Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 77

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 77

.....the leaders of the group are again second to him. In this week there is also a big project that they will release. He got his wish and he was given leadership including the children under him, but the children of Dagger were not divided and given to him as he wanted. They are the new kids that we don't know. They were given training called training. Then he felt fear and doubt again about the matter of the dark group. Their philanthropy is very real. Then they went beyond all the expected places. No matter how hard you predict, you can't outrun them. They have hidden things that only GOD knows except them. The only thing that upset him was that they assured him that he must leave their house Nimrah. It is not possible for him to live with him today and tomorrow, because they know who Zak-Shadow is, they have studied him and they believe that he is a clever man. Second, hiding his face and avoiding Nimrah will allow him to achieve his goal of bringing her back into his life. And her soul will know who he is to her and she will feel his dignity and pride as a father. He was satisfied, even though it made him worried. But they advised him to visit the house from time to time, eve

Standalone post1,498 words

77

........Ana gobe suna su Gwaggon Alawiyya suka iso. Ai fa gida ya kacame. Su Nimrah amarori. Dan ma ita damuwa ta raba mata hankali biyu, dan ta gama shirya a cikin rarumar sunan nan zata haɗu da Dagger. Shiyyasa ma tai luff abinta a kwanakin da suka gabata kamar komai baya damunta. Amma da yake ita Ruƙayya na tare da ita tsaff ta gane damuwar kwanaki tana neman dawo mata. Koda ta dameta da tambaya sai tace rashin zuwa makarantar su ne ke damunta. Har tana bada shawarar idan anyi suna su sami Dada da maganar, dan gani suke kamar Mammah ce bata son su koma tana tsoron a musu wani abu. Ruƙayya ta gamsu da hakan shiyyasa ta saki maganar. Itama kuma Nimrah sai ta sake canja takunta. Dan yarinya ce mai shegen wayo da iya rikiɗa kamar hawainiya. Cikar gidan kuma ta sake maidata busy, dan ranar su aunty Ummi ma duk anan suka kwana. Dada ne dai basu gashi a gidan ba kwata-kwata tun safe. Babu ma wanda zaice ga sanda ya fita.....

<>%<>%<>%<>

A ɓangaren Malam Buba jinsa yake sharr, dan kuwa shugabannin ƙungiya sun sake zama na biyu da shi. A cikin satin nan ma akwai babban aikin da zasu fitar. Ya samu cikar burinsa an bashi shugabanci harda yara a ƙarƙashin sa, sai dai ba yaran Dagger aka raba aka bashi ba kamar yanda yaso. Sabbin yara ne waɗan nan da baima san dasu ba. An basu horo mai suna horo. Sai yaji ya sake tsoro da shakkar al'amarin ƙungiyar duhu. Dan hatsabibancinsu na gaske ne ƙwarai da gaske. Sannan sun wuce dukkan inda ake zato da tsammani. Duk iya hasashenka baka isa iya ƙare musu gudu ba. Suna da ɓoyayyun abubuwa da sai UBANGIJI ne kawai ya sansu sai su. Abinda dai ya tayar masa da hankali shine sun tabbatar masa dole ne yabar gidann su Nimrah. Dan zamansa bazai yiwu ba dan yau da gobe zata iya kwaɓewa kasancewar sun san waye Zak-Shadow, sun karanceshi sun kumayi imani da mutumin ne mai shegen wayo. Na biyu ɓoye fuskarsa da nisantar Nimrah zai bashi damar cimma burin dawo da ita cikin rayuwarsa. Duk kuma randa zata san shi waye a gareta zata ji martaba da girmansa matsayin uba. Ya gamsu, duk da hakan ya saka shi a damuwa. Amma sun bashi shawarar ziyartar gidan lokaci-lokaci koda da nufin gaisuwa ne, hakan zai sa ya dinga ganin nata...

