Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 78

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 78

...and she held her hand. She said, "Aunty, why don't you think too much about yourself, even though you don't know Momy's intentions when you come back to this house, you should be safe. You should know that the battle for your house is in your hands, and you should do it. And now, even though she didn't tell what happened, she went to the part where the door was broken. It was enough for you to understand that it was against the consent of the people of this house. son, not only his brothers, but also Mammah on this side arranged that". Ismat's words really affected Nabeeha. She couldn't say anything but followed Ismat with her eyes. Hajiya Hasiba chose the department that Zaima Nabeeha lined up for herself, the company did their tests, as they had already chosen the clothes they wanted. Some of the names of their entertainment part of Nabeeha are being teased in a row. Hajiya Hasiba and Ismat are standing on top of everything, showing where to fix and what to add. Everyone thought that Dada was about to come home from the hospital where he was being treated. However, no one from the owners side of the house said anything and no one showed that they knew what Hajiya Hasiba is doi

Standalone post1,533 words

78

.......★A ɓangaren Hajiya Hasiba tana komawa wajen su Nabeeha tai kiran wani yaronta mai yin ƙofifi. Babu jimawa kuwa yazo. Bata gayama su Nabeeha abinda ya faru ba. Ta kuma gargaɗi Amima. Yaron nata ne yay dabarar kwance injin key ɗin ƙofar gaba ɗaya, sai dai kuma ya kasa maidawa dan ya lalata shi. Bata damu ba tace ya ajiye musu, idan sunga zasu gyara sa gyara. Ko su cire ƙofar su canja. Matuƙar haɗuwa fa sashen ya haɗu. Sai dai yanda tsarin ƙasa yake ya tabbatar da na zaman mace biyu ne, kasancewar ƙofofin duk a buɗe suke suka shiga ko'ina. 2 bedrooms ne, da falo ɗaya babba sosai, sai ƙarami, sai kicin, store. A kwai bayi a babban falon sannan akwai a bedrooms ɗin. Acan sama ma ƙaton falo ne guda ɗaya sai bedrooms biyu, sukam ma duk suna a kulle ne. Cikin kuka Nabeeha ta ce, “Momy mi hakan ke nufi? Haysam na nufin harda waccan yarinyar.....?”. “Haysam ko munafukar uwarsa da ƴan uwansa da wannan shegen Imran ɗin. Shi da baya nan sukai gini miye nashi”. Nabeeha zata sake magana Ismat ta riƙe mata hannu. Ƙasa-ƙasa ta ce, “Aunty wlhy kada kima kanki ganganci, duk da baki san manufar Momy akan dawowar ki gidan nan ba koba komai kin tsira. Ya kamata ki sani fa yaƙin gidanki a hannunki yake, ke ya kamata kiyi. Kuma yanzu duk da bata faɗi abinda ya faru ba da taje can sashen yanda aka ɓalla ƙofar nan ya isa ki fahimci bada yardar mutanen gidan nan bane, sun hana keys ɗin kenan. Ina baki shawara kada kiyi abinda zaki rasa Dada gaba ɗaya a wannan karon, dan ba ƴan uwansa kawai ba har Mammah a wannan gaɓar ta shirya hakan”. Sosai zantukan Ismat sun shigi Nabeeha. Dan kasa cewa komai tai sai bin Ismat ɗin da idanu. Hajiya Hasiba ta zaɓa sashen da za'aima Nabeeha jere da kanta, kamfani sukai gwaje-gwajen su, kasancewar dama sun riga sun zaɓi kayan da suke so. Ƴan suna na shagalinsu ɓangaren Nabeeha ana zafga jere. Hajiya Hasiba da su Ismat na tsaye kan komai suna nuna inda za'a gyara, da kuma abinda za'a ƙara. Kowa na tunanin Dada na gab da dawowa gida kenan daga asibiti da aketa ƙishin ɗin yana jiyya ne. Sai dai yanda a ɓangaren masu gidan babu wanda yace komai babu kuma wanda ya nuna yama san mi su Hajiya Hasiba ɗin keyi yasa ƙananun maganar basuyi tasiri ba. Har suka kammala komai zuwa bayan azhar kamfanin da Hajiya Hasiba suka wuce, su kuma yaran suka hau shara da goge....

