
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 68
..... yes many. The name of their village, the name of her mother, her name, and a picture of her as a child, and the other picture is of her holding her bloodied body in her arms as if she were sleeping. The whole thing is a disaster, especially with the window and also some pictures and information about someone called Dagger and things related to the name of a dark group. The information was too hard for her, she couldn't understand anything, but she didn't put it down and continued to look... Suddenly, the door of the data room was opened. As she jumped and released the file, everything inside ended up scattered on the bed. He put Dada whom he did not know in the room without standing still. When they came back from the mosque, he did not sit in the living room and went up. But when he saw Ruky alone in Mammah's body, he had to ask his heart where her twin was. Nimrah, who was completely shocked to see him, suddenly saw what she saw, she started collecting the documents and pushing them into the file, she couldn't stop crying, but she was trying to wipe them away so that he wouldn't see them. The old man stared at her and started to walk in the room very stupidly that he didn't
68
.........Cikin ɗan jin takaici ta furta, “Wayyo ji salon ƙara min aiki” Ta furta a hankali, tana ƙoƙarin fara tattaresu. A bazata taci karo da hoton Umman ta da shima ya faɗo daga cikin file ɗin. Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi, ta ƙurama hoton ido zuciyarta na hanƙoro, “Miya kawo hoton Ummana wajensa?” ta sake faɗa a fili tana fara ɗaukar sauran hotunan da suka kife tana birkitosu. Hotunan farko guda uku sojoji ne bata san su waye ba, sai dai a baya an rubuta sunan (Captain Musa, Ojo.... Da sauransu) sai a hoto na huɗu Kakanta ne cikin jini ga handcuffs a hannu kamar dai a video ɗin can data gani, banbancin kawai anan hoto ne. Koda tazo hoton bayansa jitai kanta na neman tarwatsewa, nan ma hoton Ummanta ne a cikin jini Daddy Imran tallafe da kanta shi kuma Dadan na tsaye da bindiga a hannu gefe ga wani mutum kwance da bindiga shima sai dai da jini jikinsa alamar an kashe shi ne. Hawaye masu zafi ne ke kwaranya a idanunta, ta ajiye hotunan ta fara buɗe file ɗin, bayan hotunan da bayanai masu yawa. Sunan ƙauyensu, sunan mamanta, sunanta harda hotonta tana yarinya, ɗayan hoton kuma tana ɗauke a hannunsa jikinta kaca-kaca da jini kamar tana barci ne ma oho. Gaba ɗaya tai masifar birkicewa, musamman da taga har ma wasu hotuna da bayanai game da wani wai shi Dagger da abubuwan da suka shafi sunan wata ƙungiyar duhu. Bayanan sun mata tsauri da yawa, ba komai take iya ganewa ba, amma duk da haka bata ajiye ba ta cigaba da dubawa...... A bazata aka buɗe ƙofar ɗakin data sakata razana. Yanda ta zabura da sakin file ɗin, komai na ciki ya ƙarasa tarwatsewa a gadon. Ya saka Dada da bai san da ita a ɗakin ba tsayawa cak. Dan dawowarsu kenan daga massalaci shi ko zama a falon baiyi ba ya hauro sama. Koda yaga Ruky ita kaɗai a jikin Mammah sai da ya tambayi zuciyarsa ko ina twin ɗin tata, ashe tana nan ɗakinsa tana abinda bai san mizai kira shi ba. Nimrah da gaba ɗaya ta gama birkicewa da ganinsa a bazata ga abinda ta gani takardun