Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 42

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 42

.....Ledar, the manager turned his attention to the place. Just like that, Lolo took out the books in the bookcase. Now you are laughing and Fedo, Ruky, Bintu took him away. While Nimrah remained neutral. Aunty Asma'u asked them who brought it? The news of Feedo and Mu'azz was lost, even Mu'azz all listened to them, but surprisingly all their faces changed, the son of Khalifa said, "We are going to eat the mother of this guy, our younger brother who was sent to school is the one who is chasing them with love? His father's son is married and he is going to marry them?". The Imam said in sadness, "We have to go to the school and warn him, this is foolish". Mu'azz was the same and he couldn't help but praise the garden too. The Khalifa and the Imam were behind him. Then the game broke up. Ammie, who was in the living room, saw them coming in one by one. She did not say anything to them, she was on the phone with Daddy Imran.... The next morning, from Nimrah to her friends, no one followed the subject of Sayyadi Kamal's books like that time when they even left them at Aunty Mimi's house. As soon as they got up, they congratulated the workers for fixing the house and preparing breakfast

Standalone post2,236 words

........Bayan la'asar su Nimrah suna a garden suna basket ball su duka huɗu sai Yaya Khalifa, Yaya Mu'azz da Yaya Imam da suka zo gidan babu jimawa, sai Auta Lolo. An raba team ɗin biyu, amma Nimrah da Ruky sunƙi yarda a rabasu, dan haka sai ƙwange sukema su Mu'azz da rinto. A yanzu ma ana tsaka da gardama Nimrah da Ruky sun dage kuma akan rinto ne Khalifa ya hararesu da faɗin, “Kufa matsalar ku rinton jaraba, shiyyasa sam bana son haɗa sabga da Ninah da Ruky munafukan yara ne ALLAH”. “Ashe ka gane Broth, wlhy haka suke”. Cewar Mu'azz shima yana hararsu. Baki Ruky da Nimrah suka taɓe, Nimrah zatai magana sallamar maigadi ta dakatar da su. Imam ne ya amsa masa duk suka juyawa suna kallonsa. Kai tsaye inda Nimrah take ya isa, ya miƙa mata ƙaramar ledar hannunsa yana faɗin, “Saƙo ne wani ya kawo wai a baki. Yace malamin ku ne na islamiyya Kamal”. Tsit wajen yay ana kallan kallo, sai Bintu ce da tai dariya da faɗin, “Humm guy ɗin nan fa ya dage wlhy”. Kafin wani ya bata amsa Lolo ya amshi ledar, maigadi ya juya abinda yabar wajen. Dai-dai Lolo na fiddo littatafan cikin ledar. Yanzu kam dariya Feedo, Ruky, Bintu suka kwashe da shi. Yayinda Nimrah taja tsaki. Aunty Asma'u kuma ta tambayesu waye ya kawo?. Labari su Feedo suka bata, har su Mu'azz duk na saurarensu, sai dai abin mamaki duk fuskokinsu sun canja, dan cikin faɗa Khalifa ya ce, “Zamu ci uwar guy ɗin nan kuwa, ƙannenmu da aka tura makaranta ne abin bibiyarsu da soyayya? Dan ubansa aure akace za'ai musu?”. Cikin ɓacin rai Imam ya ce, “Dolene muje har makaranta muja masa gargaɗi kam, wannan ai rashin hankali ne”. Mu'azz kam daya kume bai iya ya tanka ba, dan fuuu yabar garden ɗin ma. Khalifa da Imam suka take masa baya. Daga haka wasan ya watse. Ammie dake falo sai ganinsu tai suna shigowa ɗai-ɗai. Bata ce da su komai ba dan tana waya da Daddy Imran ne....

