
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 31
..... trusting him with her wealth and knowing the big people who are involved in business that they don't say anything about (🥱đź¤đ꤫), or this beautiful house of his has been destroyed like turning a tin can upside down on a plate 🥱🤣. Now Adeel is getting wet. Although there is no fatigue with them, everyone is cautious. They all went down to the ground floor and took a deep breath, the manager and his wife came to them with their goods and greeted them. They were barely able to get up after a while and went over the top of them all. They all have rooms to sleep in, even Mamawo is not a very good resident in the country. They started to introduce themselves and asked for food. They finished eating and everyone asked for a place to stay. They didn't wake up until about twelve o'clock. So they bathed and looked for food. Sunko got Joy to finish everything by noon, they sent him to eat and everyone was shocked. Around three o'clock, Nabeeha said she wanted to go to her house to get something. A message from Mamawo to their Momyn who gave birth to her with misfortune. At first she was silent, but later she started crying. It was their body and it was cold, so Momyn said that she is ready
31
........Sun iso cikin dare. Kasancewar a babban birnin suka sauka yay bucking hamshaĆ™in hotel na gani na faÉ—a da yafi kowane hotel tsari da Ć™ayatarwa. Su kuwa gidan Hajiya Hasiba suka sauka. Dan tun a can ya nuna musu baya son asan tafiyarsu É—aya da shi har ya kammala aikin nasa su koma. Ba laifi gidan babba ne sai dai ba Ć™ato ba. Six bedrooms ne. Sai faluka guda uku. Akwai na baĆ™i da bedroom É—aya, sai falon Ć™asa shima da bedrooms 2, sai upstairs da falo da 3 bedrooms shi kuma. Akwai kitchen a Ć™asa. Sai can gate akwai É—akin maigadi. Shi kaÉ—aine kuma a gidan da matarsa da yaransu biyu. Kasancewar idan suna nan itace ke musu aiki. Dan haka tun suna can ta sanarma maigadin zuwansu. Haka matar ta yini yau tana Ć™alĆ™ale gidan, da yamma mai musu abinci tazo tai musu, sai da ta shirya komai a dinning sannan ta wuce dan dama ba'a nan take kwana ba. Tun kan Hajiya Hasiba ta shiga siyasa tana da kuÉ—i, dan kuwa tako wace hanya nemansu akeyi. AlaĆ™arta da manyan Ć™asar musamman first lady ya sake armasa dukiyarta da sanin manyan mutane da ake harkokin da basai ance komai ba (🥱đź¤đ꤫), ko wannan gidan Ć™yautarsa aka bata sukutum kamar juye alalar gwangwani a plate 🥱🤣. A yanzu kuma ga Adeel ya ida jiĆ™eta. Duk da ba wata gajiya ce a tare da su ba kowa sai wayyo-wayyo yake yi. Duk suka zube a falon Ć™asa suna sauke numfashi, maigadi da matarsa nata kai-kawon shiga musu da kaya da jera musu sannu. Da Ć™yar suka iya tashi bayan wani lokaci suka haye sama su duka. Dan duk can suke da É—akunan barci har Mamawo É—in ma daba wani zama take sosai a Ć™asar ba. Wanka suka fara gabatarwa sannan suka nema abinci. Suna kammala ci kowa ya nema makwanci. Basu tashi farkawa ba a washe garin ma sai Ć™arfe kusan sha biyu. Haka sukai wanka suka sakko Ć™asa neman abinci. Sunko samu Joy ta kammala komai har na rana, aiko suka far masa da ci sai da kowa yay Ć™at. Wajen Ć™arfe uku Nabeeha tace tana son zuwa gidanta É—akko wani abu. Aiko daga Mamawo har Momyn tasu suka hayayyaĆ™o mata da masifa. Da farko shiru tai musu, sai daga baya ta saka musu kuka. Jikinsu ne kuma yay sanyi, dan haka Momyn tata tace ta shirya amma su Ismat ne zasu rakata su dawo tare, amma yau yamma tayi ta bari sai gobe. Bata musa ba tace ta yarda.......
