Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 79

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 79

.....mystery. This led to a pleasant conversation until the afternoon when they left the mosque. After they returned from prayer, they were planning to say goodbye to Hajjo and Baffah, but when Baffah wanted to talk about his old age, he kept them busy with his story. As soon as he released them, they came out and left him with Uncle Nasiru. They went directly to the private house they found called UNIT ZERO. I am not directly at home now. Everything in it is organized and safe. They also follow the system they enter, especially the security of the door that does not open except with a password. And only the two of them know. Imran entered the password and the door went in. They entered and sat Imran trying to open the laptop and saying, "Dabo sent me a message right now, if you give them permission they will kill him and Yusuf". Before Dada responded to him, his phone made a Samsung design for about the third time, making him blush a little. Put the pen in one of his hands and take it on top of the paper to write on, then he raised it and picked up the phone. Seeing the name of Mu'azz, the miss calls him and he continues to call him.

Standalone post1,508 words

79

........Mammah ma sai da aka biyota da takalma. Securitys ɗin wajen gate najin abinda ya faru suka watsar da plates ɗin abinci. Su Adeel sun bar wajen dan sun kira Ammar yace musu baya nan, kuma a gaban securitys ɗin nan akayi, ɗan sanin da sukaima Yohan dakan fito daga gida kullum motsa jiki ko idan zai wuce wajen aiki sukan gaisa yasa basu kawo komai a ransu ba. Kafin kace mi gayyar mutane sun zagaye su Zailani. Kamar yanda sukai bayani a waya haka suka maimaita. Jikin Mammah rawa yake sosai, dama tunda ta tashi yau gabanta ke faman faɗuwa. Sai ta barshi akan wannan taron ne maybe, da su Hajiya Hasiba sukazo kuma sai take ganin ko sunzo da wata fitina ne dan su ɓata mata taro, shiyyasa ta kwaɓi al'amarinsu cikin sauƙi tanata addu'a, ashe ga abinda ke shirin faruwa nan...

