
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 40
.....orders went up to everyone where it is best for him to go, everyone and what is in his soul and heart. Ismat at this point decided to go back to their father's house. She promised that she would never go back to Dubai again, except where she would visit with her husband, Yaya Ja'afar, thank God. But this time the battle will be a real one, there is no running and no retreating. She wiped away the small tears that filled her eyes, a kind of fire of his love was burning in her heart again, because seeing him did not disturb her a little. He is more beautiful and full of body and openness like the housewives who get all the privileges from their families. Since he got married, she didn't allow him to see his wife because she didn't need it, but today she feels the urge to see Shariffa even though she knows the right to be there. She opened the box of things that she brought from Dubai, as it was really big and she collected all her important things from there, then she packed the ones in the house and loaded them inside, seeing that it was too full, she took another small one and put the rest of the things that were left and closed them. She sat on the bed and picked up her phone
40
.........Gaba ɗaya ran Hajiya Hasiba a dagule yake. Koda su Nabeeha suka koma gida da nasu ɓacin ran sun sameta tana faman kai-kawo a falo. Aunty Mamawo zaune itama ta rabga tagumi. Ismat ce kawai tai ƙarfin halin tambayar su ko lafiya? Amima da Rayhana kam da ƙorafin abinda ya faru suka fara. Nabeeha dai ranta a ɓace yake, dan haka bata tankama kowa ba ta wuce upstairs abinta. Dan a wannan gaɓar ta gama yarda dole ta nemawa kanta mafita. Mafitar kuma ɗaya ce jal shine komawa gidan su Haysam. Dan a can ne kawai zata samu damar maganin wannan shegiyar mayyar yarinyar da ganinta ya gama birkita mata dukkan lissafinta, sannan ta samu mafakar gujema Adeel da bata san manufarsa ta biyosu ƙasar nan ba. Tsakanin Aunty Mamawo da Hajiya Hasiba babu wanda ya kula tambayar Ismat, sai ma umarnin su wuce ciki da Mamawo ta basu. Hakan ya sake tabbatar musu babu lafiya. Wucewar sukai, dan sun san halinta da masifarta bata musu ta wasa. Shiyyasa ma suka fi son Hajiya Hasiba dan tafita sauƙin kai. Koda suka hauro saman ma kowa inda yafi masa ya nufa, dan kowa da abinda ke ransa da zuciyarsa. Ismat dai a wannan gaɓar ta gama yanke shawarar komawa gidan mahaifinsu. Dan tayi alƙawarin bazata sake komawa Dubai zama ba sai inda ziyara itama tare da mijinta Yaya Ja'afar in sha ALLAHU. Dan a wannan karon yaƙi zatai ɗan gaske babu gudu babu ja da baya. Ta share ƙananun hawayen da suka cika mata ido, wani irin wutar sonsa na sake ruruwa mata a zuciya, saboda ganinsa ba ƙaramin tayar mata hankali yayi ba. Ya ƙara ƙyau da cikar jiki da buɗewa irin ta magidantan dake samun dukkan gata a wajen iyalansu. Tunda yay auren nan bata yarda taga matarsa ba saboda bata buƙatar hakan, amma a yau tana jin kwaɗayin ganin Shariffa ɗin duk da ta santa dama can. Akwatin kayan da tazo dasu daga Dubai ta buɗe, kasancewar ƙaton gaske ne dama kuma ta haɗo komai nata mai muhimmanci daga can sai ta sake tattare na nan gidan ma ta loda a ciki, ganin ya cika da yawa ta sake ɗaukar wani ƙarami ta zuba sauran abinda ya rage ta rufesu. Bakin gado takai zaune ta ɗauki wayarta ta fara kiran Aunty Jiddah. Gidanta take son fara zuwa, dan tai mata rakkiya gidan Abban. Da mamaki Aunty Jiddah data ɗaga wayar ta ce, “Yaushe ke kuma a gari haka?”. “Aunty mun jima da zuwa. Kina gida ne dan ALLAH?”. “A'a ina gidan Aunty Fateema, zata aurar da ƴarta Aminatu muna shirye-shirye dan za'a fara gobe idan ALLAH ya kaimu.” “ALLAH ya sanya alkairi, yaushe zaki koma?”. “Amin ya rabbi. Lafiya kuwa?”. “Aunty zan zo ne, ni dai yaushe zaki koma?”. “Ki tafi kawai ai yara na nan, Shafa'atu ƙanwarsa ma na gidan tazo weekend”. “Okay tom. Ki gaida Aunty Fateeman, in sha ALLAHU dani za'ai kamun gobe”. Daga haka ta yanke wayar tabar Jiddah da mamakinta....
★ Anan falo kam bayan wucewarsu Aunty Mamawo ta furzar da iska mai zafi tana kallon Hajiya Hasiba. Ta ce, “Aunty tunani ko damuwa bazata kaimu ko ina ba. Kawai muje wajen wani mutimina, shima yana ƙoƙari ya iya aiki, da rafanai yake aiki na tabbata zai mana nasa ƙoƙari kafin muje India ɗin. Dan dole gaskiya muyi wani motsi a wannan gaɓar, dan ina ji a jikina shirun Adeel bazai zama alkairi ba”. “Kina ganin zamu samu mafita kuma?”. “Tabbas Aunty, dan na yarda da aikin Malam Ƙolo sosai”. “To shike nan muje ai kawai mi zamu jira. Dan mutumin nan na tabbatar shima yana can ya bazama hanyar samun damar ganin Haysam, dan gaskiyarki kam shirunsa bazai zama alkairi ba.” “Wlhy ni wannan bai dameni ba Aunty, idan ma ya saka an kashe shi matsalarsu ce. Miye amfanin wani Haysam a rayuwar Nabeeha, banda soyayyar wahala da take masa ma. Garama ya kashesa ta samu wanda ya fisa koda ace zata bar Adeel ne, idan ma babu wata illar da ita First lady ɗin ta ambata ba shike nan ba. Dan ni ban yarda ma da matar ba kin san dai mutane da baƙar hassadar tsiya a wannan zamanin. Kowa yafi son ace shi shine kai kana ƙasanshi kana masa bauta bare ma manyan ƙasar nan”. “Mizai hana nayi hakan”. “Yanzu yanzu fa. Ko zaka kira abokinka ne Ammar?”. “Kodai kayi haƙuri zuwa anjima, kuma ba Ammar ya kamata a tambaya ba dan kar ya zargi wani abun tunda mun samu ya fara sakin jiki damu.” Ji Adeel yay kamar yace bai yarda ba, amma sai ya daure dan baya son Yohan yaga zalamarsa a fili da yawa, har ya kawo masa raini dan har yanzu bai san shi ɗin waye ba. Kuma baya son ya sani har ya gama abinda ya kawo shi ya bar ƙasar nan. Duk da yau da safe yaga saƙon Ummu ɗinsa ta Email akan tana son ganinsa da gaggawa, ya tabbatar koma miye take nemansa a kansa ba na wasa bane. Kuma dole ya amsa wannan kiran dan baya tsallake maganar iyayensa..... Bai sake magana ba sai ma barin wajen da yayi ya koma kan kujerar da take a balcony ɗin ya zauna zuciyarsa fal abubuwa. Dan gaba ɗaya yarinyar can ta rikita masa lissafi ko zancen abinda ya kawo shi ƙasar nan bai sake waiwaye ba. Kai su kansu su Hajiya Hasiba ɗin tunda suka iso bai bi takansu ba, sai ma da yaga Nabeeha yanzu ya tuna da al'amarinsu...........