<<%>><<%>><<%>>
Kamar kullum yau ma a dai-dai lokacin da aka saba tashinsu islamiyya aka tashe su. Kasancewar Yaya Mu'azz ne ya kawosu sun tabbatar bazai zauna zaman jiransu ba kamar driver har zuwa yanzu. Sai dai zai dawo ya ɗauke su. Su duka zukatansu cike suke da zumuɗin komawa gida saboda Uncle Bilal, dan ba ƙaramar kewarsa sukai a watannin nan da baya nan ba. Sune farko fitowa a aji, ajin nasu kuwa daga shi sai na ƴan sauka, duk da suma dai gab suke da kaiwa sittin ɗin in sha ALLAHU. Hayaniyar dake tashi a ajin ƴan saukar ne ya daki kunnuwan su Nimrah da suka fara fitowa, kallon juna sukai ita da Ruky, sai kuma suka nufi ajin da sauri dan ganewa idanunsu abinda ke faruwa. Gaba ɗaya ajin ya hargitse da ɗaliban ƴammata da samarin cikinsa, dan kuwa sun girmi su Nimrah su zasu iya kaiwa sha bakwai ne. Yanda suka dunƙule waje guda suna jefe-jefen takalmansu yasa Nimrah data kutso kai cikinsu kallon abinda suke jifar. Abin takaici abin mamaki ba komai bane sai mage. Wata baƙar mage ce da jariran ƴaƴanta biyu, ɗaya fari tas ɗaya baƙi da kwalliyar golden a jikinsa. Mai kwalliyar golden ɗin na kwance kansa da jini alamar wani ne ya jefesa, farin kuwa ya maƙale jikin uwar da itama har an jimata ciwo sai wani irin nishin kuka take. Ai bama tasan ta zabura inda magen take ba jikinta na rawa. Ihu ƴan ajin suka fara mata da kiran karta je ba mage bace aljana ce ko wata mayyar ta rikiɗa tunda ance mayu na zama mage, amma kota kansu batabi ba ta ƙarasa. Hannu ta saka ta ɗauki magen ta rungume, tare da ɗaukar farar itama dake jaririya abin sha'awa, tana kai hannu zata taɓa golden ɗin dake kwance a ƙasa kawai cikin ƴan ajin wani ya wulwulo dutsina har biyu. Ai ko ɗayan ya sauka akan magen babba ɗaya akan Nimrah. Juyowa Imam yay yana hararar Ruky da tai maganar. Kafin yace wani abu cikin sake lanjarewa Nimrah ta ce, “Dan ALLAH Yaya. ALLAH su Afry ma naso ko?”. Ta juya tana kallon su Aheel. Magiya suma suka fara. Sai lokacin Mu'azz daya ɗan juyo ya hararesu ya sake maida kansa ga titi sannan yay magana. “Ku yaran nan kun cika nemarwa mutane hanyar kashe kuɗi. Ga asarar salla a jam'i da kuka jawo mana. Wai kun manta yau Uncle Bilal zai dawo ne” Su dai basu kula faɗansa ba suka cigaba da maguyarsu duk da ransu cike yake da farin cikin batun dawowar Uncle Bilal da zaiyi a daren nan. Sai da yay ƙwafa sannan ya rage gudun motar. Canja hanya yay zuwa inda yasan ana saya musu ice-cream ɗin da suke so. Basu wani jima ba suka iso. Har zasu fito ya hararesu yana faɗin, “Ina zaku bimu da uniform a jiki ace satoku mukayi, ke kuma ga rauni a kai”. “Abinda ba'a ganin ciwon na rufe da hijjab. Dan ALLAH ka barmu muje”. Nimrah ce mai maganar cikin tura baki. Mu'azz zai ƙara magana Imam ya ce, “Barsu dan ALLAH Bro. Muje, muna sake tauye lokacin salla ne kawai a wannan surutun”. Ba yanda Mu'azz ya iya yayi gaba suka bishi, Ruky harda masa gwalo. Su Imam na gaba riƙe da hannayen su Abees, su kuma suna biye da su, suna gab da shigewa Ruky ta riƙe hannun Nimrah ta tsayar da ita, batare da tayi magana ba takai hannu tana gyara mata hijjab ɗinta ganin bandage ɗin kanta ya fito. Hakan yasa suka rigasu shigewa. Dai-dai suma suna ƙoƙarin shigewa suna gulmar su Mu'azz ɗin ƙasa-ƙasa suka kusa cin karo da mutanen dake ƙoƙarin fitowa. Da sauri Ruky tai baya tana jan hannun Nimrah, sai dai cikin rashin sa'a ta tafi zata faɗi, a cikin waɗan can ɗin ɗaya yakai hannu zai riƙota. Cike da tsiwa ta ce, “Malam miye haka, karka taɓani”. Duk da da hausa tayi, bai ji mita faɗa ɗin ba saboda ba yarensa bane yanda sautin muryarta mai cike da tsiwa ta daki kunnensa sai ya tsaya cak, tare da ɗago manyan idanunsa ya kalleta. Sai akai sa'a kuwa dai-dai itama ta balla masa harara...........✍️