
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 60
..... the school administration is like how Nimrah was taken away. The boy named Zahir still hasn't recovered, even though he was taken to the hospital with the principal since then, and they took Nimrah with them. But when the former president arrived at the hospital and his wife saw the condition of their son, he ordered to go back and arrest the school board. Dada was standing and the officers came out with the vice principal saying that the children's father should be included. He was talking and pointing at Daddy Imran in sadness. But they didn't listen to him, they just followed his orders, and he told them to arrest the father of the children, since the children were in their hands, the parents had to take them themselves. When they passed Imran finished, seeing Dada's look at him, he gasped a bit and said, "They took the boy to the station, and I heard that they were talking about the boy in the hospital. He didn't recover. I don't know how they hurt him like that. I can't believe where they took him." Dada didn't say anything, they left the area to where their car was. They kept following the car of the security officers until their station. That's how they understand what
60
..........★Ko sakan ashirin Daddy Imran baiyi da barin wajen ba motar ƴan sandan farin kaya ta iso. Ta ɓangaren da yake sukai parking. Dan haka kunensa ya jiye masa abinda ɗaya daga cikinsu dake waya yake faɗa. Da kallo ya ɗan bisu har suka bar wajen, kamar zai share ya cigaba da aikinsa sai kuma ya dakata, ƙofar da Imran ya shiga suma ƴan sandan suka shiga ya kalla, tare da ɗaukar waya dake gefensa. Ɗauke idonsa yay yana ƙoƙarin kiran layin Imran, bugu ɗaya kuwa ya ɗauka. “Mike faruwa?”. Banji mi Imran ɗin ya sanar masa daga can ba, naga dai kawai ya yanke kiran yana sauke laptop ɗin tsakkiyar kujerun, hakama takardun ya tattare su ya riƙe a hannu har sai da ya fita ya ajiye su a kujerar daya tashi. Motar ya kulle gaba ɗaya, ya saka norse mask daya cira a gaban motar, dan a sati gudan nan in har suka fito idan ba'a mota ba zaka ganshi da facemask ne.....
A dai-dai lokacin a office ɗin vice principal jami'an farin kayan nan ke magana cikin gadara. Acewarsu dole su tafi da su kansu hukumar makarantar kamar yanda aka tafi da su Nimrah. Dan har yanzu yaron mai suna Zahir bai farfaɗo ba, duk da an wuce da shi asibiti ne tare da su principal tun ɗazun, su kuma suka tafi da su Nimrah. Amma koda shi tsohon shugaban ƙasa ya isa asibitin da matarsa sukaga halin da ɗansu ke ciki sai ya bada umarnin komawa a kama suma hukumar makarantar bayan suma nan su principal an tattare su dukansu an wuce da su station ɗin. Dada na tsaye jami'an suka fito da vice principal dake faɗin ai ga mahaifin yaran nan sai shima a haɗa da shi. Yana maganar ne yana nuna Daddy Imran cikin ɓacin rai. Sai dai su kuma basu saurareshi ba, dan umarni suke bi kawai, kuma shi akace su kamo ai na mahaifin yara ba, tunda yaran na hannunsu ai dole iyayensu sukai kansu da kansu. Sai da suka wuce Imran ya ƙaraso, ganin kallon da Dada ke masa ya ɗan furzar da iska yana faɗin, “Sun kaisu station, yaron kuma naji kamar suna batun asibiti ma wai bai farfaɗo ba. Ban san mi sukai masa haka da zafi ba. Ina ga mu bisu dan musan ina suka kai mana su”. Komai Dada bai ce ba, suka bar wajen zuwa inda motarsu take. Haka suka dinga bin motar jami'an tsaron a baya har station ɗin su. Ta hakan ne suka fahimci wane irin jami'ai ne ma. Da farko hanasu