
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 41
.....with full security we will take her out completely." Imran raised his head and stared at him with his eyes that were turned into jade. He directly said, "Is that outside?" "Sure sir! We should go to a special hospital outside. One to two month stay. If this is done as soon as possible, we will keep his life in perfect health." Imran didn't say anything, he stood up slowly, but the weight of what he was feeling couldn't be hidden on his face and his body energy. The son turned and looked at the Doctor, full of warning and said, "No one will know this after the three of us." Dr. Idris nodded respectfully. "We have already taken the oath of secrecy, sir." Imran turned to Faro, their eyes met in the same place. "I will inform the president now." Faro smiled and shook his head, except for the smile that hides anger. "Let him know. But tell him one truth: Zak-Shadow did not come out of prison to die in the hospital." Imran shook his head and picked up his phone, he started walking and stopped at the door of the room, he said briefly, "I will not die if I drink ALLAH." after that he left and left Faro and Doctor Idris to continue talking. Dada, who didn't know, he heard what he didn'
41
........Da ƙyar Daddy Imran ya iya fisgo kalma ɗaya wajen furta, “Wace irin guba ce?”. “Slow-acting toxin. An tsara ta ne don ta lalata jiki a hankali ba kashewa nan take ba. Hakan na nuna wanda ya aikata ya so yaga yana rayuwa cikin rauni ne.” Shiru ɗakin yay dan kowa da kalar da raɗaɗin da zuciyarsa ke masa akan jin wannan baƙon al'amari mai rikita lissafi. Suna cikin farin cikin babu wani damuwa a tare da Dada a kwaje-kwajen farko, ashe tashin hankalin na gaba. Da ƙyar Faro ya yanke shirun nasu. “Doctor yanzu minene mafita? Tana da makari ne?”. Doctor ya ɗan gyaɗa kansa. “Tabbas za'a iya samun makarinta, abin da ya rage mana shi ne inda zamu same sa, musamman a ƙasar nan tamu kuma da bana jin zamu samu ɗin kai tsaye, idan ma mun samu hankalinmu bazai kwanta ba ga duk wanda zai bamun. Dan duk wanda ya samar da gubar dama dole shine mai makarinta. A yanzu kuma mu kowa ba abin yarda bane a wajenmu. Musamman tunda bamu san wanda ya aikata masa haka ba. Sai dai mubi wata hanyar sirri da cikakken tsaron da zamu fitar da ita gaba ɗaya.” Imran ya ɗago kansa ya zuba masa idanunsa da suka juye jazur. Kai tsaye ya furta, “Waje ke nan?” “Tabbad Sir! Asibiti na musamman a waje ya kamata mu kaishi. Zaman wata ɗaya zuwa biyu. Idan aka yi hakan da wuri zamu tsare rayuwarsa da cikakkiyar lafiya.” Komai Imran bai sake cewa ba, sai ma ya tashi tsaye a hankali, sai dai nauyin abin da yake ji ya kasa ɓoyuwa akan fuskarsa da kuzarin jikinsa. Ɗan juyowa yay ya kalla Doctor ɗin, cike da gargaɗi ya furta, “Babu wanda zai san wannan bayan mu ukun nan.” Dr. Idris ya gyaɗa kai da girmamawa. “Mun riga mun ɗauki rantsuwar sirri ai Sir.” Imran ya juyo ga Faro, idanuwansu suka haɗu a waje guda. “Zan sanar da shugaban ƙasa yanzu.” Faro ya ɗan murmusa da gyaɗa kansa, sai dai murmushin da ke ɓoye fushi. “Ka sanar da shi. Amma ka faɗa masa gaskiya ɗaya: Zak-Shadow bai fito daga prison don ya mutu a asibiti ba.” Imran ya gyaɗa kansa yana ɗaukar wayarsa, harya fara tafiya ya tsaya a ƙofar ɗakin, a taƙaice ya furta “Ba zai mutu ba in sha ALLAHU.” daga haka ya fice ya bar Faro da Doctor Idris na cigaba da tattaunawa.
