
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 33
.....in. All this behavior that you see Adeel doing is very afraid of following the rules of his family. Neither Nabeeha, nor the daughter of the president of this country, our descendants will not let him marry. Maybe the Europeans in the area should let him do that, they are more esteemed than the African people who respond to the name of black people. We are only slaves to them, slaves who will serve them in houses and factories, and slaves who will quench their thirst with humiliation and ridicule. There are very few of them who look at people, let me give you a small example. It is said that a Muslim is a brother of a Muslim, but even in Saudi Arabia, if you are religious, have you never noticed how when you join the prayer line with the one who pulls his ears, he is trying to prevent his body from falling? If they don't want to be disappointed in the ranks of worshiping the same LORD, assure them that there is no difference between them and us, except for those who fear him, how can they come to join us in such a great deal? So I will prove to you again that Adeel has a goal to follow Nabeeha, there is a goal he wants to achieve and I don't think it is a desire."
33
..........Fuskar former First Lady ɗauke da murmushin ƙasaita take kallon Hajiya Hasiba, sai kuma ta girgiza kai da faɗin, “Hummm.. Adeel! Adeel. Yanzu kina nufin tare da shi kuka zo ƙasar nan?”. “Sosai kuwa ranki ya daɗe. Dan yanzu haka ma yana masauki. Kuma abinda na sanar miki ya ambata ne ya kawo shi, wato kashe Haysam. Sai dai bamu san ta wace hanya zaibi ya tabbatar ba”. “Yana da daman bin kowace hanya, dan yana da ƙarfin ikon dukiya da sunan zuri'ar gidansu. Sai dai abinda ke ban mamaki wace manufa yake da ita akan Nabeeha har haka? Dan nasan Adeel matuƙar sani, nasan al'amarinsa akan mata. Tabbas idan yana a giyar kwaɗayin tarayya da mace komai yana iya aikatawa, da zarar ya cika burinsa kuma shike nan.” “Amma yana iƙirarin auren Nabeeha zai yi ai. Shiyyasa ma ya iya juriyar shekaru kusan tara kenan a kanta.” Murmurshi mai haɗe da ƴar dariya First Lady tayi. “Bazan ce miki ƙarya yake kai tsaye ba Hajiya Hasiba, sai dai zan iya miki yaƙinin ba haka bane ainahin abinda ke ransa. Duk wannan iskancin da kike ganin Adeel nayi yana matuƙar tsoro da bin dokokin ahalinsa. Ba Nabeeha ba, ko ƴar shugaban ƙasar wannan ƙasar tamu zuri'arsa bazasu bari ya aura ba. Maybe da a yankin turawa ne su barshi yay hakan, dan sunfi ɗaukarsu da kima da daraja fiye da al'ummar yankin Afirika da suke amsa sunan baƙaƙen fata. Mu a wajensu bayi ne kawai, bayin da zasu musu bauta a gidaje da masana'antu, sannan bayin da zasu gusar da kishirwarsu cike da wulaƙantarwa da izgili. Ƙalilan ne a cikinsu masu mana kallon mutane, bari na miki ƙaramin misali mana, Kinga dai ance musulmi ɗan uwan musulmi ne, amma ko a saudia idan kinje ibada baki taɓa lura da yanda in kika haɗa sahun salla da mai jan kunne ke ƙoƙarin hana gangar jikinsa raɓar taki ba?”. “Tabbas nasha ganin hakan ranki ya daɗe”. “Good. Idan har basu so baƙin fata a sahun bautama UBANGIJIN daya tabbatar musu su da mu babu banbanci ba sai wanda yaji tsoronsa ta yaya zasu zo mu a haɗaka ta mu'amula mai girma irin wannan? Dan haka zan sake tabbatar miki ƙarya Adeel yake yana da manufa akan bibiyar Nabeeha, akwai burin da yake son cimmawa kuma bana jin na sha'awa ne”. “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un kai biri yayi kama da mutum gaskiya. Bazan ɓoye miki ba kullum cikin yima kaina irin tambayar nan nake. Sai dai ganin yanda take masa rashin kunya da nuna halin ko'in kula balle nuna jin haushi kan shafe min tantama ta. Yanzu ranki ya daɗe minene mafita? Kin san mutumin nan nada ƙarfi, kota wace hanya zaibi dan cimma manufarsa a kammu”. “Tabbas zai bi, dan shafe babin rayuwar ɗan adam ƙaramin aiki ne daga tarin ƙananun ayyukansa. Sannan kunyi gangancin sanar masa mijin Nabeeha na rufe ne, duk da nasan idan yaso sanin hakan zai yi koda bata hanyar ku