Kenza eBookz
Cover art for KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 46

Post

KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 46

.....she stopped them from taking Ruky to the school and decided to go back. How did she manage to talk to this man this weekend so they could meet in tahfiz. She was with this thought until Rukayya came back from school. The men of the house got ready for the masjid and went out.. ★Ammar came out in the car to go to the Friday masjid with Abees and Mu'azz and saw Adeel on the way also going down, only Ammar stopped and they took him. Mu'azz who was in front went back and Adeel entered. They went to the Central Mosque together, after praying as usual, they went to greet their Baffan, Imran and Hajjo, then they went with Adeel, and there they met Yaya Ja'afar and Ma'aruff. Ammar introduced Adeel as his friend and neighbor. They are people who respect human beings, no one showed anything but respect to Adeel, they had a meal at Akasha's house and had a conversation even though Adeel does not speak Hausa but English, so the conversation turned to the language of victory. It was only when Baffa gave them Yaya Ma'aruff advice on the matter of their Uncle Tasi'u to go back to Lagos that they should forget everything and be patient and accept him like how Mammah was patient and he returne

Standalone post1,487 words

.........Kwana biyu Nimrah na jiyyar zuciya da jiki ko muce sunayi ita da Hassanar tata Ruƙayya, dan itama dai duk ta zama sukuku da ita. Sannan komai Nimrah tace tana so zata tashi tai mata cike da kulawa. Ita Biebah har dariya ma suke bata kamar ba waɗanda suka gama shan faɗa ba a daren ciwon Nimrah ɗin. Uncle's ɗinsu kam da su Aunty Shariffa kowa ƙoƙarin tattalinta yake, bare kuma Mammah da suka dawo ɗakinta ma kwana tare da ita, dan tace har Nimrah ɗin ta samu sauƙi sannan. To Alhamdullah sauƙi ya samu, dan yau juma'a ma har cewa tai zata makaranta Mammah ce ta hanata tace dai Monday, amma taso zuwa kodan ta samu hanyar samun wayar da zatai kiran number ɗin can da aka faɗa mata a video ɗin. Dan duk yanda take yaƙin ture abun a ranta da hakan kanta yin abinda suka ce ta kasa. Kamar wadda ake mintsini da azalzalarta haka take ji. Dan ma bata samun sukunin yin tunani saboda Mammah bata barinta koda yaushe tana tare da ita musamman idan du su Ruky sun tafi makaranta. Amma yau da Mammah ta hana tabi su Ruky makarantar ta gama yankema kanta shawarar koma ta yaya sai ta samu tayi magana da mutumin nan a cikin weekend ɗin nan su haɗu a tahfiz. Da wannan tunanin ta kasance har su Ruƙayya suka dawo daga makaranta. Mazan gidan sukai shirin massalaci suka fita..

★Ammar ya fito a mota zaije massalacin juma'a shi da su Abees da Mu'azz sai ga Adeel a hanya shima zai je a ƙasa, sai kawai Ammar ya tsaya suka ɗaukeshi. Mu'azz dake gaba ya koma baya Adeel ya shiga. Haka sukaje Central mosque ɗin tare, bayan idar da salla a ƙa'ida sukan wuce gaishe da Baffan su Imran da Hajjo, dan haka tare da Adeel sukaje, acan kuma suka samu su Yaya Ja'afar da Ma'aruff. Ammar ya gabatar da Adeel matsayin abokinsa makwafcinsu. Su mutanene masu daraja ƴan adam, babu wanda ya nuna komai akan Adeel sai mutuntawa, sukaci abinci a gidan akasha hira duk da shi Adeel baya jin Hausa sai turanci, dan haka hirar duk sai ta koma da yaren nasara. Sai da a gaɓar da Baffa ke ma su Yaya Ma'aruff nasiha akan batun Uncle ɗinsu Tasi'u daya koma Lagos akan su manta da komai suyi hakuri su karɓesa kamar yanda Mammah ta hakura ne ya koma Hausa. Ya kara musu nasiha sosai duk da kuwa randa su Nimrah suka zo gidan suka samu Uncle Ammar ya fita da shi sun haɗu ne a gidan Uncle Nasiru dama sun musu faɗa akan batun Uncle Tasi'u ɗin. A ranar dai sun ce komai ya wuce, amma basuce sun yafe masa ba. Shine ya koma Lagos ɗin da nufin zai kawo yaransa gidan Mammah ɗin, washe gari ya tafi. Shine yanzu Baffan ya sake musu nasiha shi da hajjo. Daga haka suka koma batun kasuwanci. Dan shima Baffa ɗan kasuwa ne da sukaci zamani a lokacin ƙuruciya....

