Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 71

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 71

.....name, but she is slowly struggling to remember who they are. Although there is childhood with her, she will never forget her family members, especially her aunt and uncle Tanimun, and their national team mates Lawwali. She didn't burst into tears, it was a matter of things coming back to her in her life with Kawu Tanimu in their village. She was in this state of crying for a while before she wiped her tears, her heart assured her that now is not the time to cry, it is the time to calm down and check the truth, when she should know who she really is? When to find out who is Dada and who is Daddy Imran? When knowing this word, every word is great for her, that is the word that came out of Daddy Imran's mouth. (Marriage) She could not understand at all, whose marriage? She felt like Daddy Imran said she and Dada. (I don't think it's right) A part of her heart said. Then she was satisfied with that. She stood up and put everything back where it was. Despite the fear clinging to her heart. But she began to think how to control the secret that she found today in her heart, she began to understand that her mother was in a big story, and there is a danger that will affect her life. Th

Standalone post1,514 words

71

.........Nimrah kam maimakon komawa falo ɗakin su ta shige, ta dannama ƙofar key tana sauke ajiyar zuciyar jin daɗin ganin Ruky bata ciki. Kai tsaye wadrobe ɗinsu ta nufa, can wani lungun wadrobe ɗin data san hankalin Ruky zai daɗe bai je ba ta zaro abinda Dagger ya bata watanni biyu da suka shuɗe. Ƙasa ta zauna share-share ta zazzage. Hotuna suka faɗo. Hoton farko data fara cin karo da shi shine hotonta, kuma abin mamaki exactly irin wanda ta gani a ɗakin Dada yanzu. Sai dai na nan ma biyu ne, ɗaya tana a cikin kwalla, ɗaya tana a hannun Dadan jikinta duk jini. Hoto na biyu Ummanta durƙushe tana kuka a gaban Dada, akwai sojoji kusan biyar tare da shi. Ɗayan sojan shima taga hoton shi a ɗakin Dadan, an rubuta Captain Musa, sai wanda ke gefen haggunsa yana miƙa masa bindiga shi kuma Ojo taga ansa a nashi hoton acan ɗakin Dadan dai. Sauran hotunan ta cigaba da bi ɗaya bayan ɗaya, mabanbanta fuskoki, yara da manya, harda Iya kakarta. Wasu kuma sai ta jima tana kallonsu ma dan ta manta suna, amma kuma duk a hankali take ta faman tuna su wanene. Dan duk da akwai ƙuruciya a tare da ita bazata manta ƴan gidansu ba, musamman Iya da Kawu Tanimun ta, da abokan wasan ƙasa su Lawwali. Ai bama tasan ta fashe da kuka ba, dan abubuwa ne ɗai-ɗai ke dawo mata a rayuwarta da Kawu Tanimu a ƙauyen su. Ta jima a wannan yanayi na kuka kafin ta share hawayenta, zuciyarta na tabbatar mata yanzu ba lokacin kuka bane, lokacin nutsuwa da bincika gaskiya ne, lokacin daya kamata tasan ainahin wacece ita ne? Lokacin gane waye Dada waye Daddy Imran ne? Lokacin sanin kalmar nan da tafi kowace kalma mata girma ne, wato kalmar data fita a bakin Daddy Imran. (Aure) Ta kasa fahimta sam, auren waye? Sai da taji kamar Daddy Imran yace ita da Dada. (kai ina bataji daidai ba ne) Wani sashi na zuciyarta ya faɗa. Sai taji ta gamsu da hakan. Miƙewa tai ta tattare komai ta maida inda yake. Duk da fargabar dake manne da zuciyarta. Amma ta fara tunanin yadda zata sarrafa sirrin da ta tsinta yau a zuciyarta, ta fara fahimtar cewa mahaifiyarta ta kasance cikin wani babban labari, kuma akwai haɗari da zai shafi rayuwarta. Akwai ɓoyayyen al'amari daga zuriarta da tushenta da ake ɓoye mata kuma ya kamata ta sanshi. Sai ta ɗan yi murmushi mai ciwo, tana tunanin yadda Mammah zata ji idan ta san ta tsinci wannan. “Yanzu ya kamata in fara tunani… amma yadda zan yi, ba komai ba ne.” ta faɗa a zahiri hankalinta na sake komawa akan hotuna da videos ɗin baya masu gogayya da juna. Tabbas duk abin da ta gani, yana haifar mata da tunanin cewa lokaci ya yi da zata fara fahimtar gaskiya da kuma ɗaukar mataki. Sannan dole tai amfani da wayonta akan Dada, ta cusa kanta jikinsa cikin hikima ko hakan zai sa taga fiye da abinda ta gani a yau, sannan tasan ainahin waye shi, ainahi fuskar da yake ɓoyewa da ƴan uwansa basu sani ba. Daga yanzu WASAN YA FARA...... Da wannan ta shiga bayi ta wanke fuskarta tayo alwalar la'asar da ake kira. Koda ta fito gaban mirror taje ta canja kwalliya sannan ta shimfiɗa abin salla. Dai-dai nan Ruky tai knocking ƙofar, buɗe mata tayi. Ruky na shigowa ta rungumeta cike da farin ciki tana faɗin, “Albishirin ki Ninah?”