Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 44

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 44

.....they turned on Rukyn, and she was all scared as she should be. She quickly said, "GOD doesn't matter, Uncle, I'm just looking at books." The way she did it made everyone understand that there is something they need to know after that. Then Yaya Ammar said, "You come here". "Uncle, I said, it doesn't matter to GOD". "It's okay too, Ruky, you just came to me." She was afraid that Nimrah's love would be told to them, but there was no way she could find out where they were. Sometimes Yaya Bilal easily teased the three of them, even Dadan. But today Yaya Ja'afar is persuasively asking her to tell them that they will not tell them. What is between Nimrah and their Sayyadin?. "And if you don't say it, I will inform Yaya." She was referring to their daddy, so she started shaking her head, "No, Uncle, son of GOD, don't tell him. It's just that the Sayyadin loves Ninah. But why don't you care, and you should ask him." "If you don't have a cup, why is it in your house?". It was Yaya Ma'aruff who spoke now. Rukyn quickly said, "Randa brought the magician, and then the day Baby Nawal took a message to Mah-mah's house for books, and we forgot them there. Last year at Daddy's house too" Amma

Standalone post806 words

44

..........“Da alama fa Sayyadi Kamal ya buɗe wuta Sisi, kwanaki a gidan Aunty Mimi books, kwana biyu da suka wuce ma haka, yau kuma mi muka samu?”. Har Nimrah ta sakar mata ledar sai kuma ta amshe da sauri saboda tuna takardar cikin wancan saƙon. Dai-dai Mu'azz na ƙarasowa yana tambayar, “Sayyadi Kamal ɗin dai again yau ma?”. “Ai kuwa dai Yaya Mu'azz, halan bakuyi masa maganar da kuka ce ba?”. Ruky ta bashi amsa cike da shaƙiyanci. Sai dai kafin yay magana Nimrah tabar gurin da sauri, ga kuma su Yaya Ma'aruff sun shigo suma gidan da alama daga wani waje suke dan a ƙafa suke, sai ya zam hankalinsu Ruky ya rabu har su Yaya Ammar ɗin suka tambayesu lafiya ganin yanda Nimrah ta wuce ciki kamar da sassarfa. Cikin takaici Mu'azz ke sanar musu wai saƙo sayyadinsu na islamiyya ya aikoma Nimrah. “Saƙon mi?”. Yaya Ma'aruff ya tambaya. Kallon Ruky Mu'azz yayi da faɗin, “Wlhy Uncle ban sani ba nima. Ruky ce tasan komai duk da dai ranar muna gidan Daddy ya aiko mata books nan ma”. Hankalinsu duk suka maida akan Rukyn, sai duk taji tsoro ya kamata. Da sauri ta ce, “ALLAH ba komai fa Uncle, kawai dai ina ga litattafai ne.” Yanda tayi yasa duk suka fahimci akwai abinda ya dace su sani bayan hakan. Dan haka Yaya Ammar ya ce, “Kinga zo nan”. “Uncle nace fa ba komai ALLAH”. “Nima ai bance da komai ba Ruky, canai kawai kizo naji.” Ita tsoronta kar suji son Nimrah yake a musu faɗa, amma babu yanda ta iya ta ƙarasa inda suke. Wani lokacin Yaya Bilal ya fisu sauƙi su ukun nan har Dadan ma. Amma yau sai ga Yaya Ja'afar cikin lallashi yana tambayarta ta faɗa musu bazasu musu faɗa ba. Minene tsakanin Nimrah da Sayyadin nasu?. “Idan kuma bazaki faɗa ba zan sanar da Yaya.” Tasan Daddynsu ake nufi, dan haka ta shiga girgiza kai, “A'a Uncle dan ALLAH karka faɗa masa. Dama kawai shi Sayyadin yana son Ninah ne. Amma wlhy bata kulashi, kuma ka tambaya ma kaji”. “In bata kulashi miyasa yasan gidan ku?”. Yaya Ma'aruff ne yay magana yanzu. Da sauri Rukyn ta ce, “Randa ya kawo mage ne, sai kuma ranar sunan Baby Nawal ya kai saƙo gidan Mah-mah na books, kuma can gidan ma muka mantasu. Shekaran jiya ma a gidan Daddy haka” Ammar zai yi magana Yaya Ja'afar ya hanashi ta hanyar riƙe masa hannu, ƙofa ya nunama Rukyn da faɗin, “Shike nan shige ciki”. Aiko da gudu ta wuce. Koda ta shiga falo ba taga Nimrah ba sai su Aunty Biebah, sai kawai ta rungume Biebah ɗin, kafin ta saketa ta koma kan su Aunty Lailah tana tambayar ina Mammah?. Bedroom suka nuna mata inda Nimrah dama tana ciki, dan itama tana shigowa ta gansu sai ta shanye tashin hankalinta tayi kamar yanda Ruƙayya tayi sannan ta shige bedroom ɗin Mammah. Tana rungume da ita itama Rukyn ta shigo, sai kawai itama ta rungume Mammah ɗin dan kewarta suke ji mai girman gaske......

==============

Da daddare kamar yanda Daddy Imran ya faɗa yazo yay ma Mammah sallama akan zaije wani aiki. Amma zai jima dan zai iya ɗaukar wata ɗaya ma. Mammah ta jimanta sosai, amma tai masa addu'a ranta duk babu daɗi. Ganin Imran na rage mata kewa Dada sosai a zuciyarta. Shiyyasa bata cika son taga shima zaiyi nesa da su ba. Sai dai babu yanda suka iya tunda aikinsu ne. Su kansu su Yaya Ma'aruff sunji babu daɗi, dan kamar dai Mammah ɗince Imran na ɗauke musu kewar Dada. Amma da yake su maza ne sai suka danne suka bishi da addu'a suma. Daga nan suka taɓa hira Ruky da Nimrah na jera masa tsarabar da suke so idan zai dawo harda wayoyi. Duk da dai Nimrah dauriya kawai take yi tun ɗazun hankalinta nakan saƙon Sayyidi Kamal da bata samu ta duba ba. Ƙarfe tara dai-dai Imran yabar gidan, daga nan kuma airport zai wuce dan a can zasu haɗu da Dada kawai...

Bayan wucewarsa Nimrah ta faki idonsu ta wuce ɗaki ganin hankalin Ruky ya koma wajen yima su Abees homework ita da Mu'azz. Gabanta sai faɗuwa yake, tana shiga ta maida ƙofar ta rufe harda mirza key dan jikinta ma rawa yake. A haka ta buɗe ledar ta leƙa, a mamakinta yau ma books ne kamar koyau she. Sai dai yau guda ɗaya ne kawai, hisnul muslim ne kuma ƙarami. Received at 4:00 PMƘaramin table ta jawo duk da akwai ƴar ƙura haka ta zauna ta saka wayar Mammah a plane mood dan karma a kira, ta zare memory ɗin ciki ta saka wanda tun jiya ke maƙale a jikinta. Tana tabbatar da ya hau ta wuce wajen videos kawai. Videos uku ne kacal a ciki, jikinka har rawa yake ta shiga na farko tai playing...........✍️