Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 45

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 45

.....one has his picture window in this house and is called by the name DADA, Dada is respected by everyone as the father figure of this house. He immediately raised his gun with a cruel expression, in disbelief he shot the two people as she felt the certainty of their importance to her is very high. Unprecedented growth, not to mention the limit of imagination. The fourth thing is the shooting of young children by the soldiers, the children whose faces are pointing at her, I am sure she knows what they are doing. Not Nimrah's heart, even my memory was beating as if it would break apart with the trembling of her body, wet with sweat and sweat, you think she was splashed with water. But even if she can't remember anything, this one face that looks like hers will not be forgotten in her heart and memory. The face of her Ummah, definitely her Ummah, her Ummah is her Ummah who has lived a life in the past in a different place than the one she is in now that she can't remember anything. Then the second face, the face of one of the soldiers who shot Ummanta, Dadan knew him too but she could not remember anything about him. The second face with her.....

Standalone post1,529 words

KIƊA A RUWA45 ......Babu abinda kallon videos ɗin nan suka zamewa Nimrah face rikicewar tunani da ruɗanin zuciya. Sakamakon abu uku masu tsayawa a zuciya. Na farko kamammin matar dake kama da ita matuƙa. Matar da ƙwaƙwalwarta ke son hasaso mata abubuwa da yawa game da ita da tuna mata sunanta na uwa mahaifiya da take kira da UMMA a wani ƙarni da ba komai take iya tunawa da ƙyau ba sakamakon ƙaracin shekaru. Sai dai wayonta da kaifin basira na hasko mata abubuwa daban-daban, dan wani ɓangare na brain ɗinta na ƙoƙarin hasko mata kamanin Umman tata da rashin ganin ko hotonta bayan rabuwarsu yasa suka fara disashewa kaɗan, amma dai bata manta da ita ba. Abu na biyu dattijon tsoho shima dake kammani da Umman tata dai, duk da furfurar sajen gemunsa ya lulluɓe kaso mafi yawa a zahiri, abin tsoro da ruɗani shima dai tamkar waccan fuskar ta Ummanta an harbesa da bindiga hannunsa da aka juyar a bayansa da handcuffs tamkar wani dabba. Abin sake rikita lissafin mutum ɗaya ne duk yay harbin, mutum ɗaya tak da taga hotonsa a wannan gidan kuma ake kira da suna DADA, Dada dai da kowa ke girmama sunan matsayin uba jigo na wannan gidan. Shi ɗin nan dai ɗaya tak ya ɗaga bindiga fuskarsa da murmurshin rashin tausayi, rashin imani ya harbi mutane biyun nan dai da take jin tabbacin muhimmancinsu a gare ta mai matuƙar girma ne. Girma mara misali balle iyakar hasashe. Abu na huɗu harbe yara ƙanana da sojoji sukayi, yaran da fuskokinsu ke mata kai-kawo na tabbacin ta sansu fa. Ba zuciyar Nimrah ba, hatta ƙwaƙwalwata bugawa take tamkar zasu tarwatse a tare da rawar jikinta daya jiƙe sharkaf da zufa kai kace an watsa mata ruwa ne, ruwan ma na zafi dake saurin bayyana gumi.. Shekarunta sunyi ƙanƙanta sosai a wancan lokacin da har ta gagara iya tuna abubuwa da yawa. Sai dai ko bazata iya tuna komai ba wannan fuskar guda ɗaya tak mai kama da tata bazata mantu a cikin zuciya da ƙwaƙwalwarta ba. Fuskar Ummanta, tabbas Ummanta, Ummanta dai Ummanta da sukai wata rayuwa a baya a wani wajen daba wannan da take ba a yanzu da ba komai zata iya tunawa ba. Sai fuska ta biyu, fuskar sojan daya harbi Ummanta, Dadan nan dai da itama ta sanshi amma ba komai