
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 37
.....and she removed herself from his gaze and went towards Mammah. Hannu Mammah took the cup of tea in her hand and said, "Put on your hijab and go to your teacher and he will bring you a magic spell". Nimrah's face was smiling and she happily said, "Well, Mammah. She took the hijab from where they keep it and put it on. Mr. Buba was following her, and she just found herself looking behind him even though her heart was beating. Imran was saying goodbye to Mammah and he called her Pharaoh to come to him on the phone, and he knew it might be Dada. When I reached the gate, she looked at Sayyadi, but she didn't know what he was doing. He looked at Kamal from where he was standing, and he was looking at Mr. Kamal without wasting time she frowned and pulled her body back, while her face was losing its charm.....
.........Imran ya miƙe kenan zai wuce Malam Buba yay sallama. Amsa masa suka yi shi da Mammah, kafin Mammah ta bashi izinin shigowa. Koda wasa bai kalla sashen da Imran yake ba, dan haka kawai yake jin tsarguwa idan Imran ɗin na kallonsa. Daga bakin ƙofar ya rissina ya gaishesu, sannan ya isar da saƙon Nimrah tayi baƙo. Cike da mamaki a tare Mammah da Imran suka furta, “Baƙo kuma?”. Har yanda sukai ɗin ya bama Malam Buba mamaki. Amma sai ya shanye mamakin nasa yay ƙarin bayani da, “Yace malamin su ne na islamiyya, mage ce ya kawo mata, yace kuma itace da kanta ta buƙaci haka.” Mammah tasan labarin mage, dan har Nimrah a kwanakin tana mitar batun kawota da malaminsu baiyi ba. Kusan yanzu ma take jiyosu daga kitchen Nimrah na batun da tasan number sayyadinsu data kira a wayar Biebah ta tuna masa batun magenta. Sunan Nimrah ɗin ta kira, ta amsa tana fitowa daga kitchen ɗin hannunta da kofin tea, ganin sabon driver ɗin su da ko sunansa bata riƙe ba har yanzu ya sata ɗan tsayawa turus, sai kuma ta ɗauke kanta daga kallonsa ta ƙaraso wajen Mammah. Hannu Mammah tasa ta amshi kofin shayin hannun nata tana faɗin, “Saka hijjab kije ga malamin ku yazo kawo miki magen taki”. Washewa fuskar Nimrah tayi da murmushi, cike da farin ciki ta ce, “To Mammah. Ta ɗauki hijjab a inda suke ajiyewa ta saka. Malam Buba na gaba tana biye, haka kawai ta samu kanta da zubawa bayansa ido duk da zuciyarta dake bugawa. Imran na daga ciki sallama yay ma Mammah ya fito dan kiran Faro nata shigo masa a waya, yasan kuma zai iya yiwuwa Dada ne, shi kuma baya son ɗagawa a gaban Mammah dan ko a fuska bai nuna mata fitowar Dadan ba. Dai-dai Nimrah na kaiwa gate, cikin ɗan risinawa ta gaida Sayyadi Kamal daya zuba mata ido. Ita kam kanta a ƙasa batama san yana yi ba. Idanu sosai Imran ya zubama Kamal ɗin daga inda yake tsaye cike da nazari, yayinda shi kuma hankalin Malam Buba yake kan Imran