Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 39

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 39

.....ask them their mother. Nabeeha said, "She is fine. Mammah, we will answer the key." Mammah smiled and looked at Nabeeha beautifully. She has become very beautiful and fat which means she is safe and healthy. The old lady answered, "Aiko, there is a problem Nabeeha, there is nothing in your department. Since everything is going to be fixed and everything is thrown out, only your important things are left in this department, but the funichars have all been given and you don't have to add others because no one is staying, don't waste it." "But Mammah, I would have been told before it was taken away, especially my bedroom and kitchen furniture. I need them all. I keep important things and it is my secret that it is appropriate for me to lift them there and not anyone else". By now, Nimrah understood who she was before, that is, Dada's wife who cut her thigh, and the scar is still there. Speaking to Mammah with a lack of respect and respect, Nimrah's heart sank again. Also, Biebah, who has come out so far, lost her soul and ended up there. However, Mammah warned them all not to say anything. Almost at the same time, Nimrah and Biebah tried to answer her. Babu yanda zasuyi,.....

Standalone post2,394 words

39

........Mammah data fahimci halin da suka shiga da yanda suke kallon Nimrah ɗin sai ta ɗan murmusa, batare da ta sake magana akan abinda ya farun ba ta kama hannun Nimrah tana barin wajen da faɗin, “Bismillah ku ƙaraso ku zauna”. Sai da suka kalla juna, kafin su bi bayanta jiki a saɓule. Karasowar su falon dai-dai Nimrah da Mammah ke miƙama ruwa alamar tasha na faɗin, “Mammah su waye su?”. “Sha ruwa”. Mammah ta faɗa batare data bata amsa ba. Sai da ta tura baki gaba sannan ta amshi ruwan tasha. Ismat dake fatan al'amarin ya tsaya iya haka ta zamo a kujera tana gaishe da Mammah da Ummu da taƙi cewa komai sai mamakin ma ganinsu Ismat ɗin daya cika zuciyarta. Saboda tuna kusan wata ɗaya kenan da kiran Jiddah da sukai akan an hanasu baro Dubai. Da mamaki Nabeeha da su Amima ke kallon Ismat, itako ta fuske dan tasan abinda tai shine dai-dai. Mi Nabeeha ɗin ta gani oho mata, itama sai ta daure ta gaida Mammah kaɗai banda Ummu. Mammah ta amsa mata da kulawa tamkar komai bai faru ba, harda tambayarsu mahaifiyarsu. Nabeeha ta ce, “Tana lafiya. Mammah dama zamu amshi key ne”. Ɗan murmushi Mammah tayi da kallon Nabeeha da ƙyau. Ta ƙara ƙyau sosai da ƙiba alamar tana cikin kwanciyar hankali da ƙoshin lafiya. Cike da dattako ta bata amsa da, “Aiko akwai matsala Nabeeha, dan sashen nan naku babu komai a ciki. Tunda za'ai gyara aka fidda komai, abubuwanku masu muhimmanci ne kawai aka bari suna cikin nan sashen ma, amma funichars duk an bada su kuma ba'akai ga zuba wasu ba ganin ba kowa ke zama ba kar aita asara”. “Amma Mammah da an gaya min kafin a kwashe ɗin, musamman kayan bedroom ɗina dana kitchen dan duk ina buƙatarsu. Gashi na ajiye abubuwa masu muhimmanci da sirrina ne da ya dace ace ni da kaina na ɗaga su a wajen ba wani ba”. Zuwa yanzu Nimrah ta fahimci wacece a gabata, wato matar Dada data taɓa yankata a cinya, har yanzu tabon na nan kuma. Yanda takema Mammah magana cike da rashin taunawa da girmamawa, yasa zuciyar Nimrah sake zuwa wuya. Hakama Biebah da duk suka fito zuwa yanzu ranta a ɓace ta ƙaraso wajen. Sai dai da ido Mammah tai musu gargaɗi su duka akan kada suce komai. Dan kusan lokaci guda Nimrah da Biebah ɗin suka yunƙuro zasu bata amsa. Babu yanda zasuyi, dan Mammah tafi ƙarfin basu umarni su tsallake. A karo na farko Ummu tai magana tana kallon su Nabeeha ɗin. “Amma wannan maganar taki babu tarbiyya a ciki, dan ko Adda A'isha bata haifa miki Haysam ba matsayin ƙanwar