Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 32

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 32

.....when they passed by this place, he got his attention and told them to come in. He saw that carpets were being sold. In English, he told him what Nimrah said. He just laughed. He is alive in his soul (That is, she thinks she is a woman, don't touch her). In fact, when he went outside, he ended up leaving, but he stopped in their car and stared at the way in and out with his eyes.... Soon Nimrah came out and Mu'azz followed them. In front of their eyes, they all got into the car, and when he saw one Imam answering the steering wheel, he started the car and also got into them, telling his companions to follow him. He didn't deny it since it was a financial job. He kept following them behind in such a way that they would not recognize him until home. From there, they stopped a short distance away, until the car entered and the gate was closed. Adeel directly said, "What is the name of the street? And whose house is it?". The hotel staff shook him by saying, "I don't know whose house it is. But the name is KOBI STREET." He repeated the name of Kobi Street in a broken tongue, before saying, "Okay, can you bring me again tomorrow?". "May I drink ALLAH Sir!". With a smile on his face,

Standalone post1,764 words

32

.........Ba ƙaramin motsawa zuciyar Adeel tayi ba, batare da ya shirya ba ya saki murmurshi mai faɗi yana ƙare mata kallo. Sake balla masa harara Nimrah tayi tana bin Ruky dake jan hannunta sukai ciki. Yako lumshe idanu ya sake buɗewa a kansu. Zai iya rantsuwa tunda yake bai taɓa ganin baƙar fatar data gama tafiya da duniyarsa lokaci guda irin yarinyar nan ba. Gata dai ba wata ƙatuwar budurwa ba, hasalima a ƙasarsu bata wuce babyn raino ba, amma tayi masifar tafiya da dukkan zuciyarsa. Abin mamaki kuma ba irin son da yake jin yanama matan baya bane na sha'awa, wannan wani baƙon al'amari ne mai girman gaske a gareshi da ban mamaki... “Oga ya dai?”. Wanda suke tare ya faɗa yana taɓa shi. Juyowa yay ya kallesa, sai kuma ya ɗan sake murmusawa da faɗin, “Mi ta faɗa ɗazun?”. Murmurshi wacan ɗin yayi, duk da bai san wanene Adeel ba a matsayi na rayuwa balle ma ƙasar da ya fito. Dan kuwa daga hotel ɗin daya sauka ne ya buƙaci ɗan rakiya zaga gari shine aka bashi ma'aikacinsu ɗaya da mota, har sun wuce wajen nan ya ɗauki hankalinsa yace su shigo dan ya ga harda kilishi ake saidawa. Cikin harshen turanci ya sanar masa abinda Nimrah ta faɗa. Kawai sai ya sanya dariya. A ransa yana raya (Wato ita tana jinta wata mace ce karna taɓa ta). A zahiri kam waje ya ƙarasa fita, sai dai ya tsaya a jikin motar su ne ya zubama hanyar shiga da fitar idanunsa.... Babu jimawa kuwa su Nimrah suka fito su Mu'azz biye da su. A gaban idanunsu duk suka shiga mota, sai da yaga Imam daya amsa tuƙin yanzu ya tada mota sannan shima ya shiga tasu yana faɗama abokin tafiyar tasa su bisu. Bai kuwa musa ba tunda aikin kuɗi yake. Haka ya dinga binsu a baya ta yanda bazasu gane ba har gida. Daga can ɗan nesa kaɗan suka dakata, har motar ta shige aka maida gate ɗin aka rufe. Kai tsaye Adeel ya ce, “Ya sunan Street ɗin? Sannan kasan gidan waye?”. Kai ma'aikacin hotel ɗin ya girgiza masa da faɗin, “Ban san gidan waye ba gaskiya. Amma sunan nan ɗin KOBI STREET.” Sunan Kobi Street ɗin ya maimaita da karyayyen harshensa, kafin yace, “Okay zaka iya sake kawoni gobe?”. “In sha ALLAHU Sir!”. Fuskarsa da murmushi yace, “Muje inda zan samu layin ƙasar nan da waya”. “Okay Sir”. Daga haka suka bar wajen.

