Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 36

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 36

.....that's eight. As for the girl, I don't know if she is his younger sister or the real girl. I didn't get any detailed information about her, she is at home, and she is the maid of the house". The hotel worker, Adeel, explained everything in English. The son and I spoke to him because he doesn't speak his own language, but they both shared the English language. Adeel, who was listening to him, was heartbroken and went to download. Since yesterday evening, when he saw Nimrah, he didn't feel peace in his heart. Today, he has a meeting with the former president, but he couldn't go. He didn't even know the girl's name anymore. He said, "What's her name?" To make sure she was beautiful, his heart was filled with her beautiful pink lips and black eyes.

Standalone post977 words

36

........Ciwon kai sosai ya gallabi Nimrah a makaranta saboda raunin kanta da bai gama warkewa ba. Babu shiri wajen sha biyu aka maidata gida bayan an kaita clinic ɗin cikin makaranta sun dubata. Ba ƙaramin tashi hankalin su Mammah da su Aunty Ummi dake gidan yayi ba. Dan duk ciwon da zakaga ya kwantar da Nimrah haka ba ƙaramin jinsa take ba. Ga jikinta zafi zau da zazzaɓi. Mammah ɗakinta ta Kaita ta kwantar bayan kowa ya gama jera mata sannu da addu'a. Da kanta ta zame mata uniform ɗin jikinta ta barta da vest da shot kawai, ita ta goge mata jiki da ruwan sanyi tasa aunty Mimi ta ɗakko mata riga mara nauyi a ɗakinsu. Aunty Shariffa ta kawo mata kunun madara, da ƙyar aka lallaɓata tasha tana hawaye dan ji take kamar kan zai rabe mata biyu, kaɗan tasha kunun tasha magani Mammah ta kwantar da ita tana tofa mata addu'a har barci ya ɗauketa......

<<<<<★★★★>>>>>

“Sir na bincika kamar yanda kace. Gidan nan gidan wani soja ne, akwai mahaifiyarsa a ciki da ƙanensa, amma shi yana ɗaure shekaru takwas kenan. Ita kuma yarinyar ban sani ba ko ƙanwarsa ce ko ƴa gaskiya. Dan ban samu wani cikakken bayani a kanta ba, a dai gidan take, kuma ƴar gidan ce”. Gaba ɗaya ma'aikacin hotel ɗin yayima Adeel bayanin ne da harshen turanci, dan da shi suke magana kasancewar shi baya jin yarensa shima baya ji, amma dukansu sunyi tarayya akan yaren turanci. Ajiyar zuciya Adeel dake saurarensa ya shiga saukewa. Dan tun marecan jiya da yaga Nimrah bai sake jin cikkiyar nutsuwa ba a zuciyarsa. Yau ɗin nan yana da zama da tsohon shugaban ƙasa, amma bai iya yaje ba saboda ba waccan damuwar bace yanzu gabansa ta yarinyar da ko sunanta bai sani ba ce. Hatta su Nabeeha bai sake bi takansu ba. Ko wanda yasa yana bibiyarsu da yazo da safen nan masa bayani kamar yanda ya bashi umarni cayay yaje kawai yana buƙatar hutu. Da turancin ya ce, “Miye sunanta?”. “Nimrah!”. Sai da ya wani lumshe manyan fararen idanunsa ya buɗe sannan ya saki murmurshi. Dan kuwa sunan ya dace da ita. Dan a cikin sakannin da suka haɗu ya tabbatar da ita ɗin zakayyarce, zuciyarsa ta shiga wassafo masa ɗan mitsitsin bakinta na tsiwa mai ɗauke da kyawawan lips pink da baƙi. Yanda ta zazzaro masa dara-daran idanunta farare tas masu suffar ƙwai da masa gargaɗin kada ya taɓata da yaren da bai gane komai ba. Ya saki ƴar dariya da sake hango idanunta da suka watsa masa harara. Galala ma'aikacin hotel ɗin yay hana kallonsa, dan lallai ya yarda wannan guy ɗin ya faɗa da yawa. Koda yake baiga laifinsa ba. Dan yaran fa sun haɗu, su duka biyun wanke hannu ka taɓa ne. Daga gani kasan ƴan hutu ne kuma ƴan gata ƴaƴan manyan ƙasa. Duk da basu wani gama cika manyan ƴammata ba ko a haka za'aje da su, damma a cikin hijjab suke ba komai nasu ake gani ba face fuskoki..... “Ka samo number wayan ta?”. Adeel ya katse masa tunani. Kansa ya girgiza da faɗin, “A'a Sir, bayan waɗan nan bayanan babu abinda na samu gaskiya. Dan gidan nan ba ƙaramin gida bane da samun information ɗinsu zai mun sauƙi. Wannan ma sa'a akaci na ga wanda na sani a street ɗin, shima kuma bai wani jima da kama haya ba.” “Good kaje ka zomin da shi”. Kai ya jinjina masa a ransa yana mamakin irin wannan haukacewa haka daga ganin yarinya? To amma ina ruwansa, aikin kuɗi yake yi, ya tabbatar kuma idan Adeel ya samu abinda yake so shima zai ja kaya. Dan Vvip ɗin da ya kama kawai ya isa ya sanar dakai mugu-mugun mai kuɗi ne shi. Balle manyan agogo da designers kayansa zuwa takalmi, kai wayar hannunsa kanta kai kasan lallai akwai manda. Dan zai iya rantsuwar bai taɓa ganin irinta ba balle kamfanin da ake yinta. (😜Ƙaryar marubutan ta motsa anan. Ya kuka iya🤣 ku karanta kawai🥱. Amma in gaskiya za'abi ai akwai masu kuɗin nan dai ko🥱😎). Hannu Adeel ya ɗaga masa, ya ɗan risina na girmamawa sannan ya fice.....