Na biyu Sanda. Sanda har yanzu yana wasan ɓuya da Dada, bai taɓa bari Dada ya ganshi ba. Yaƙi kuma sanarma maigadin komai. Tun yana tambayarsa harma ya daina. Nimrah kuwa dakan ari wayarsa bai taɓa hanata ba. Gashi Sarkin wayon data gama take goge number ɗin. Sai dai yana nan ya shirya. Dan yana son yasan abinda take ɓoyewar. Tunda duk da akwai camaras a gidan ta iya kaucewa hakan ta ɓuya a inda babu tayi wayarta. Ya saka mata ido sosai batare data sani ba. Dan ita tana ɗaukarsa ne a garan ƙauye da baya gane komai....

•••••••••••••• ••••••••••••••

RANAR SUNA.....

RANAR DA ABUBUWA UKU MASU MUHIMMANCI SUKA FARU A CIKINTA.

NA FARKO....

Yau take suna a gidan Mammah, tun daga sallar asuba aka raɗa sunan yaro da yaci Uncle Nasiru. Wato Naseer. Dada ne kuma ya zaɓa masa wannan suna bai kuma sanarma kowa ba sai a yau ɗin. Kowa yayi farin ciki da abinda yayi, musamman Mammah dake ta saka musu albarka. Tun kafin tara tayi su Nimrah suka cika gidan da hayaniya. Dan party suka shirya ita da Ruky, Bintu, Feedo. Babu wanda kuma yasan sun shirya abinsu sai Mammah. Sai Uncle Bilal da suka tasa a gaba ya basu kuɗi. Sunyo gayyar ƙawaye sai dai ba wani da yawa ba, yawancin su ma ƙawayen Feedo da Bintu ne, dan masifar Ruky da Nimrah tasa ko ƙawaye basa iya zama da su. Su biyun nan sun ishi kansu suke cewa, sai su Bintu. Girkinsu suka ƙirƙira daban, duk da an biya kuɗi za'ai na suna su sunce zasuyi nasu a gida, saboda ba abinci sukai ba duk kayan kwaɗayi ne da shiririta. Hakan yasa su wannan sammakon tashi suketa cacai-cacai. Dada da suka isa da hayaniyarsu, dan tun daga sama yana jiyo su, ga kiɗa sun kunna ya tashi kawai yay shirinsa. Dan gara yabar musu gidan shi kam. Zai je kawai ya gaida Baffa suyi hira tunda ya dawo dama bai nutsu sunyi hira ba sai dai yaje ya gaishe su shi da Hajjo sama-sama. Lokacin da yake sakkowa sam su Nimrah basu sani ba, dan sun dage suna shan rawa abinsu bil haƙƙi. Biebah na musu video ita da Mu'azz. Kansa kawai ya girgiza ya wuce abinsa batare da kowa ya lura da shi ba sai Aunty Mommy, da ido kuma yay mata alamar kar tai magana. Dole tai shiru tana murmurshi, shi kuma ya fice.

