
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 43
..... His servant turned and went out to the hall and motioned for them to sit down as well. My uncles greeted me respectfully, then sat down to greet him. He could only answer them with his head. After that, silence followed for a few seconds, no one spoke, everyone had what was on their mind. The general interrupted their silence by saying, "Where is he?". Faro showed him the door of the room where Dada was. "Your soul has been sleeping inside for a long time". "Let's go and see him". He said as he stood up. They also all straightened up. Imran is in the front, General is in the middle and the beginning is the end. To their astonishment, when they entered with greetings, they found Dada sitting and leaning on the bed with his eyes closed. After a while, Imran and Faro reached out to him to the point that they were conspiring to ask, "Are you up?". He slowly opened his eyes and looked down on them. Then he bowed his head and looked back at the General. As the General looked at him without even blinking, Dada let out a small smile for the first time, then he started trying to remove the blanket he was wearing in his calmness. For the first time, the president came to the front of t
43
........Shima Imran lumshe idanu kawai yayi a wajen yana jingina da kujera. Ya san wannan ganawa ba ta siyasa ba ce, ganawa ce ta gaskiya, ta amana, ta zumunci, ta yarda da bashi na tarihi. Ciki ya koma ya sanar ma Faro, dan haka suka nufi ɗakin da Dada yake duk da su a zatonsu har yanzu barci yake.....
★2:42am★
Shugaban ƙasa Yusuf Shu'aibu Tafida suka iso cikin base ɗin. Fita ce ta sirri dan a cikin ɓadda kama ma yake. Dan haka daga shi sai dogarinsa ne a motar. Su Imran dake faman zaman jiran tsammani na zaune a falo dan tunda suka leƙa ɗakin Dada suka samu yana barci har lokacin basu zauna ba suka sake dawowa falon. Sai dai abinda basu sani ba likimo Dadan yay musu yana jin motsin shigiwarsu a lokacin, baya son su san yasan abinda suke ɓoyewar, dan haka yay likimo ɗin. Shigiwar Shugaban ƙasa Yusuf Shu’aibu Tafida ba tare da hayaniya ba ya sakasu miƙewa tsaye a tare. Basuyi mamakin ganinsa a shigar ɓadda kamar ba, kuma ba tare da yan rakiya ba sai dogarinsa kaɗai. Sai da ya zauna, dogarin nasa ya juya ya fita a falon sannan yay musu nunin su zauna suma. Kawuna suka jinjina cikin girmamawa, sannan suka zauna suna gaishe shi. Da kai kawai ya iya amsa musu. Daga haka shiru ya biyo baya na tsawon sakanni kaɗan, babu wanda ya yi magana kowa da abinda ke a ransa.. Janar ne ya katse shirun nasu da faɗin, “Yana ina?”. Ƙofar ɗakin da Dada yake Faro ya nuna masa. “Ranka ya daɗe yana ciki yana barci”. “Muje in gansa”. Ya faɗa yana miƙewa. Suma duk miƙewar sukai. Imran a gaba Janar a tsakkiya sai faro ƙarshe. A mamakinsu suna shiga da sallama suka samu Dada a zaune ya jingina da gadon idanunsa a lumshe. Da ɗan sassarfa Imran da Faro suka ƙarasa garesa har suna haɗa baki wajen tambayar, “Ka tashi?”. Idanun sa dake lumshe ya buɗe a hankali ya sauke a kansu. Sai kuma ya jinjina kansa yana maida dubansa kan Janar. Yanda Janar ɗin ke kallonsa ko ƙyaftawa babu ya saka Dada sakin ƙaramin murmushi a karo na farko, sai kuma ya fara ƙoƙarin yaye blanket ɗin da yake ciki cikin nutsuwar sa. Karo na farko shugaban ƙasa ya matso gaban gafon, tsayawa yay a gabansa sosai yana mai dafe hannunsa da girgiza kai alamar kar ya sauka. Nan ma murmurshi ƙarami Dada yayi. Sai kawai Imran ya gyarama janar kujera a gaban gadon suka fice shi da Faro a ɗakin tare da rufe musu ƙofa...
