
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 38
.....what if he was not allowed in except by law?". "It's not like that, Hajiya, I'm on my job". Amima angrily opened the door and he came out, and that was just as the taxi arrived there. There was no one inside but the owner and his guest. Malam Buba concentrated himself and said, "Alhamdulillah Malam Almu, how are you coming?". "Mr. Malam Buba, are we safe? I saw you outside, so you and them...." He swallowed the rest of the words because he saw Amima. "No, Hajiya, are you here? Mr. Buba opened the door for them, they are the family members." Mr. Buba answered him as he was turning around, and Amima went back to the car and came out ready to wash the man's face with a slap. When their car entered, Mr. Almu looked at his companion and said, "And who are they?". After taking a breath, Mr. Almu answered him, "The wife of their children's father that I am telling you about is in a foreign country, the other is her younger brother. She does not stay in the house but occasionally comes to check on her. It's been more than three years since she came again until today". He just waved at him and said nothing, and then they went inside. Malam Buba said hello to them and brought them water
.........“Tofa, gyaran gidan nan aka sake yi haka Aunty Nabeeha?”. Ɗago kai Nabeeha da hankalinta ke kan wayarta tai ta kalla gidan a karo na farko. Ba ƙaramin ƙyau gidan yayi ba kam dan tun daga waje zaka shaida hakan, flowers ɗin da suka ƙawata katangar gidan ta wajen kawai abin kallo ne, ƙamshinsu ya cika wajen sosai kuma. Balle baƙin gate ɗin. Ajiyar zuciya Nabeeha ta saki a hankali batare da tace komai ba. Ismat da Raihana kuwa suka cigaba da santin su har Malam Buba ya leƙo sakamakon horn da Ismat ɗin tayi dan itace ke jan motar. Malam Buba bai sansu ba, dan haka ya fito sosai yana tambayar “Su waye ku?”. Sai da duk sukai masa kallon sama da ƙasa, a yamutse Amima uwar rashin kunya ta ce, “Matar gidan ce da ƙanen ta”. “Kiyi haƙuri Hajiya kumin bayani yanda zan gane, ni baƙone anan, dan dole zan fara sanar da masu gidan kafin na barku ku shiga”. Sai a lokacin Nabeeha da taja tsaki ta kallesa a wulaƙance. “Kai sha-sha-sha ka buɗe mana gate mu wuce. Shi gidan ya zama na shugaban ƙasa ne yanzu da ba'a shigarsa sai da doka komi?”. “Ba haka bane Hajiya, ina kan aiki na ne”. A fusace Amima ta buɗe ƙofa ya fito, hakan kuma yay dai-dai da isowar taxi wajen. Ba kowa bane a ciki sai ainahin maigadi da baƙonsa. Malam Buba ya maida hankalinsa kansa yana ɗan murmurshi da faɗin, “Alhamdulillahi Malam Almu sannu da zuwa?”. “Yauwa Malam Buba, mun sameku lafiya? Ya na ganka a waje haka kai da su way....” Ya haɗiye sauran maganar saboda ganin Amima. “A'a Hajiya ashe kune, sannunku da zuwa. Malam Buba buɗe musu ƙofa ai ƴan gida ne”. Amsa masa Malam Buba yay yana juyawa, Amima kuwa taja tsaki tana komawa cikin motar dan ta fito ne da shirin wanke fuskar mutumin nan da mari. Sai da motar tasu ta shige Malam Almu ya kalli abokin tafiyarsa da ya ce, “Su kuma su wanene su?”