zata iya tunawa a kansa ba. Fuska ta biyu da itama dai Soja kuma Dada ya harba da kansa dake ɗaure cikin sarƙar handcuffs, fuskar tsohon dattijo mai kammani da fuskar Ummanta da tata, wanda tunaninta ya fara dawo mata da matsayinsa na kaka da suke zuwa gaidawa ita da Ummanta, sai dai ba komai take iya tunawa game da shi ba shima. Shima dai wannan soja Dada ne ya harbesa ya faɗi ya mutu, mutuwa fa dai da kowa ya sani kuma yake tsoro. Kai wlhy ita kam zata haukace, lallai tana buƙatar fashin baƙi, fashin baƙi a wajen wanda ya aiko mata da wannan rikitaccen video mai sabauta tunani da ƙwaƙwalwa. Kuma da gaggawa take buƙatar hakan, kai in zai yiwu ma a daren nan maybe hakan yasa ta fahimci abinda ake nufi da a yanzu ta gagara fahimta. Sai dai a daren nan dai da tasan bazai yiwu mata ba. Karo na farko da taji zafin rashin waya da riƙe number kowa a rayuwarta, dan data san koda number ɗaya ce tak ta Sayyadi Kamal data nemeshi a yanzun batare da ko zaman yin wannan tunanin mai son tarwatsa mata kanta dake sarawa ba. Kamar an bata umarnin shiga videon ƙarshe da bata kalla ba ta ɗauka wayar da sauri ta koma ciki tai playing. Cikin sa'a kuwa sai ga wata fuska ta bayyana. Fuskar wani mutumi da bata taɓa sani ba. Yana zaune ne kawai tamkar suna video call yana ganinta tana ganinsa. Dan kai tsaye idanunsa akan screen ɗin suke. Kalmar farko daya fara ambatawa ta sakata sake nutsuwa a kallonsa. “Naja'atu Nimrah! Na tabbatar idan har kin iso kan wannan videon nawa yanzu tom kin kalla bidiyon baya kenan. Bani da isasshen lokacin janki da nisa. Amma zan baki dama da albishir guda ɗaya da zai fiddaki daga ruɗanin da ko tantama banayi dole ne sai kin shiga a lokacin da kika kalla waɗan can bidiyon guda biyu kafin wannan. Da farko dai sunana Dagger, nine na aiko miki da waɗan nan saƙwanin guda biyu ba Sayyidi Kamal Ba kamar yanda kika ji, na saka sunansa ne dan ki amshi saƙon da muhimmanci tunda shi kin sanshi. Nimrah kina buƙata ta a wannan gaɓar fiye da kowa a rayuwarki, dan kuwa nine kawai zan iya banbance miki tsakanin aya da tsakuwa ta ainahin RAYUWARKI. Ni ne kawai zan miki fashin baƙi akan abinda kika gani a videos ɗin can. Nine kawai zan kaiki inda UMMANKI take. Ba ruɗani zan saka miki a zuciya ba, amma ni ne kawai zan sanar dake gaskiya akan mutanen da kike rayuwa da su a yanzu. Idan kuma baki yarda dani ba na baki ɗan lokaci ki bincika ina wanda kuke kira DADA anan gidan yake? Da gaske yana wata ƙasa ne ko yana prison saboda abinda ya aikata a wannan videos ɗin dana nuna miki. Idan kika samu wannan amsar tayi kama da abinda na kawo miki zaki iya nemana ta wannan number ɗin ni kuma zan sanar miki inda nake na miki dukkan bayanin da kike buƙata. Sai dai da sharaɗi guda biyu tak, wanda in har kina buƙatar duk wannan dole kiyi abu biyun nan. Na farko ki rufe wanan zancen daga UBANGIJI sai ke, idan kikace zaki bari wani ya sani zaki iya rasa Ruƙayya dan akwai masu son kasheta. Abu na biyu na ƙarshe. A duk inda kika ɓuya yanzu dan ganin wannan video ɗin ki tashi ki saita kanki tamkar komai bai faru ba ki koma harkokinki karki sake ki bari wani ya fahimci halin da kike ciki koda Ruƙayya ɗin ce. Idan ba haka ba zan sake maimaita miki wasu zasu kashe ta. Kar kiyi tunanin kirana da wayar da kika kalla video ɗin nan, idan kina son kirana ki samu wayar wani daban ba ɗan gidan ba. Na barki lafiya. Ki kasance cikin aminci ƴar albarka”. Ƙitt videon ya ƙare, ya kuma ƙare ne tare da tsayawar duniyar Nimrah a lokaci guda.......