Washe gari daga Nimrah har ƙawayenta babu wanda ya sake bin batun litattafan Sayyadi Kamal kamar wancan karo da suka ma barsu a gidan Aunty Mimi. Dan tunda suka tashi ma suka taya masu aiki gyaran gidan da haɗa breakfast. Bayan sun karya kuma sukai shiri wucewa gidan Baffa dan Hajiyar Daddy Imran ta dawo daga ƙauye jiya da yamma. Tunda Aunty Asma'u ta sanar musu sukace yau can zasu yini. Duk da Ammie na son su zauna babu yanda ta iya. Dole ta haɗa lafiyyayen farfesu da kunun aya da kunun gyaɗa tace su kaima Baffah da Hajiyar (Iyayen Imran kenan). Nimrah ce ƙarshen fitowa a ɗakin. Ta kammala rolling veil ɗin abayarta kalar maroon da adon milk da taji stone tana maida kayan kwalliyarsu a make-up kit ɗinsu idanunta suka sauka akan books ɗin Sayyidi Kamal dake zube a side drawer inda tun jiya Bintu ta zube su. Samun kanta tai da ƙarasawa inda suke ta ɗaukesu su duka uku yau dai tana kallo. Zuuu taɗan buɗesu a tare, sai ga wata ƴar ƙaramar takarda ta faɗo a ɗaya daga cikinsu. Takardar tabi da kallo, ganin rubutun jikinta ta kai duƙe ta ɗauka. _Ba litattafan bane muhimmanci a gareki yau kamar saƙon farko, ainahin saƙon yana a littafi mai jan bango shafi na hamsin da uku da shafi na tamanin, ki tabbatar ke kaɗai kikaga abinda ke ciki batare da kowa ba har aminiyarki, saboda muhimmancin abinda ke ciki da zai amfaneki ke kaɗai. Idan kuma kika bari wani ya gani bayan ke to tabbas zai mutu._ Takardar ta ɗan jujjuya cike da mamaki zuciyarta na wani kalar bugawa da sauri-sauri saboda kalaman ƙarshe, dai-dai nan akai knocking ƙofar ana kiran sunanta. Dan haka ta maida takardar kawai cikin littafin farko tana amsawa da haɗiye abinda ke shirin hargitsa mata brain, sai kuma ta buɗe handbag ɗinta ta saka duka books ɗin a ciki dan basu da wani girma sosai. Haka ta fito zuciyarta na kai-kawo akan abinda ta karanta. Amma da yake tana da wayo sai ta danne ta yanda kowa bazai fahimta ba. Received at 2:38 Yau kam Yaya Khalifa ne ya kwashe su zuwa can gidan Baffan. Cike da farin ciki suka zagaye nutsatstsiyar tsohuwar mai cike da kwarjinin ibada da lafiyar data haɗu da jin daɗin rayuwa. Hajjo tsohuwa mai ran ƙarfe kenan, mahaifiya gasu Imran da a yanzu ta zama uwa harga su Mammah, sannan kaka gasu Nimrah. Dan dattakonta yasa itama bata san raba ɗaya biyu ba, ta zama ginshiƙin dunƙule familyn nan uku da basu da alaƙar jini a yanzu sunfi ma waɗanda keda alaƙar jinin gina ƙyaƙyƙyawan zuminci... “Oh ni Bilkisu, yaran nan ina zakuje da girman jiki? Ba'a kauda uwarku Biebah ba balle yayunku amma neman dannesu kuke da girman jikin ku, anya bazance a haɗeku rana ɗaya da Habibah da su Asma'u ba”. A tare suka gwalalo mata idanu, cike da shagwaɓa har suna haɗa baki wajen faɗin a'a gaskiya su auren su sai sannan da shekara goma. “Shekara goma? Kuji min shaƙiyan yara, sannan kuma in sha ALLAHU ai sai dai lissafin auren ƴaƴanku. Ni yanzu kunga tunda gaku ku duka huɗun yau ba lalaci da surutu zaku yimin ba. Tashi zakuyi kumin kwalemar ɗaki a fitar da komai a canja min jere na, dama su Asma'u zance suzo suyi, amma tunda gaku shike nan sun huta”. A tare suka amsa mata da to. Sai kuma Nimrah da duk bata da kuzari ta ce, “Granny ina Baffa wai?”. “Naja'atu sun fita shi da baban ku Ammar, dan kamar ma suna can gidan kakanku Nasiru. Amma nasan anjima kaɗan zasu dawo”. Kai Nimrah ta jinjina, har sun miƙe Hajjo dake binta da kallo ta kira sunanta, juyowa tai, sai kuma ta tako inda Hajjon take. Sai da ta kama hannunta ta zaunar kusa da ita sannan taima su Fiddo da suka tsaya suna kallonsu alamar suje su. Basuyi musu ba suka wuce hanyar bedroom ɗinta. Ita kuma ta maida hankalinta ga Nimrah. “Naja'atu mike damun ki? Ko baki da lafiya ne?”. Sai da gaban Nimrah ya faɗi, dan bata taɓa zaton wani zai gane halin da take ciki ba. Amma sai tai ma Hajjo murmushi da girgiza kanta. “Ba komai Granny, mi kika gani?”. Hajjo dake kallonta cike da nazari ta ce, “Ban yarda ba Naja'atu, nafa san halin kowa a cikinku, ko yaya kuka canja kuma ina ganewa.” Har Nimrah ta buɗe baki zatai mata bayanin abinda ta gani a takardar nan sai kuma ta tuna kalaman ƙarshe na cewar duk wanda ta bari ya sani zai mutu, da sauri ta canja zancen tana kwantar da kanta jikin Hajjo ɗin. “Granny da gaske ba komai. Kawai dai yau na tashi ne duk zuciyata wani iri ba daɗi, kuma gabana nata faɗuwa”. Ajiyar zuciya Hajjo ta saki a hankali, sai kuma ta shafa kan Nimrah ɗin cike da lallashi da so da ƙauna ta ce, “Ki yawaita ambaton Hasbunalahu wani'imal wakil da talatin ANNABI kinji. In sha ALLAHU babu abinda zai faru sai alkairi. Barsu ma suyi aikin muyi hirar mu”. “Granny zan taya su ina son nima nayi. Amma kin zo mana da farar mu?”. “Buhu guda ma kuwa, tana nan a store dama in baku zo yau ba zan bayar a kai muku, damma na manta ne da A'isha tazo ɗazun ita da Bilalu ban basu ba”. Farin ciki sosai ya bayyana a fuskar Nimrah, sai kawai ta nufi ɗakin Hajjo tana ƙwalama su Ruky kira. Da kallo Hajjo ta bita tana murmushi, dan har cikin ranta take ƙauna da tausayin Nimrah.......