★••★•••★••★

A dai-dai wannan lokacin kuma Nimrah data tabbatar kowa ya gama shagala da bikin suna ta gama shirinta tsaf na silalewa domin ganawa da Dagger. Yayinda Sanda yay mugun saka mata ido kamar yanda ya saba a kwanakin nan. Sai dai abinda bai fahimta ba Nimrah nada shegen wayo. ALLAH ya bata basirar iya tsara abubuwa duk da ƙarancin shekarunta. Hatta wannan fatin ita ta ƙirƙiresa ta sakama Ruky son ayi a zuciya dan kawai ta samu damar. Dan ta tabbatar koda hidima ta ɗauke hankalin su Mammah a kanta banda Ruky. Amma yin wannan fatin zata samu hankalin itama Rukyn ya koma can ɗin. Lallai dabarar tata kuwa tayi, dan kamar yanda suka tsara anayin sallar azhar suka fita can bayan sashen Dada da babu yawan mutane da hayaniya suka fara shirya kujeru, wajen an gyara shi ne da green carpet da flowers masu ƙyau. Duk da ba zaman sashen ake ba sanda na ƙoƙarin tsaftacesa bisa umarnin su Ammar. Dan wani lokacin sukanje can suma su ɗan huta.....

Lokacin da suka fara aikin su kuma su Nabeeha hankalinsu nakan nasu aikin, shiyyasa babu wanda ya maida hankali akan wani, musamman daya kasance bata wannan bangon ɓangaren Nabeeha ɗin yake ba. Sun kammala suka koma sashen Mammah yin shiri, dan sabon ɗinkuna su Uncle Ja'afar suka musu har kala uku-uku na suna. Afrah na maƙale da Nimrah, dan haka ta fara shiryata ta mata wayon aikata wajen Mammah. Daga haka itama tahau shiri, su ma su Ruky nayin nasu. Sauri-sauri ta kammala nata shirin, ta idar da sallar la'asar sai ga wasu ƙawayen Bintu sun kira akan basu gane Street ɗin ba. Caraf Nimrah tace ta bata wayar tunda ita ta shirya zataje ta tarbosu. Basu kawo komai a ransu ba ta amshi wayar Bintu ta fito, dan suna da waya daga ita har Feedo. Lokacin da Nimrah ke fita a gate Sanda na cikin bayi, sai baba maigadi kawai. Shi kuma bai kawo komai a ransa ba jin tana waya tana yin kwatance alamar wasu zata tarbo. Hakama securitys ɗin dake waje, yanda ta tsaya tana waige-waige ga waya tanayi yasa suma basu maida hankali ba, gashi ma abinci da aka kawo musu suke ƙoƙarin fara ci. A wannan lokacin da gaske Nimrah ta fito ne da niyyar tarar baƙin Bintu, amma daga nan tana son tayi waya da Dagger ta sanar masa da anyi magriba ya fito su haɗu. Amma sai mi ta ɗan bar gate ɗinsu kaɗan sai ga su Adeel da Yohan da yake gidansa zaune. Nimrah bata san shi ba, kai ko Yohan ɗin bata sani ba, dan haka ko kallo ma basu isheta ba ta cigaba da tafiyarta tana tunkaro su. Cak Adeel ya tsaya kansa na wani irin tsuwwa da ganin Nimrah a bazata. Dan yau kwanansa biyu kenan da dawowa ƙasar amma ko mai kama da ita bai taɓa gani ba. Kai koda Ammar ma basu haɗu ba. Ganin kallon da yake mata Yohan ya fahimci akan ta ne kenan Adeel yazo anguwar ya tare, shi kansa yaran biyu suna birgeshi dan yana shan ganinsu idan za'a wuce dasu makaranta haka a mota. Ita dai Nimrah tazo ta gittasu a taƙaice tace musu “Good Afternoon”. kawai, dan gaishe da na gaba da su koda basu sanshi ba wannan tarbiyyarsu ce. Da ƙyar Adeel ya iya controling kansa baibi bayanta ba, sai dai yace da Yohan su dakata a ƙofar gate ɗin su kira Ammar idan yana nan, dan yau bazai iya haƙuri ba sai ya shiga gidan nan duk da yaga anata shiga da fita alamar wata hidima sukeyi. Nimrah data gotasu kaɗan tana ƙoƙarin sake kiran su Teemerh dan har yanzu bataga wata alamarsu ba kuma ta fara gajiya gashi tayo nesa da gida kawai wata farar mota ta tsaya mata. Ganin motar ba wata babba bace sosai tayi tunanin su Teemerh ɗin ne, dan haka tabi ta da kallo tana ƙoƙarin kai wayar kunnenta kawai taji an fesa mata abu a fuska. A kiɗime ta ɗago numfashinta na fisga zatai magana kawai ta tafi gaba ɗaya, duhu ya mamaye mata cikin idanu, sautin motsin anguwar da ba wani mai yawa ba yay nesa da kunnenta. Daga haka bata sake sanin abinda ke faruwa ba...

