Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 73

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 73

..... the child, finally she got up on her knees and kneeling and she put her hand on his thigh, her hands were on his thigh as well. There is no one who is not laughing in this hall. Even Mammah just turned her head away and whispered to him. "Get up here for me?". Dada said in a law voice that only she heard him. Instead of getting up, she let out tears. She said, "Dada, son of GOD, give it to me, you see." Today he saw the end of addiction. This girl does not know where they are. "Do you want everything?". He said to himself again. She pressed her shoulder against him and pushed her mouth. He didn't say anything to her again, he took both of her hands. He would talk and he would look at her with a sad look all the way down. Without any sign of joking, he said again, "Get up, go and cook Noodles and come back and answer". "Dada, did you make an appointment?". When he stared at her, he couldn't even speak, making everyone hide their faces and stifle laughter. They all know what to say. When he saw the way she looked at him with eyes that showed no sign of fear, he just bowed his head to her. She got up quickly and went to the kitchen, but she was looking at the baby as she walked.

Standalone post1,684 words

73

.......... “Bala'i”. Cewar Ammar suna fashewa da dariya shi da Bilal. Ja'afar ya ce, “Haba Ninah harda Dadan kuma?”. Baki ta tura cike da shagwaɓa ta ce, “To Uncle dan ALLAH kace masa minti uku kawai ya bani. Ko kuma na saka masa a ƙafafu daga hannuna ya gani.” Dariya Ja'afar da Ma'aruff suka gimtse suma, karo na farko Mammah ta ce, “Adai yi haƙuri a bashi Auta. Kinga kafin ya gama gani sai kije ki dafa Noodle kizo kici dan abinci ma ya huce yanzu, ni kuma bazan bari ki kwanta da yunwa ba”. Mammahn ta kalla kamar zatai kuka. “Mammah ALLAH bana jin yunwa nifa”. Kafin Mammah ta bata amsa kawai taji za'a ɗauke mata jaririnta. Ai firgigita ta juyo. Suka kuwa haɗa ido da mai shirin ɗaukar. Ba kowa bane kuma face Dada. Dan shi kam ya gaji da jan ran da ake masa. Kannewa kawai yake. Amma ya ƙagara shima jaririn yazo hannunsa. Rabonsa da ɗaukar jariri kamar haka har ya manta. Idanunta da suka tara ƙwalla ta risinar, dan bazata iya jurar kallon nasa ba. Sai dai fa tsabar ƙarfin hali taƙi sakin yaron, ƙarshe ma tashi tai akan gwiyawunta tai kneeling a haka ta saka masa jinjirin saman cinya, hannayenta nakan cinyar tasa itama, dan ita sam a wannan yanayin bafa ta gane ma dawa take tare balle abinda tayi. Babu wanda bai gimtse dariya ba a falon nan. Dan hatta Mammah kauda kai kawai tayi tana murmurshi. “Tashi min anan?”. Dada ya faɗa cikin law voice ta yanda ita kaɗai taji shi. Maimakon tashin sai ta saki hawaye sharr. A matuƙar shagwaɓe tace, “Dada dan ALLAH ka bani to, ai ka gani”. Shi kam yau yaga lukutar jaraba. Yarinyar nan bata san a ina suke ba ne. “Kina son duka?”. Ya sake faɗa ciki-ciki. Kafaɗa ta maƙe masa tana tura baki. Bai sake ce mata komai ba, yasa hannu ya zare hannayenta duk biyu. Zatai magana ya wulla mata kallon daya sakata duƙar dakai ƙasa. Babu alamar wasa ya sake furta, “Tashi ki wuce ki dafa Noodle ki dawo sai ki amsa”. “Dada kayi alƙawari?”. Yanda ya zuba mata ido ya kasa magana ma yasa kowa ɓoye fuska yana danne dariya. Dan duk sunji mita faɗa ɗin. Shi ko ganin yanda ta tsatstsare shi da idanu babu alamar tsoro balle shakka yasa shi jinjina mata kai kawai. Tashi tai da sauri ta nufi kitchen ɗin, sai dai tana tafiyar tana waigen babyn. Kaɗan ya rage taci karo da kujera. Mu'azz ya fashe da dariya. Sai dai hararar da Dada ya watso masa ta sashi saurin danne bakin. Nimrah data hararesa itama tai ƙwafa tana shigewa kicin ɗin. Bilal ya ce, “Kai jama'a, anya duk randa Ninah ta haihu zata bari a ɗauka ɗan kuwa?”