mahaifinku take Nabeeha. Kayan da kike magana basu suka taɓa miki ba ai Jiddah ce tai komai da ƴan uwanki su Halimatu”. Rai ɓace Nabeeha ke kallon Ummu, sai dai kafin ta fara maganar da take tattarowa a zuciyarta Ja'afar da suke shigowa shi da Yaya Ma'aruff, Bilal da Ammar ya katseta. “Ummu daina ɓata lokacinki wajen yi mata bayani. Ke Nabeeha kike ko wa? Tashi ki tattara waɗanan tarkacen ku wuce anan.” Wani mugun kallo Nabeeha ta zuba masa. Ya ɗage gira sama cike da rashin mutunci. Tasan waye Ja'afar dan karonsu babu daɗi. Shi da Ma'aruff shegen zuciya ne da su mai zafi fiye data Dada, kawai dai su suna da barkwanci ne da hira ba kamar shi da baida yawan magana ba. Sannan shi akan jima ba'aga fushinsa ba saboda ya iya shanyewa... “Malama kina kallona ko akwai magana ne? Nace ku tashi ku bar mana gida..” “Ni kuma twiny na ƙara mata da gargaɗi na ƙarshe. Kada na sake ganinki a wannan gidan namu, dan baki da sauran hurumin zamansa sai in har Dada ne ya dawo yace ki dawo da kansa. Yanda kika saka ƙafa kika fita da kanki, ki cigaba da zama acan bama buƙatarki a cikinmu. Idan kuma taurin kai yasa kika cigaba da zuwa kina nunama mahaifiyarmu rashin tarbiyyarki, wlhy Ninah da Ruky kaɗai zamu barki da su sai sun saitaki a layi”. Ma'aruff ya ƙare maganar yana nuna mata Nimrah da Ruƙayyan. Aiko ƴar wulaƙancin suka wani tuntsure da dariya Nimrah na faɗin, “Yess Uncle, wlhy ni kaɗai na ishesu su duka ma koba Buddy na. Idan mutum shi ɗan daba ne mai yankan mutane da wuƙa, ni Zakanyar Mammah ce mai kai manyan namun dawa ƙasa harma da ƙananu. Darje baki nake cikin ƙasa, na cikashi da ƙasar taf ta yanda zai iya yima manya magana”. Ihu Ruky da Bintu da Fiddo suka saka cike da ƙarin haushi suna faɗin, “Naja bomb! Naja bomb! Sai dake Zakanya, Trouble Queen”. “Mai bombing ɗin ƙananun tantirai ba”. Nimrah ta basu amsa cike da salon iyayi tana wani juya manyan idanunta. Yanzu kam dariya harda su Yaya Ja'afar ɗin, Mammah ta kai mata rankwashi. Tashi tai da gudu tana dariya taje bayan Aunty Biebah ta maƙale. Ummu dake murmushi itama ta ce, “ALLAH ya shirya ku yaran nan. Nimrah dai kin zama Gang leader? Ga mabiya nan irinki kin tara yayunku kuma na ɗaure muku ƙugu. Bari Abban Jiddah yazo aure zance ai muku”. “Aure Ummu?”. Suka faɗa a tare suna waro idanu. Asma'u dake dariya tace, “Wlhy Ummu da kin taimake mu, dan yaran nan jinsu suke kamar muma sun girmemu ma”. Amshewa Halimatu tai da, “Ashe angunan zasu sha shirme da rashin kunya”. Cike da shagwaɓa suka kalla su Uncle Ma'aruff a tare sukace, “Uncles kun gansu ko? Ai dama sun saka mana ido”. “Ku barsu sune za'aima aure ba kuba”. Cewar Bilal yana kallon Asma'u ƙasa-ƙasa. Cike da farin ciki suka dawo inda yake suna ma su Asma'u gwalo. Su Nabeeha sun fahimci fa an ma manta da su a falon gaba ɗaya, yayinda Ismat ta shagala a kallon Ja'afar idanunta cike da ƙwalla. Shi ko ko kallon inda take ma baiyi ba. Bare ma da taga su Aheel sunzo inda suke sai taji wani kishi ya cika mata ƙirji, tana jin inama itace ta haifi su Aheel ɗin.....

_____★

Tunda Adeel ya dawo gidan Yohan baida aiki sai zaman balcony dake facing gate ɗin su Nimrah. Ga alaƙa ta ƙullu tsakaninsa da Ammar a dalilin fita morning jugging. Dan a washe gari saka Yohan yay suka jira har Ammar ya fito a gida, kasancewar sun saba gaisawa normal Ammar ya bama Yohan hannu suka gaisa, sannan ya bama Adeel shima. Daga haka suka fara abinda ya fito da su, suna gudu kaɗan-kaɗan Yohan ke gabatar da Adeel ga Ammar matsayin abokinsa. Hannu biyu Ammar ya amshesa, haka sukaje suka dawo tare, su suka shiga gida shima ya wuce. Tun daga ranar kuma sai hakan ta cigaba da faruwa, kamar wasa bayan kwana biyu suka haɗu a massalacin anguwar nan ma, tun Ammar baya wani sakin jiki da Adeel bayan gaisuwa harya fara suna ɗan yin hira kaɗan-kaɗan.