★★★★★

A kusan dai-dai wannan lokacin Nimrah ce ta faki idon su Mammah datai baƙi Ruky kuma na barci ta nufo gate. Ƙanin Baba maigadi kawai ta samu zaune yana latsa ƴar wayarsa rakani kashi harda ƙyauro a jikinta. Sallamar da tai masa ya saka shi ɗagowa yana kallonta, dan tunda yazo gidan magana bata taɓa haɗasu ba daga ita har Ruky. Saboda kallon marasa ji da rashin kunya yake musu ma shiyyasa bai taɓa fatan wani abu ya haɗasu ba. Amma mi, a mamakinsa sai ta masa sallama, baima san lips ɗinsa ya fara rawa wajen amsawa ba. Bata damu ba ta ɗora da gaishesa. Nan ma mamaki ya kama shi. Cikin kasa haƙuri ya ce, “Hajiya kina son wani abu ne?”. Nimrah ta ɗan sauke numfashi da waigawa ta kalla hanyar cikin gida, har yanzu babu alamar kowa kamar yanda tai fata, sai sabon driver data hango can wajen mota yana fitowa daga ciki alamar wani abun yake yi wanda ta san bai wuce goge motar ba dan ɗazun taga suna wankewa shi da Sanda ɗin. Kauda kanta tai daga kallonsu dan bazai yiwu yaji maganarsu ba daga inda suke, kuma taga hankalinsa gaba ɗaya baya a kansu ma. “Waya zaka ara min”. Tai furucin idonta akan wayarsa. Shima da mamaki ya kalla wayar sannan ya sake ɗagowa ya kalleta. “Hajiya waya dai? Kalli fa wayar tawa yanda take.” “Karka damu ba wani abu zanyi da ita ba.” A zuciyarsa ya furta (wannan yarinyar kuwa anya ba zargina take ba, dan na fahimci shegen wayo ne da ita. Ko kuma wani ne dai ya turota gareni a cikin gidan...) “Malam Sanda”. Nimrah ta katse masa tunani. Firgigit ya dawo hayyacinsa. Ganin yanda ta tsatstsare shi da manyan fararen idannunta baima san ya miƙa mata wayar ba. “Na gode”. Ta faɗa a hankali tana barin wajen. Da kallo ya bita, kamar yanda Malam Buba driver ke binta da kallon gefen ido, dan tun ɗazun dama hankalinsa a kansu yake duk da baya iya juyo abinda suke faɗa. Ganin ta amshi wayar Sanda ya sashi fahimtar mi take shirin yi, da sauri ya koma cikin motar kamar bai gama abinda yake ba, ya zaro tashi ƙaramar wayar ya shiga neman layin Dagger daya san zai iya samunsa da gaggawa. Aiko babu wani jimawa ya ɗaga shima daga can, dan kwanakin nan gaba ɗaya cikin ƙaguwar jiran kiran Nimrah yake yi, amma shiru kake ji, sai da ma Molen ke sanar masa bata da lafiya ne kwana biyu sannan. Ko gaisuwa basu yi ba Mole ya fara sanar masa, “Oga ka kasance cikin shiri na tabbatar kai zata kira. Dan gata can ta amshi wayar Sanda ta nufi bayan ɗakin janareton su.” Sai da Dagger ya sauke wata wawiyar ajiyar zuciya sannan ya ce, “Mole waye Sanda kuma?”. Cikin ƙaguwa Mole ya ce, “Wannan ƙanin Almu ɗin fa da nake gaya maka sunzo ranar daya dawo tare”. “Oh-oh na tuna, bara na ɗaga inaga gata tana kira.....” Bai jira amsar Mole ɗin ba ya katse kiran.....