ta fara tattarewa da hotunan tana turawa cikin file ɗin kawai, ga hawaye sun kasa tsaya mata sai dai tana ta ƙoƙarin sharesu dan kar ya gani. Dada daya zuba mata ido takowa ya fara yi cikin ɗakin sosai batare da yayi magana ba har lokacin, wanda suka zubo ƙasa ya ɗauke, ya matsa da nufin ɗauke laptop ɗinsa da take neman hayewa ta firgita. Wani irin wantsalowa tai a gadon tare da wurgar da file ɗin a saman gadon ta nufi ƙofa. Sai dai yanda ta birkice ƙofar toilet ta nufa saɓanin ta fita. Nan ɗin ma dai da kallo kawai ya bita, shi yama rasa wane tunani zai yi akan yanayin nata. Ganinsa ne? Ko kuwa abinda ke cikin file ɗin ne?... Tunaninsa ne ya katse sakamakon sake fitowa da tai a bayin alamar ta fahimci ba hanyar da take nema bace. Ta nufi ƙofar a yanzu. Sai dai anan ma ta gagara buɗewa tanata kici-kici da key kamar sabuwar marainiya. Kansa ya girgiza kaɗan, tare da ajiye hotunan hannunsa da takardu daya kwashe a ƙasa ya shiga takawa wajen ƙofar, tsayuwarsa a bayanta ya ƙara harmutsata, kici-kicin ta ya ƙaru, har tana neman buga kai da bango. Dan ta tafi gaba ɗayanta da nufin kifewa a jikin bangon ko zata samu sassaucin halin da take ciki. A hankali ya lumshe idanun da suke neman juyewa ya sake buɗesu a kanta, kafin ya kai hannunsa jikin bangon dai-dai saitin inda ya tabbatar goshinta zai sauka, dan ya tabbatar yanda ta tafi gaba ɗayanta in har goshinta ya bugu bangon nan sai ya fashe. Nimrah ma ta gama sadaƙarwa harta runtse idanunta da ƙarfi, sai taji saɓanin saukar goshinta a bango ya sauka kan tattausan abu. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ce ta kufce mata, ta sake runtse idanun da ƙarfi. Yayinda can wani gefe na zuciyarta ke faɗa mata (Nimrah relax, wai mi kike yi haka? Bai kamata ki haukata kanki ba harya fahimta, ki tuna da zantukan mutumin daya baki videos ɗin nan mana). Tasirin maganganun zuciyarta ya sakata fara sauke ajiyar zuciyar nutsuwa, ta shiga maimaita kalmar: ”لاَ إِلَهَ إِلاَّ الله“ “La ilaha illal-lah”. A hankali nutsuwa ta fara riskarta, numfashinta ya daidaita, ta haɗiye hawayenta tare da kai hannu ta share wanda suka jiƙa mata fuska. Jinta a takure tamkar an mata rumfa ya sata jan jikinta baya a hankali tana ɗagowa, abinda ya bama goshinta kariya ta fara kalla, zuciyarta ta harba da ƙarfi ganin hannun Dada, gashi kamar ta jingina da abu ta bayanta kuma, ai bama ta san sanda ta juyo da sauri ba, sai da kanta ya bugi ƙirjinsa kuwa saboda a yanda yake tsaye. Ta waro idanu sosai tana mannewa da bango, tare da duƙar da kanta tana ambaton ALLAH a zuciyarta. Duk abinda take Dada bai motsa ba daga yanda yake tsayen tamkar ya mata runfa ma, ga hannunsa har yanzu yana a bangon bai cire ba. Sai dai ya zuba mata idanunsa masu kaifi. Kusan mintuna biyu suna a haka, Nimrah ji take kamar ta saki fitsari, dan yanda yake ɗin, gasu gab da juna, fuska a haɗe sai kace yana filin yaƙi. Rasa abin yi ya sata buɗe baki a karo na farko ta furta, “Dan ALLAH Dada kayi haƙuri”. Bashi da alamar zai tanka mata har shuɗewar wasu sakanni, kafin a bazata ya jefa mata tambayar data sakata ɗagowa ta kallesa da manyan idanunta da sukai ja saboda kukan da tayi da halin da take ciki, duk da tana ƙoƙarin shanyewa. “Kinyi laifi ne?”