana a gaban Janar ya ƙame jikinsa waje guda irin aƙidar sojoji da girmamawarsu, sannan ya sara masa da Salute na girmamawa mai harsuna da yawa har Janar na iya jin ƙarar bugawar ƙafafunsu shi da Faro da shima ya miƙe ya ƙame. A tare suka furta, “Yes, Sir. I'll handle it quietly”. Daga can shima Salute ɗinsu Janar yayi yana wani shegen murmushi mai matuƙar bayyana tsantsar makamancin farin cikin da yake a cikin zuciyarsa. Daga haka ya yanke wayar. Ba ajiyeta yayi ba, sake lalubo wata number yayi. Lambobi ne da ba kowa ke da su ba, lambobin da suka tsaya tsayin shekaru biyu babu wanda ya kira shi da su. Badan bai isa ba, sai dan shiri irin na masu makirci dake da dama a hannu. Sai dai yau shi zai kira, kiran da dole a ɗauka masa kuma a risina masa, dan wannan kiran ya zama dole ga masu amsawar.. A bazata kiran tsohon Janar ya shiga wayar babban hafsan tsaro da zai hau aiki tare da shi a sabuwar gwamnatinsa. Kiran daya saka General a ƙaulani, firgici, ruɗani duk da bai san takamaiman dalilin sa ba. Amma shi ya san jiya ba yau bace, ko giyar waye yasha bai isa hana kansa amsa wannan kiran ba a yanzu. Cike da rawar jiki kuwa ya amsa, cike da girmamawa da risinawa da ƙanƙan da murya ya fara gaishe da tsohon Janar ogansa a gun aiki, sabon shugaban kasar sa mai jiran gado kuma a yanzu. Janar Yusuf Shu'aibu Tafida yay wani murmushi mai ma'anoni da yawa yana mai jinjina kai. Lallai ƙasa ta lalace, lalacewar da mutane sun koma girmama kujerun iko sama da girman daraja da kimar ɗan adamtaka da UBANGIJI yayi ma bayinsa. Bai ja tunaninsa da nisa ba ya fara magana ba daɗi, ba sirri mai nauyi, amma da umarni. “Ina bukatar sashin ku ya fara nazarin batun jami’in SOJA da aka jefa cikin gidan maza shekaru takwas da suka wuce. Ba tare da hayaniya ba.” Cikin matuƙar bugawar zuciya Genaral ya furta, “Sir! Zak-Shadow?”. “Eh. Na san akwai ɗan hazo. Ina so ku share min hanyar ganin shi cikin sirri kafin na shiga ofis.” Yawu mai matuƙar kauri Genaral ya haɗiya jininsa na tsitstsinkewa, a take zufa ta jiƙe jikinsa sharaf. Ya kasa magana har sai da Janar Yusuf yay gyaran murya irin ta manyan da umarni kawai suke badawa sau ɗaya tak. Kamar wanda aka farkar a suma General ya amsa da sauri har harshensa na sarƙewa. “Za’a yi, Ranka ya daɗe. Amma wannan… zai bugi wasu mutane.” “Ai dama so nake ya buge sun da bulala mai zafi da dafi. Dan lokaci yayi da zasu ji su kuma sani. Gaskiya ba ta tsorata da MAKIRCI ko ƘARFIN IKO. Gaskiya ce take tsoron TUGGU koda MAKIRCI yayi nasarar ƁOYETA.” General ya kaɗa kai kamar tsohon ƙadangare dan ya kasa magana ma. Sai sake wanke masa jiki zufa take dan tabbas a wannan gaɓar yana a tsaka mai wuya ne.....

<<%>>★<<%>> PRISON

*8:30pm* aka samu baƙuncin jami’an tsaro na musamman, dole a kirasu jami'an dana musamman, domin ko sun iso ba tare da hayaniya ba balle yanayin rububi. A nutsensu suke cikin Uniform. Kai tsaye kuma sun nema ganin shugaban prison ɗin ne ta hanyar bama securitys ɗin dake kula da shiga da fitar kowa takarda. KIƊA A RUWA 2