ba. Yanzu kije gida ki bani lokaci zanyi tunani, abinda na yanke zan kiraki mu haɗu ko nazo gidan na sameki, shima kuma zan je har masaukin nashi duk da banda isasshen lokaci, saboda gobe zamuje gidan gwamnati domin ganawa da sabuwar First Lady. Kin san ɗan takarar CSP candidate ɗin Excellancy ne. Dama nayi niyyar nemoki a satin nan kizo ƙasar saboda rantsuwa da akai, sai kuma gaki ALLAH ya kawo ki ma duk da an riga an gama dai”. “Ranki ya daɗe duk abinda kuke so zamuyi, ni dai a taimaka na fara maganin wannan matsalar dan samun nutsuwa”. “Karki damu Hasiba. Idan ta kama Excellancy ya shiga wannan maganar zai shiga. Zan saka ya nema Adeel da kansa koya gayyato shi nan gidan idan ALLAH ya ɗaura mu akansa dan abune mai wahala yazo ɗin. Amma zamu gwada sa'ar mu”. “Nagode sosai ranki ya daɗe. ALLAH ya bar zuminci. Ya tabbatar da nasarar ku daga nan har ƙarshen rayuwa”. “To amin Hasiba”.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ★★..10/9/2021..★★ 🔥8:55 AM🔥
Duk da kasancewar hantsi ya ɗaga kurkukun ya yi shiru yau fiye da kowanne rana. Tun 8 aka kammala basu abincin safe kamar yanda komai yake a tsari aka saka kowa komawa ciki saboda baƙin sirri da zasu shigo. Sai irin su Dada da ba'a bari su fito sai da ƙwaƙwƙwaran dalili dan haka kai musu akeyi su har ɗakunansu. Received at 12:27 A bakin ƙofar gate 8:55am motocin sojoji ne masu duhun glass guda biyu suka tsaya kamar taurari a cikin duhun dare. A motar farko kawai aka sauke gilashi ƙasa tare da miƙama securitys ɗin ƙofar takarda. Suna duba abinda ke ciki suka ƙame jikinsu tare da salute ɗin motocin. Kafin da hanzari a wangale musu ƙofar suka shige a jere. Basu tsaya ko'ina ba sai a ƙofar sashen da Dada yake. Inda shugaban prison ɗin da kansa ke tsaye tare da jami'an soji na gidan guda uku alamar jiransu suke dama. Sai da sojojin ɗayar motar suka gama fitowa da hanzari suka zagaye wajen kafin a buɗe ta ƙarshen. Col. Imran Abbas ne a ciki, cikin farin kaya na musamman bana soja ba, sai Brig. Haydar Usman Galadima (Faro). Cikin nutsuwar girma irin na masu kamewa suka fito a hankali, a take sojojin da suke tare da su harda na cikin prison dake tare da shugaban su suka ƙame tare da sara musu. Suna ajiye hannu shugaban prison ya ƙaraso shima gabansu, ƙame jiki yay shima tare da salute nasu irin na girmamawa, suma sai suka ƙame ɗin sukai salute ɗinsa na girmamawa. Hakan na nufin kowa ya girmama girman kowanne, dan su duka ukun kowanne nada matsayin girmama ɗan uwansa a dokance. A karo na biyu sukai musabaha, kowanne fuska da murmushin mutunta juna. Kafin Colonel Imran Abbas ya miƙa takardar Presidential Pardon ga shugaban prison. Sai da ya ƙame a karo na biyu yay salute ɗin Imran sannan ya amsa takardar. Shima sai Imran ɗin ya sake salute nashi a karo na biyu idanuwansa sun yi kaifi tamkar yana hango duk wani inuwa da zata takura masa a cikin idanun shugaban prison, sai dai babu dama, babu dalilin bijirewa. A karo na farko, kai tsaye Brig. Haydar Usman Galadima ya furta, “Muna so a fito mana da Lieutenant Colonel Haysam Abdul-rasheed Shehu yanzu.” Duk da shugaban prison yasan abinda ya kawosu kenan sai da numfashinsa ya tsaya cak na wucin gadi, jikinsa yay wani yamm kamar an jefasa da dusar kankara. Amma bashi da zaɓin daya wuce bin umarni na zahiri da gaskiya. Gudun kada yaransa dake zagaye da shi, da yake da tabbacin akwai idanun ɓoyayyun mutanen da suka kawosa wannan gidan suka ɗora a wannan kujerar yasa ya ɗanyi jarumtar son cizawa. Murya a takure ya furta, “Sir… zuwa yanzu babu wani…” Cikin zafi Imran daya gama fahimtarsa ya katsesa da faɗin, “Shi kawai muke buƙata a gabanmu. Wannan umarnin shugaban ƙasa ne. Ko akwai wani daga cikinku da zai ce bai san ma’anar wannan tambarin ba?”. “I'm sorry, Sir!”. Shugaban prison ya faɗa yana ƙara ƙamewa. Kafin ya juya yayma yaransa umarni da idanu. Duk da mamaki na neman kashe da yawansu saboda fahimtar abinda ke shirin faruwa basu da zaɓin daya wuce bin umarnin suma. Dole da sauri suka shige domin zartar da abinda aka saka su.....