____

A cikin gida kuwa tunda su Nimrah suka fito a mota sabon driver malam Buba dake tsare da gate a yau ya zuba mata ido. Duk yanda yaso daurewa sai ya kasa, sai da ya iso inda suke yana tambayar lafiya kuwa yaga bandeji a goshin Nimrah ɗin. Imam ne ya bashi amsa a taƙaice da cewar “Ciwo taji a islamiyya”. Itako da tunda tai masa kallo ɗaya tsigar jikin nata ta fara tashi ta kauda kanta. A taƙaice ta gaisheshi kamar kowa sukai gaba ita da Ruky. Haka ya bisu da kallo yana jin kamar ya bisu ciki. Sai dai ya danne zuciyarsa da ƙar, amma can ƙasan rai ayyanawa yake (Lokaci yayi da zai fitoma Nimrah ɗin a mutum tasan shi ɗin waye). A ciki ma hankalin Mammah da su Aunty Shariffa ba ƙaramin tashi yayi ba. Dan su Yaya Ja'afar sun tafi Airport ɗaukar Yaya Bilal dake gab da sauka, tuni sun cire mata hijjab suna duba wajen. Sai ita ke magana cikin shagwaɓa da son kwantar musu da hankali tana faɗin, “Babu fa zafi. Tunda aka min allura ya daina ciwo”. Faɗa Aunty Biebah ta fara akan cewa bazasu yarda ba, gobe sai taje islamiyyar da kanta dole yaron nan a hukunta shi. Sai da Mammah tai maganar “Baza'a kai ga nan ba. Tunda ance kuskure ne to a barshi a hakan ALLAH ya kiyaye gaba.” Badan sun so ba suka haƙuran. Amma Mu'azz dama ya ayyana a ransa sai yaci uban yaron tunda shima islamiyyar yay sauka, yanzu kuma weekend kawai suke zuwa Tahafiz shi da Aunty Biebahn. Ɗaki suka wuce yin salla. Mammah tace Biebah ta bisu tasa towel a ruwan zafi ta gasa mata goshin da fuskarta. Da to ta amsa tana bin bayan nasu...

<<<<<<<。⁠◕⁠‿⁠◕⁠。>>>>>>> ★RANTSUWA★ A yau sati uku da fadar da tabbatar da Janar matsayin shugaban ƙasa ta cika, a yau kuma ake shirye-shiryen rantsar da shi da shiga gidan gwamnati da aka kammala gyarawa tsaf. Tuni a cikin sati ukun nan ya kammala komai akan fiddo Dada, office kawai yake fatan shiga ya zartar da hukunci. Yanda kuma suke komai a sirrance daga shi sai Imran, da Haydar yasa zai mamayi mutane da yawa akan wannan kyakkyawan ƙudiri nasa. Kamar yanda aka tsara an gabatar da rantsuwa tako wane fanni a ƙasar, sabbin shugabanni da wanda suka sake komawa tenure ta biyu duk sun shiga gidan gwamnati a wannan rana ta litinin tare da sabbin ofisoshin su. Sai dai mu cigaba da musu fatan alkairi da nasarar yin adalci ba satar kuɗaɗenmu ba😝🏃🏼‍♀️. (Mai son soyayya da ɗan shugaban ƙasa tamun magana mu sasanta ta biya cin hanci na haɗasu🥱💃. In baki da ko sisi karma kizo😏🙄🤭🏃🏼‍♀️.)

★A yau daren farko na sabon shugaban ƙasa Janar Yusuf Shu'aibu Tafida cikin gidan gwamnati. Tsaye yake cikin ƙayataccen falon daya kasance na ƙarshe sai bedroom ɗin barcinsa, tunda ya shigo gida bisa rakkiya bai buƙaci ganin ko ɗaya daga iyalansa ba, sakamakon son fara zartar da babban birinsa. Komai kashe yake a falon in ka cire ac kawai shima ba'a wani sakashi da ƙarfi ba, an sauƙaƙa hasken fitilu gaba ɗaya dan falon na cikin ɗan duhu-duhu, zaune yake shi kaɗai kamar yanda yafi buƙata, tunaninsa gaba ɗaya ya tsaya ne akan mutum guda ɗaya, mutumin da yake ma kallo mafi muhimmanci na farko da zai shimfiɗa wannan mulkin mai cike da cakwakiya da ƙalubale kashi-kashi da shi, dan tun a yau ɗaya da fara shigarsa office ya fahimci hakan. Saboda haka bazaiyi ƙasa a gwiwa ba ko sakaci, yana buƙatar Haysam Abdul-rasheed Shehu a cikin wannan tafiyar tasa tamkar yanda ƴan ƙasa ke buƙatarsa koda basu san muhimmancin sa a garesu ba. Ƴar ƙarar buguwar agogon dake bango falon ya katse tunaninsa, numfashi ya sauke a hankali, dan ƙarar ta bugane tamkar da bugawar umarnin zuciyarsa dake ambaton (lokaci ya cika, ka fitar da takardar zartarwa kawai, rikicin da kake kallo da ƙalubalen bai fi nauyin burin nan naka ɗaya ba, cikashi tun a wannan daren masalaha ce ta zuciya da kwanciyar hankali ka, fitar Zak-Shadow daga dunkulallen makircin da aka garkame shi cikin kurkuku tsawon shekaru takwas itace zai tabbatar ma masu shirin mamayeka kai ba kurar wasansu bane, aiki kazo yi ga ƙasa da al'ummar ƙasa ba aikin aljihunansu ba). Cike da gamsuwar shawarar zuciyarsa ya sauke numfashi, cikin nutsuwa ya ɗauki wani file da takarda a cikinsa mai tambarin ofishin shugaban ƙasa (Presidential Seal). Wannan shi ne takardar ikon afuwa da zai miƙa wa Ministan Tsaro, wanda zai tafi kai tsaye zuwa hannun Babban Hafsan Rundunar Sojin Ƙasa. Duk da yasan aikin bamai sauƙi bane a garesu; dan akwai al’amuran cikin gida da ya sani zasu taso, munafukan dake da hannu akan lamarin Haysam, waɗanda ba a san ainihinsu ba har yanzu, amma yasan zasu bayyana ne da wuri akan wannan fitar ta Haysam, dan dole suna da tasiri a cikin gwamnati harda tasa kamar yanda Haysam ɗin ya faɗa. Shi kansa daya samu wannan mulkin cikin sauƙi duk da yasan komai hukuncine daga UBANGIJIN, amma sanin wacece wannan ƙasar tasu akwai tambayoyi a ransa: Su wanene ainihi? Kuma me yasa Zak-Shadow ya zama barazanar da suka ƙuduri aniyar kawar da ita? Miyasa kowa Haysam dai Haysam dai?. (Fitar tasa ce zata baka hasken samun wannan amsar) Zuciyarsa ta ayyana masa. Murmurshi ya saki mai ƙayatarwa cike da gamsuwa ya ɗauki wayarsa dake gefe. Kai tsaye number Imran yay kira.....