. “Gaskiya kam da kamar wuya”. Ja'afar ya bashi amsa. Mammah dake murmurshi ta ce, “Hummm ina wannan tunanin nima kam, dan kwanaki fa da suka rakani barka tunda ta amshe yarinyar mutane ta hana, duk wanda yazo sai dai ya gani a hannunta. Babyn ta fara kuka akace ta bada ita maman ta shayar da ita taƙi, wai sai-dai maman ta saka nn a fida ita zata bata.” Dariya suka sanya sosai. Shi kansa Dada da hankalinsa ke kan Baby yana masa addu'a duk da yayi kamar baya jinsu sai da yay ɗan murmurshi. Mammah ta cigaba da basu labarin kicimillin da akasha ranar. Ta ce, “In dai fa akai haihuwa a gidan nan Nimrah da Ruƙayya basa ƙara shiri, kullum cikin faɗa suke saboda ƙarfa-ƙarfar Nimrah akan Baby. Shiyyasa yaran nan duk suka shaƙu da ita, dan rainon datai musu ko iyayen iyaka kenan”. Motsawar Babyn ya saka Dada cema Mu'azz yazo ya kaishi dare yayi a kwantar da shi haka nan kada sanyi ya kamashi. Tasowa Mu'azz ɗin yay ya amshesa. Ya fita kenan shima Dada ya miƙe zai haura sama dan hutawa ihun Nimrah ya ratsa kunnuwansu. “Wayyoooo yaji wayyo idona?”. Gaba ɗaya suka kalla hanyar kitchen ɗin, Dada ya tsaya cak. Kafin wani ya miƙe Nimrah ta fito tana laluben hanya da faɗin, “Wayyo Mammah ki cire min zan haukace idona. Zafi-zafi na shiga uku Mammah zan mutu....” Mammah da duk ta rikice itama har zata miƙe dan kamo Nimrah ɗin, duk da ga Dada a kusa da inda take amma taga bashi da niyyar hakan sai kuma Nimrah ɗin data iso gab da Dada tana lalube ta taɓa shi. Ai tana jin mutum bama ta tsaya son sanin waye ba kawai ta damƙeshi tana cusa fuskarta a jikinsa, dan wani irin tashin hankali take ji da raɗaɗi har tsakiyar ƙwaƙwalwa, sakamakon yajin ya shiga mata sasai cikin idon. Gata dama koda hannu ta taɓa kayan miya sai su yini suna mata zogin yaji shiyyasa ta ƙara tsanar girki. Dada bashi da zaɓin daya wuce riƙeta, dan duk wanda ya kalleta yasan a gigice take, kuma dole ka tausaya mata. Gashi iyayen nata duk sun miƙe suma fuska cike da tashin hankali kamar zasu tayata kuka. Ya tabbatar yayi sake zasu iya cewa ma baya ƙaunar ƴar tasu ko ya mata mugunta. A nutsensa ya furta, “Ki nutsu”. Ina ita ba saurarensa take ba, dan ita tasan mitake ji. Shima ya fahimci hakan, dan haka ya kamata kawai yana komawa zaune a kujerar daya tashi, ita ko da yake tana a jikin nasa sai kawai ta zauna a cinyarsa. A nan ɗin ma Dada bashi da mafita, baiyi magana ba kawai ya hau ƙoƙarin buɗe mata idon, ita kuma ta ƙanƙame masa hannu tana faman tirje-tirjen da kuka da kiran Mammah-Mammah. Matsowa Mammah tayi ta kama hannun nata cike da lallashi tana faɗin, “Kinga ya isa nutsu a cire miki. Da ya fita zaki ji zafin ya daina.” “To Mammah dan ALLAH ki cire. Wlhy ji nake kamar zan haukace.” Bilal ya kawo tissue, riƙe mata hannun da Mammahn tayi yasa Dada samu ya buɗe idon nata. Sai ko ga ƙaton yaji a ciki harda ɗiya. Idon kuwa yayi wata masifar rinewa jazurr kamar garwashin wuta. Tissue ɗin hannun Bilal ya amsa, yana saka mata taji zafin yafi nada, sai kawai ta sake ƙanƙameshi tana son ƙwace kanta. Sai dai riƙon na manya ne, dan haka ya matseta da ƙyau sai da ya cire shi gaba ɗaya. Babu wanda baiji tausayinta ba da ganin yajin babba da shi. Ita ko ta kife kanta tana sauke numfashin wahala da sauran azabar da take ji akan ƙirjinsa. Dada da ya san wannan yanayin haɗari zai zama mai girma da shiga cakwakiya sai kawai ya miƙe a hankali da ita a jikin nasa ya nufi doguwar kujera ya kwantar da ita. Yana ɗagowa zai bar wajen suka haɗa ido da su Ma'aruff dake murmushi. Da sauri suka gimtse shi da Ja'afar. Shima sai ya ɗauke idanun nasa cike da basarwa kamar bai gansu ba ya bar falon gaba ɗaya. Sai da suka tabbatar ya gama haurawa staircase ɗin suka fashe da dariyar. Kallonsu Mammah tayi itama, da sauri suka sake gimtsewa. Ammar, Bilal da Mu'azz daya dawo yanzu basu fahimci inda dariyar Yaya Ma'aruff da Yaya Ja'afar ta nufa ba sam. Itama Mammah da farko ba fahimta tai ba, sai da taga suna satar kallon upstairs suna ƙus-ƙus sannan ya harbo jirgin su. Kanta kawai ta girgiza tana maida hankalinta ga Mu'azz tace yaje ya ƙarasa dafama Nimrah indomie ɗin taci taje ta kwanta.......

