
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 34
.....and he went to the middle, taking his phone that was on the side and holding it tightly. He reached his ear, but he said briefly, "You can come out". Then he hung up the phone. There was silence in the hall, then the sound of the TV coming out downstairs and the AC. In less than five minutes, someone came out. At least he will not be more than thirty-six years old. He was also very excited and took one look at Almu. He had to sit on the chair and that man was looking at him with a smile that he hadn't seen on his face since Almu came in. Almu shows that he is fixing his seat. "This is the man I'm telling you about. He's been working as a guard at the house for about four years now, after we fired him because he couldn't do anything for us." "Is he doing what he wants?" The young man spoke for the first time. "Of course he does. Ever since he started working, there have been no mistakes and unpleasant conversations. His name is Almu." "Okay". He said briefly. The man did not show that he was worried and continued to say, "Are you ready to go together? Or will you follow him later?". "Let's just go through it, the metal is being hammered with heat. But I should know what work I
34
..........“Almu na maka kiran gaggawa ne saboda ƙarin abokin aiki da zaka samu”. Cikin tashin hankali maigadi ya ɗago yana kallon mutumin dake zaune cikin lallausar kujerar ƙayataccen falon. Sai kuma ya sake maida kan nasa ƙasa da sauri. Zuciyarsa na bugawa da yin rawa a cikin ƙirjinsa ya furta, “Ranka ya daɗe nawa aikin baya tafiya dai-dai ne?”. Sai da mutumin yaja fin sakan uku kafin ya amsa cike da isa. “Aikin ka na tafiya dai-dai Almu, anzo gaɓar da shima wannan ɗin dole sai ya shiga gidan ne”. “Shike nan ranka ya daɗe, yanda kace haka za'ai. Ni dai ALLAH ina sake roƙon arziƙi kada a cutar min da ƴar uwa. Kaima ka sani mu marayu ne, bamu da kowa a wannan duniyar sai kammu mu biyun nan rak.” “Bijirema umarni na ne kawai zai iya sakawa ta cutu. Idan ka kiyaye ta kiyaye lokaci kaɗan ya rage muku ku samu freedom.” “Zamuyi duk abinda kake buƙata in sha ALLAHU ranka ya daɗe. Amma dan ALLAH zan iya ganinta?”. Wani banzan kallo daya saka maigadi sake nutsuwa mutumin ya watsa masa. Sai kuma yaja tsaki yana ɗaukar wayarsa dake gefe yay danne-danne. Kunnensa ya kai, sai dai a taƙaice ya furta, “Zaka iya fitowa”. Daga haka ya ajiye wayar. Shiru falon ya ɗauka, sai ƙarar tv dake fita ƙasa-ƙasa dana ac. Cikin abinda bai gaza mintuna biyar ba wani ya fito. A ƙalla dai bazai wuce shekara talatin da shida ba. Shima cike da tashi izzar yay ma Almu kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Sai da ya zauna a kujera sannan wancan mutumin dake kallonsa fuska da murmurshin da tun da Almu ya shigo bai gani a fuskarsa ba. Almu ya nuna yana gyara zama. “Wannan shine mutumin da nake gaya makan. Yana aikin gadi a gidan kusan shekara huɗu ke nan, bayan mun tsige wancan ganin bazai iya mana komai ba.” “Shi wannan yana yin abinda ake so kenan?”. Saurayin yay magana a karo na farko. “Tabbas yana yi, dan tunda ya fara aiki babu wani kuskure da zance mara daɗi. Sunansa Almu.” “Okay”. Ya faɗa a taƙaice. Mutumin bai nuna ya damu ba ya cigaba da faɗin, “Zaka shirya ne ku wuce tare? Ko zaka bishi daga baya?”. “Kawai mu wuce taren, ai da zafi-zafi ake dukan ƙarfe. Sai dai ya kamata nasan wane aiki zan iya samu a gidan?”. Yanzu kam mutumin baice komai ba, illa juyawa da yay shima ya kalla Almu. Da sauri Almu yace, “Ranka ya daɗe sai dai in munje can ɗin, amma a yanzu gaskiya a gidan nan babu wani aiki. Dama a wata biyu daya wuce ne driver ɗinsu ya samu hatsari to da an samu sai ya maye gurbinsa. Amma yanzu ma inada tunani guda, akwai mai sharar tsakar gidan kullum da bama filawoyi ruwa. Yakan zo da safe yayi ya dawo da yamma. Sunyi-sunyi ya dinga zama nan koma kwana yaƙi, acewarsa yana wasu ayyukan ne idan ya kammala da nan. To ko shi zamu tunɓuke ta hanyar maƙarƙashiya sai shi ya maye shi?”