. Cikin ɗan sauke ajiyar numfashi Malam Almu ya amsa masa da, “Matar Baban yayansu ɗin nan da nake gaya maka sunce yana ƙasar waje ce, sauran ƙanenta ne. Ba zama take a gidan ba sai lokaci-lokaci take zuwa tana iskance-iskancenta. Nama fi shekara uku banga ta sake zuwa ba sai yau”. Kai kawai ya jinjina masa batare da yace komai ba, daga haka suka shige ciki suma. Malam Buba nata jera musu sannu, ya kawo musu ruwa sannan ya zauna suka gaisa yana tambayar mai jiki. Malam Almu ya ce, “Da sauƙi sosai, ɗan uwana dake Niger yazo ya tafi da ita can a nema mata magani, shiyyasa ƙanina ma ya biyo ni nan dan kar a barshi shi kaɗai. Sunansa Sanda”. “Kai masha ALLAH, ALLAH ya ƙara lafiya. Malam Sanda sannu da zuwa kaji”. Yay maganar yana bama Sanda hannu suyi musabaha. Hannun shima Sanda ya bashi suka gaisa.. Dai-dai nan Rayhana ta ƙaraso wajen cike da tsawa da gadara ta ce, “Kai wani yaje can sashen ya amso mana key ɗin ɓangaren mu”. Su duka kallonta sukayi, Malam Buba zai yi magana Malam Almu ya katsesa da faɗin, “Hajiya ai ɓangaren nan babu komai a cikinsa tunda aka kammala aikin gidan nan. Ina ga zaifi ƙyautuwa ku shiga wajen hajiyar da kanku dan tana nan. Ko ta fita ne Malam Buba?”. Yanda yay maganar ƙarshe yana kallon Malam Buba da sigar tambaya ya sashi amsa masa da, “A'a tana nan bata fita ko ina ba. Dan yau ma gidan cike yake da baƙi kamar jikokin gidan ne duk suka zo. Sai dai naga matan su Ja'afar sun fita su kam”. “To kinji Hajiya, ku shiga kawai zai fi”. Harara Rayhana ta zuba musu su duka, batare da tace komai ba ta juya ta koma inda su Nabeeha ke tsaye a ƙofar sashen nata suna jiranta. Abinda ta sanar musu ya saka Nabeeha jan tsaki. Cike da takaici ta ce, “Nifa ban son iyayi, to ina suka kaima mutane kayansu?”. “Muje dai wajen Mammah ɗin sai muji kamar zaifi”. Ismat ta faɗa tana binsu da kallo....
★Gaba ɗaya falon ya cika da hayaniyar su Aheel dake wasan guje-guje, sunma falon kaca-kaca da tarkacensu. Amma hakan bai hana Mammah dake zaune yin hirarsu ita da Ummu (Hajiya Zuwairah matar Uncle Nasiru) hirarsu ba. Sun juyama ƙofa baya, hakan yasa har su Nabeeha suka shigo falon basu sani ba. Babu tabbacin sunyi sallama ko a'a, sai wani kallon yaran suke a yamutse kamar sunga wasu abin ƙyama. Yaran da suma shigowarsu bai hanasu wasan su ba duk da wasu sun gansu wasu basu lura da su ba, Abees dake bin Ishaq da bindiga da aka zuba ruwa ciki yana fesa masa suka iso inda suke. Ishaq ya shige tsakkiyarsu yana ɓoyema Abees suna dariya, shiko Abees ya cigaba da fesa ruwa har a jikinsu. Cikin wani irin takaici Rayhana ta kwaɗe Abees da marin daya saka yaron sakin gigitacciyar ƙarar data saka su Mammah juyowa da sauri. Dai-dai Nabeeha ta finciko Ishaq dake bayanta ta hankaɗashi kan Abees itama. Wannan al'amari na mari da hankaɗewa yayi dai-dai ne da fitowar Nimrah daga lungun ɗakinsu ɗauke da magenta zata haɗo mata madara. Magen ta dire saman stairscase tayo wajen ranta a ɓace. Miƙewa Mammah da Ummu duk sukai suna kallonsu, haka sauran yaran tuni sunyi tsit kamar anyi ruwa an ɗauke. Sai khairat ce mai ɗan wayo ta ƙaraso inda su Abees suke da sauri. Isowar Khairat dai-dai da ƙarasowar Nimrah da babu ma wanda ya lura da ita a kaf falon sai yanzu. Kafin Mammah data buɗe baki zatai mata magana tayi kawai sukaji saukar mari mai ƙara a fuskar Rayhana, ba kuma kowa yayi mata shi ba sai Nimrah. Kafin ma Rayhana ta dawo cikin hayyacinta ta watsama su Amima da suka wani yunƙuro kanta a fusace manyan idanunta. Babu tsoro babu shakka duk da sun fita girman jiki da tsayi, dan ma itama ɗin dai doguwar ce, amma kasancewar sun girmeta nesa ba kusa ba sun fita tsayin. Amma tsabar bushewar idanu ko'a jikinta. Sai ma cike da gargaɗi da kaushin murya ta ce, “Oh zaku rama mata ne?”. Cikin matsanancin baƙin ciki Amima ta ce, “Ai ba rama mata mari kawai ba duka zaki ci”. “To bari kema na baki rabonki sai ku rama mata ɗin”. A bazata ta sake sauke wani marin a fuskar Amima. Rayhana ta yunƙuro zata cakumeta tasa ƙafa ta taɗeta sai gata a ƙasa wanwar. Ai ko yaran suka saka ihun dariya suna tafi da tsalle da faɗin, “Aunty Ninah! Aunty Ninah!”