Janar yakai zaune, har lokacin hannunsa na riƙe dana Dada tamkar mai gudun ya ɓace masa, murya ƙasa amma da nauyin fitar sauti ya furta, “Na yi maka laifi. Haysam”. Dada ya ɗan murmusa, murmurshi irin na dattako da kamewar nutsuwa, sai kwarjininsa ya sake bayyana da cikar kamala. Kaɗan ya motsa lips ɗinsa ya furta, “Ranka ya daɗe, bazaka taɓa zama mai laifi ba a wajena. Duk abinda ka gani a rayuwar bawa ƙaddararsa ce, sai dai idan tazo a mummunar ƙaddarar saɓama UBANGIJI wannan kam daga mu ne da jagorancin shaiɗan. Ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya, ina kuma tayaka murnar tare da addu'ar baka ikon sauke nauyi da haƙƙokin al'umma. ALLAH yasa baka cikin shugabannin da zasuyi dana sanin samuwar mulki a garesu a ranar rarrabe ayyuka”. “Amin ya rabbi Haysam na gode sosai. Sai dai ka sani shi gudanar da wannan mulkin namu ne a tare, dan kana da muhimmanci a cikinsa wajen sauke nauyin haƙƙin al'ummar ƙasar nan. Shiyyasa nake jin kaicon kaina na kasa kare ka da nayi a shekarun baya.” Dada ya sauke numfashi, kafin cikin nutsuwa irin tasa ya furta, “ALLAH ya fi kowa iko. Shi ne Alƙali mafi adalci. Wannan rubutacciyar ƙaddara ce tun daga alkalamin farko. Sir ka daina damun kanka” Kai Janar ya jinjina yana sauke numfashi mai nauyi, tabbas ya yarda ilimin addini duniya ne, wanda ya samu wannan ilimin yay kuma aiki da shi ya more, dan kasancewar Haysam a yau ya tabbatar masa da hakan. Sake duban Dada yayi cikin katsewar tunani ya cigaba da faɗin, “Na zo ne ba a matsayin shugaban ƙasa kawai ba. Na zo a matsayin soja… a matsayin mutumin kuma da ke bin ka bashi.”. Ya ɗan dakata, yana kallon idanuwan Dada kai tsaye. “Akwai guba a jikinka Haysam.” Maigadi ya buɗe musu gate, Mu'azz ya shige da motar yana samun waje yay parking. Sun fito suna gulmar ƙanin maigadi Sanda dan gayene, akwai son yin gayu sai dai irin namu na ƙauye. Har zasu wuce ciki sabon driver ya iso wajen yana kiran sunan Nimrah. Kusan lokaci guda Nimrah, Ruky, Mu'azz suka juyo da mamaki. Nimrah da ƙirjinta yay mummunar bugawa da ƙyar ta iya daurewa ta amsa masa. Sai dai ta kasa motsawa taje inda yake sai shine ya ƙaraso. Ledar hannunsa ya miƙa mata yana faɗin, “Yaron nan daya kawo mage ranar ne yace a baki. Yace a gaishe ku ke da yar uwarki”. Ji Nimrah take kamar jikinta na rawa. Ta dai daure ta amsa tana gyaɗa masa kai dan ta kasa magana. Shi kuma bai damu ba ya juya ya bar wajen. Sai ma Ruky ce dake ƴar dariya cikin tsokana ta ce,.........✍️ Jininta na tsinkewa ta ciroshi, haka ta shiga buɗeshi zuciyarta na rawa. Kamar Ranar kuwa sai ga takarda ƙarama a ciki, ɗauka tai ta buɗe. _Da alama baki duba saƙon ranar ba ko? To ki sani, cigaba da sakacinki na nufin yin dana sani. Duk da kuwa a cikin dana sanin kike shekaru da dama. Idan kuma bakiyi gaggawar dubawa ba zaki dawwama a dana sanin har karshen rayuwarki musamman idan kika fara cin karo da gawar wani a cikin gidank....._ Batama iya ta ƙarasa ba saboda wani yuuuu data risketa na hajijiya. Ta miƙe zambar tana nufar inda suke ajiye handbags ɗinsu. Laluben ta wadda tai amfani da ita a ranar ta shiga yi dan ko books ɗin batama cireba a ciki. Haka ta zazzageta litattafan suka zubo ƙasa. Tsabar ta rikice tama manta littafin da ka rubuta saƙon yake a ciki a ranar, dan haka dukansu ta shiga buɗewa ɗaya bayan ɗaya sai ana ƙarshe taga takardar, ɗauka tai ta sake karantawa, jin book mai jan bango yasa ta ɗaukesa ta fara buɗo shafukan ƙarshe tana duba lamba harta samu wanda akace. Data buɗe shafin bataga komai ba, sai da ta maida zata rufe ta farga da memory card da aka tura ciki sosai kaɗan ake ganinsa. Tana jawo shi ta wani sauke ajiyar zuciya mai nauyi, sai da ta zuba masa ido ranta fal tambayoyin da basu da amsa. Dai-dai nan aka fara buga ƙofa dan haka ta miƙe tana tattare books ɗin da sauri ta maida a bag ɗin, memoryn ta saka a cikin bra dan dole ta nema waya yanzun nan. Koda taje ta buɗe ƙofar sai taga Afrah ce. Da ƙyar ta daure ta ce, “My Afry ya akayi?”. “Aunty yunwa nake ji, kuma ke nake so kimin noodles”. Kai ta iya jinjina mata kawai ta kama hannunta suka fita......
