
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 70
....is included. It was safe and sound and she slapped her face. But now she just bowed to Mammah after greeting their Uncles and their noise filled the hall. There is no Ruky, there is no Small Mom and Mamy either. That's why she took the food from the table and turned and went back to the top, until Mu'azz scolded her saying, "Oh, today, Ninah, we are careful". Ammar laughed and Bilal said, "Don't praise the leper, it's just Dada's job, but Ninah likes to beat the body. Ruky wants to work." "Also if she doesn't feel safe". Ammar said. They laughed too. Dayan and Afeef did not agree. They are still full of Nimrah and Ruky in their minds... __ Nimrah came back upstairs and stood for a while like an observer before she ended up in front of the door. But she stopped because of Daddy Imran's statement. "You mean everything in Zak's file...?" A few seconds passed before she heard Dadan reply, "You see, I woke them up on the bed, I know I left them in the file you brought them. Naga was crying, but I don't understand the reason for doing it, because I don't think there is anything she would understand." "Well, there's no reason for me to understand...
70
........Shigowar Imran baisa ya buɗe ido ba, dan tunda Nimrah ta fita yana a yanda yake bai motsa ba. Sai dai ya zubama ƙofar data maida ta rufe idanu, shiyyasa a kan idonsa Imran ya shigo. Ganin haka yasa Imran nufin tsokanarsa. “Ikon ALLAH ashe kana ciki! Shiyyasa naga yarinyata ta fita a birkice. Alhajin ALLAH mi kai mata ne?”. A mamakinsa yau kam murtani ya samu, dan cike da gatse Dada daya buɗe idanun sa da suka canja launi yana harararsa ya ce, “Abinda zuciyarka take tunani”. Dariya Imran ya fashe da ita yana kaiwa zaune da faɗin, “Naga tabbacin a idanunka kam haƙun. Haba Suger Daddy ai ka bari na baka ita tukunna”. “Kai dai ALLAH ya kimtsa wannan gurɓataccen tunanin naka”. Dada ya faɗa yana sauke ƙafafunsa ƙasa da miƙewa ya shige bathroom. Shi dai Imran dariyarsa yake da cigaba da tsokanarsa. A haka bayan wasu mintina kusa goma sha ya dawo ya zauna inda ya tashi batare daya tanka masa ba....
★A ƙasa Nimrah na sakkowa Mammah tace mata ta ɗauki abincin Dadan ta kai masa gashi nan an haɗa. Da lafiya-lafiya ne sai ta shagwaɓe fuska. Amma yanzu sai kawai ta jinjina ma Mammah ɗin kai bayan ta gaida Uncles ɗin nasu da surutunsu ya cika falon. Babu Ruky babu Small Mom da Mamy ma. Hakan yasa ta ɗauka abincin salin alin ta juya ta koma saman, har Mu'azz na gulmarta da faɗin, “Oh yau su Ninah anyi hankali”. Dariya su Ammar sukayi, Bilal ya ce, “Daina yabon ɗan kuturu, dan dai aikin Dada ne kawai, amma Ninah da son jikin tsiya. Ruky ta fita son aiki”. “Itama in bata jin tsiyarta ba”. Cewar Ammar. Nan ma dariyar sukayi. Dayyan da Afeef dai basu tanka ba. Dan har yanzu cike suke da Nimrah da Ruky a rai...