shiga station ɗin akayi, sai da Daddy Imran ya nuna id card ɗinsa sannan. A yanzun ma Daddy Imran ne kawai ya shiga, Dada yay zamansa a mota. Da farko hana shi ganin su Nimrah akayi, sai da ya nuna id ɗinsa anan ma sannan, a hakan ma wani a cikinsu ne yay kiran ogansu ya sanar masa, shine yay magana kan a bar Daddy Imran ya gansun, dan sauran idanunsu ya rufe umarnin da aka basu kawai suke iya kallo da girman wanda ya basun, duk da baya kan mulki a yanzu. Sai dai tunda ƙasar tamu in dai wane na amsa suna wane dole abu umarninsa shike nan. Idanu ya zubama Ruky da Nimrah ganin su hankalinsu ma kwance. Dan suna ganinsa ma suka nufoshi fuska da murmushi suna faɗin, “Daddy kai ne?”. “A'a aljanun ku ne”. Ya basu amsa yana hararsu. Bakuna suka rufe da hannaye alamar dariya ma suke son yi, sai ya girgiza kai kawai da cewa, “ALLAH dai ya shirya min ku”. “Amin Daddy. Kuma wlhy a shirye ma muke. Kawai idan aljanun suka motsa ne al'amarin namu ba daɗi”. Cikin ɓacin rai jam'in daya fito da su ke hararar su da faɗin, “Yaran nan kanku rawa yake na lura, aljanu ko? Zamu sauke muku su kuwa. Dan yanzu zaku koma cikin call ai marasa kunyar ƙarya”. Daddy Imran ya fara nuna musu hakan bazai yiwu ba, sai dai a jira daga nan har wasu awanni aji daga asibitin dole. Amma sunƙi saurararsa sai wani gadara suke masa dan a farin kaya yake ba uniform ba. Har wani maimaita masa minti goma suka bashi a maida su suke. Sosai zuciyar Nimrah takai wuya, cike da tsiwa da takaici ta ce, “Daddy ka barsu, dan ALLAH ba cell ba su kaimu cikin kabari, daga ni har Ruky ba tsoron su muke ji ba. Shi daya aikata rashin ɗa'a ba'ace za'a kalleshi ba ma sai mu? Kuma wlhy shi da ire-irensa yanzu ma muka fara musu haka, tunda su bunsuraye ne. Ai duk wanda uwarsa tace masa JEKA KA GANI idan har ya yarda ya fito ɗin MU ZAI GANI. Duk an saki yara ba tarbiyya kamar ɗiyan aladu a ƙasa. Tunda shi yace ɗan iska ne miyyasa bazai je ya rungumi uwarsa ko yayarsa ba. Sai mu tunda iyayenmu basu taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙasa ba, balle kuji tsoron su ko?.” Caraf Ruky ta amshe da faɗin, “Barsu Ninah. Ɗan shegiya ni wlhy yanzu ma da zaku kaimu mu gansa sai mun danne masa kai da pillow ta yanda ko ya farfaɗo ɗin zai sake komawa mutuwar gaskiya......” Sai kawai suka cafke ita da Nimrah suna dariya. “Eh lallai yaran nan baku da mutunci da kunya. Anya kunsan gaban wanda kuke kuwa? Hukuma ce fa”. Wani ya faɗa a cikin jami'an farin kayan yana latsa waya da kaita kunensa. Baki kuwa Nimrah ta taɓe irin na kai ka sani ɗin nan ƙasa-ƙasa tace, “Ko gaban gwalando muke miya shallemu, mu ubanmu soja ne ma baban ɗan sanda”. “Mi kika ce?”. Ɗan sandan ta tambaya dan baiji mita faɗa ba. Kanta ta ɗauke kamar bata jishi ba itama. Sai Ruky dake dariya ƙasa-ƙasa. Daddy Imran daya rasa abin faɗa sai ya girgiza kai kawai shima. Ya ɗauki waya zai kira lawyer ɗinsa. Nimrah kuwa na hararar jami'in nan da suka fahimci kamar yafi kowa nuna gadara da tsanarsu kamar ɗansa sukama abinda suka yin. “K! Ni kike harara?”. Nimrah ta yamutse fuska zatai magana Dada ya shigo office ɗin a bazata..... Ɓamm ta ɓame bakinta batare data bari kalmar dake ƙoƙarin fitar ta ƙarasa fita ba. Dan a cikin tsakiyar idanunta nasa idanun suka shiga, duk da fuskarsa akwai norse mask hakan bai hanasu gane shi ba. Shi ko ɗan sandan ya hasalo ne kamar zai mareta kiran daya shigo wayarsa ya katse shi. Sai ya ƙare da balla mata harara shima yana kai wayar kunnensa yana fita a wajen. Hakan yasa ɗakin komawa daga su sai su.
