
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 69
..... my third). He didn't repeat it again, he had to turn around. "Juwairiyya, you're looking for something to talk about, are you checking the time? I told you I'm going to accompany Baffa to the wedding ceremony, and it's just a mosque. Look at the clock, what time is it now? I haven't had a shower or hair. And it's only a short walk from the city?". "I'm sorry, I'm sorry for the whole thing, since I've been up for a long time. My son or the children who are going to go to school have to go to your side." "Don't worry if I come back and say hello. She hasn't come back to the house yet?". "Well, my mind is starting to rise." "Why is there such a tension since you know where she is going? You are right to be persistent, but I know these children will never change. Their mother has already put them on a line that will be effective with them". "Pray for them, and today I will check, no matter how many times I call her phone, she doesn't answer. I will call Jiddah to come to their mother's house and check." Uncle Nasiru was just speechless, reaching for his things. She didn't talk to him again, or after that she mixed the water for him. She finished and came out again with the clothe
69
.......Duk tana aikin tattare takardun data watsar da kanta ne tana wannan tunanin, yayinda take jin idanu a kanta, idan ta saci kallonsa kuma sai taga idonsa a rufe suke shi kam. Haka ta daure da ƙyar ta kammala har gyaran gadon. Ta kalli tsintsiyin shara ta kalla inda yake, a mamakinta sai taga ya maida ƙafafunsa saman table. To kenan yana kallonta, tunda har ya fahimci yanayin ta. Nan ma sai taji ta sake daburcewa, ta dai danne da ƙyar ta fara sharar dan gara tayi-tayi tabar ɗakin nan kafin zuciyarta ta fita waje. Sauri-sauri ta kammala ta hau mopping, turaren wutar data shigo da shi na SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Ta zuba a bonner ta kunna socket. Cikin sanɗa ta nufi ƙofar zata fita a tunaninta ko yanzu barcin gaskiya yake yi, duk da tana ji a jikinta ana kallonta, amma ita shari'a ko'a gaban alƙali ai sai da hujja, a yanda yake ido a rufe ita kam bata da hujjar cewa shine kenan. “Zonan”. Cak ta tsaya tana mai runtse idanunta da ƙarfi. A zuciyarta ta furta (Na shiga uku na). Yanda bai sake maimaitawa ba, ya sata juyowa dole....
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
“Wai halan zaka je wani wajene? Naga kanata sauri Abban Jiddah”. “Juwairiyya da neman magana kike, kina duba lokaci kuwa? Nafa gaya miki zan raka Baffa ɗaurin aure, kuma da'an sakko massalaci ne dai-dai. Kalla agogo yanzu ƙarfe nawa? Gashi ko wanka banyi ba. Kuma da ƴar tafiya ba'anan cikin gari bane?”. “Yi haƙuri na shafa'a ne gaba ɗaya, tunda dana tasheka ai tun ɗazun. Dan ko yara da zasu wuce makaranta sai da sukai cigiyarka.” “Karsu damu idan na dawo ma gaisa. Ita wannan bata dawo gidan ba har yanzu?”. “Wlhy kuwa, ni hankalina yama fara tashi”. “Miye abin wani tashin hankali tunda kin san ina ta tafi. Dama kece ai kika dage, amma ni nasan yaran nan bazasu taɓa canjawa ba, uwarsu ta riga da ta ɗorasu akan wani layi da yayi tasiri a tare da su”. “Kayi musu addu'a, kuma yau zan bincika dai duk da na kira wayarta yafi sau nawa bata shiga. Zan kira Jiddah taje gidan maman nasu ta bincika.” Baki kawai Uncle Nasiru ya taɓe yana miƙewa abinsa. Itama sai bata sake masa magana ba tabi bayansa dan haɗa masa ruwan wanka. Ta kammala ta sake fitowa tattare kwanikan da yaci ɗumamen tuwon a dinning ta tadda baƙuwar bazata. Ba kowa bace face Hajiya Hasiba. Tayi wani zaman ƙasaita ɗan ƙwali agaban goshi. Duk da Ummu taji