
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 35
.....he had no plans to lean against the wall, his hand was holding the Presidential Pardon paper that he and his father were holding, which was heavier than paper in his hand, it was like the weight of a stone. Just then, a soldier who was with him moved a little and wanted to speak, but CSP Alpha waved at him with a warning of fear and uncertainty.... "Go! Go all of you...!" His voice came out a little thick, full of giving orders like adults. The soldiers immediately left the place, but their hearts were jumping, the jump they made sure that if it goes beyond the heart, it will come to the tongue, they will regret it forever. So everyone put aside what they heard and saw here for a while and there was silence. In particular, they were given a real warning as if they were chosen for the matter... Then CSP Alpha also remembered what President General Yusuf had said to him two days ago on the phone... "Keep your secret more than your life. If you make a mistake, I will not be able to protect you from the security agency or from the people outside who are waiting for Zak-Shadow. And whoever knows about this matter before the right time, you yourself should guide him to his afterlife
35
.......... ★PRISON★
9:30am dai-dai motocin sojojin biyu suka fice daga cikin prison ɗin cikin tsaro mai cikakken sirri, yayin da hukuncin UBANGIJI da ƙarfin ikonsa suka tabbata a daidai wannan lokacin wani razani ya gitta a zukatan wasu mutane daga ɓangaren Ƙungiyar duhu, a ƙasan rayukansu suka dinga jin cewa abu mafi hatsari ya faru. Sai dai daga ina? Daga wane yanki? Akan mi? A dalilin mi? Duk UBANGIJI ya toshe wannan amsoshin daga garesu, koda ata hanyar yaransu dake cikin prison ɗin babu wani labari da suka samu saboda gargaɗin shugaban ƙasa......
★A ɓangaren su CSP Alpha shugaban prison bayan fitar motocin su Imran biyu sai wajen ya sake nutsuwa takar an ɗora dutse a zukatansu, ga iskar da suke shaƙa ji suke kamar ta rikice da wani irin nauyin da babu mai iya fassara shi. CSP Alpha bai iya ya motsa daga tsayen da yake ba har bayan an kulle ƙofar gate ɗin. Jikinsa ya ƙara sanyi, numfashinsa na fita a cure, zuciyarsa ta kumbura cikin ƙirjinsa. Jin tamkar hajijiya na neman zubar da shi babu shiri ya jingina da bango kaɗan, hannunsa na riƙe da takardar Presidential Pardon da yake jinta da uban nauyin da yafi na takarda a hannunsa, ta koma mata tamkar nauyin dutse ne. Dai-dai nan wani sojan da ke tare da shi ya matsa kaɗan yana son yin magana, amma CSP Alpha ya kaɗa masa ido cikin gargaɗin tsoro da rashin tabbas.... “Ka tafi! Ku tafi ku duka…!” Muryarsa ta fita da ɗan kauri cike da bada umarni irin na manya. Kai tsaye sojojin suka bar wajen, sai dai zukatansu nata tsalle-tsalle, tsallen da suka tabbatar da in ya wuce zuciya yace zai zo kan harshe zasuyi nadama ne ta har abadan. Dan haka kowa ya ajiye abinda yaji ya kuma gani anan dan wata shirun tafi alkairi. Musamman ma daya kasance an musu gargaɗi na haƙiƙa dan tamkar an zaɓesu ne akan al'amarin... Sai a lokacin shima CSP Alpha ya tuna da maganar da shugaban ƙasa janar Yusuf ya yi masa kwanaki biyu da suka gabata a cikin waya… “Ka kiyaye sirri fiye da kiyaye rayuwarka. Idan ka yi kuskure, ba zan iya kare ka daga hukumar tsaro ko daga mutanen dake a waje suna jiran Zak-Shadow ba. Kuma wlhy duk wanda ya san wannan al’amari kafin lokacin da ya dace, to kai kanka ka yi masa jagora zuwa lahirarsa”. Wannan kalamai ne da har cikin jinin CSP Alpha suke da tasiri mai saka razani da ƙaulanin zuciya har yanzu. Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi, goshinsa ya cika da zufa. Hannu ya kai ya sharce gumin, kafin ya furta da ƙasa-ƙasa kamar mai roƙon iska. “Ya ALLAH an sakani a tsakiya?. Wane irin mutum ne wannan Zak-Shadow ɗin da shugaban ƙasa ya zo kan al'amarinsa haka da gaggawa?”. Bashi da amsa, babu kuma mai bashi ita a yanzu. Dan haka bai yiwa kansa dogon tambaya ba ya haƙura. Tsoron da yake ji game da maƙudan mutanen da ke bayan fage ya fi ƙarfin neman amsoshin tambayoyin nan dake danƙare a zuciyarsa.......
