
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 72
.....they were sent down to replace them. Even though they are still the rest of the world. It's just a student of the school that follows the rule of thumb. Seeing how they persisted, Mammah said to check if the driver is here, if he is not here, they should be patient, since now they will also return as they were born safely in the hospital, they will not hold them. Nimrah is very excited, because she has two goals. But Ruky went to look and the privilege came back to the sky. Mr. Buba is said to have left. Little did Nimrah stop her from crying, she just tried not to let Mammah understand her situation. While they were doing that, the hospital staff brought back a beautiful baby who looked like Uncle Ja'afar, Masha ALLAH. That's not how Nimrah grew up, she didn't have a small heart and wanted to meet this man today. But she knew this opportunity and she missed it. She had to relax and continue with the joy of the baby, she was a bit sick and stopped anyone from taking it because Nimrah loves children very much. It was almost the sight of the crescent moon that took away most of her worries and she hid from her face, even though Mammah asked her to see her eyes change and she sai
72
.........Gaba ɗaya gidan Mammah ya hargitse da farin cikin saukar Shariffa lafiya. Bakin Uncle J kam har kunne. Suka rungume juna shida Twinyn sa. Bilal da Ammar ma suka haɗasu suka rungume. Dole suyi farin ciki zuri'arsu nata ƙara yawa da faɗi. A take sukai kiran Mammah suka sanar mata, dan tana gida bata bisu asibiti ba, sai ma su Nimrah ne dake ta damunta suje-suje?. Da farko ta hana su ne, dan bata son su tafi su barta ita kaɗai a gidan, dan Dada da Imran sun fita. Su Kulu kuma yau juma'a sun tafi gida su gaisa da mutane kamar yanda sukeyi duk bayan sati biyu. Su Dayyan kam sai a hankali, dan zatace ma tun bayan dawowa massalaci ta sake ganinsu ba. Garama Hanoon uwar son kallo da tana maƙale da tv kafin ta tashi itama ta shige. Hankalin Nimrah a rabe yake, ga farin cikin samun ƙaruwa da sukai ga lamarin son haɗuwa da Dagger. Ta tabbatar idan su Ammyn suka dawo gida ba lallai ta samu wata dama ba kuma balle suna hutun tahfiz ma gobe babu, dan cikin satin sama za'ai bikin saukar ƴan ajin sauka su su maye gurbinsu. Duk da suma dai saura ƙiris ne fa. Kawai dan makarantar nada ƙa'idar bin komai daki daki ne. Ganin yanda suka dage Mammah tace su duba idan driver na nan, idan baya nan sai dai su haƙura kam, tunda yanzu suma zasu dawo kasancewar an haihu lafiya asibiti bazasu riƙesu ba. Nimrah tafi kowa zumuɗi, kasancewar tata fitar da manufa biyu ne. Koda Ruky taje ta duba sai gata ta dawo baki a sama. Wai Malam Buba ya fita. Kaɗan ya hana Nimrah ta saki kuka, ta dai daure dan kar Mammah ta fahimci halin da take ciki. Suna cikin hakan ma sai ga ƴan asibitin sun dawo da kyakkyawan Jariri mai kama da Uncle Ja'afar Masha ALLAH. Sam ba haka Nimrah taso ba, dan ba ƙaramin ƙwallafa rai tayi da son haɗuwa da mutumin nan tai ba a yau. Sai dai ta san wannan damar kuma ta suɓuce mata. Dole ta saki jiki aka cigaba da murnar jariri, dan tabi ta katantane ta hana kowa ɗauka saboda Nimrah akwai son yara matuƙa. Kusan ma ganin jinjirin ne ya kwashe kaso mafi yawa na damuwar tata ta ɓuya daga fuskar ta, duk da sai da Mammah ta tambayeta ganin idonta ya canja tace abu ne ya faɗa mata.....