>>>>>>>%<<<<<<<

Kamal na ƴar dariya da shafa kai ya ce, “To kusan haka baba, amma ai da sauran lokaci tunda nasan baza'a mata aure yanzu ba nima kuma haka”. “Kai! A wannan shekarun naka?”. “Baba tsahon ƙafa ne kawai, amma ba wasu shekaru bane dan ashirin da biyar ne kacal”. “To ai sune dai-dai auren ɗana. Mutum ya more yanda yake so ba auren bariki ba sai an gama tsofewa a ɗakin soro. Mu kaga iyayenmu sun mana gata a sha tara ma suka mana auren”. “Baba sha tara fa?”. “Sosai. Ba gashi mun mora auren yanda ya kamata ba. Itama kuma ai in a ƙauye ne yanzu ta isa haihuwa ma ta biyu ko ya yaye na farko tana da cikin na biyu. Shekara sha biyar fa tana cikin ta sha shida koba haka ba?”.. “Tabbas haka ne Baba”. “To ka gani, ai karka wani damu kanka, ka fara yaɗa manufa kawai muma zamu tayaka”. “To baba ALLAH ya tabbatar mana da alkairi”. “Yawwa haka nake so naji ka faɗa”. Cewar Malam Buba yana miƙewa. Ya cigaba da faɗin, “Kaga jirani bara na kirata, dan naga kwana biyu ma bata zuwa makaranta sunce bata da lafiya. Kwana kusan biyar kenan taji ciwo a islamiyyar su ne...” Cike da jimami Kalam ya amsa masa da, “Haka ne Baba, wlhy a islamiyya ne fa.....” Ya kwashe labari tsaff ya sanar masa. Malam Buba dake saurarensa cike da nazari yay wani murmushi mai ma'anoni da yawa. Dan kuwa tabbas yau ya samu hanya mai sauƙi da yake nema da fata. Tabbas Kamal shine zai kasance makamin amfaninsa akan cimma burinsa kan Nimrah. Labarin nan kuwa yay masa matuƙar daɗi da ɗaukar hankalinsa. Tuni ya nufi cikin gida kiran Nimrah.........✍️