bugawar zuciya da wannan ziyara ta bazata sai ta hau ambaton ALLAH kafin ta ƙaraso falon. ALLAH ma yaso ta cikin kwalliyarta take fes Masha ALLAH. Ga ƙamshin turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Suna da turare wuta da khumra kaloli har uku: black humra, white humra, brown humra. Akwai oil perfume da kullacham da genine da Turare kabasa kaloli uku shima. white, black, and brown. Akwai man kitso, da kayan gyaran jiki masu gyara fata da sanyata laushi da santsi kiyita glowing abinki hajjaju. Na tashi, dan shine tun daga kabasa har cikin gidan dama su khumra data saka. Ba Ummu ba itama kanta Hajiya Hasiba sai da gabanta ya faɗi, dan Ummu ta fita yarinta, ga nutsuwar zaman gidan aure bashi dai-dai da mata irinsu gantalallu da ba'a nan ba'a can kullum. Shi kansa ƙamshin nan ba ƙaramin rikita mata lissafi yay ba. Ta dai daure ta haɗiye tana wani yamutse-yamutse. Murmurshi Ummu ta saki da faɗin, “Oh manyan baƙi ne damu haka a gidan? Barka da zuwa”. Wani kallon banza Hajiya Hasiba tai mata ta watsar, sai kawai Ummu tai murmurshi da komawa sabgar gabanta, dan irin mutanen nan ne ita marasa ɗaukar wulaƙanci, zata baka girma fa dan girma, dan wani lokacin ma sai ka ɗauka kamar bata san ciwon kanta ba, amma data fahimci daga wane jinsin hali ka fito tofa zata nuna maka ta fika iya kalar hali naka. Aiko bata sake bi takan Hajiya Hasiba ba ba harta kammala sabgarta. Koda ta kintaci lokacin fitowar mijinta wanka yayi sai ta koma ɗakinsa. Bata faɗa masa yayi baƙuwa ba ta hau taimaka masa ya shirya suna hirarsu cike da nishaɗi. Zuwa can sai gasu sun fito suna dariyarsu Hajiya Hasiba ta gama cika, ai ko sai dariyar tasu ta sake kunnata matuƙa. Shi Uncle Nasirun ma bai lura da ita ba sai da taja tsaki sannan ya waiwaya inda take. Nan ma ido ya ɗan zuba mata kamar wani makaho. Kafin ya juya yana kallon Ummu da faɗin, “Wai wacece haka zaune kuma Juwairiyya?”.
★✨★✨★✨★✨★
Sum-sum Nimrah ta koma kamar munafuka ta ƙaraso inda yake, cikin ƴar bada tazara a tsakaninsu ta kai zaune saman tattausan milk carpet dake gaban sofa ɗin da yake zaunen. Sai dai bata yarda ta kallesan ba dai. Shima bai gyara zamansa ba, a yanda yaken kuma a haka ya cigaba da kallonta, har ita da kanta taji kallon ya mata yawa ta ɗago a hankali ta saci kallonsa. A mamakinta yana a yanda yake idanun a rufe kamar yanda ta gani, bata san ta ƙasa-ƙasa yake kallon ba musamman saboda kansa kwance yake a jikin kujerar. Samun kanta tai da shagala a kallonsa. Kallo irin wanda bata taɓa kwatanta masa ba. To inama taga fuskar yin hakan. Dada yana da ƙyau, irin ƙyawun da aka san baƙaƙen fata ƴan ƙasar nan tamu kuma yankin mu da shi. Sosai ta fahimci kamaninsa da Ammar da Aunty Ummi, kawai dai yafi su Ammar hasken fata ne sosai, duk da suma dai sauran yana kama dasu amma yafi yi da Ammar ɗin da Mamy ɗin gaskiya. Gashi dai duk ance ya girma kowa a gidan, amma jikinsa mai ƙyau ne, dan irin ƴan gayun matasan dattijan nan ne masu matuƙar kula da jiki da son gyara.... Ta matuƙar shagala a kallonsa har bata san ya motsa ya gyara zamansa ba ma. Sai da yay gyaran murya tai firgigit ta dawo hayyacinta, sai kuma ta kama sosa wuya na borin kunya. Basarwa yay kamar bai fahimci halin da take ciki ba, sai ma tambaya daya jeho mata. “Ta ya kuka san yaron yama wata fyaɗe?”. Ɗiff ta ɗanyi na sakanni, kafin ta saki numfashi da ɗagowa tana kallonsa. Ganin ba ita yake kallo ba ta sake maida kanta tana ɗan tura baki. Sai kuma ta ce, “Dada!”. “Uhumm”. Ya amsa mata yana danna waya. “Ni da Ruky mun san abubuwa da yawa a makarantar nan kawai bama faɗa ne.” Biye mata yay ya ce, “Uhmm-umm manyan yara ne ku kenan? Ta ya kuke sani?”