================
Hajiya Hasiba ta baro gidan Uncle Nasiru rai mace kiran Fomer First Lady ya sake harziƙa mata zuciya. Dan ko gaisuwa bata bari sunyi ba cikin bada umarni tace tazo tana nemanta duk inda take. Daga haka kuma ta yanke kiran batare data bari tayi magana ba. Tsabar takaici kamar zuciyarta zatai bindiga haka taji, kuma dole taje kasancewar da bazar First Lady ɗin take rawa. Akalar motar ta canja tana jan tagwayen tsaki. Mintuna kaɗan ya kawota gidan saboda gudu tai sosai. Securitys ɗin gidan sun riga sun san wacece ita a wajen masu gidan, tunma suna gidan gwamnati bata da shamaki. Dan haka kai tsaye suka buɗe mata gate ta shige. Tun a compound ta fara gamo da abin takaici, wasu matan ƴan siyasa dake zaman jiran son ganawa da First Lady ɗin sukai mata caaa. Sama-sama ta amsa su da cewar su jirata shiga tukunna, daga haka ta shige. Yanda bata tsaya falo na farko ba balle na biyu zai baka tabbacin lallai ita ɗin ƴar gida ce. Dan kaitsaye upstairs ta haura abinta. Ga masu aiki nata miƙa mata gaisuwa cike da girmamawa. A falon saman ta samu First Lady harda tsohon shugaban ƙasa, sai Zahir dake kwance a kujera zuru-zuru alamar baida isashen lafiya. Idonta akan Zahir ɗin ta gaida shugaban ƙasa da take kira Daddy, sannan ta gaida First Lady. Cikin ƙasa haƙuri ta furta, “Zahir lafiya kuwa?”. Kai tsaye First Lady ta amsa mata da, “Inafa lafiya Hasiba, wasu shegun yara ne a makaranta suka nema illatashi. Shiyyasa ma Excellency yace na kiraki, dan binciken mu ya nuna yaran nada alaƙa dake”. “Alaƙa dani kuma ranki ya daɗe? Nida yarana sun kammala har University su duka balle secondary. Sannan banda yaro namiji da har zai iya faɗa da Zahir”. “Ba alaƙar jini ake nufi ba. Sannan ba maza bane yaran mata ne”. “Mata fa! Suka masa wannan abun?. Amma ina fatan ba'a barsu ba ko Daddy?”. Daga First Lady har Fomer President cikin takaici sukai ƙwafa a tare. First Lady ta ce, “Yanzu ne dai zamu ɗau mataki, dan mun saka ƴan sanda sun kama su amma sun sake su wai basu cika shekara 18 ba. Sai dai sukai maganar kotu.” “Ai gwara aje kotun, kaji ƴan iskan yara kamar wasu ƴan daba. To wai ƴaƴan ma uban waye a ƙasar nan?”. “Wannan shine dalilin da yasa muka kira ki. Dan muna son musan ƴaƴan waye ɗin. Dan a bincike na naga abokin mijin Nabeeha ne yaje ya cire yaran daga station, ya kuma kai lawyer. Sannan sunje da wani gadararren mutum daya ɓoye fuskarsa shine ma yace aje kotun Saboda yaran sun faɗi wata magana. Yanzu haka sun shigar da makarantar ƙara gaba ɗaya. Shi kansa alƙalin Excellency ya kirashi kan ya kora ƙarar yace case ɗin yafi ƙarfinsa”. “Abokin Haysam! Imran kenan? Indai kuma haka ne zata kasance ƴaƴansa ne shi Imran ɗin. To amma waye suka je taren?”. “Wannan shine amsar da muke nema muma. Yaran kuma ɗaya tabbas ƴarsa ce, dan da sunan sa take amfani, suna ma kama. Ɗaya kuma Muhammad”. “Miye sunanta?”