<<<%>>><★><<<%>>>
Tunda suka baro cikin prison ɗin shiru ya ratsa motar, sai sautin AC da numfashin su dake fita iyakar motsin ƙirazansu. Baradan jaruman haziƙan sojojin uku Imran, Faro, Zak-Shadow. Ba wanda ya ce komai. Kowa da abin da yake tattaunawa da zuciyarsa. Sai rufaffen gilashin motar da ke nuna hasken rana daya fara zafi, launin duhun sa ya bayyana fuskokinsu dake da sanyin annuri. Daddy Imran yana kallon Dada akai-akai tamkar idan ya ɗauke idanun nasa zai ɓace masa ne, ko yana son tabbatarwa wannan ba mafarki ba ne. Faro dai sai murmushi yake yi irin wanda yake nuni da cewa (Na gaya maku wataran ƙaddara da ƙarfin ikon wanda ya fiku iko zai dawo da shi a duniyar ku). Amma shi Dada ya rufe idanunsa cikin nutsuwa, yana fitar da numfashi a hankali da shaƙar mai tsabta fiye da duk wanda ya shaƙa a cikin shekaru takwas. Yawan jin idanu a kansa dan in har ana kallonsa sai yaji a jikinsa, balle wannan kallon yana jin ƙarfin idanun mai su a cikin ƙirjinsa. Ya kuma tabbatar da Imran ne ke da wannan tasirin. A hankali ya buɗe idanuwan nasa, sai ko suka sauka kai tsaye akan Imran ɗin da yay hasashe. Hararasa ya ɗanyi, tare da ɗage masa gira ɗaya, da murya ƙasa-ƙasa amma cikin zurfi ya furta, “Kallon fa?”. Ƙaramar dariya Imran yayi da faɗin, “Ina tsoron karka sake ɓace min ne”. Kauda fuska Dada yay kaɗan da sakin ƙaramin murmushi, batare daya tanka batun Imran ɗin ba ya sake jeho masa sabuwar tambaya. “Motar nan ina take son kai mu?” Daddy Imran ya ɗan taɓe baki da matsawa kaɗan ya jingina da kujera. Shima cikin salon raɗa ya ce, “Wurin da ba wanda zai same ka. Wurin da babu ƙungiya, babu siyasa, babu duhu. Wurin da zaka samu iska ta ƴanci bayan shekara takwas daka rasa”. Dada ya girgiza kai a hankali tare da lumshe idanu ya buɗe a lokaci guda. “Na gode muku Imran, Faro, na gode sosai.” Kafin Imran yace wani abu Faro ya katse su cikin siririyar dariya mai armashi da jin daɗi. “Zaki wlhy idan ka sake irin wannan sakon godiyar, zan fara tunanin da gaske zaka canja halinka.” Dada ya kalle shi yana murmushin ƙasaita sai kuma ya maida kansa ya kwantar a jikin kujera ya lumshe idanunsa har lokacin da murmushi a kan fuskarsa. Sai a lokacin ya furta, “Ga shi kai baka da ranar canzawar da wannan sa idon naka”. Dariya Imran da Faro suka sanya, cikin irin dariyar da ta bayyana ƙyallin ruwan hawaye daga idanun Imran da ya kasa ɓoyewa.... Dada dake murmushi zuciyarsa ta tafi sabon tunani. (Shugaban ƙasa da kansa ya yanke wannan hukuncin da gaggawa? Mi yasa? Mi ya faru da ƙasata cikin wannan lokacin? Mi ake shirin bani? Mi ake buƙata daga gare ni?). Kafin ya samo amsoshin waɗan nan tambayoyi masu nauyi Imran ya katse shi da faɗin, “Muna da tsaro mai ƙarfi, babu wanda zai kusance ka har sai ka shirya. Koda likitoci sun gama duba ka zaka cigaba da zama a ɓoye. Babu wani abu da zai kusanto ka. Sai mun kammala gyara rashin adalcin da aka yi mana, dan ƙasa tana buƙatar komawar ka a Zak-Shadow ɗin data sani ne. Mammah zatafi farin ciki idan ta ganka a Haysam ɗinta itama. Balle kuma ƴaƴan Dada”. Dada ya ɗan furzar da numfashi da buɗe idanunsa