★A dai-dai lokacin da suke ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakin, Dada na zaune ne ya idar da sallar walha yana karatun Alqur'ani. Motsin buɗe ƙofar da shigowarsu bai saka ya dakata ba balle kallonsu. Dan haka suma suka tsaya tsamm alamar jira. Sai da ya kwashe mintina biyar cir da shigowar tasu sannan ya rufe Alkur'anin yana mai ɗagowa ya kallesu. A tare suka nuna girmamawar soja, kafin suyi gaisuwa da sanar masa umarnin da aka basu. Maimakon amsawa idanu ya lumshe a hankali, sai kuma ya kife zuwa sujuda. Minti biyu cir kafin ya ɗago. Ya ɗauki Alkur'anin sa ya maida inda yake. Sai kuma a dai-dai nan jami'ai biyu dake tare da su Imran suka shigo. Suma sunyi gaisuwar sannan suka fara tattara kayansa na buƙata masu muhimmanci. Komai baice ba, sai bin ɗakin da yay da kallo, kallo irin na bankwana da tuna abinda ya shuɗe, kafin ya juya a hankali ya nufi ƙofa jami'an farko suka take masa baya.....
A hankali ƙofar corridor ɗin ta buɗe. Sai kowa ya sake nutsuwa da zubama ƙofar ido musamman Imran, Faro, shugaban prison. Yaran sojojin uku da suka rage a wajen kawunansu a ƙasa na girmamawa. Sakan goma tsakani jarumin jarumai ya bayyana, bayyanar data saka gaba ɗaya sojojin wajen harda su Imran ƙamewa a tare suka sara masa.Sai da ya lumshe idanunsa ya buɗe a kansu, sannan shima ya dunƙule hannaye duka yana ɗan miƙasu gaba alamar amsar girmamawar su. A karo na biyu, shugaban prison, Imran, Faro suka sake ƙamewa da sarawa irin ta girma da girma. A yanzu kam shima sai ya ƙame ya sara musu su ukun murmushin mai nauyi ya bayyana a fuskarsa. Kai tsaye ya saka idanunsa cikin na Faro da shima ke murmushi, ido ɗaya Faro ya kashe masa da sake yin wani salute na abokantaka da amintaka. Dada ya girgiza kansa yana murmusawa da yima Faro alamar (bazaka taɓa canjawa ba) da idanunsa. Sai kuma ya janyesu a slowly ya maida kan Imran da ya tsaya cak kawai yana kallon sa shima. Idanusu ne suka haɗu cikin juna, shekaru takwas na ɓacin rai, rashin adalci, fushi da raɗaɗi duk suka bayyana cikin wannan idanuwa huɗun tamka a film ɗin da aka dannama pause. Zak-Shadow ya sakarma Imran murmushi cikin nauyin zuciyar da ya saba ɓoyewa. “…Imran Abbas?”. Dada ya faɗa a karo na farko da wani irin salo na jini yaga jini. Imran ya saki murmurshi tare da matsawa kusa da shi gab, sai kawai ya rungumeshi. “Shagwaɓaɓɓena”. Dada ya faɗa cikin kunnen Imran jin saukar hawayensa akan kafaɗarsa. Share hawayen yayi sannan ya ɗago yana murmurshi. “Alƙawarin ALLAH ya cika. Rubutacciyar ƙaddara daga littafi na gaskiya ta taƙaita. UBANGIJI ya tabbatar mana zai jarabcemu, sai dai da jarabawar nan zai ɗaga darajojinmu a sama idan mun kasance masu haƙurin cinyeta. Ƙasarka ta jira dawowarka. Zuri'a bata manta da kai ba. Rundunar soji na kwatance da sunanka. Bararka da zuwa mai son a gina gaskiya a zartar da ita koda zata ƙona kai da kai. ALLAH ya cigaba da amintar da wannan RUHIN bisa kyakkyawan gini na gaskiya. A yau zan buɗe muryar data disashe saboda kukan kewa na faɗama duniya cewar Haysam Abdul-rasheed Shehu is back again”. Murmurshi Dada ya saki mai nauyi, zuciyarsa ta rikice da son fitar da abinda ke zagaye da ita na kewa tsahon shekaru, ba dan prison ba, ba don wahala ba, sai dan kalaman Imran dasuka ratsata har cikin jini da jijiya dama ƙashi. Amma da yake mazan maza ne sai suka rikiɗe da ƙarfafa kai bayyananne. Da nayin kamewa da nutsuwa ya furta, “Imran! You are my destiny. I am proud of you........✍️