__
Nimrah data dawo sama kuwa ta ɗan tsaya kamar mai nazari kafin ta ƙarasa gaban ƙofar, nan ma sai da ɗan yi shiru na sakanni sannan ta kai hannu zatai knocking. Amma sai ta tsaya cak sakamakon furucin Daddy Imran. “Kana nufin taga komai dake file ɗin Zak...?” Sai da wasu sakanni suka shuɗe kafin ta jiyo Dadan ya bashi amsa da, “Ta gani, dan baje-baje na taddata da su a gadon nan, nasan kuma a haɗe na barsu cikin file ɗin daka kawo su. Naga tana kuka, sai dai ban fahimci dalilin yinsa ba, saboda bana jin akwai abinda zata fahimta”. “Hakane, babu dalilin ta na fahimta, sai dai ina tsoron karta gane hoton Mamanta da Babanta dana tsohon nan da nata ma. Dan kasan a shekarun baya ta taɓa ma Mammah tambayar data saka ta sanar mata Mamanta ta rasu da babanta, na tabbatar wayonta bazai sa ta manta da hakan ba kuma, kuma bazata manta da fuskar mamanta ba. Ya rabbi, ALLAH yasa bata fahimci komai ba ɗin dai. Dan bana son a yanzu Nimrah tasan abinda ya faru a baya har sai mun kammala project ɗin nan, shiyyasa ma ko batun aurenka dake kanta muka ɓoye mata”. Ƙirjin Nimrah yay wani bala'in bugawa, har bata san ta furta kalmar, “Aure?!”. a lips ɗinta ba. Yayinda kalaman Daddy Imran ke mata wani kalar amsa kuwwa a cikin kunne da ƙwaƙwalwa. (Basa son ta san komai har sai sun kammala project ɗin nan? Ke nan ta tabbatar Dada nada alaƙa da mutuwar Ummanta ko mi? Idan ba haka ba miyasa zasu so karta sani to? Wane project ne haka? Sannan waye ma keda aure? Wa kuma ake aure?). Babbar bala'i, wannan wace irin rana ce a gareta? Mike shirin faruwa?. Wlhy ta gagara gane komai fa.... “Imran ina son zan sai gida a anguwa mai ƙyau, dan aikin nan bazai yiwu anan ba. Yaran nan basa ji, na tabbatar kuma zasu cigaba da shigowa ɗakin nan musamman ita, idan na adana wani abun wani zan iya mantawa na bari ta cigaba da gani”. Furucin Dada ya katse mata tunani. Amsar da Imran ke bashi yasa ta ƙara kanga kunne. “Nima nayi tunanin hakan gaskiya, ya kamata ace kana da wani privete place kodan ma yanayi tsaro, kaima hakan zai baka damar yin aikin batare da damuwar komai ba. Sai dai yanzu sayen gida zai iya jan hankalin masu biye da lamarinmu”. “To ya kake so ayi?”. “Gashi ka duba cikin waɗan nan gidajen namu ko akwai wanda yay maka”. Imran yay maganar yana miƙa masa wayarsa. Maimakon Dada ya amsa wayar sai ya zuba masa idanu. Cikin ɗan waro idanu Imran ya ce, “Wai kallon fa?”. Kauda kai Dada yayi, sai kuma ya amshi wayar da faɗin, “Kana nufin har yanzu kana wannan business ɗin?”. Cikin ƴar dariya Imran ya ce, “Zak.. nawa, to mi za'a fasa. So nake ma ka ƙara nutsuwa na maka bayani akan yanda abubuwa suka ƙara bunƙasa, dan cikin watannan zamu fara fitar da ayyukan gine-gine kai tsaye daga kamfanin SAMRAN in sha ALLAHU.” Dada ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, yana kallon hotunan gidaje tunaninsa na komawa baya, lokacin da Imran ya matsa su haɗa kuɗi su fara sayen filaye suna sayarwa, a lokacin gidan nan ɗaki biyu ne zagaye da langa-langa, ga albashinsu bai taka kara ta karya ba, ga biyan kuɗin makarantar su Ma'aruff, ga halin baƙin ciki da Mammah ke ciki akan abinda ƙaninta Tasi'u ya aikata mata da mahaifin Biebah. Yay gajeran murmurshi daya saka Imran ma murmusawa. Dai-dai nan Nimrah tai knocking ƙofar jin basu cigaba da zancen ba. Ga ƙafafunta sun fara nauyin gagara ɗaukarta, sai ta yanke shawarar kawai basu abincin ta fita ko zata samu filin yin tunanin abinda ke faruwa da rayuwarta itama. Dan tana ji a ranta addu'ar data dage da yi ce yau UBANGIJI ya fara warware mata gaskiya... Buɗe ƙofar da Imran yayi ya sata dawowa hayyacinta, tai murmurshin yaƙe da faɗin, “Daddy abinci ne in ji Mammah”. Murmurshin ya mata shima da bata hanya alamar ta shigo. Kallo ɗaya taima Dada daya canja rigar shaddarsa zuwa baƙar t-shirt data kama jikinsa sosai ta kauda kai, duk da wandon shaddar na nan shi bai cire ba. Shi ko ko sau ɗaya baima kalla inda take ba, hankalinsa nakan waya gaba ɗaya. Ita dai tana ajiyewa ta fito abinta...