. Inda suke yanzu kam Mammah ta iso, dan Nabeeha ma ta yunƙuro kan Nimrah zata cakumota, sai dai Nimrah ta riƙe hannun nata tana mata kallo mai cike da rashin kunya da tsiwa. Yayinda Amima ta cakumi rigar Nimrah ɗin ta baya, Ismat da hankalinta ya tashi dan ita bata fatan ayi wani abu mara ƙyau ita dake fatan samun fada ta shiga janye Amima tana faɗin, “Wai miye haka dan ALLAH.” “Nimrah! Sake ta”. Mammah data iso wajen ta faɗa idonta akan Nimrah. Tashin hankali, duk fa wannan abu dake faruwa su Nabeeha basu gane Nimrah ba, haka ma Nimrah bata gane su ba, dan sanin datai musu na ƙuruciya ne, zuwan da sukeyi jefi-jefi kuwa basu taɓa haɗuwa ba tana makaranta, idan ma sun kwana kasancewar randa suka shigo kawai suke zuwa gaida Mammah harsu wuce bata ganinsu. Suma kuma rabonsu da ita tun tana ƙaramar, tsabar yanda suka tsaneta basu taɓa sha'awar idan sun zo gidan su ganta ba musamman Nabeeha. Sai gashi a yau yarinyar da suka sani mitsila ta zama budurwa, ga hasashen ƙyawu da sukama yarinyar a baya ya tabbata. Dan kuwa Nimrah akwai dogon hanci da ɗan bakinta dai-dai ita, ga manyan idanu farare tas da suka ƙawata baƙar doguwar fuskarta mai cike da tsiwa da rashin tsoro. A tsaye yarinya ce doguwa, duk da ƙirjinta ba wani cike yake taf na wuce misali ba komai dai ya bayyana na yammatanci, dan doguwar rigar jikinta ta fitar da komai, tun daga tudunsu har zuwa shafaffen cikinta da kugunta mai faɗi kaɗan dake tabbatar da nan gaba shekaru suka ƙaru zai sake buɗewa sosai, dan ko a yanzu ka kalleta kasan akwaisu har sunfi na Amima da Ismat ɗin ma dake kusan 27years a duniya. Baƙar fatarta kuwa sai wani sheƙi take da ɗaukar idanun mai kallonta, da gani kasan zatai laushi da sulɓi dan babu ɗigon ƙurji balle tabonsa a fuskata. Kanta ba ɗankwali, hakan ya bayyana gashinta mai yawa duk da kitsone a kanta shiku yama ɗan tsufa. Maganar da Mammah tai ya sakata sakin Hannun Nabeeha datai sumar tsaye, dan ambaton sunan Nimrah da Mammah tayi sai da taji kamar an kwaɗa mata guduma a saman kai ne, ta wani kafe yarinyar da ido ko ƙyaftawa batayi. Hatta su Ismat sunyi wani irin kasare suna kallon Nimrah, dan harta doke hannun Amima data riƙe mata riga ta baya da alama itama tayi sumar tsaye ne. Dan da gaske fa ƴar yarinyar da bata kai ko sha shida ba ta fisu jikin mata, sai dai su nuna mata shekaru kawai da farar fata. To zama a iya jera masu farin nasu gaban maza ɗari su tsallakesu su zaɓi Nimrah ɗin dake baƙa, dan mazan sun gama zige mata da kalmar fara ko mayyace duk sunbi sun kwaile jikinsu yanzu sun dawo baƙaƙen suke kwashewa sukai gidan aure. (Yo ko mijinki kika biyema da kankare can, tada can, ALLAH sai kin gama wahala da kashe kuɗin da ɗorama kanki ciwuka ƙarshe ya auro wadda bata kaiki komai ba ya sota ya tiritata🤣. Kai mata ku dawo habkalinku, babu biyayya ga abokin halitta akan saɓon UBANGIJI. Wanda ya halicceki ya fiki sanin abinda ya dace dake. Kici abinci mai ƙyau da nagarta kiga yanda zakiyi ƙyau, ba shafe-shafe man gyaran fata da ƙarin haske, ko saka gashi da farce, kankare gira shan supplement na ƙarin baya da gaba, ƙarin girar ido kankare haƙori ke saka mace ƙyau ba. Kiyi ibada, kici abinci mai ƙyau, ki kwantar da hankalinki kiga ƙyau hajjaju, wlhy kyau na asali UBANGIJI kawai ke bada shi ba shirme da sabon ALLAH ba. A duk sanda kika damu da yin ƙyau dan burge mutanen duniya sune zasu taru su zageki da tsine miki kafin zuwa gaban UBANGIJI da kika saɓamawa kika nuna bai iya ba sai ke ƴar iya😏🙄).........✍️
KIƊA A RUWA 2