. Cikin dauriya Nimrah dake murmurshi ta ce, “Goro”. “Ammy haihuwa zatai”. Idanu sosai Nimrah ta waro waje da faɗin, “Haba dai?”. “Wlhy, gata can ma zasu tafi asibiti. Tun ɗazun na ƙagara ki gama gyara ɗakin Dada ki sakko ai. Mammah ma bata sani ba sai yanzu. Ni da Small Mom da Mamy kawai muka sani dan muna sashen tun ɗazun.” Duk da damuwar da Nimrah ke ciki hakan bai hanata nuna farin cikinta ba. Salla sukai suka fito. Zuwa lokacin mazan gidan ma sun san halin da ake ciki. Dan har an wuce da Shariffa asibiti. Da wannan damar Nimrah tai amfani wajen zare jiki ta nufi gate, cikin sa'a ta samu Sanda kawai zaune maigadi ma salla yake, da alama sallar la'asar ce baiyi ba duk da ba'a jima da kammalawa ba. ALLAH ya sota, tana amsar wayar ta zagaya baya Dada da Imran da suka dawo salla na shigowa gidan, wuff Sanda ya shige bayinsu yana danne ƙirjin sha da ƙyar, dan yau kam ALLAH ne ya yabawa aya zaƙinta da sai anyi kaciɓus tsakaninsa da Dadan, duk da ba Dada kawai ba shi fa har Imran wasan ɓuya yake da shi daman. Shi kuma baima san Imran bai taɓa wani maida hankali a kansa ba. Number ɗin nan ta saka na wancan karon dan ta kasa mantawa da su. Sai dai har wayar ta tsinke ba'a ɗaga ba. Addu'a ta fara yi a ranta tana sake kira. Yanzu ma sai da ta kusa tsinkewa a ka ɗaga. Jin waccan muryar dai da bazata layance mata ba ta sata sauke ajiyar zuciya. Duk da Dagger a ƙage yake da wannan kira na Nimrah tsahon wattani biyu hakan bai hanashi yi mata na ƴan duniya ba. Dan maimakon amsa gaisuwar ta bayan ta sanar masa ita ce sai cayay, “Lafiya kika kirani?”. Duk da taji haushi sai ta danne, maimakon masa rashin kuwa sai ta furta, “Kayi haƙuri, sai yanzu lokacin dazan iya kiran naka yayi. Ina son mu haɗu da gaggawa dan ALLAH”. “Bani da wannan lokacin, dama na gaya miki zan iya ɓace miki ai. Yanzu ma sa'a kika ci na ɗaga wayar ki. Kuma yanzu zan kashe.” “Dan ALLAH kada ka kashe. Sannan karka manta kai ka ɗora ni a wannan hanyar daban san da ita ba, bai kamata kai walagigi dani a lokacin da nake son sanin sirrin ta ba da taimakon ka. Ni mai rauni ce a yanzu, sannan makauniya dake buƙatar koda sandar jagora ce. Na maka alƙawarin bazan sake wasa da damar da zaka bani ba”. “Shike nan naji, zanyi haka ne kuma kawai dan Ummanki data bani amanar faɗa miki gaskiya a duk lokacin da kika kai minzalin girman ki. Sannan ta bani wasu sirrika na baki. Ban baki da farko bane, sabo da ina son auna hankalinki da yardarki gareni. Yanzu sai ki faɗi ina zamu haɗu”. “Na gode sosai. Sai dai kamar yanda na faɗa maka a baya ba'a barina fita ni kaɗai, sannan a yanzu gidanmu zagaye yake da jami'an tsaro saboda dawowar mutumin dake cikin video ɗin nan. Idan suka ganka zasu zarge ka ko kazo cutar da shi ne, dan saboda shi aka ajiye su......” Wani mugun girgiza zuciyar Dagger tayi, kaɗan ya rage yawun bakinsa ya biyo masa ta hanci tsabar yanda kalmar Nimrah ta dake sa. Da rawar lips ya maimaita, “D...awo wa...?”. Ɗan jimmm Nimrah tayi, sai kuma tace, “Eh mana, ba shugaban ƙasa ya masa afuwa ba? An fiddo shi ko ka manta ne?”. “Haka ne! Haka ne! Na manta ne sam, kin san abubuwan yawa suke”. Duk da yanda yayi ɗin ya ɗan sake taɓa zuciyar Nimrah da bata mamaki sai ta share kawai. Ta ce, “Ka bani nan da mintuna goma, akwai mamanmu zata haihu suna asibiti, idan an yarda muzo zan kiraka da wannan layin, dan zan riƙe wayar a wajena sai mu haɗu a cikin asibitin”. “Shike nan ba damuwa, sai na jiki”. Ya faɗa daga can wasu jerarrun zufa na yanko masa ta ƙofofin gashin jikinsa gaba ɗaya. Ita ko da bata san yanayi ba wayar ta yanke tana barin wajen. Koda ta fito maimakon zuwa gate ta bama Sanda wayarsa sai ta wuce ciki kawai....

