
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 75
..... in crying or in her drama, even though she was really upset, he didn't respond to her greetings. Jiyay can't let her go crying, or something about her. Then he took her hand and brought her back to where she was. He did not let go of her hand and continued to look at her for almost two minutes. "Do you want me to draw you?". She shook her head at him. With a frown, he said, "I don't like this cry. Tell me what's wrong with you? Who did something to you?". She started to wipe her tears and said, "No. It's you". "Kiddo and me?". Her head bowed and pushed her lips. "The power of separation, what should I do?". "I greeted you but you didn't answer. I see that you are angry with me". He was just looking at her for a long time, he was overwhelmed by the wonder of the world. In his mind he said (you are a crazy family. What about a girl) clearly he didn't know when he said, "Today I am in the hands of a few sari! So I greeted you again and I replied that he is not here". "So you're not angry?". She spoke in the manner of a little spider with his eyes. He just shook his head trying to suppress the smile that was trying to appear on his face. She let go of her heart, and greeted him a
75
..........Harta gama zuba komai dai-dai misali ta zuba shayin lemon tsami da na'a-na'a dake ta ƙamshi bakinta na a sama. Inda yake ta nufo, ya matsar da takardunsa kafin ta kife masa abincin a kansu. Shiru bata ajiye ba, hakan ya sashi ɗagowa dole ya kalleta. Suna haɗa ido ta risinar da nata, shima sai ya kauda kansa ya cigaba da aikinsa. Kusan sakan biyar sannan ya furta, “Fishin mi kike yi?”. Bakin ta ƙara turawa taƙi magana. Yay ɗan jimm na mamaki, sai kuma ya ɗago ya sake kallonta. “Abincin naku ne baƙya son naci?”. Yanzu ma kai ta girgiza. Ya dai sake daurewa ya ce, “Idon ne?”. Sai kawai ta sakar masa kuka. Mamakin duniya ya gama mamaye shi, kaji yarinya fa dan ALLAH kamar wata mai aljanu. Bai sake magana ba ya zuba mata idanu kawai. Ganin kukan ma daɗi yake mata sai ya amshi abincinsa da kansa ya ajiye. Kafin ya furta, “Tunda bazaki yi magana ba wuce ki tafi”. Gurin tai ƙoƙarin bari tana sake fashewa da kukan da ita kanta bata san dalilin yinsa ba, kawai jitai tana son yi masa kukan ko a cikin drama ɗinta ne, duk da da gaske taji haushin bai amsa gaisuwar datai masa ba. Jiyay bazai iya barinta ta tafi tana kukan ba, ko wani abu akai mata. Sai ya riƙo hannunta ya dawo da ita inda take da. Bai saki mata hannun ba ya cigaba da kallonta har kusan mintuna biyu. “Kina son na zane ki?”. Kanta ta girgiza masa. Cikin sake tsuke fuska ya ce, “Bana son wannan kukan. Faɗa min mike damun ki? Wani ne ya miki wani abu?”. Hawayen ta fara sharewa da faɗin, “A'a. Kai ne”. “Kiddo ni kuma?”. Kanta ta jinjina tana tura baki. “Ikon rabbu, to mi nayi?”