<<<<<。⁠◕⁠‿⁠◕⁠。>>>>>

A dai-dai wannan lokacin Imran da Dada na gidan Baffa ne. Tare da shi sukai sallar la'asar sukaci abincin rana. Sun sake dasa sabuwar hira da gaba ɗayanta akan al'amarin ƙasar ne sai ga Uncle Nasiru. Wannan ya ƙarama hirar armashi har lokacin la'asar da suka fita massalaci. Bayan sun dawo salla suna shirin daga nan suyi sallama da Hajjo da Baffah, sai dai da yake Baffa akwai son hira abinka da tsufa sai ya ƙara riƙesu da labarinsa. Da ƙyar ya sakesu suka fito suka barshi da Uncle Nasiru. Kai tsaye gidan nan na sirri da suka sakama suna UNIT ZERO suka nufa. A yanzu gida ne bana kai tsaye ba. Komai a cikinsa da tsari da tsaro. Suma kansu sai sunbi tsarin suke shigarsa musamman security na ƙofa da baya buɗewa sai da password. Kuma su biyu kacal suka sani. Imran ya saka Password ɗin ƙofar ta shige. Sun shiga kenan sun zauna Imran na ƙoƙarin buɗe laptop da faɗin, “Dabo ya tura min saƙo yanzu nan, idan ka basu izinin zasu ƙaraso shi da Yusuf”. Kafin Dada ya bashi amsa motsin da wayarsa tayi ƙirar Samsung a karo na kusan uku kenan yasa shi jan ɗan siririn tsaki. Ajiye haɗaɗɗen pen ɗin hannunsa daya ɗauka shima saman takardar da zai yi rubutu yayi, sannan ya ɗago yana mai ɗaukar wayar. Ganin sunan Mu'azz ga miss calls ya jera masa kuma ya cigaba da kira ya sashi ɗaga wayar ya kai kunnensa a nutse, kafin ya motsa lips ɗinsa cikin dakakkiyar muryarsa dake a buɗe irin ta ainahin jaruman maza ya furta, “Kai ka iya damun mutane suna aiki ko?”. Cike da girmamawa daga can muryar Mu'azz na rawa ya furta, “Dada. Dama Ninah ce ta fita wai tarar ƙawayen Bintu a waje wai wata mota ya ɗauket.....” kuka ya sarƙe shi ya kasa ƙarasa faɗa. Wani irin duka zuciyar Dada keyi a cikin ƙirji. Ya dai daure cike da dakiya ya ce, “Ita kaɗai ta fita a gidan?”. “Eh ita kaɗaice sai wayar Bintu.......” nan ya bashi labarin duk yanda su Ruky sukai bayani akan fitar tata da abinda kuma masu gadin nan suka sanar musu. Kasa cewa komai yay, sai ya katse kiran gaba ɗaya yana furzar da iska mai nauyi. “Lafiya dai?”. Imran daya maida hankali a kansa ya tambaya. Sai da ya ajiye file ɗin hannun nasa kafin ya furta, “Muje gida akwai matsala.........” a taƙaice yay ma Imran bayani. Cikin ƙanƙanin lokaci Imran ya rikice. Tuni shima ya miƙe yana kashe laptop ɗin. Dada ma miƙewa yay yana sake kiran Mu'azz da saka wayar a hans free ya ajiyeta saman center table ɗin yana fara tattare takardun daya gama bazawa yanzu nan, sai dai kunnensa nakan wayar. “Dada naji ka katse ne!”. “Kai kaɗai ne a gida?”. “Eh, amma an kira su Uncle Ja'afar suma gasu nan tafe. Kaima tun ɗazun su Mammah ke gwada kiranka yaƙi shiga, shiyyasa hankalinmu ya ƙara tashi sosai.” “Gani nan zuwa gidan”. Ya faɗa yana nufar ƙofar fita. Imran yabi bayansa. Hankalisa a natuƙar tashe ya kallesa, “Haysam kodai a sanarma jami'ai ne?”. “Imran karka ruɗa kanka, ko su wanene suna da dalili....” Ya faɗa dai-dai yana ƙoƙarin ficewa, dan haka shima Imran ya zabura. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gidan. Gaba ɗaya a compound suka same su, idan ka cire Mammah dake falo da su Ja'afar da suka ƙaraso. Amma sauran mutane da yawa ƴan suna duk suna compound, a hakama kasancewar yamma tayi mutane sun ragu sosai sai iya na jiki-jiki. Yanda ya ɓalle murfin motar ya fito. Ya isa ya sanar maka lallai kam shi ɗin tsayayyen mutum ne kuma jarumin sadaukin gaske da ko'a cikin sojojin ya isa a kirashi BARDE. Ga dai shekaru sun ja amma da alama har yanzu jinin jikin da ƙarfinsa yake gudana. Dan yanda yake taku ma kawai ya isa ka shaida asalin ZAKI ne, kuma tabbas a ƙuruciya an baza capacity iya capacity na manyan BARADA. Daga shi har Imran ɗin nasa a tsayensu suke. Badan da yawan wanda ke wajen sun san shi waye ba da