★Daga can wani office na station ɗin wani ɗan sanda ne dake tabbatar da oga ne a wajen, zaune yana kallon duk abinda ke faruwa ta computer dake desk ɗinsa. Sakamakon ɗakin da su Nimrah suke akwai cctv. Babu abinda yake saki sai murmushi, dan ba ƙaramar dariya yaran nan ke neman saka shi ba. Ganin ma suna neman hasala ɗan sandan da ke tare da su ɗin ne ya sashi kiranshi a waya. Dai-dai nan ya shigo office ɗin, sai da yay salute ɗinsa sannan ya ce, “Gani Sir!”. Ogan daya kafe Dada da idanun ta desktop ɗinsa bai maji shigowar yaron nasa ba balle abinda yace, sai da ya sake maimaitawa sannan ya kawo ajiyar zuciya yana kallonsa. Cike da mamaki yaron ya ce, “Sir! Akwai matsala ne?”. Kai ya girgiza masa, tare da faɗin, “Waye ya shiga wajen yanzu?”. “Ban sanshi ba Sir, amma da alama tare suke da shi. Dan yana shigowa naga sun nutsu alamar suna shakkar sa.” Oga ya sake kallon Dada da ƙyau, sai kuma ya furta, “Koma inda suke, amma kasan maganar da zata fita a bakinka, baka gani yara ne”. Cike da girmamawa ya amsa yana fita. Mamakin ogan nasu fal ransa. Badan yasan halinsa ba daya zargi wani abu, sai dai yasan ba hakan bane ba....
★Anan kuwa. Maƙalewa Ruky tai bayan Nimrah ganin yanda Dada ya zuba musu zafafan idanunsa da suka gagara fassara abinda ke cikinsu. Itama Nimrah kanta a ƙasa tana faman cuɗa yatsunta cikin juna. Murmurshi Imran yayi a ransa yana raya, (Marasa ji ashe ni kuka raina da su Ma'aruff). A zahiri kam sai ya mike abinsa yana faɗin, “Bari na shigo da lawyer”. Bai jira amsawarsa ba ya fice abinsa. Kusan mintina biyu da fitar Imran sannan yaja kujera ya zauna. A take suka ƙara jin ya cike musu waje. Duk girman wajen kamar an sake matse su. Ruky ta fara gaishe shi da rawa baki, kafin itama Nimrahn ta gaishe sa. Duk ɗin su babu wadda ya amsawa, sai ma bayan wasu sakanni ya jeho musu tambaya idanunsa akan wayarsa daya fiddo daga gaban aljihu. “Mi kuka aikata?”. Kalmomi uku ne kacal, amma sai da suka jisu suna maimaita kansu a cikin kunnuwansu sau sittin. Ruky da Idanunta suka cika da hawaye ta fara faɗin, “Wlhy Dada shine yaja duk abinda mukai masa, maganar banza yazo yana mana shine kawai muka....”
Ta kasa ƙarasawa. Shiru ɗakin yayi na sakanni, sai kuma yanda ya ɗago yana kallon su yasa Nimrah fara magana itama hawaye na ciko mata ido. Muryarta na nuna ɗaci ta fara bayani tun daga farko ba kamar yanda Ruƙayyan tayi a taƙaice ba.........✍️