a kaikaice shima yana nazarin kallon da yake ma Kamal ɗin. Nimrah kam bata ɓata lokaci ba ta miƙa hannu amsar kwalin magen. Kamal na murmushi da kallonta ya miƙa mata tare da miƙewa, kaɗan ya matsota yana magana ƙasa-ƙasa. Nimrah ta yamutsa fuska da ɗan jan jikinta baya, yayinda fara'ar fuskarta ke raguwa alamar maganar daya gaya mata ce batai mata ba. Dan kamar wadda take a ƙage ma yana sakar mata kwalin ta baro wajen tana masa sallama da tafiya duk a lokaci guda. A haka ta ƙaraso inda Imran yake tsaye yana kallon Kamal dai dake binta da kallo.. “Daddy kaga mage na”. Nimrah ta faɗa dai-dai tana isowa gabansa, murmushi ya saki yana ciro hannunsa daga aljihu ya amshi kwalin cike da kulawa. Da kansa ya kwance ɗaurin zaren da akaima kwalin yasa hannu ya ciro kyakkyawar magen fara tas ƴar ƙarama. “Masha ALLAH Babyn daughter ta iso gida lafiya. ALLAH ya rayata ta haifa mana yara da yawa duk a raba mana”. “Amin Daddy”. Nimrah ta faɗa cike da farin ciki. Maida mata ita yay a kwalin. “To ya sunanta?”. “Uhmm Daddy sai Ruky ta dawo zamu saka mata suna”. “Oh na manta, Ussaina bata yanke hukunci sai Hassanarta na nan. Bari na wuce idan an saka sunan maji a waya”. Nimrah na dariya ta ce, “Daddy ALLAH ya tsare hanya. Ka gaida Ammie da su Aunty Ma'u gobe zamuzo daga nan muje gaida Grandpa tunda Grandma taƙi dawowa daga ƙauye. Sai mu wuce mu gaida Ummu da Grandpa suma ko”. “Tunani mai ƙyau Daughter, ALLAH ya kaimu. Amma ki kwantar da hankalinki ma su Asma'u suna hanyar zuwa nan gaida Mammah suma.” Wani irin farin ciki ya sake kamata. Tai ciki tana murna da faɗin zataje tai ƙwaɓa fulawa nayin ɗanwake da kalallaɓa”. Fuskarsa da murmurshi ya bita da kallo harta shige. Kasa riƙe abinda yake ayyanawa a zuciyarsa yayi sai da ya ambata, “My Zaki ɗiyata ta zama macen nan da kake tunanin za'a jima bata kai ba, Abu na farko kenan da zai fara baka mamaki idan ka taka ƙafarka a gidan nan”. Sai kuma ya sake sakin murmushi yana girgiza kai saboda hasaso cakwakiyar dake gaba. Har yanzu Nimrah bata san akwai aure a kanta ba, shiyyasa suke kaffa-kaffa da al'amarinta ko nan da can ba'a barinsu zuwa su kaɗai sai da driver ko Mu'azz.. dai-dai yana isowa wajen motarsa, kallon da yaron nan da akace malaminsu ne ya faɗo masa a rai. Juyawa yay ya kalli gate ɗin, sai yaga sabon drivern nan daya sakama alamar tambaya ne kawai a wajen yaron baya nan alamar ya wuce. Lallai dolene yay saurin tsaida wannan alaƙar, dan ya lura akwai wani abu mai girma a idanun yaron game da Nimrah. Mota ya buɗe ya shiga, bayan an buɗe masa gate ya fice yana mai kallon agogon motar dan yana son daga massalaci ya ziyarci Janar ne su tattauna batun ƙarasowar Zak-Shadow gida tunda likitoci sunce bawani damuwa, sai dai sakamakon gwaji ɗaya da ake jira kawai yau ya fito suji......
