
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 76
.....only. Some photos and information are stored in the dead vault, they are not opened unless three conditions are met. A dead-drop system is used to exchange information, without direct connection. There are many types of weapons that are not registered in any register. Listening devices, tracking, and masking. There are also emergency exits in case of an attack, and hiding places for the secret agents who carry them. As soon as you enter this room, you will understand that the battle is a real battle, not a child's game. It's not just equipment that's stopped. Underground drainage channels are provided, which directly connect to the main watercourses of the area. Underground roads hidden in the architecture. Not one way but three. Some lead to different places in the neighborhood, places you would never think are connected to the house. Of course, the president tried to invest money on this project, although it was not taken out of the government fund directly with this purpose, it was hidden behind a project that was given a direct contract, behind the scenes and for this project. Everyone who will be working with UNIT ZERO does not know the real leader of the team. Work order
76
.........Cameras marasa gani da ido, ba su da haske, ba su da amo. Wasu an saka su a cikin bango, wasu ma a cikin furanni. An tanadi blind-spot tracking a inda babu camera, akwai sensor. Duk motsi ana adana shi ne a local encrypted server, ba tare da haɗin internet ba. A wasu sassa ma babu wata waya da ke kama signal, musamman a EMI shielded rooms. Hatta talabijin da ke nuna dukkan motsin gidan ta hanyar cameras suna cikin ɗakin kula da tsaro. Akwai na'urorin aiki na musamman da shugaban ƙasa ya samar, irin waɗanda manyan ƙasashe ke amfani da su a duniya. Manyan monitors suna nuna duk motsin gidan, sarrafa cameras, da ajiye bayanan sirri. Babu waya, babu recorder, babu wani motsi da zai faru ba tare da sun sani ba, ko da basa cikin gidan. Abin da aka faɗa a nan, ya mutu a nan. Ko hoto ma ba ya ɗaukuwa a gidan, balle a ɗakin sirri. A tsararren ɗakin sirri, dukkan takardu suna cikin classified physical files da aka kulle da code da fingerprint. Wasu bayanai ba su da suna, sai lambobi kawai. Wasu hotuna da bayanai ana ajiye su ne a dead vault, ba a buɗewa sai an cika sharaɗi guda uku. Ana amfani da dead-drop system wajen musayar bayanai, ba tare da haɗuwa kai tsaye ba. Akwai makamai iri-iri makaman da ba a rubuta su a kowanne rijista ba. Na'urorin sauraro, bin sawu, da ɓoye fuska. Haka kuma akwai kayan fitar gaggawa idan aka kai hari, da wuraren ɓoye ainihin jami'an sirri masu kai ɗauki. Da zarar ka shiga wannan ɗakin, zaka fahimci cewa an shirya yaƙi ne yaƙi na gaske, ba wasan yara ba. Ba kayan aiki kaɗai aka tsaya ba. An tanadi hanyoyin fitar sirri ta ƙasa, waɗanda kai tsaye ke haɗuwa da manyan magudanan ruwan unguwar. Hanyoyin ƙasa da aka ɓoye cikin tsarin gine-gine. Ba hanya ɗaya ba fiye da uku. Wasu suna kaiwa wurare daban-daban a unguwar, wuraren da ba za ka taɓa tunanin suna da alaƙa da gidan ba. Tabbas shugaban ƙasa yayi ƙoƙari wajen zuba kuɗi akan wannan aiki, duk da dai ba'a fitar da su daga asusun gwamnati kai tsaye da wannan manufar ba, an laɓe bayan wani aiki ne da aka bada kwangilarsa kai tsaye, a bayan fage kuma akai wannan aikin. Kowa da zaiyi aiki da UNIT ZERO bai san ainihin shugaban tawagar ba. Umarnin aiki zai dinga zuwa ne ta code name. Idan aka kama mutum, babu abin da zai iya faɗa da zai rushe tsarin gaba ɗaya. UNIT ZERO ba gida ba ne kamar na shirin Film kawai, babbar FADAR YAƘI ce a ƙarƙashin umarnin ZAK-SHADOW. Wani gawurtaccen station blinding ne da zai ruguza duk wani mai tsautsayi da zai iya shiga tarkon ZAKI. Dan duk wani shiri an kammala shi yanzu kam hatta filin saka mazare rawa da sarƙa a kafa. Shi kansa uban gayyar ya furta “YANZU NE AIKIN ƘARSHE ZAI FARA. A kashe ko ya kashe, wannan shine ƙarshen BURI......”