. Maimakon samun salama da kalmomin nasa guda uku ita wlhy sake hargitsata sukai. Sai kawai ta hau jinjina kai, kamar kuma wadda ta fahimci mi tayi, sai ta girgiza alamar a'a. “Uhhm! Mi kike yi anan?”. “Mammah!... Mammah ce tace nazo nayi maka gyara”. Tai maganar idanunta na sake cikowa da hawaye, dan a yanda suke tsayen ta takura, da ace wani ne ba shiba da tuni ta hankaɗe shi ta wuce, kota kirashi da ɗan iska, ƙilama ta ƙara da zagin tsamar nama. Amma ina, shi wargi ma waje yake samu. Sannan ko kura tasan gidan mai babbar sanda.... “An saki aiki, amma kina min bincike?”. Ba ƙaramin dukan ranta furucin nasa yayi ba yanzu ma. Sai kawai ta fashe masa da kuka da faɗin, “ALLAH Dada ni banyi maka binciken komai ba. A gadon fa na gansu zan ɗauke suka faɗi, shine nake kwashe wa”. “Hy Kiddo! Nayi ƙarya kenan?”. Nan ma kai ta shiga girgiza masa tana tura baki. Ga hawaye share-share da ke neman sakashi murmurshi yana dannewa da ƙyar. Handkachiff ya fiddo ya miƙa mata, ɗagowa tai ta kallesa da yanayin kamar mai mamaki. “Na maida abuna ne?”. Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa. Sai ta samu kanta da tura baki, caraf kuma ta riƙo handkachiff ɗin da yake ƙoƙarin maidawa aljihu. Ƙin sakar mata yayi, cikin sake ƙasa da murya ya furta, “Ai na fasa, dama aro ne”. Cikin shagwaɓa tana sake sakar masa hawayen da take maƙalewa ta ce, “Dan ALLAH”. Lips ɗin data tura ga hawaye na shatata ya zubama idanunsa da sukai matuƙar shigewa ciki, ga launinsu ya canja matuƙa. A bazata taji saukar yatsansa a tsinin hancinta ya ɗan ɗalle shi. Daburcewa ta nema yi, shi ko ya sake tsuke fuska yana wara mata idanunsa da faɗin, “Ni kike ma wannan shagwaɓan?”. Itama sai ta waro masa nata idanun da faɗin, “Da... dahh!”. “Uhumm Kid.... doo”. Ya amsa mata da yanayin da tayi kiran sunansa. Ai da gudu kawai ta saki masa handkachiff ɗinsa ta juya baya ƙirjinta na wani irin motsi, dan gaba ɗaya ya juye mata kamar ba Dadan ba. Sai ta dinga jin ma anya ba mafarki take ba. Shi ma bai sake ce mata komai ba ya janye jikinsa a wajen. Sai ko data saki wata wawiyar ajiyar zuciyar data saka ɗan mitsilin murmushi kufce masa. ALLAH ya so shi ma ya riga ya juya ne bata gani ba, duk da koda kallonsa take ba lallai ma ta fahimci yayin ba. Sai da ya zauna akan sofa yana ciro wayarsa a aljihu, kallonta ya ɗanyi, tana a inda ya bartan tana faman cuɗa yatsu cikin juna, ya fara karantar wannan dabi'a tata ta cuɗa yatsu da har in tanayi akwai abinda ke damunta ko bata jin kanta free a inda take. “Zo ki ƙarasa aikin ki”. Ya faɗa yana cire hular kansa da kwantar da bayansa da kan jikin kujerar ya lumshe idanunsa kawai. Simi-simi Nimrah ta tako bayan ta saci kallonsa, a yanayin da take ciki da ace ba shi bane ALLAH bazata iya ƙarasa aikin nan ba, dan kaɗaici tafi buƙata a yanzu. Tunanin take son yi, so take tai nazari akan abubuwa masu yawa. Tana ganin a yau kuma dole ta yi ƙoƙarin kiran mutumin nan, amma sai ta duba saƙon ƙarshen nan daya bata a randa sukai haɗuwar farko kuma ta ƙarshe da shi kafin taga idan ya dace suyi wayar. Tambayoyi take son yi masa, wanda da ace zata iya Dadan zata yima su, sai dai yi masan tamkar ganganci ne. To taya zata bama kura ajiyar nama, daga shi har Daddy Imran a yanzu zuciyarta rawa take a kansu. Idan ba rami miya kawo rami to?...........✍️