NA BIYU

Fitar Dada babu jimawa labari da ɗumi-ɗuminsa ya iso sashen Mammah. Wai ga wasu mutane sunzo sashen Dada da babu kowa a ciki tare da Nabeeha da ƙannenta. Falon yay tsitt, kafin kowa ya iya magana sai ga Hajiya Hasiba ta shigo Amima biye da ita. Sai da ta gama bin falon da kallo sannan tai murmurshi tana ƙarasawa inda Mammah take da su Gwaggo Khadijah. A ranta kam faɗi take (Ni Hasiba yaushe mutanen nan sukai kuɗi haka? Ya akai Banda labari) a zahiri kuma da murmushi nan na fuskarta takai zaune a kujerar da Aunty Badiyya matar Uncle Jamilu ta bata tana faɗin, “Hajiya A'isha ashe suna ake gidan haka bamu da labari”. Mammah a duk yanda kake ta iya da kai, sai itama ta saki murmurshi. “To ayi haƙuri munyi laifi. Wani lokacin abubuwan nauyi suke a kai sai ka manta da wasu”. “Haka ne kam, ALLAH yasa mu dace. Dama ɗiyarki ce zata dawo ɗakinta, shine muka zo da kamfanin da zasu saka kaya a sashen nasu, kinga ba'a maida waccan ba ai”. Nan ma murmurshi Mammah tayi, ga falon yayi tsitt kowa na jiran yaji amsar da Hajiya Hasiba zata samu. Musamman su Aunty Mimi da wani tarnaƙin baƙin ciki ya lulluɓesu. A bazata suka ji Mammah ta ce, “Keys ɗin suna hannun Muhammad ai, ta kira shi nasan zai kawo muku. Dan babu ma jimawar nan ya fita”.. Dariya Biebah ta ƙumshe, haka ma Aunty Mimi. Su dai su Nimrah basu fahimci komai ba. Hankalinsu ma nakan ƙulla kayan da zasu raba dan Mammah ta saka sun kashe kiɗan dan kunensu ya huta. Maimakon Hajiya Hasiba ta nuna jin haushi, sai sukaga tayi murmushi kawai da faɗin, “A to shike nan ai ba damuwa. Bari naje sai ta kira shin”. Tai maganar tana watsama Ummu kallon banza, ita bama tasan tanayi ba, dan tunda ta shigo ko kallonta ma batayi ba. Tana fita su Aunty Ummi suka saka dariya. Aunty Mommy tace, “Kai Mammah kin iya bada amsa, ALLAH yau sai naga kamar bake ba. Dan na gama shirya zanyi rashin mutunci fa”. Mammah ta harareta da faɗin, “Ku kuna son bala'i yay barci ne? Shiyyasa ga yaranku nan sun nuna sun fiku iyawa ai.” ta ƙare maganar da kallon su Ruky dake ta hidimarsa. Dariya manyan suka sanya, daga haka hirar ta koma kan su Nimrah ɗin ko tada zancen Hajiya Hasiba babu wanda ya sake yi. Sai bayan kusan mintina arba'in har Mammah ma ta manta da zuwanta sai ga Mu'azz ya shigo wai yaga ana shiga da kaya sashen. Mamaki ya kama kowa, su Aunty Ummi zasu fita Mammah ta hana su. “Haba Mammah ya zaki ce a barsu, kenan fa ɓalla kofar sukayi?”. Gwaggo Khadijah ce tai magana yanzu kam. “Suma ɓalla ginin, kar wanda yace musu komai. Itafa shari'a idan zakayi ta yana da ƙyau kayita da hujja. Kuda kuka tara mutane kuna hidima ina zaku biye ai tashin hankali da ku. Ai amsar da Maman Ma'aruff ta basu ya wadatar, abinda kuma suka aikata sai ku jira Haysam ɗin, ai sun san ba kanwar lasa bane ba. Dan wannan karon na roƙeku kada wanda ya shiga wannan maganar a gidan nan, Maman Ma'aruff kema dan ALLAH ki bar Haysam yayi yanda yake so”. Murmurshi Mammah tayi. “In sha ALLAHU bazan tauye shi ba Addah Khadijah. Dama na saka a raina su ƙarata.” Daɗi ne sosai ya kama su Mimi. Dan dama sun san Mammah ce matsalar Dada. Idan kuma ta cire hannunta komai zai tafi yanda suke so. Ai koda akace kada suyi magana wlhy sai sun gasama Nabeeha aya a tsakiyar tafin hannu. Suda suke da babban makami a hannu yanzu Nimrah. Ai zama zasuyi su zuge su Gwaggo Khadijah Nimrah ta tare itama idan son samu ne ma kafin su koma ɗin nan. Dama tunda Dada ya dawo suke wannan ƙulle-ƙullen. Yanzu haka ana gama sunan nan su Ja'afar zasu wuce kawo kaya daga nan zasu haɗo kayan Nimrah dana Biebah. Iya su suke ƙulle-ƙullen su sunƙi bari Mammah ta sani balle Dada ko uwar gayyar Nimrah da bata ma san da auren ba........✍️