+++++++++++++

“Tabbas gaskiya mutumin nan ya faɗa Oga, Zak-Shadow na cikin ƙasar nan, a cikin gidansu. Kuma a ƙalla sati guda kenan yake cikawa. Kaga kenan kwanaki huɗu kacal tsakani da sanar da afuwar shugaban kasa. Wato mutumin nan lallai ya masifar raina hankalinmu. Dan a majiya mai ƙarfi na samu tabbacin Zak-Shadow yafi wata biyu da barin prison, a ƙalla satin da ya fara shiga office ya fitar da shi.” Gaba ɗaya Oga Jush yama gagara iya cewa komai saboda yanda zancen yay masa dukan tasar ruwa a kai. Shin Yusuf Tafida ne ya raina musu hankali? Ko yaran da suka zagaye ko'ina a ma'aikatun ƙasar ne suka maidasu wawaye jahilai?. To lallai lokaci yayi da sabon wasa zai tashi, badai sai sun bari ayi mulkin lafiya ba. Daga shi Tafidan har Zak-Shadow ɗin zasu ɗanɗana kuɗarsu ne. Batare daya tofa komai ba akan batun ya bama Iron Fang umarnin sanar da meeting, ko ina kake kuma dole ka dawo ayi wannan zaman dakai, ba'a buƙatar kowa ya kiran waya ko video call. A zo kawai.. Iron Fang yasan oga ya ɗau zafi, sai kuma abinda ALLAH yayi, dan dole itama ƙasa ta ɗauki zafi a wannan gaɓar, zafin daya tabbatar muninsa sai yafi na baya girgiza kowa. Bai musa ko ja da nisa ba ya rubuta text message ya turama kowane member na ƙungiya. Shima ya kaɗa kansa ya tafi tashi sabgar sa........✍️