
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 74
..... that's why. And he saw that their house was very noisy today. Mammah said he is here, let the dish be brought to him. She hung up the phone and told Nimrah to wake up. Nimrah was shocked and said, "Mamma is not okay". "Oh little one, then who do you want him to take? Isn't Rukayya sleeping? Your mother is working in the kitchen." Caraf Hanoon said, "Mammah, bring me." Before Mammah could answer, Nimrah gave her a shout and stood up. She gave Hanoon a blank look again, pointing at the tray she had brought and saying, "A man should take care of himself. We, our fathers, will not marry the best. A woman should be touched, not above or below." Laughing as if it would kill Kulu, she could hardly move to enter the kitchen. Hanoon didn't even look at Nimrah, but she didn't understand anything. Mammah shook her head and smiled, in her heart she was praying that ALLAH will prepare Nimrah and Ruqayya for her. The children are talking in their mouths like a family of butchers. Muhammad was the one who started talking bad when he was a child, not much noise, but when he compliments you, it is as if you are dead. So here are the heirs and they are looking for a successor. Even when Nimrah
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Washe gari gidan Mammah ya cika da ƴan barka. Musamman sashen su Lailah. Danginsu sai zuwa sukeyi. Sai dai duk wanda ya shigo sai yazo ya gaida Mammah. Kuma duk wanda zai shigo securitys ɗin nan sai sun masa ƙwaƙwaf. Yanayin da Nimrah ta tashi akan idonta ya taƙaita al'amarin tana nanuƙe da Mammah. Ruƙayya kam duk ta damu kamar zatai kuka. Kaɗan-kaɗan saita ce, “Ninah ba zafi?”. Tun Nimrah nace mata eh, harta koma tsokanarta idan ta tambaya sai tace akwai, sai taga ta damu sai ta saka dariya. Mu'azz ya tasa su gaba da tsokana sai da Mammah ta Koresa a falon. Hakama Afeef ko sau ɗaya bai nuna tausayin Nimrah ba balle Hanoon. Biebah kam har ɗan gasa mata idon tayi da ruwan zafi dan fuskarta ya ɗanyi fushi, a haka ma dan Dada ya saka mata magani ne ai da ba'a san yanda zata tashi ba. Har kusan sha biyu Dada bai sakko ba. Dan haka Mammah tace Nimrah dake zaune Ruky tayi filo da ƙafarta tana barci ta tashi ta kai masa abincin breakfast. Saboda ta kirashi a waya yace aiki yake shiyyasa. Kuma yaga yau gidan nasu hayaniya tayi yawa. Mammah tace shike nan bari tasa a kawo masa. Shine ta yanke wayar tace Nimrah ɗin ta tashi. Cike da shagwaɓa Nimrah ta ce, “Mammah banda lafiya fa”. “Haba auta, to wa kike son ya kai? Bakiga Ruƙayya barci take ba? Mamanku kuma tana aiki a kitchen”. Caraf Hanoon ta ce, “Mammah kawo naje”. Kafin ma Mammah ta bata amsa Nimrah data watsa mata harara ta miƙe. Ta sake watsama Hanoon kallon banza tana nufar tray ɗin da kulu ta kawo da faɗin, “Dama mutum ya kama kanshi. Mu uban mu bazai auri finga-fiyau ba. Mace sai kace taɓaryar gwari ba sama ba ƙasa.” dariya kamar zata kashe Kulu, da ƙyar ta iya matsawa ta shige kitchen. Hanoon kam da kallo tabi Nimrah dan ba komai ta gama ganewa ba. Mammah ta girgiza kai tana murmushi, a zuciyarta addu'a take ALLAH ya shirya mata Nimrah da Ruƙayya ita kam. Yara baƙar magana a bakinsu kamar dangin mahauta. Muhammad ne yay tashen baƙar magana yana yaro, ba yawan surutu amma idan ya yaɓa maka mai zafi kamar ka mutu. To ga magada nan ya samu har suna neman zartashi. Koda Nimrah tazo kofar ɗakin sai abinda ya faru jiya ya shiga dawo mata. Bana tattaunawarta kawai da shi ba, harda na abinda ta gani, har yanzu take neman mafitar fita amma ta gagara samu. Tafi minti ɗaya a tsaye kafin tai sallama dan babu daman knocking hannunta da tray. Sarai ya jita amma yaƙi tasowa ya buɗe mata balle amsawa. Yau ƴan sarautar ne aka. Itama jin shiru babu motsin kowa tayi kuma har sau kusan huɗu sai kawai ta rungume tray ɗin da hannu ɗaya, cikin dabara ta saka ɗayan ta buɗe. Koda taci karo da shi a zaune sai da taji shock. Ta ɗanyi diri-diri sai kuma ta nutsu jin tana neman yin ɓari. Yi yay kamar baima jita ba. Nan ko ya gama kalleta ta gefen ido. Amma sai ka rantse hankalin nasa akan rubuce-rubucen da yake yi yake. Ƙananan kaya ne a jikinsa, yanda rigar ya kamashi sosai gashi ƙaramin hannu yasa kallo ɗaya datai masa bata sake gigin yin na biyu ba. Sai kuma ta tafi tunani mara dalili daya sakata shagala a wajen ta kasa ƙarasawa ta ajiye abincin.. “Idan kikai ɓarin abincin nan sai kin cinye shi”. A bazata furicinsa ya shiga kunnenta. Da sauri ta dawo hayyacinta. Saman table ɗin gaban sofa taje ta ajiye tray ɗin. Dan shi yana a study chair ne zaune. Desktop ɗin sa a kunne gefe yana rubuce-rubuce. Ta bayansa kaɗan ta risina ta ce, “Dada ina kwana”. “Haɗa min abincin”. Ya faɗa batare daya amsa gaisuwarta ba. Baki ta zumɓura dan taji haushin ƙin amsa matan da yayi.........✍️