A ɓangaren Nimrah data zagaya bayan ɗakin Gen... Ɗin gidan kuwa da sauri ta fara loda number wayar data kwafe a jikin ƙaramar takarda, sai da ta danna kira ta tabbatar ya shiga sannan ta nema waje ta zauna dan ta tabbatar babu mai zuwa nan a cikin ƴan gidan balle yay tunanin tana nan. Sai dai ma'aikatan gidan irin su maigadi, kuma sai da ta leƙa ta tabbatar babu kowa a ɗakin dan dama maigadi ne bata gani ba acan waje, shiko ƙaninsa Sanda da Malam Buba tunda sun ganta tasan baza su zo b...... Sallamar da akayi ce ta katse mata tunaninta. Duk da yanda muryar mai maganar ke a buɗe ba daɗin ji dai ta daure ta amsa. Daga can Dagger ya sake matse murya shi a dole yau yana waya da masoyiya, dan jikinsa har tsuma-tsuma yake yana dannewa da ƙyar. Saboda yanda muryar Nimrah ɗin ta dakesa ji yay kamar zai shiɗe.... “Kana magana da Naja'atu Nimrah ne? Dan ALLAH waye kai?”. Da ƙyar Dagger ya iya dannewa ya daidaita yanayin sa ya bata amsa da, “Sani na a yanzu ba shi bane mai muhimmanci, ina ya kamata mu haɗu ya dace ki nema kawai. Dan lokacin da kike da shi a gareni bashi da wani yawa, zan iya ɓace miki a kowane lokaci.” Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, tare da faɗin, “Shi ke nan a ina zamu haɗun? Yau she kuma? Amma ka sani ina son ganin ka da gaggawa”. “Baki da matsala indai ni ne. Kamar yanda nai niyyar sanar miki gaskiya ba zan guje miki ba. Na baki damar ki faɗi a indai zai miki sauƙin mu haɗun batare da ko ƴar uwarki ta sani ba, saboda gudun kar a cutar miki da ita”. Ba tsoro Nimrah ke ji ba, tsoronta kawai kada a taɓa mata lafiyar kowa a ahalinta ne. Dan haka ta ce, “Ni bani da inda na sani bayan gidan mu, kuma ba'a barina fita ni kaɗai”. “Okay na gane, makaranta fa?”. “Makarantar bokon mu ma baza'a bari na fita ba, sai dai mu haɗu a tahfiz gobe, shima lokacin da ake kawo ma ɗalibai abinci”. “Ta yaya kenan?”. “Zan ma drivern gidanmu magana”. “Amma nace miki bana son kowa ya sani ko? Shi drivern baƙya tsoron ya bamu matsala?”. “To ni ban san yaya zan yi ba, wannan hanyar gareni kaɗai gaskiya. In dai ba ita ba sai dai a haƙura....” Da sauri Dagger daya fahimci zata ƙwaɓa masa aiki ya ce, “Karki damu bar komai a hannuna zan san yanda zanyi. Goben kawai ki saurare ni”. Kanta ta gyaɗa tana ɗan juyawa jin kamar motsi, sai kuma ta sauke wayar a kunnenta. Ganin babu komai ta sauke ajiyar zuciya tare da goge number ɗin daga cikin wayar ta muƙe zata bar wajen. Da sauri Sanda dake laɓe jikin window ɗin bayinsu dake ta wajen ya duƙe dan duk yana jinta.47