. “Eh wannan ma kazo da zance mai ƙyau. Amma miyasa ban san da labarin driver ba? Bayan kuma na sanar maka ko sabuwar kaza akai a wannan gidan nasan da ita. Ko cokali ya faɗi nasan da sautin ƙarar faɗuwarsa....” “Ka gafarceni ranka ya daɗe, na nemeka amma ban samu ba, idan baka manta ba jiya daka turo min saƙon kana son ganina na tura maka amsa da dama inada wata magana. To dama maganar kenan”. Maimakon amsa zancen sai cayay, “Kaje waje ka jira shi zai fito”. Idanun Almu cike da ƙwalla ya jinjina kai. Yayi kamar zai miƙe sai kuma ya sake komawa ya duƙa. “Ranka ya daɗe dan ALLAH ko zan iya ganin ƴar uwata ɗin?”. “No!”. Ya bashi amsa a ɗan tsawace. Da sauri maigadi ya miƙe jikinsa na rawa ya fice a falon. Idanunsa kuwa tuni sun cika da ruwan hawaye. Zuciyarsa kam raɗaɗi take masa. Tabbas badan da ƴar uwarsa da mutanen nan suke amfani wajen juyashi yanda suke so ba sun san basu isa ba. Shine fa Almu, Almu na babba ƙarfe bashi ratsa jininka. Guduma mai fasa kan tantiri.... Ƙwafa yayi yana mai cije laɓɓansa, daga haka ya samu waje a bakin baranda ya zauna......
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° A gidan Mammah rashin barcin wuri saboda murnar dawowar Uncle Bilal yasa yau kusan kowa sai da ya makara. Gasu Nimrah zasu je makaranta tunda an koma hutu. Ganin yanda lokaci yaja suka so lanjarewa akan bazasu je ba, gashi yau monday fa. Amma Uncle Ammar ya buɗe musu wuta dole suka shirya suna faman ɗaga baki. Uncle Bilal dake biye musu kuwa suna fitowa ya fara lallashinsu, ƙarshe yace shine ma zai kaisu school ɗin da kansa. A take bakunansu suka washe da farin ciki, dan suna matuƙar ƙaunar Uncle Bilal. Breakfast ɗinsu aka shirya musu a lunch box Mammah tace suci a mota. Sun fito Mu'azz na tsokanarsu wai sun zama su Abees ƴan Nursery, Uncle Bilal ne yace karsu kulashi, dan haka harara kawai suka zuba masa suka shige mota. Tunda suka ɗauki hanyar school suna karyawa suna ma Uncle Bilal hira, duk da kuwa jiya babu kalar labarin da bai sha ba da ƙyar suka barshi ya kwanta. Su Aheel ya fara saukewa a tasu school ɗin, su Rukyn suka taimaka masa ya raka su har ajinsu yay magana da class masters ɗinsu. Dan Aheel da Abees ajinsu ɗaya. Afrah da Ayyan ma haka. Basu ɓata lokaci ba suka fito suka koma mota. Suma har aji Uncle Bilal ya raka su, sunyi sa'a Teacher Khalil ne a ciki. Ya gaisa da Uncle Bilal cikin mutunci kasancewar sun san juna. Sannan ya bada hakuri akan makarar ƴaƴan Mammah. Fuskar Teacher Khalil da murmurshi ya ce, “Ba komai Uncle ai yau da gobe sai ALLAH. Sai nazo gida cin tsarabar turai.” Ƙaramar dariya Bilal yayi da faɗin, “Sai kazo ina nan ina jiran ka.” daga haka yayma su Nimrah bye ya wuce. Ƴan ajin kam da yawansu sun ƙyasa, yo sunga handsome masha ALLAH. Cike da neman magana Nimrah taja tsaki da taɓe baki tana magana cikin ƙunƙuni. “Mudai kar a cinye mana uba, naga mayu sunyi yawa a ajin nan haba irin wannan kallo haka kamar sabbin kwartaye”. Dariya Ruky ta sanya, sai kuma tai saurin toshe baki saboda tunawa akwai Teacher Khalil a ciki. Kuma sarai yaji mi Nimrah ɗin ta faɗa da dariyar Rukyn. Dan kai tsaye ya juyo daga rubutun da yake akan allo. Sai dai baiyi magana ba, suma duk sun wayance sun ɗauka books kamar basu suka aikata ba. Yayinda mafi yawan ƴan ajin suka shaƙa da baƙar maganar Nimrah, sai dai sun san ba damar maida murtani Zakanya da Damisa su daki banza. Hibba dai tunda taci duka a wajensu take neman shishshige musu ayi ƙawance. Amma wulaƙanci irin na Ruky da Nimrah sai yarfata suke.....