>>>>>>>%<<<<<<<
Dariya taso kufcewa Ummu, amma dai ta daure ta gimtse, sai itama ta ce, “A ina kenan?”. “Oh kema baki san da mutum ba ma ashe?”. Uncle Nasiru ya faɗa da iya gaskiyarsa. Zaram Hajiya Hasiba da ke jin kamar zuciyarta zata kama da wuta ta ce, “Aikin banza aikin wofi, to sai me daga hakan? Shi daya ajiye ki bai isa bama balle ke sha-sha-sha kawai. Kai kuma Nasiru nazo maka gargaɗine akan saƙon daka aika Ismat ta isar min, ta isar da shi dalla-dalla, sai dai ka sani idan kace zakai wannan wasan da ni zaka faɗi ne ƙasa wanwar wlhy. Ai na faɗa maka ka manta ka taɓa haihuwar wasu yara a baya ko? Idan ba haka ba kuwa zakai kuka da idanunka. Idan ba jaraba da masifa ba yara sunce uwarsu suke so amma sai bibiyar su kake yi. Ka aurar da biyu an sakani na ƙyaleka shine itama Ismat kake yaudararta kai mata yanda kai musu. Ita kuma Nabeeha ka maidata gidan waɗan can faƙirin faƙara'u ɗin da basu ajiye ba basu ba wani ajiya ba jinin talauci da gallafiri. To wlhy ahir ɗinka, aniyar moɗa tabi randa. Dan Nabeeha tabar Haysam har abada kenan, yaje ya zauna da tsintacciyar magen daya kawo. In ce dai shike nan ai ko?. Kuma......” Cikin katseta Uncle Nasiru ya girgiza kai kawai yana kallon matarsa da faɗin, “Juwairiyya kinga nikam nayi nan. Ga kiran Baffa nan na shigowa. Ai min dambu fa kar a manta, yaji gyaɗa sosai da man kyaɗa da zogale. Sannan ayi abincin dare da Haysam dan yace zai shigo, ban sani ba ko shi kaɗai ko da su Ja'afar ne”. “Ba damuwa duk za'ayi Abban Jiddah, ALLAH ya tsare ya kiyaye hanya. A gaida Hajjo da Baffan”. “Zasu ji, a gaida yara idan sun dawo, Imam ya ɗauka motar nan ya kaita service yau kar yace min ya manta”. “In sha ALLAHU”. Ummu ta faɗa tana masa murmushi. Da alama tun fara maganar tasu Hajiya Hasiba tai kamar wadda tai sumar tsaye, ganin sun manna mata hauka. Har Uncle Nasiru ya fice bata farfaɗo ba, sai da ya maida ƙofa ya rufe. Ai wata ashariya data mulmulo Ummu bata san dariya ma ta kufce mata ba, ta dai samu ta shige cikin bedroom abinta ta sake mannawa Hajiya Hasiba hauka. Ai ko ta haukace ɗin, dan zage-nage ta dinga jerawa kamar wata ƴar tasha, lamarin sam babu aji a ciki dai zattakaici. Nan kuma da za'a taɓata sai tace ita mace ce mai aji manyan mata, ke ko ta kusa da matar tsohon shugaban ƙasa ai ba'a magana. Surukar Adeel ɗan Larabawa jinin masarauta, ga kuɗi.........✍️
Gaskiya ya kamata mu fara girmama Hajiya Hasiba, ita kuma Ummu ta fita sabgar ƙawar Zainabu ehe.😜🤭🥱...