>>>>>>%<<<<<<
Bayan sakkowa massalacin juma'a gidan Mammah ya kacame da hayaniya. Tuni su Ruky sun dawo gida, ga yaran gidan Uncle Nasiru da matarsa Hajiya Zuwairah da kowa ke kira (Ummu). Yaya Imam, Aunty Halimatu, sai ƙawa aminiyar su Ruky Bintu, da autoci Sadiq da Adam. Hakama daga gidan Daddy Imran akwai Babban Yaya Haysam da suke kira Khalifa, sai Asma'u dake bimasa suna kiranta Aunty Ma'u, Ruƙayya ke bima Asma'u, sai Auta Marwan suna kiransa (Lolo). Yaran Aunty Ummi huɗu suma sun iso, Firdausi itace ke bima Mu'azz, itama sa'anni suke da su Nimrah, sauran uku duk maza ne. Abdul-rasheed suna kiransa Dady, sai Harun, da auta Saddam. Sai na Aunty Mimi itama uku. Ita kam duk maza ne da ita jinjirarta ce kawai nace a yanzu, Fu'ad, Salman, Ishaq. Sai na Aunty Momy huɗu itama. Maza biyu mata biyu. Kasancewar mazan sune manya matan sai suka kasance ƙanen su Nimrah. Itama tana da Na'eem, dan sunan surukinta yaci suke kiransa Na'eem, sai Sauban. Matan Nusaiba, da Khairat. Tunda aka kammala kaya-kayar cin abinci kowa yaja sa'anninsa suka dasa hirarsu. Halimatu da Asma'u suna tare da Aunty Biebah duk da dai ta girmesu, sai dai da yake suma sun gama cika ƴammata sunfi su o'e ƙwailoli iyayen kankanba da rashin ji nustuwa😂. Sai Imam, Mu'azz, Khalifa suma suna ɗakin Mu'azz abinsu matasan samari kenan ƴan shiga jami'ar bana. Suma sauran na ƙasan kowa yaja tashi da irar sai ƙananun sosai su Afrah dake manne da Mammah da Ummu. Ƙawayen juna masu ji da tashen farkon balaga ma dai suna can sun kulle kansu a ɗaki ana cafta. Nimrah, Ruky, Bintu, Feedo. Kai da kaji yanda suke hirar kasan basa ɗaukar kansu fa ƙwailoli sai manyan ƴammata. Dan Feedo ke basu labarin saurayi da tai cousin ɗinsu daya dawo daga karatu Saudiyya shine fa aka baje kolinsu cike da iyayi ana cafkewa......
++++++++++++++
Da ƙyar abokin ma'aikacin hotel ɗin nan ya yarda ya biyoshi kiran Adeel, sai da yazo yaga kuma mai kiran nashi duk ya rikice. Dan duk da bai san waye Adeel ɗin ba a zahiri abubuwan dake zagaye da shi ya tabbatar masa wani shegen duniya ne. Cike da gadara kuwa Adeel ya ajiye masa rafofin kuɗi masu kauri yana sanar masa buƙatarsa akan gidan da yake zaune yake son ya bashi wajen zama a ciki. Sannan ya masa bayani akan gidan su Nimrah. Gaye yaga kuɗi duk ya gigice, yo dala wasa ce. Jiki na rawa ya tabbatar masa da ya amince yazo su zauna. Batun gidan su Nimrah kuwa yace shi ba komai ya sani game da su ba gaskiya, amma yana gaisawa jefi-jefi da wani yaron gidan da safe idan ya fito zaije jugging shima zai je. Fuska a ɗan yamutse Adeel ya ce, “Ba damuwa wannan alaƙar ɗin ta wadatar. Zamu iya wucewa gidan naka yanzu, dan bana son ɓata lokaci. Miye sunan ka?”. Da ɗan rawar baki yana kallon abokinsa ma'aikacin hotel ɗin ya ce, “Yohana!”. “Okay yayi, zamu iya tafiya”. Duk da zuciyarsa na rawa haka ya amince, dan shi da abokin nasa ma suka ɗauki ƙaramin traveling bag ɗin Adeel ɗin daya kasance ƙaramin troly ne zuwa harabar hotel ɗin. Sai dai yabar wasu ɗan abubuwan sa a ɗakin hotel ɗin dan haka da card ɗin buɗe ƙofar ma ya wuce. Kusan ƙarfe takwas suka iso anguwar, ko'ina da haske fes ga anguwar shiru babu hayaniya sai securitys kawai dake kai kawo. Ta gaban gidan su Nimrah suka wuce. Sai Adeel yaji kamar ya sauka anan ya shiga ya ganta. Sai dai babu dama. Tsakanin gidan Yohan da gidan su Nimrah bai wuce gidan huɗu ba. Kuma su suna ɗayan hannun ne ta yanda daga gidajen su Yohan ɗin ma kana iya ganin gate ɗin su Nimrah tsaf musamman idan kana upstairs ne. Can ma gate aka buɗe musu suka shiga, da yake wani ɗan ƙaramin estate ne yake, mai ɗauke da apartment da basu wuce goma ba gaba ɗaya.........✍️