. Ajiyar zuciya ta sauke duk da ɓoyayyar damuwarta a kansa na nan a ranta bata gushe ba, to amma ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi ne. Dan haka ta fara jera masa zance. “Wanda ke son ƙawance da mu ne ke faɗa mana. Wani kuma mun sani ne dan muna gani. Suma fa malaman inaga dan suna jin tsoron students ƴaƴan masu ƙuɗi ne, kada a daina biyan kuɗin school fees ɗin su halan. Amma makarantar nan freedom yayi yawa, shiyyasa kaga mun zama jan wuya, dan mun gane ƙarfin, shike ƙwatarka kawai. Duk wanda ya mana sai mun masa. Shi shegen yaron nan ya jima yana abubuwa, dan dasu aka buɗe makarantar wai, gashi da ƴammata da yawa, haka zaita haɗasu faɗa wai shi namiji, ko ina mazan suke?....” Yanzu kam kaɗan ya rage dariya ta kufcema Dada ya dai daure, jifa wai ƴar yarinyar nan har ta wani san maza da wanda ba maza ba. Kai jama'a ƴar amana ta girma... Ita ko da bata san tunanin da yake ba ta cigaba da baza masa zance hankali kwance, har ma da abinda bai tambaya ba, shi ko yana recording. Tun yana basarwa har ya zuba mata idanunsa da sukai wani kalar laushi da ƙyalli-ƙyalli kamar ruwan kogi mai irin light blue ɗin nan na motsi. Kamar an kaɗa mata ƙararrawa ta farga da yanda ya zuba mata ido, sai ta tura baki cikin suɓutar baki da manta a gaban wanda take ta ce, “Dada banda kallo”. Samun kansa yay da faɗin, “Mi yasa?”. “Babu ƙyau ne ana ganin munin mutum”. A zuciya ya furta, (childish) a fili kam sai ya samu kansa da furta, “Ke mummuna ce?”. Hannu takai ta shafa fuskarta, sai kuma ta taɓe baki da girgiza kai alamar a'a. Sannan ta ce, “Hummm ai mutane suna cewa farare sunfi baƙaƙe ƙyau. Wasu fa har zagi suke da kalmar baƙar banza, ko irin dai hakan, wasu kuma da shafe-shafe ne, idan zaka bayyana tasu halittar sai ka gudu dan muni. Amma idan muna ganin ƴan comments na media a wayar Small Mom zakaga masu aibanta halittar mutane kamar ALLAH abokin wasan su ne. Ai naga shine dai yayi halittarsa, kuma mutum ko cinnaka babansa ma bazai iya yi ba balle shi. Amma jahilci da daƙiƙanci na damunsu. Idan kuma kace musu jahilai sai suce suba jahilai bane. Shifa jahilcin mai karatu yafi na jahili muni. Dan ILIMI DABAN, KARATU DABAN.” A wani kalar slowly ya lumshe idanunsa dake neman fallasa sirrin zuciya. Ya haɗiye wani busashshen yawu daya saka maƙoshinsa yin sama ya dawo da sauri. A ƙasan zuciyarsa kam ayyanawa yake (Idan na biye abar nan ba gajiya zatai da zance ba) a zahiri kam buɗe idanun yayi a kanta, tsabar rashin man kai yasa ɗiyar ga bata gane komai da yanayinsa ba, koda yake banga laifinta ba, dan fuskar dai a tsume take kamar yanda suke ganinta kullum, sannan a zaunen ma a kamenwar sa yake cike da ƙasaita, launin idanun ne kawai suka sauya kamar abinda ke cikinsu zai amayo kansa. Haka ma muryarsa ta shaƙe tamkar mai mura. Dan ko kalmar ƙarshe daya furta da ƙyar ya iya fisgota. “Kiddo tashi kije.” Dama a takure take, kawai dai surutun ne baki ya riga ya saba. Ko'a wane hali sai an furta. Yanda ta nufi ƙofa da sassarfa ya tabbatar masa dama hanyar fitar take nema. Sai kawai ya runtse idanunsa yana ambaton ALLAH dan shine kawai mafita.....
Itama data fito yanda ta sauke wata wawiyar ajiyar zuciya tana kallon ƙofar ɗakin ya saka Imran dake haurowa hannunsa da kaya tsayawa kallonta. Kusan mintuna biyu kafin ta juyo da nufin barin wajen suka haɗa idanu. Da sauri ta haɗiye yanayin nata tace, “Daddy sannu da zuwa”. Shima haɗiye nasa mamakin yayi ya amsa mata da, “Yauwa Daughter dama kina nan?”. Sai da ta ɗan tura baki gaba da shagwaɓa ta ce, “Mammah ce tace nazo nayi shara”. Murmurshi yayi da faɗin, “To ALLAH ya bada lada. Dadan naku fa?”. “Yana ciki”........✍️