“Alhamdullahi komai ya kamala, lokacin fara aiki yayi. Yanzu minene shiri na farko?”. Iska Dada ya ɗan furzar yana ajiye takardun hannunsa ya gyara zama da kallon Imran mai maganar. Cikin sake maimaita godiyar ga UBANGIJIN shima ya bashi amsa da, “Inaga zan gana da su dabo a daren yau. Kai ma lokaci yayi da zaka koma aiki sosai kafin su fara tsarguwa da rashin zamanka office.” “Nima nayi wannan tunanin. In sha ALLAHU kuma zan koma wannan Monday ɗin. Yaya batun karatun yaranka, ya kamata su koma makaranta fa. Dan in ka biye musu su wannan zaman shiriritar daɗi yake musu, musamman daya zam babu islamiyya. Ammien su tace a zaman jegon nan babu abinda suke sai rashin ji, kawai dan baka yini gida ne kai ma. Dan jiya ALLAH ya kiyaye suda yarinyar nan Hanoon da anyi babu daɗi.” Murmushi kawai Dada yayi. Daddy Imran ya hararesa. “Kace mune ke ɗaure musu ƙugu, amma ka fimu. Nazata dawowarka zata saka su nutsu amma shirun da kake musu yayi yawa, ya kamata ko sau ɗaya kaci ƙaniyarsu.” “Basuyi abinda zanci ƙaniyar tasu bane shiyyasa. Makaranta kuma zasu koma. Dan baza'a canja musu ba akwai shirin da nakeyi kafin su koma ɗin, da kaina zan maida su”. “Hakan yayi ALLAH ya kaimu. Sai mutuminka ya dameni akan batun Auta. Wai kunyarka yake ji shiyyasa ya kasa magana. Kar kaga kamar yayi gaggawa.” Nan ma murmushi Dada yayi da faɗin, “Ai yayi ƙoƙari, ya kamata ka duba masa. Sai ka haɗa da Bilal da Ammar. Dan suma bana son zamansu haka. Ya kamata duk su ajiye iyali”. “Eh wannan shawara ce mai ƙyau. Amma ban taɓa ganin Ammar da budurwa ba. Gara Bilal”. “Na tambaye shi nima yanata min ƙunshe-ƙunshe. Shine nace masa yaje ya tura min saƙo to. Sai jiya yake tura min wai ai bata girma ba, kuma tana a gidan tare damu. Amma bai taɓa nuna mata ba sai ta kammala Secondary”. “Tofa ji ja'iri, wacece haka?”. “Bai faɗa ba, amma ni na fahimci Ruƙayya yake nufi”. “Kai amma Ammar mashiririci ne. Yarasa mata sai wannan kayan shirme da shiriritar. Kuma a haka kake cewa a haɗa da shi, ciwon kai kawai ka nemar masa”. “Ko?”. Dada ya faɗa yana ɗan ɗage gira sama. Baki Daddy Imran ya taɓe. “Kaima ka san yarinyar nan taka sai a hankali”. “Ba komai zata bari wataran. Ai dama na gaya maka aure zan mata”. “To ALLAH ya taimaka. Sai kai kuma uban gayyar. Dan ALLAH kayi haƙiri muje bikon Nabeeha. Dan ina cikin mamakin yanda har yanzu bataji ko labarin dawowarka ba. Ko har yanzu tana fushi ne”. “Dawa zaka je ɗin?”. “A! Dakai mana. Zakina dan ALLAH ka rage taurin kan nan. Sufa mata ba'ai musu haka. Lallaɓasu ake, a riritasu. Ayi haƙuri da halayensu marasa ƙyau. Tunda har akace mana tun daga tushe a karkace suke, tsaurin mu bazai sa su miƙe ba fa. Idan ma muka tsananta zasu karye ne.” “Ni babu inda zanje, ƙafarta data fiddata idan ta gaji da zaman ta dawo da ita”. “Kai kuma halin da kake ciki fa?”