. “Na gaishe ka baka amsa ba. Sai naga kamar kana fushi da ni”. Sagale kawai yay yana kallon ta, mamakin duniya ya gama mamaye shi. A ransa yace (Ƙuruci dangin hauka. Kaji yarinya fa) a fili kam baima san ya furta, “Ni kuma yau a hannun ƴan sari na tashi kenan!. To sake gaisheni sai na amsa ba shike nan ba”. “To ba fushi kake ba?”. Tai maganar cikin yanayin ɗan waro masa idanu. Sai kawai ya girgiza mata kansa yana ƙoƙarin danne murmushin dake neman bayyana a tsukakkiyar fuskarsa. Ajiyar zuciya kuwa ta saki, sannan ta sake gaishe shi. Ɓoyayyar ajiyar zuciya shima ya saki ya amsa yanda take son, harda ɗorawa da, “Yaya idon ki?”. “Da sauƙi, amma yana zafi kaɗan”. “Tunda kina kukan da babu dalili ba dole yay zafi ba. Ɗauka min leda gashi can a mirror na sa miki magani”. Ya kai ƙarshen maganar yana sakar mata hannu. Inda ya aiketan ta tafi, ya bita da kallo yana girgiza kai kawai. Tabbas yana da son yara, bai sani ba kodan baida su. Duk da Nimrah da Ruƙayya sun girma a yanzu, ganinsu yake ƴan 7years ɗin nan daya tafi ya bari... Dawowarta da ledar ya saka tunaninsa katsewa. Amsa yay ya buɗe, ya ciro maganin sannan ya kalleta, kamar ta fahimci mi yake nufi ta tsugunna kawai tana mai dafa hannun kujerar. Kanta ya dafa da hannu ɗaya, tare da buɗe idon sosai da babban yatsansa ya zuba mata maganin..... “Wayyo Dada zafiiiiii”. “Shiiiii!”. Ya faɗa yana riƙe da kan nata, dan ya hanata ɗagowa kar maganin ya fita. Sai da ya tabbatar ya shiga sannan ya barta. Har zata miƙe ya ce, “Ɗauka wannan abinci ko canja ya huce. Kije ki kira min Ruƙayya itama”. Cike da tsantseni ta amsa, dan duk wannan biye matan da yake shakkarsa na nan damar a zuciyarta. Musamman da fuskar na tsukenta ne babu ko murmurshi. Sai dai son cikar burinta da shirinta a kansa yasa take danne zuciyarta da bama kanta ƙwarin gwiwa. Alhamdullahi kuma taga tasirin hanyar data biyo masa. Bayan ta ajiye wani sabon abincin dan ALLAH yaso ba plate ɗaya Kulu ta saka ba, haka ma kofi. Tana kammalawa ta fita a ɗakin. A ƙasan ransa ya furta (Kiddo kina bani ciwon kai)... Babu jimawa suka dawo ita da Ruƙayyan, dan ta iske ta tashi barcin. Yanda yay ma Nimrah tambayoyi jiya cikin wayo da dabara akan makarantarsu haka ya dinga musu a tare yau, suka dinga bashi labarai kala-kala, har kansa ya fara ciwo sai da ya gaji ya korosu. Oho ko'a jikinsu, dan daɗi ma suka dinga ji Dada yayi hira da su, koda suka dawo wajen Mammah sai suka dinga yi ma Mu'azz wulaƙanci. Har sai da yaji haushi ya haura saman yace shima ya tafi ɗakin Dadan. Mammah dai murmurshi take kawai da jinjina shiriritarsu. Sauran Uncles ɗin nasu ma duk wanda ya shigo sai an bashi labari yau sunyi hira da Dada. Congratulations suka dinga ce musu suna dariya..
Wannan hira ta bama Dada haske sosai akan makarantar su Ruky. Koda suka tattauna da Daddy Imran yayi mamakin wayon yaran. Dan abune ma da shi kam bai taɓa kawoma ransa ba...