<•><•><•><•><•><•><•>

★ SECRET MEDICAL BASE ★

Yanda Imran yake a ruɗe ko damuwa da kallon lokaci baiyi ba ya dannama shugaban ƙasa kira. Cikin sa'a kuwa ba a jima ba aka amsa. Sai da ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi kafin yay sallama. Daga can shugaban ƙasa da alamu ya nuna barci yake ya amsa, duk da dai a cikin murya mai nutsuwa ne. “Imran.” “Ranka ya daɗe ka gafarce ni na tashe ka a barci bazan iya haƙuri bane shiyyasa ko lokaci ban damu da dubawa ba na kira ka.” “Karka damu Imran nima barcin ya ɗauke ni ne kawai batare da na shirya masa ba. Nima ina son kiran naka a daren nan ai. Amma minene ya tada maka hankali haka?”. Dada bai nuna mamaki ba, sai ma murmurshi da ya saki da ɗan taɓe baki kaɗan ya ce, “Na fahimta tun kafin likitoci su faɗa.” Shugaban ƙasa ya ɗan zuba masa ido da jinjina baiwar da ALLAH yay masa, irin su Haysam wata ajiyar ALLAH ce a cikin al'umma da sai mai hankali ke fahimta, kaɗan ya ɗan murmusa shima cikin baƙin ciki da ɗacin murya ya furta. “Har yanzu kai ne Zak-Shadow ɗin da na sani Haysam. ALLAH ya cigaba da ɗaga darajarka da baka kariya, UBANGIJI ya cigaba da ɗora nasararka akan maƙiyanka?”. Ya ɗan yi shiru na sakan biyu har Dada ya samu damar motsa lips ɗinsa kaɗan wajen amsawa da amin. “Ba zan iya barinka a nan ba. Za ka tafi waje. A ɓoye. Ba suna, ba matsayi, ba labari kamar yanda muka fara ka ƙarasa jiyyarka a can”. Dada ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya furta, “Zan je. Amma ba dan tsirana kawai ba. Sai dai ina kewar Mammah da son ganin su”. “Na sani Haysam. Amma kayi haƙuri bana son kowa naka ya ganka a cikin wannan halin, in sha ALLAHU wata biyu tamkar gobe ne indai da rayuwa. Mammanka zatafi farin ciki da son ganin Haysam. Saɓanin hakan raunana mata zuciya zaiyi daga ita har ƴan uwanka. Ka duba halin da Imran ke ciki a yanzu haka kawai ya isa misali”. Cike da gamsuwa Dada ya jinjinama shugaban ƙasa kai. Kafin cikin ɗan furzar da iska ya furta, “Zan dawo in sha ALLAHU. Ba a matsayin wanda aka yima afuwa kawai ba. A matsayin wanda ya dawo ya gyara abin da ya samu karaya daga BURINSA.” Da ƙarfi Shugaban ƙasa ya sauke ajiyar zuciya yana miƙa masa hannu. Kama hannun nasa Dada yayi sukai musabaha irin ta amintattun sojoji masu kishin ƙasa da tsayayyar zuciya, musabaha ta tarihi, ta alƙawari da cikakkaiyar JARUMTA. Janar dake murmurshi ya furta, “Ina ji a jikina Haysam, da izinin UBANGIJI a ranar da ka dawo ƙasar nan zata fara canjawa da canji irin na masu son a shinfiɗa gaskiya. Da taku irin na masu girgiza zukatan ɓoyayyun munafukai. Daren gobe in sha ALLAHU zaku wuce”. “ALLAH ya kaimu”. Dada ya faɗa......