. “Ni na gaya maka ina cikin wani hali ne?”. “Kasan na sanka fiye da kowa. Ai ba sai ka faɗa min ba. Koda kake ganin dama can kana azumin ka ai na yanzu yasha banban. Sannan yanzu fa kake faɗar su Bilal su ajiye iyali saboda shine cikar kamala. Amma kai kana bijirewa. Kai ne fa uba, ko Mammah na tabbatar ta maka shiru ne taga iya gudun ruwanka. Idan kai bazaka je ba, ni ka barni naje to”. “Wlhy bazaka ba”. “Harda rantsuwa? To shike nan Nimrah ta tare”. “Amma baka da hankali”. Dariya Imran yayi sosai, ya ce, “Naji banda shi. Miye a ciki to. Naga yaran ƙauye ana musu aure ƙasa da shekarunta. Balle su suna cin abinci mai ƙyau kuma ALLAH ya kawo girman da wuri. Kadai duba al'amarin nan. Bar ganinsu haka sun san abubuwa da yawa tunda suna zuwa islamiyya. Idan ba hakaba kana nan wasu zasu fara koya mata abinda kai kake ganin bata sanshi ba. Dan kwanaki sai da naci ƙaniyar wani malamin islamiyyar su wai shi Kamal. Daga baya ma na bincika wai yabar makarantar, amma da ya dage shi son Nimrah yake yi. Har ya fara zuwa gidan fa”. Wani mugun kallo Dada kema Imran kai kace shine Kamal ɗin. Aiko mi Imran zai yi inba dariya ba. Sai kawai Dada ya miƙe abinsa daga nan hirar ta watse ma. Har ya kawo shi gida bai sake kulashi ba. Haka ya sauke shi shima ya kama hanyar gida yana kwasar dariya. Dan shi kaɗai yaga bala'in daya hango a idanun zakinsa. Ai ko a fagen fama albarka. Ƙasa daurewa yay sai da ya bama Ammie labari. Itama taita dariya. Daga ƙarshe tace, “Ni kaina nayi tunanin fara shiri sai naga bakuce komai ba, amma share masa ɗaki a sashen Mammah. Amma magana ta gaskiya bana son Nabeeha ta dawo gidan nan Yarinyata bata tare ɗakinta ba.” “Ai kunji matsalarsu iyayen zamani, zaku fara koya mata kishin banza ko”. “Ba wani koya kishi Daddyn Khalifa magana ce ta gaskiya. Tunda ita bata da hankali dan mijin ya ƙara aure kin ɗauki ƙafa kin tafi gida. Ya shiga wani hali ki dawo ɗakin ki ki zauna kuyi jimami, kuyi kuka tare da ƴan uwansa da Mahaifiyarsa amma kin biyema taki uwar sai yawon gantali. Yanzu duk randa yasan wannan zaman Dubai ɗin da taje tayi mi kake tunani dan ALLAH. Zargi ma bazai shigo ciki ba”. “Ai babu ma wanda zai gaya masa. Yanzu dai mubar maganar, gyara kuma kiyi tayi, sai ki haɗa da Biebah da Asma'u harma da Ruƙayya”. Idanu sosai ta waro na mamaki. “Ruƙayya fa?”. “Eh, ubanta yace aure zai mata, yama mata miji. Gara ma yayi hakan, dan zanfi samun dama a kansa nima game da tarewar Nimrah ɗin”. Ammie da abin ma ya bata dariya ta ce, “To ALLAH ya sanya alkairi, yasa ayi damu, amma dai wannan miji zai kwasa.” Dariya Daddy Imran yayi itama tana taya shi. Ya ce, “Kamar kina wajen abinda na faɗa kenan nima. Amma tunda mai abu da abunsa sai ka tayashi da sambarka.” “Haka ne kam, ALLAH yasa ayi da rammu to”. “Amin ya rabbi”.........✍️