. “Naja'atu Muhammad”. “Mom anfi kiranta da Nimrah, a register kawai ake kiranta da Naja'atu ”. Zahir yay magana da ƙyar a karo na farko. “Nimrah, eh lallai wannan yarinya sheɗaniyar yarinya ce. To ai itace nake gaya miki shi Haysam ɗin ya tsinto a ƙauye shekarun baya wai an kashe iyayenta. Nabeeha tace bata yarda ƴarsa bace shine ya aureta. Mafari kenna na samu Nabeeha ta baro gidan”. Salati First Lady ta fara, shiko tsohon shugaban ƙasa da bai fahimci zancen ba ya nema ƙarin bayani. Nan fa sukai masa. A kuma lokacin ne tunanin Hajiya Hasiba ya dawo baya. Ta ce, “To kodai zancen Ismat gaskiya ne. Kusan sati guda kenan muna Chaina ni dake ba Amima ta kirani ba take min bayanin.....” “Tabbas anyi haka”. Cewar First Lady. Hajiya Hasiba ta ce, “To shine fa ni kuma na kullesu a ɗaki har yanzu na hana su fita, yanzu haka ma daga yima Uban nasu gargaɗi nake dan na zata shine ya shiryo makircin dan itama Nabeeha ya janye hankalinta. To lallai bana raba ɗayan biyu Haysam ne. Dan babu mai wannan ɗabi'ar gadarar irin tasa. To amma yaya haka? Duka yaushe shugaban ƙasa yace ya masa afuwa? Kodai makirci ne abun dama ba'a prison ɗin yake ba?”. Gaba ɗaya tsohon shugaban ƙasa ya ma kasa magana, sai first lady ce ta furta, “A lallai biri yayi kama da mutum. Kuma yanzu na yarda gargaɗi mai razani akama alƙalin nan. To ai inaga Hajiya Hasiba kawai ki bar Nabeeha ta koma gidan, ta haka ne zamu san gaskiya. Dan tabbas bazamu bar wannan abin ya tafi a banza ba, dole ne yaran nan sai sun ɗanɗan kuɗarsu. Bazasu illata min yaro a banza ba, dan yanzu haka likitoci sunce sai an fiddashi waje, in ba haka ba nan gaba ya samu matsala a privete part ɗin”. “Kai jama'a wann shaggun yara. Banƙi ta taki ba ranki ya daɗe, kanku komai kuma zan iya yi. Amma baƙya tsoron sharrin Adeel. Jiya jiyan nan nake ganin saƙonshi wai na shirya zai sake sauka a ƙasar nan, kuma wannan karon komai yake so ayi a gama”. “Karki wani damu, ki barmu dashi. Yanzu kawai kije ama Nabeeha gyara kona kwana uku ne ta koma a cikin satin nan. Zan tura miki kuɗi, zan kuma kira ƴar Kamaru ta sameku gida”. “An gama raki ya daɗe. ALLAH ya ƙara girma”.....
×==×===×==×===×==×
Sai dare Dada ya dawo gidan, lokacin kusan tara. An kawo masa jinjiri domin ya gani. Nimrah dake maƙale da shi ce kuma ta kawo. Dan har faɗa sukai da Ruky babu jimawa da taƙi bata shi shine tai zuciya taje tai kwanciyarta. Itako ko alamar barci bata ji, ga yunwa na cinta taƙi cin abinci, Mammah da Ammie dake gidan sunyi faɗa har sun gaji. Tunda ta shigo falon ya zuba mata ido. Dan yanda ta rungume jaririn famm abinta sai tai masa ƙyau. Kai tsaye ta nufo inda yake tunda shi akace ta kawo mawa. Cikin tsokana Ammar yace, “To ALLAH yasa dai shi Dada a bashi kona minti biyar ne, dan mu minti bibbiyu aka bamu”. Dariya Mammah tayi, “Ai ku kun samu minti biyun ma, Mu'azz sai a hannunta ya gani. Ruƙayya kam yanzu ba jimawa ta shige tayi fushi”. Dariya Bilal da su Ma'aruff suka sanya, Mu'azz ya dalla mata harara da faɗin, “Ai wlhy sai na rama”. “Sai dai kuwa ka rame”. Cewar Nimrah tana murguɗa baki. Kasancewar Dada a falon kuma ya sa ta tsaya iya hakan. Takawa tai ta ƙarasa inda Dadan yake, dan shima Mu'azz ya mata shiru saboda Dadan na nan. Maimakon ta bashi sai ta durƙusa a gabansa tana faɗin, “Dada gashi ka gani a haka. Idan aka tattaɓashi da yawa zai yi ciwon jiki”...........✍️
🤣🤣ASHE Dadan ma bazai tsiraba Ninah😂🏃🏼♀️🏃🏼♀️🏃🏼♀️.