dake a rufe, zuciyarsa cike da wani nauyin da bai gama wargajewa ba. Tabbas a yanzu ba wanda ya fi buƙatar son fara gani kamar Mammah da ƙannensa, amma zai daure ya jure dan yasan duk yawan kwanakin da suke so yayi anan bazasu kai yawan wanda yayi a baya ba. Shima zai fi son Mammah ta gansa cikin ƙyaƙyƙyawan kamanni ba wannan kamannin da yake a yanzu ba da zasu iya raunana zuciyarta har ta gagara mantawa da su. Numfashi ya sauke a hankali, a yanayinsa na Zak-Shadow da suka sani ya furta, “Imran kun tabbatar babu wanda ya san dawowa ta?”. “Ai ko motar nan ta bari wasu suka ji Zak-Shadow ya dawo, ta riga ta mutu.” Imran ya ƙare maganar yana dariya mai taushi. Faro ma hannu ya ɗaga yana dariya da faɗin, “Duniya zata san dawowar ka ne lokacin da ka yanke hukunci, ba lokacin da kowa yake jin yanada ƴancin faɗar abinda ya gani ba koda Imran da Faro da shugaban ƙasa ne.” “ALLAH ya shiryeku, yau kuma kun zama ƴan comedy”. Cewar Dada yana ɗaukar takardar dake gefensa. Yanzun ma dariya suka sanya, dan har ƙarƙashin zukatansu suke jin wannan nishaɗin mara misali. Shi kansa Dada yana jin fiye da nasu, kawai dai ya fisu kamewa ne, sannan halayyar su dama can ba ɗaya bace, su sunada faran-faran da magana, sabanin shi da ko wasa bai iya ba, dama dai da Imran ne wani lokacin idan ya matsa masa, sai shima Faro ɗin idan ya gallabesa wasu lokutan yakan maida musu murtani.....
⭐ 10:43am dai-dai Motocin biyu suka isa secret medical base wuri na musamman mai tsafta, nutsuwa, da ƙa’ida. A yanda gurin yake a killace zaka ɗauka Shugaban ƙasa yasa an tsara shi ne tamkar dan ɓoye Dada ɗin ne anan. Dan tuni har likitoci suna jiran su, likitoci kam na musamman ne aka tanada dan duba lafiyarsa, saboda duk ƙarfin halin da Dada ke nunawa su sun san abu na farko da yake buƙata shine duba lafiyar tasa. Sun masa tarba ta girmamawa suma, dan duk da halin da yake ciki kwarjinin yawan ibada da UBANGIJI ya bashi yana nan a tare da shi sai ma ƙaruwa da yayi da sake ɗaga darajarsa ga duk mai kallonsa. Received at Shi ɗin DODO ne a kowane irin yanayi, dan haka a nutse yake bin komai da aka shirya da nazari irin na masu nutsuwa: Kayan aiki, ma’aikata, da tsaro mai ƙarfi. Sai da Idanunsa suka gama tantance kowanne daga cikinsu, kamar yadda yake nazarin duk wanda zai shiga cikin binciken sa. Imran dake lure da shi ya saki murmurshi ya juya kansa zuwa ga Faro. “Faro, ka tabbata babu wanda zai san dawowar sa.” Faro daya fahimci saƙon da Imran ke son isarwa ya ɗaga hannu tare da kashe masa ido ɗaya ya ce, “Babu wanda zai sani, har sai lokacin da Zak-Shadow ya yanke hukunci.” “Kayi ƙyan kai Faro. Lokaci zai bayyana komai da kansa. Duk wanda ya ga fitowarsa ba a shirye ba kuwa zai zama....” Imran yay alamar mutuwa. Su suke maganar, amma Dada nazartar likiticin daya tabbatar su su Imran kema wannan zaurancen yake. Ganin yanda suka duƙar da kawuna yasa shi fahimtar suna fahimtar komai suma. Baiyi magana ba yay gaba kai kace yasan wajen ne. Da sauri likiticin suka zabura dan masa jagora, Imran da Faro suka sake kallon juna da murmurshi, sai suma sukabi bayansu..........✍️