<<<<<。⁠◕⁠‿⁠◕⁠。>>>>>

Wauta da ƙuruciya suka haɗu sukai tasiri mai ƙarfi ga al'amarin Nimrah da abinda take ta ƙoƙarin hana bayyanarsa a fuskarta da zuciya. Kamar wasa a daren wannan ranar ko sau ɗaya bata rintsa ba, da Ruky ta dameta da tambaya ma sai ta gaya mata baƙar maganar da ta saka sukai faɗa Rukyn tai zuciya itama ta watsar da ita. Ƙarshe ma ta bar mata ɗakin ta koma ɗakin Biebah ta kwanta. Hakan ba sabon abu bane ga Biebah, dan lokaci-lokaci Nimrah da Ruƙayya kanyi faɗa, wanda yafi shaƙa sai ya dawo ɗakinta ya kwanta ko ɗakin Mammah, hakan kuma baya hana gari na wayewa kaga sun shirya, dan sukan jima ma basuyi faɗan ba. Shiyyasa koda Ruky ta dawo ɗakinta a wannan daren batace mata komai ba ba kuma ya hanata kwanciyar ba. Dan ta tabbatar itama Nimrah ɗin da wuya ta kwana a ɗakin nasu zata wuce ɗakin Mammah ne. Sai dai hasashen Biebah bai tabbata ba, dan kuwa a yau Nimrah bama ta iya motsawa a gadon da take kwance ba balle fita a ɗakin duk da taji sanda Ruky ta fice ta bar mata ɗakin. Hasali ma sai lokacin ta samu damar fashewa da kuka saboda nauyin da ƙirjinta yay mata. Daga wannan kukan ne zazzaɓi mai azabar zafi ya rufeta, dama gashi tana period. Haka ta kwana tana rawar sanyi tama kasa tashi ta kashe acn ɗakin, kai ko jan bargo ta rufa ta kasa yi ma. A haka sanyin asuba ya sake bayyana ya kuma mata rijif. Lokacin da Ruky ta shigo ɗaukar rigar sallarta da nishinta ta fara cin karo. Tuni ta manta da wani batun faɗan su ta zabura kanta jiki na rawa. Ai tana taɓa jikinta taji matsanancin zafin da yayi sai ta sake rikicewa, tama fita a guje tana ƙwala kiran Small Mom. Zambar Biebah data idar da rakata'ainul fijir ta miƙe tayi ƙofa. Hannunta kawai Ruky ta kama suka juya tana maimaita sunan “Ninah! Ninah batare data iya mata cikakken bayani ba. Sai da suka shiga ɗakin itama hankalinta ya tashi da ganin halin da Nimrah ɗin ke ciki.....

Ana idar da sallar asuba doctor ɗinsu da aka kira ya iso gidan. Kasancewar an maidota ɗakin Mammah har nan aka kaisa ya dubata da mata ƴan tambayoyi. Da ƙyar take bashi amsa wasu ma sai Mammah ke bashi. Ya gama ƴan rubuce-rubucen sa yace yana ganin malaria ce ta saka mata zazzaɓi. Sai ƴar damuwa da kukan da tayi. Ba ƙaramin mamaki Mammah tayi ba da jin batun damuwa dana kuka. Amma sai batace komai ba tabar doctor yay aikinsa. Allurori yayi cikin drip ya saka mata, kasancewar akwai masu saka barci a take barcin yay galaba a kanta. Mammah bata sanarma kowa abinda likita ya faɗa mata ba, ta bar komai a hannunta zata saka ido kan Nimrah ɗin harta fahimci damuwar tata..........✍️46