sai suce kamar babu damuwa a tare da shi ma. Amma shi Imran yasan waye Zakinsa. Tarnaƙi baya bayyana kai a fuska sai a cikin zuciya da kwanji. Suna isowa wajen cike da girmamawa aka fara gaishe su, Imran ne kawai ke amsawa. Shi kam hannu kawai ya ɗaga musu ya wuce hanyar falo Agogon hannunsa ƙirar Maawad Company ya kalla, ganin lokacin sallah na sake matsowa. Tura ƙofar da shigarsa ya saka duk wanda ke a falon juyowa, sai kuma duk suka miƙe a kusan tare, banda Mammah da Gwaggo Khadijah. Kai tsaye Ja'afar da Ma'aruff suka nufosu suna musu sannu shi da Imran, shima idonsa a kansu dan haka ya jinjina musu kai. Ruƙayya dake jikin Mammah tana kuka ta taso da gudu ta shige jikinsa tana sake fashewa da kuka. “Dada Ninah ɗita, zasu cutar min da ita, dan ALLAH kuje kaida Daddy ku dawo da ita...” “Ya isa haka. Ki mata addu'a ALLAH zai kareta a duk inda take”. Kai Ruky ke jinjina masa amma hawaye sun gagara tsayawa. Kama hannunta yay suka ƙarasa cikin falon sosai. Cike da girmamawa su Ammie dake falon suka shiga gaishe shi. Dan har sun gaisa da Imran ya zauna shi. Amsa musu yay batare da ya kallesu ba, sai kuma ya nufi inda Mammah take. Har ƙasa ya rissina yana gaisheta, ta amsa da kulawa da tsantsar damuwar dake shimfiɗe a fuskarta. Tashi yay ya koma a kujerar kusa da ita ya zauna, tare da riƙo hannunta cikin nashi, dai-dai nan Ammar da Bilal suma suka ƙaraso. Suma gaishe su suka yi. Imran ya amsa musu da kulawa, shi ko hankalinsa nakan Mammah yana mata magana ƙasa-ƙasa. Hawaye Mammah ta share tana jinjina masa kai. Imran ya katse shirun da faɗin, “Ya akai ta fita ita kaɗai?”. Aunty Ummi ta share hawaye tana bama Imran ɗin amsa da, “Babu wanda yasan ta fita wlhy Yaya, gaba ɗayansu suke hidimar su can bayan sashen Dada, sai da aka kira la'asar suka shigo sukai wanka, dan ita tama sakko ta kawo Afrah wajen Mammah ta sake komawa, ni wlhy hankalina ya fara tashi, mi Ninah zataima wani da har zai yi kidnapping ɗinta, dole yana cikin gidan nan tun ɗazu tare da mu. Kuma ni gaskiya ina zargin.......” Kallon Da Mammah ta mata ya hanata ƙarasawa. Imran daya lura da abinda Mammah tayi sai shima bai nema ƙarin bayani ba. Kallonsa ya maida kan Ruƙayya, cikin bada umarni ya ce, “Tashi zaune”. Tashi tayi sosai ta zauna. Kafin ma ya tambayeta ta faɗa masa komai daya faru. Aka kira Bintu da Feedo suma. Wayar Bintu ɗin ya amsa. Yay ƴan bincike-bincikensa ya miƙa mata. Ya maida hankalin sa ga Dada dake kwance jikin kujera idanu a lumshe Mammah tai magana muryarta na nuna damuwa sosai, “Ni nama rasa wane irin tunani zanyi. Dan koma su waye suka aikata idanunsu na kanta ne shiyyasa har suka san fitar tata kamar yanda Ummi ta faɗa. Idan suka cutar min da yarinya bazan yafe musu ba, Imran kuje ku nemomin yarinyata kar ku barta ta kwana a wani waje dan ALLAH.” Dada ya ƙara damƙe hannunta dake cikin nashi, sai kuma ya buɗe idanunsa dake rufe amma duk abinda ake yana saurarensu, cike da lallashi da kulawa, murya a tausashe ya ce, “Please Mammah calm down, in sha ALLAHU babu abinda zai faru...” “Muhamamd ta ina hankalina zai kwanta kuwa, kasan mi ake nufi da rashin budurwar yarinya kuwa?. Dan ALLAH kuje ku nemo min yarinyata”. “In sha ALLAHU Mammah, bari muje muyi salla gata can ana kira. Kuma kuyi, kuyi mata addu'a ita tafi buƙata a yanzu kamar yanda Haysam ya faɗa”. Kanta ta jinjina ma Daddy Imran mai maganar tana share hawayen da suka cika mata ido da hijjabin jikinta. Miƙewa su Ja'afar sukayi. Imran ya kalla Dada da bai motsa ba. Idan ka kallesa sai ka rantse bashi da wata damuwa, amma ya fisu jin tashin hankali, musamman ma furucin Mammah, kawai dai mazan maza ne shiyyasa ya shanye komai yanata nazarin abubuwa ne. Tare suka fita da ƙannen nasa da Imran masallaci.........✍️