★A yau gaba ɗaya Imran ya kasa barin office har zuwa wannan lokacin, zaman jiran kiran mutum ɗaya tak yake, kuma bazai ƙosa da wannan jiran ba daga nan har wayewar gari in sha ALLAHU. A dai-dai wannan lokacin da Shugaban kasa ke neman layinsa yana tsaye jikin windown ofishin sa yana kallon titin da ke cike da motocin jami’an tsaro. Rabonsa da cikakken barci tun dare shekaran jiya, gaba ɗaya barci ya gushe masa a cikin idanu tun bayan samun saƙon shugaban ƙasa ta text message bayan kammala rantsuwa. Dan haka ya ƙare wannan yinin gaba ɗaya da ƙagautar jira, jiran kiran Janar da a yanzu ya shigo wayar tasa a bazata. Jikinsa har tsuma yake wajen kai hannu ya ɗaga. “Assalamu alaikum Your Excellency…” ya faɗa cikin ladabi da kuma farin ciki da bai iya ɓoyewa ba. Janar daya fahimci ƙagautar Imran a bayyane ya saki murmurshi, batare da jan rai ba ya furta “Imran, lokaci yayi. Takardar afuwa ta kammala.” Ya ɗan yi shiru, irin shiru mai nauyin tasiri, kafin ya cigaba da faɗin, “Ina so ka shirya tawaga mai tsabta. Ba na son hayaniya, ba na son labari ya fito. Ka tabbatar da babu wanda idonsa ke buɗe a kanku”. Da wata irin sauke ajiyar zuciya mai masifar nauyi Imran ya lumshe ido cikin jin daɗin kalmar da ya dade yana jira kamar mafarki. Muryarsa na rawa ya furta, “Za’a yi sir. Da izinin ALLAH Zak-Shadow zai fito gobe ƙarfe tara na safe.” “Good. Kai nake son ka jagoranta Imran. Na san kai kaɗai zaka iya tsallake duk wata inuwa daga ƙalubalensu. Zaku wuce inda na tanada dan duba lafiyarsa da saituwar al'amarinsa. Ka tsare shi da ranki. Har sai ya koma randa zai dawo ƙasa ya zama barazana, dan Zak-Shadow nake son a gani ba firsinan shekara takwas ba”. Daddy Imran ya murmusa, murmushin jarumi wanda ya dace da mai ɗauke da nauyi mai girma na tsakanin soja da dangi. Sai da ya ƙame tare da salute sannan ya furta, “Na rantse da ALLAH za’a yi fiye da umarninka Sir. Ba zan bari koda iska tai barazanar kaɗa nauyin daya rage masa ba kafin ka gan shi duniya ta ganshi zuri'armu su ganshi.” “I'm proud of you, Soldier”. “Thank you, Sir. I'm proud of you too”...

Daga haka suka katse kiran, amma zuciyar Imran kamar zatayi tsallen kwaɗon sojoji dan farin ciki. Sai da yay sujidar shukur sannan ya miƙe bakinsa ya kasa rufuwa dan murmushi, ji yake kamar UBANGIJI ya sauke masa wani babban nauyi daya toshe bugun zuciyarsa a tsawon shekaru. Wayar ya ɗauka ya tura sako ga ɗaya daga manyan abokan amana da zai jagoranci motar sirri zuwa prison wato Haydar Galadima (Faro)........✍️