★★★
“Wai Mammah ko duk farin cikin dawowar Bilal ne. Tunda na shigo gidan nan na fahimci farin cikin ki a bayyane yake”. Murmurshi Mammah ta sake yi tana kallon Aunty Ummi mai maganar, ganin suma su Shariffa da su Mimi sun zuba mata ido sai ta sake sakin murmurshin da faɗin, “Inaga dawowar Bilal ɗin ce, dan yau kam wani farin ciki mai girma da ni kaina na gagara misaltashi ne zagaye da zuciyata. Dan haka na saka su Kulu suyi abinci mai yawa a fitar sadaka.” Addu'a suka shiga jero mata da fatan ALLAH ya ƙara mata farin ciki da nisan kwana masu albarka. Ta amsa musu da amin tana shafa kan Mimi data kama hannunta ta sumbata. Dai-dai nan Bilal daya dawo daga kai su Nimrah school ya shigo falon. Ture Aunty Mommy abokiyar karawar tasa yay daga kusa da Mammah ya zauna yana faɗin, “Mi ake tattaunawa auntys.” Aunty Mommy dake harararsa ta ce, “Anƙi a faɗa ɗin. Kawai dan neman faɗa kazo ka wani ture ni, da kama samu nazo ganinka tuzuru kawai”. Cikin dariya Bilal dake amsar Babyn Aunty Mimi a hannun Aunty Lailah ya ce, “Humm kwantar da hankalinki yarinyar nan, kwanan nan kalmar nan ta tuzuru zaki bar faɗarta ne.” Cike da zumuɗi Aunty Mimi ta taso ta dawo kusa da shi. “Dan ALLAH da gaske Yaya Bilalu? Dan ALLAH guntsa min wacece?”. “Uwar gulma kenan”. Cewar Bilal. Dariya gaba ɗaya suka sanya. Aunty Shariffa ta ce, “Wlhy dama nasan sai ka faɗa haka. Dan ALLAH a bamu musha Yaya Bilal. Dama gidan shiru kwana biyu babu shagali dan ma mun ɗan rage da sunan Baby Nawal ne”. “Aunty Shariffa karki damu, lokaci ne zaku sani, amma shagalin biki sai Dada na nan in sha ALLAHU”. A take falon yay tsitt, Dan shima yayi maganar ne muryarsa na ɗan rawa. Mammah ce tai gyaran murya, dan tasan yanzu zasu fara mata koke-koke. Cikin canja hirar ta ce, “Mudai yanzu tashi ka ɗakko mana tsarabar mu nan duk ita mukai zaman jira”. Cikin dariya Bilal ya ce, “Kai Mammah harda ke? To kowa yay haƙuri baza'a buɗe tsarabar nan ba sai yarana sun dawo school gaskiya. Dan sune zasu buɗe ta”. “Yau muna ganin jalala, har sai su kafi auta sun dawo za'a bamu tsarabar?”. Yanda Aunty Lailah tai maganar yasa kowa fashewa da dariya........✍️