Yau ma kamar yanda ya saba yana a balcony ɗin tsaye, gaba ɗaya kuma hankalinsa akan gate ɗin gidan yake. Kunensa da headphone mai shegen ƙyau, sai dai babu tabbacin waƙa yake ji ko wani abun daban. Ganin an buɗe ƙaramar ƙofar gate ɗin ya sa ya ƙara nutsuwa da maida hankalinsa da ƙyau, cikin wata irin bazatar mamaki Nabeeha dake fitowa ta bayyana cikin idanunsa. Da sauri ya cire headphone ɗin daga kunnensa dan tsabar mamaki, ya ciro wayarsa ya shiga camara. Zooming ɗinta yay ta ciki dan gani yake kamar idanunsa ne ke faɗa masa hauka. Itace ɗin kuwa idanunsa ba ƙarya sukai masa ba, dan dai-dai nan Ismat ta fito itama tana waige-waige alamar nemanta take. Ganinta a gefe ta dafe kai da hannu ya sata ƙarasawa inda take da sauri, sai dai baya jin mi take ce mata har aka wangale gate ɗin duka mota ta fito. Dai-dai inda su Nabeeha suke Rayhana tai parking, buɗe motar da fitowar da sukai ita da Amima suma suka nufi su Nabeehan ya sake cire masa tantama. Sai ma ya rasa abin cewa shi kam. Yana anan tsaye tamkar wani gunki Yohan daya fito ya kai dubansa inda yake kallo, bai san su waye matan ba, dan haka ya juyo ya kallesa tare da faɗin, “Sir ka sansu ne?”. Shiru kamar Adeel bazai tanka ba sai kuma ya ce, “Ba saninsu bane mai muhimmanci, sanin alaƙarsu da wannan gidan. Zaka iya bincika min”. Received at 4:37 PM “Nima irin wannan tunanin naki na zomin a rai. Musamman dana fahimci ba tayi wani serious bane kan batun sai ma zancen ƙulla auren da suke sonyi tsakanin ƴar su da ɗan shugaban kasa. Duk da yaron ya nuna ba sonta yake ba sun nace.” “Kinji ba! Ai halin ɗan Adam sai shi wlhy.” Da wannan zantukan suka fice a gidan batare da sunma yaran nasu sallama ba. Sai fitar motarsu sukaji a gidan. Da wannan damar Ismat tai amfani ta fito itama tabar gidan da kaya niƙi-niƙi. Sai dai maigadi ta saka ya tare mata taxi a waje bata ɗauki motar kowa ba. Dan dama dai Mamansu da Aunty Mamawo da Nabeeha keda mota kawai a gida. Su basu da ita......

================

Anan gidan Mammah bayan tafiyar su Nabeeha Malam Almu ya kawo ƙaninsa ciki dan su gaishe da Mammah su mata barka da dawowa. Da fara'a kuwa ta tarbe su. Tare da amsa musu gaisuwa da kulawa tana tambayar Malam Almu mai jiki. Kamar yanda yay ma malam Buba bayani itama haka yay mata duk su Yaya Ma'aruff na jinsa. Ya kuma nuna ƙaninsa Sanda ya musu bayani a kansa da aiki da ya fito nema idan ya samu. Sai dai bai nuna anan gidan ba kamar yanda suka shirya. Cikin sa'a kuwa Mammah ta ce, “To ai bai kamata yay nesa da kai ba ko Malam Almu. Sai a bincika anan idan da wani aikin sai ya dinga yi, kaga sai kuyi zamanku ka samu abokin hirar dare tunda shi driver ba kwana yake ba yana tafiya gida da yamma”. “Nagode Hajiya Mama, ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara lafiya da nisan kwana mai amfani. Sanda kayi godiya mana”. Godiyar Sanda ya fara shima kamar yanda yaga malam Almu nayi, suka juya suna sake godiya gasu Yaya Ma'aruff suma. Sai da Mammah tace ya isa sannan sukai shiru. Daga haka ta ɗan yima Sanda tambayoyi yana bata amsa. Kai ta dinga jininawa cike da nazarin al'amarinsa, kafin ta sallamesu su koma bakin aikinsu...