Dada da basu san duk ya gama jin abinda basa son yajin ba ya bar jikin ƙofar yana murmurshi. Drip da ake faman saka masa a kwanakin nan dama doctor ɗin ya saka masa bayan sallar isha'i, shine ya saka shi barci har su Imran ɗin suka shigo gidan bai sani ba. Yanzu ma ya farka ne sai yaga ruwan ya ƙare ya cire da kansa, ruwa da yake buƙata na sha daya duba babu a ɗakin ya saka shi ƙoƙarin fitowa duba Dr Idris ɗin, dan koda yaushe Doctor na tare da shi a gidan. Barin wajen yay ya koma ya zauna a bakin gado. A zuciyarsa yana faman maimaita kalmar poising ɗin, sai dai fuskarsa da murmurshi, dan ya jima da fahimtar hakan a tare da shi, musamman a watannin nan da suka gabata. Har ma yana tunanin yaushe hakan ta faru? Tun yana a prison ɗin, dolene a ɗayan biyu gubar ta shigesa. Mafi ƙarfi a zuciyarsa shine television da aka kawo ɗakinsa watannin da suka wuce, ko kuma ta hanyar securitys ɗinsa......
%★%★%★%★%
A ɓangaren su Hajiya Hasiba kam abinda suka jiyo ga bokan Mamawo ya matukar rikitasu, amma sai Hajiya Hasiba tace ita dai su sake zuwa wajen wani mana. Ko suje India ɗin kona kwana biyu ne. Mamawo ta yarda da shawarar, amma tace su fara fuskantar Adeel. Itama Hajiya Hasiba bata musa batun ba, sai dai sun nema ganin Adeel ɗin shi kuma ya toshe hakan. Dan yama ɓoyema ganinsu gaba ɗaya dan haka dole sukai hakuri dan zuciyarsu na kitsa musu ko wani abu yake shiryawa. Ga First lady ta takurama Hajiya Hasiba akan harkokin bikin ƴarta, dole ta haƙura da batun India ɗin ta maida hankali a kanta. Har takai ma bata fahimci Ismat bata gida ba sai bayan kwana biyu. Sai dai tana taɓota tace tana gidan Aunty Jiddah zatai kwana biyu sai ta saki batun ta. Dan bata kawo a ranta wani abu Ismat ɗin ke shiryawa na komawa gidan babansu ba. Shiru kaɗan ya biyo baya Imran ya gagara magana saboda abinda ya toshe masa maƙoshi. Shima sai Shugaban ƙasa bai iya yace komai ba yana dai saurarensa cikin shiru, irin shiru na masu fahimtar juna ba tare da doguwar magana ba. Tsohon minti guda Janar ya katse shi da faɗin, “Ka samu abin da ka je nema ne Imran?” Imran ya sauke numfashi karo na farko a hankali. Muryarsa da ɗaci ya furta, “Eh, ranka ya daɗe. Amma abin ya fi yadda muke zato nauyi.” “Faɗa min kawai”. “Akwai guba a jikinsa. Ba ta gaggawa ba, amma an tsara ta ne don ta lalata shi a hankali. Likitoci sun tabbatar da cewa a nan ba za a iya magance ta gaba ɗaya ba, koda akwai makarinta zai iya kasancewa a hannun wanda sukai aikin yake ko suna da alaƙa da wanda suka yin, dan dole mai makarin shike da gubar. Fitar mu nemata zai basu ƙofar sanin sirrinmu”. Shiru ne ya sake biyo bayan bayanin Imran ɗin. Dan Janar ya kasa koda motsin kirki tsabar yanda zancen ya buge shi shima. Imran ya san wannan shirun na Janar shiru ne na mutum da ke ƙoƙarin riƙe fushinsa shima, dan dole Janar zai ji kamar yanda suka ji a lokacin da Doctor ke sanar musu. “A wajen akwai maganin? ta hanyar da muke buƙata?”. Janar ya faɗa cikin wata irin murya mai bayyana ɗaci da zafi. Amsa Imran ya bashi, “Akwai, ranka ya daɗe. Amma zai iya ɗaukar wata ɗaya zuwa biyu inji Doctor.” Muryar Janar ta sauya kaɗan zuwa matsayin shugaban ƙasa, cikin nauyin umarni ya furta. “Amincewar UBANGIJI kawai muke nema. Amma babu wanda zai ji wannan har Haysam.” “Mun riga mun kulle komai Sir.” “Zan zo yanzu. Ina son na gansa.” Imran bai yi mamaki ba, dan haka kai tsaye ya ce. “Muna maraba da zuwanka ranka ya daɗe.” “Uhhm”. Janar ya faɗa yana yanke kiran.........✍️