Wani mai gadi dake ƙofar gate ɗin wani gida da yay facing inda Nimrah ta tsaya, sai dai motar tai blocking ɗinta dan har yana jin haushi saboda tunda Nimrah ta ɓullo suka zuba mata ido shi da abokin zamansa suna magana kawai sukaga motar tabar wajen a guje. Koda suka duba inda sukaga Nimrah kafin zuwan motar sai sukaga wayam babu komai. “Anya lafiya kuwa Zailani? Kalli fa yanda motar can ta bar wajen kuma babu yarinyar fa”. Wanda aka kira Zailani ya miƙe cikin mamaki yana faɗin, “Ai ni nazata ko wanda ta sani ne. Amma gaskiyarka fa wannan gudun marasa gaskiya ne”. Da wannan surutun suka tsallako titin zuwa inda Nimrah ta tsaya, sai ko ga wayar Bintu yashe a ƙasa, harda abin hannunta da mayafi alamar fita sukai. Wayar su Zailani suka ɗauka, dai-dai nan kira ya shigo. Bintu ce ta kira da wayar Feedo jin Nimrah shiru bata koma ba. Zailani na amsa wayar kafin ma yayi magana daga can Bintu ta ce, “Ninah wai har yanzu baki gansu ba ne?”. Zailani yaja numfashi ya fesar, sannan cikin son fahimtar da ita yace, “Ba ita bace ba.” “Kai! Waye to? Ina mai wayar? Ya akai tazo hannunka?”. Kai tsaye ya bata amsa da, “Akwai fa matsala. Yanzu wata mota ta ɗauki mai wayar suka gudu da ita, shine suka yadda wayar, sai kiyi ƙoƙarin faɗa a gida azo a amshi wayar da mayafinta kuma....” Wani kalar razannanen ihu Bintu ta saka. Ihun daya dawo da hankalin kowa dake falon ɗakinsu Nimrah ɗin. Suma su Ruky dake ɗauri a gaban mirror tuni sunyi kan Bintu a hargitse. Dan sai kwarara ihu take tana faɗin, “Ninah! Ninah! Ninah”. Ruƙayya ta fashe da kuka tana faɗin, “Ki gaya min miya samu Ninah ɗin dan ALLAH Bintu, wlhy zuciyata zata buga”. Itama ta fashe da kuka jikinta na rawa. Cikin ƙanƙanin lokaci ɗakin ya cika, kowa Bintu yake tambaya dan ita keta faɗin, sunan Nimrah. Sai da Ummu tai mata tsawa da faɗin ta nutsu tai musu bayani sannan ya faɗa abinda wanda suka kira ya faɗa. Wayar Feedo aka amsa daga hannunta akai kiran layinta, kai tsaye nan ma Zailani ya amsa. Irin bayanin da yayma Bintu kuma yay musu. Hankali ya ƙara tashi, akace ya faɗi inda yake. Babu kwana-kwana ya sanar musu. Tsabar rikicewa wasu ma ko gyale babu akansu suka fito,........✍️