Suna fita Yaya Ammar ya ce, “Mammah wai baƙya jin tsoron ɗauke-ɗauken nan kada wataran mu ɗauki abinda zai dame mu. Yanzu fa akan al'amarin Dada kowa zai iya shigowa jikinmu dan ya cutar damu. Shiyyasa kikaga ma Yaya Imran kullum yana kaffa-kaffa”. “Hummm Ammar kenan, banda abinka bawa na iya gujema ƙaddararsa daman? Duk abinda kaga ya faru hukuncine na UBANGIJI. Jarabawa ba tawaya bace. Ba kuma faɗuwa bace ga bayi, sau tari kankarewar zunubi ce ko tsanin nasara daga wata ɗaukaka da UBANGIJI zai kai bawa kanta. Kar ku damu da makircin masu makirci, idan duk wanda ke zagaye da kai mugune mai fuska biyu, in har ka tsaida gaskiya, kai ka zauna da shi da kyakkyawar zuciya bisa umarnin ALLAH, wlhy ko shine ibilis akan sheɗanci da mugunta sai dai yayi ya barka. Dan shi bai isa canja komai daga ƙaddararka ba koda murmushi fuskarka ne, sai dai yayta wahalar banza da ɓata lokacinsa akan ka amma ko badaɗe ko ba jima saika cimma wannan nasarar. Ƙilama UBANGIJI yay masa tsahon ran da zai koma neman taimakon ka. Kudai kuyi addu'a kawai, idan ma da manufa mutum yazo mana, ALLAH zai hanashi nasarar cutar damu. Shima da yake can ALLAH zai kuɓutar da shi idan lokaci yayi, dan bana yanke ƙauna da rahamar UBANGIJI akan Muhammad zai fito ya dawo garemu. Ban taɓa jin na sare akan wannan fatan ba, duk da ina jin tsoron kar su cutar mana da shi. Amma ALLAH na tare ta shi, addu'a ta da taku na tare da shi. In sha ALLAHU indai gaskiyarsa ce ta kaisa wancan wajen komai tsahon lokaci zata ƙwatoshi daga hannun azzaluman makirai...” “In sha ALLAHU Mammah”. Suka faɗa a raunane, Biebah da Ammar kuwa sai da suka share hawaye. Su Ja'afar dai idanun sun canja launi amma babu hawayen. Su Nimrah dake laɓe suna sauraren su suma dai duk jikinsu yayi sanyi. Cikin Zuciya Nimrah ke jin tana son sanin inda Dadan yake? Miya faru da shi? Mi ake ɓoye musu game da shi?. A zahiri kam batace komai ba ta nufi komawa ɗakinsu, sauran duk suka bita dan dama tun shigowar maigadi Mammah tace su koma ɗaki abinsu. Shine suka laɓe, da farko dariyar shigar ƙanin Maigadi suka maƙe sukeyi, dan yayi wani shigar gayun ƙauye irin masu iyayin nan ne abin dariya......

•••••••••••••••••••••••••••••• ★ONE WEEK LATER★ ★10:15 AM★

SECRET MEDICAL BASE “Colonel Imran… mun kammala dukkan gwaje-gwajen da muka yi masa.” Dr. Idris Ali, ya faɗa yana ɗan gyara gilashinsa. Imran bai ce komai ba. Ɗaga masa kai yay alamar ya ci gaba. Doctor ya jinjina kansa, kafin ya buɗe baki ya cigaba da faɗin, “Mu godema ALLAH jikinsa ya nuna ƙarfin juriya mai ban mamaki. Idan ba haka ba, da gubar da aka saka masa ta riga ta yi mummunan tasiri a lafiyarsa zuwa yanzu.” Cikin wani irin bugawar kai Faro ya ɗan matsa gaba, murya ƙasa-ƙasa da alamar tashin hankali a ciki ya furta, “Guba kuma Doctor?”. Dr. Idris ya ɗan numfasa, kamar yana neman kalmar da zai musu bayani da ita da bazata ɗaga musu hankali ba fiye da kima. “Eh. Poisoning ne… dan abinda sakamakon bincikenmu ya nuna mana kwanaki uku kenan shiyyasa ma muka sake masa sabon gwaje-gwaje akan hakan, kusan wannan dalilin ne ya hanamu faɗa muku komai a ranar wednesday data gabata mukace ku saurare mu. Sai dai ku kwantar da hankalinku poising ɗin bai jima da fara shigarsa ba, da dai ya jima a inda yake ne zai cigaba da shiga kamar yanda koma su waye suka tsara, sanan zai dinga tasiri a jikin nasa ne a hankali har sai ya gama yima jikinsa illa ne zai bayyana. Dan haka ko a yanzu babu wani damuwa mai girma. Sai dai idan aka bar shi haka a jikinsa, akwai haɗari sosai anan gaba”. Imran da gaba ɗaya yake jin jinin jikinsa na tsiyayewa tamkar an ɓula ledar ruwa da tsinin allura ya rumtse idanu yana matse hannunsa.........✍️ KIƊA A RUWA 2