<%><<%>><%>
A yau Adeel ya sake dawowa ƙasar bayan tafiyar kwanaki da yayi amsa kiran mahaifiyarsa. Sai dai masaukinsa na hotel ɗin can ya fara sauka, dan kwana biyu kawai yake ganin zai yi ya sake komawa sai ya kammala uzirin daya taso masa sai ya dawo sannan yayi shirin da yake so. A bazata Hajiya Hasiba da suka samu labarin yaje gida batare da gaya musu ba a bakin First Lady taga kiran nasa a yau. Sai da gabanta ya faɗi, ta daure da ƙyar dai ta ɗaga dan voice call ne na WhatsApp yay mata. Tashi tai a falon dan duk suna zaune ne idan ka cire Mamawo da bata ƙasar ma. Nabeeha na charting da ƙawayenta ne. Su Amima na kallon Film, sai dai hankalin Nabeeha ya rabu ne gida biyu da tunanin hukuncin data gama yanke ma kanta na komawa gidan Abbansu itama kamar Ismat. Dan haka koda taji Momyn tana gaisuwa da yanayin girmamawa taji a ranta Adeel ne, dan duk da tana tare da manyan mutane girman da take bama Adeel da banne dana kowa. Kuma zata iya girme masa, sai dai bazata haifeshi ba a kwatance duk da tayi karatu kafin aure, ita ba'ai mata auren ƙarancin shekaru ba kamar yanda take basu labari........
((%))★((%))★((%))
Har washe gari duk yanda Nimrah taso samun waya ta saka memoryn nan hakan ya gagara, ba kuma samun wayar ne mai wuya ba, keɓewa gefe ne ta gagara samu. Dan kowa yau na gida su Mammah ce ma ta ɗan fita tare da Uncle Bilal kuma zuwa sha biyu suka dawo. Gashi tana fashin salla. Ruky ce kawai ke shiga yi balle ta fake da wannan. Da dare kuma suna tare da Ruky, bata son fito mata da abinda ke faruwa saboda ance wani zai mutu. Koda Rukyn ta tambayeta ma littafan da Sayyid ya kawo kawai ta nuna mata cewar ta kaisu cikin littatafan su dake shirye a ƴar kanta, wajen yana a ƙasan hannun bene ne matsayin study table ɗinsu.. Ita kuma tana bata labarin yanda sukayi da su Uncle's jiya. Nimrah bata samu yanda take so ba sai da kowa ya tafi sallar magriba , ta tabbatar sai isha'i kuma. tana ganin Ruky ma ta kabbara salla ta zare jikinta tabar bedroom ɗin zuwa sama da wayar Mammah a hannu, dan tasan itace zata jima bata fargaba fiye da sauran. A sama a kwai ɗakin kusan ƙarshe da ƙofarsa ta ɗan juya ma nasu Yaya Ammar, shi ta shige. Babu kowa a ɗakin babu ma wanda ya taɓa zama cikinsa. Amma akwai kaya da aka ajiye sai dai komai na a leda a jingine kawai.