))))★(((((★))))))★((((
A bangaren Hajiya Hasiba kamar yanda First Lady tace tayi hakan tayi, ta buɗe su Nabeeha. Ta kira likitanta ya fara duba su saboda damuwar da suka sakama kansu duk sun rame. Ya tabbatar mata da basa tare da wata matsala sai damuwar kawai. Amma ya basu shawarwari sosai da suka fahimcesa. Bayan tafiyarsa itama ta zauna da su. Ta nuna musu ta haƙura, amma su kiyaye gaba. Sannan tace Nabeeha ta fara shirin komawa gidan mijinta. Ba Nabeeha ba hatta Ismat ta shiga matsanancin mamaki. Dan har sai da ta furta, “Momy da gaske kike yi?”. “Oh na saba miki ƙarya ne Ismat?”. “A'a Momy kiyi haƙuri. Wlhy mamaki ne kawai abin ya bani”. “Humm to sai ya daina baki. Kawai shawara likitan nan ya bani akan na barta ta koma kada ta kamu da wani ciwo. Dan haka na amince ta koma. Kema kuma na baki nan da wata uku ki kawo mijin aure, idan ba haka ba ni inada wanda zan bama ke. Masu gyaran jiki zasu zo gobe idan ALLAH ya kaimu sai ki shirya”. Tai maganar ƙarshe tana kallon Nabeeha. Kai kawai Nabeeha ta jinjina mata, dan al'amarin Momyn tasu a wannan gaɓar ya razanata fiye da ko yaushe. Tana sonta sosai, amma maganar gaskiya ta fara jin tsoron ta mai girma. Tun daga ranar suka fara ganin canjin abinci masu ƙyau, saɓanin wanda ake basu a kwanakin nan da suke a kulle. Sannan ta dawo musu da wayoyinsu. An kuma dawo da network ɗin gidan. Sukan fita falo su zauna, har ma tayi hira da su. Ƴar Kamaru tazo ta fara aikinta na gyaran jiki wa Nabeeha. Dan maƙudan kuɗaɗe First Lady ta biya kamar bata san ciwon kuɗi ba. Koda yake bata san ciwon nasu ba tunda an tara musu, ta yanda ko jikokinsu bazasu yi talauci ba idan ba wata jarabawar UBANGIJI ba kuma....
<•••><••••><••••><•••>
A lokacin da can ake gyara Nabeeha anan Dada da Imran sun matuƙar maida hankali wajen haɗa runduna ne akan aikin da zasu fara. Dan kamar yanda shugaban ƙasa ya bama Dada damar samar da masu taya shi aiki cikin kowanne jami'an tsaro dama farar hula haka yaketa tattarasu. Sai dai fa dukansu kowa bai san da zama ɗan uwansa ba. Hasali ma su Dabo aka saka suke yi basu san waye shugaban tawagar ba. Har yanzu suma su Dabo basu ga Dada da idanunsu ba, sai dai su duka yayi waya da su ta hannun Imran. Duk abinda zasuyi Faro ke basu umarni. Sai yau ne ma yake tunanin zama da su. Dan akwai tsofaffin bayanan da yake so a hannunsu. Sannan yana son jin bayani akan duk wanda suka ɗakko a cikin tafiyar dan tantance ko zai iya aiki da shi ko bazai iya ba. Kwanaki biyar kenan da haihuwar Shariffa, tunda kuma akai haihuwar kullum su Aunty Ummi na gidan nan. Hakama ɓangaren dangin su Imran tunda abu ne duk na gida. Shiyyasa sam Dada baya zaman gidan. Bama zai iya cewa yasan wace waina ake toyawa ba. Suma sun maida hankalinsu akan wancan gidan da suke shirin maidawa na sirri. Tabbas, wannan gida a zahiri Dada da Imran sun maida shi tamkar gida na yau da kullum, amma a gaskiya UNIT ZERO ne, cibiyar sirri da aka gina domin yaƙin da ba a sakawa suna ba a fili. An sauya duk wani abu mai ƙarancin tsaro zuwa mafi girman matakan tsaro. Tun daga ƙofar shiga, komai ya sauya. Ba ƙofa ce da ake buɗewa da hannu kawai ba. Ana amfani da multi-layer authentication: lambar sirri, na’urar biometric, da kuma time-based access. Ko su da kansu, idan lokacin bai dace ba, ƙofar ba za ta buɗe ba. Tagogi kuwa an maida su bullet-resistant glass harbi ba zai iya ratsa su ba. An saka ɓoyayyun cameras ko’ina. An kuma tanadi ɗaki guda na musamman domin ajiye ayyukan sirri, ɗakin da Dada shi kaɗai ke shiga, sai Imran da Faro. Smart perimeter sensors sun zagaye gidan gaba ɗaya ba wai don mutane kawai ba, har da motsin iska, ƙasa, ko duk wani abu da bai dace ba. Akwai silent alarm system: babu ƙara, babu haske, amma UNIT ZERO ya riga ya zama ido da kunne na komai. Thermal cameras suna iya gano mutum ko da cikin duhu ko ta bayan bango. Ƙofofi kuwa EMP-resistant ne ko an katse wuta, ko an yi hacking, ba za su buɗe musu ba..........✍️