=================

Ranar Lahadi su Nimrah suka dawo gida da yamma. A kuma ranar Daddy Imran da tunda suka je gidan bai kwana ba dan Ammie ta faɗa musu yana wajen aiki yazo gidan da safe, sun nuna farin cikin ganinsa shima kuma yaji daɗin ganinsu. Dan haka suka zagayeshi da uban surutunsu yana biye musu. A ƙasan ransa kam ji yake badan yau ne tafiyar nan tasu ba daya shiryata da Nimrah a ciki. Amma lokaci ya riga ya ƙure, dan yau ne jirginsu zai tashi ƙarfe goma na dare shi da Haysam. Tunanin ya ture gefe ya cigaba da biye musu, dan sunata masa shagwaɓa wai zasuyi missing ɗinsa saboda ya sanar musu zai yi tafiya, kuma zai jima dan wata ɗaya zai yi ko sama da haka. Da yammar ma da kyar suka yarda suka bi Yaya Khalifa da zai maidasu gida. Shi Daddy Imran yace sai anyi isha'i zai shigo yayi ma Mammah sallama...

Da yamma Mu'azz yazo ɗaukar su shima, sai kawai Khalifa yay zamansa dan dama yana da uzirin aikin makaranta. Ammie ta haɗa musu kayan kwalliya da kayan ƙamshi na musamman na turarrukan SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Suna da turare wuta da khumra kaloli har uku: black humra, white humra, brown humra. Akwai oil perfume da kullacham da genine da Turare kabasa kaloli uku shima. white, black, and brown. Akwai man kitso, da kayan gyaran jiki masu gyara fata da sanyata laushi da santsi kiyita glowing abinki hajjaju. Duk da kuwa Aunty Biebah ta saya musu kwanaki. Yanzu ɗin ma harda na Biebah Ammie ta bada, sannan taima Mammah gasashen nama mai ɗan karen daɗi itama a kai mata. Suka wuce Asma'u na musu tsiyar yau zatai barci mai daɗi. Lolo kuwa yana islamiyya ma suka wuce da ansha rigima duk da shima fa ya zama ɗan saurayi tunda 2years kawai Rukyn ta bashi. Gasu yanzu suna shekara sha biyar da watanni. Sai da suka fara sauke Fedoo a gidansu, sannan Bintu. Dan gobe in sha ALLAHU Monday ba batun tafiya gidan Mammah a cigaba da shargalle. Su kuma su biyu Mu'azz ya wuce da su gida cike da jin kewar ƴan uwansu da aka rabu. Duk abinda suke Ammie na jinsu, itama kuma hirar tasu ta fara kai hankalinta akan al'amarin Asma'u ɗin da Bilal, dan kwan biyun nan ta fahimci ko yaushe Asma'u na maƙale da waya, idan ta tambayeta sai tace wai assignment take yi. Ashe ita ta maida assignment ɗin. Kai yaran yanzu sai a barsu dai kawai. Tai murmushi mai yalwa, dan har cikin ranta wannan haɗin ya mata. Wlhy idan duk ƴaƴan data haifa zasu kasance matane ace yaran gidan Mammah suka auresu zatafi kowa farin ciki, dan jinin Mammah jinin alkairi ne. Abotar Imran da Haysam babban rahama ce kuma alkairi ga zuri'arsu guda biyu. Addu'ar fatan alkaici tayi ta cigaba da sabgarta.........✍️