^^^^^^^^^^^^^^^^

A wannan daren ƙungiyar duhu sukai meeting na sirri. Meeting ɗin da gaba ɗayansa ƙulle-ƙullen masifu ne na tashin hankali ga ƙasa dama shugabanta Janar. Dan abinda yay musu sun tabbatar da babu bashi sai sun hukuntashi. Sai Dada, gaba ɗaya shirinsu a kan Dada kuwa ya ta'allaƙa ne akan yin amfani da Nimrah. Sun fahimci dole su canja taku, takun da zasu haifar da rauni mai raɗaɗi da ƙuna a zuciyar sa. Wannan kuma raɗaɗi da ƙunar ba zasu iya samar da shi ba sai ta hanyar taɓa zuri'arsa. Ta ko ina kuma sun fahimci dole sai da wani na jikinsa zasu iya hakan, musamman da a yanzu tsaro yayi yawa a gidan, dan Mole ya zama mai kawo musu bayanai sosai akan gidan yanzu fiye da Dagger. Hatta haihuwar Shariffa ta yau ɗin nan tazo kunensu, shima Dagger ya sanar musu kiran da Nimrah tai masa da buƙatar su haɗu da tayi sai dai hakan bai faru ba sakamakon rashin fitowar ta. Ta haka ne ma suka sake samun tabbacin Zak-Shadow ɗin ne dai a gida Mole baiyi ƙarya ba. Sai da suka gama tsare-tsaren su iya su manyan Sannan aka sake wani sabon meeting da saura members duk a daren dai. Hukuncin da suka yanke da tsarin da suka kammala yi yasa shima Dagger suka buƙaci ganinsa zuwa safiya. Dan yanzu kam aiki ne zai tashi ba wasan yara ba. Sannan zasu bama Mole dama irin ta Dagger, sai dai ba'a kan Nimrah ba. Nimrah Dagger zai cigaba da aiki kanta kamar yanda ya fara tunda ta riga tasan fuskarsa. Canjawa zai saka ta iya zargin wani abu daban tunda sun fahimci tana da wayo............✍️

Idanunsa dake lumshe shima ya buɗe yana sauke ƙaramar ajiyar zuciya, kafin ya ɗagota a hankali zai maidata ya kwantar ta sake ƙanƙamesa cikin ƙunƙunan barci name magagi tace, “Uhmm-uhmm Mammah, ni zan kwanta ana....” Batare data ƙarasa ba ta cigaba da barcinta. Wani ɗan murmushi mai fidda sauti cikin ƙirji kawai ya saki. A ransa yace (Trouble maker, idan kin kwanta anan ni kuma twin ɗinki ta farka ta ganni fa?). A zahiri kam kwantar da ita ɗin yayi a hankali, sannan ya haska mata fuska da waya. Idon da gefensa har ya kumbura, yakai hannu ya ɗan shafa wajen kaɗan, sai kuma ya ɗan furzar da iska yana zame hannunsa data riƙe gam a ƙirjinta. Sake ƙoƙarin cafkowa tayi, kawai ya saka mata bargo a ciki. Sai ko ta damƙe tana juya kwanciya ta matse bargon har abin yaso bashi dariya ma, ya dai gimtse ya tashi abinsa da ledar maganin ya fita, dan yasan idan ya bari da safe sai sunta shelar neman waya ajiye a gidan, ba man kai ne da su ba.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°