
Post
KIDA A RUWA BOOK 2 PAGE 59
.....in Dada it's the same as coming home. A lot happened during the week. From all sides everything is hard and hot. However, the enemies have not yet been able to confirm Dada's return to his lineage. In the end, they also ignored the investigation of the hospital that they suspected was treating them. He or Malam Buba is walking around with Dagger carefully, saying that he has lost the way to tell Nimrah this document is always with Rukayya. Since Dagger agreed until his soul began to feel sad, until now he began to think of following a new way to find Nimrah, the fool, knowing Mr. Buba. He or Malam Buba never thought that Dagger would look for another way, his mind was completely waiting for their suspicions that they gave him a week to meet him face to face, so he was ready for that, he made sure that if he got this opportunity, Dagger was not enough to continue to turn him, he also became his own teacher, but the children that Dagger is leading should be divided into two and give him half. ★SCHOOL★ As usual, when we break, you will find them in groups, each one doing his own thing. Some are conversations with friends, some with their boyfriends as the school is co-ed. Some of
59
..........“Waye ya tura wannan saƙon?”. “Baban yarinyar nan ne da Dagger ya kawo mana hotunanta kwanaki”. “Shi ba a ƙarƙashin Dagger ya ke ba?”. “Tabbas a ƙarƙashinsa yake, shiyyasa nima nayi mamakin saƙon. Dan haka na kawo maka ma ka gani, dan zancen sa ya ɗauki hankalina kuma ba abin wasa bane ba”. “Kayi ƙyan kai, kuma tabbas muna buƙatar mu sanshi a zahiri. Kwanaki nama Dagger umarnin ya kawo min shi amma shiru, ban san mi yake nufi ba. Ga Scythe shima shiru bayan yasan shi muke jira da bayanai”. “Oga na tabbatar zuwa anjima zamu iya ganin Mr Scythe, dan a daren jiya na samu tabbacin ganawarsa da Tafidan. Na wannan ne abin dubawa. Dan ya kamata musan wane saƙo yake son isar mana da baya son Dagger ya sani harya zagayo ta bayan fage”. “Haka ne, ka masa reply da muna son ganinsa. Sai kayi ƙoƙarin yanda za'a yazo nan ɗin daga yanzu zuwa sati guda bayan ka gama karantar al'amarinsa da bincike sosai akansa.”. “An gama oga. Ka daɗe kayi ƙarko”....
=================== ★1-WEEK LATER★
Satin Dada ɗaya kenan da dawowa gida. Abubuwa sun faru sosai a cikin satin. Ta kowane ɓangare komai yayi tsauri da yin zafi. Sai dai har yanzu maƙiya sun kasa samun tabbacin dawowar Dada cikin zuri'ar sa. Ƙarshe ma sun ɓige ne da binciken asibitin da suke zargin yana jiyya ne. Shi ko Malam Buba sai yawo yake ma Dagger da hankali, acewarsa ya rasa hanyar da zai bama Nimrah wannan takarda kullum tana tare da Ruƙayya. Tun Dagger na yarda har ransa ya fara ɓaci, zuwa yanzu ya fara tunanin bin sabuwar hanyar samun Nimrah ɗin batare da sanin Malam Buba ba. Shi ko Malam Buba bai taɓa tunanin Dagger zai nemi wata hanya ba, hankalinsa ma gaba ɗaya nakan jiran shubaninsu da suka bashi sati guda akan ganawa da shi fuska da fuska, dan haka a ƙagare yake da hakan, dan ya tabbatar da in har ya samu wannan damar Dagger bai isa cigaba da juya shi ba, shima ya zama ogan kansa sai dai a raba yaran da Dagger ke jagoranta biyu a bashi rabi.
★SCHOOL★
Kamar yanda suka saba idan anyi break zaka samesu group-group ne kowa na sha'aninsa. Wasu hira ce ta ƙawaye, wasu da samarinsu kasancewar makarantar haɗe take maza da mata. Wasu kam samarin ne zalla ke sabgarsu suma. Da yawan ƴammatan kan so haɗa ƙawance da su Nimrah, sai dai sanin halinsu kesa suji shakkar raɓarsu. Hakama samarin suna son suyi mu'amula da su, sai dai sanin kaɗan daga aikinsu su maka zagin ƙare dangi kesa su kama kansu. A yanzu ma suna gefe su biyu zaune, note Nimrah ke ƙwafa a littafin Ruky dan ita ɗazun ƙinyi tai, duk da ba wani note ɗin kirki bane kasancewar kowane subjects ɗinsu suna da textbooks ɗinsa. Ruƙayya na gefenta tana cin cin-cin, hirar Hanoon suke suna dariya, dan wani rashin mutunci suka mata yau da safe kafin su taho school. Nimrah ta ɗiba cin-cin ɗin tana faɗin, “ALLAH yasa mu tarar Dada baya gidan, yanda in ta tambaya muci uwarta da armashi, shegen fuska tasha mayukan bleaching kamar an silala carrot”. Sake tuntsurewa da dariya Ruky tai tana faɗin, “Sai da ke Trouble Queen. Hot pepper! Naj... Naj... Naja bombs”. Ƙulli Nimrah tai mata a baya da faɗin, “Muguwa irin jera min wannan suna haka, so kike sai na mutu naji ana Naja bomb yau zaki sha bamai-bamai...” Dariya sosai yanzu kam Ruky keyi, itama Nimrah na tayata.... “Hy beauty Barbies”. Wani yaro mai sanye da irin uniform ɗinsu ya faɗa. Tsagaitawa sukai da dariya suna masa kallon daga sama har ƙas. Ya girmesu sosai, dan kuwa ɗan ss3 ne. Hasalima shine headboy ɗin ƴan ss. Yaron baya ji a makarantar, dan ya tara ƴammata yanata haɗasu faɗa. Kasancewar sa ɗan tsohon president yasa ko ƙararsa makaranta bata taɓa kaiwa ba gidan su, dan tun yana js yake tsula tsiyarsa. Ya jima da sanin su Nimrah sai dai bai taɓa shiga sabgarsu ba duk da suna birgesa, amma fahimtar da yay yaran basu da kunya ya sa ya kama kansa. Yau dai yana zaune cikin group ɗin dake haɗe maza da mata ana shafta amma hankalinsa duk yana kan su Nimrah, ji yay ya kasa haƙuri ya taso ya samesu. Shine maimakon sallama ya ce musu wai (Hy Beauty Barbies). “Lafiya dai ko?”. “Eh to da sauƙi gaskiya. Mutanen naka ne dai suka aikata abinda suka saba, ga kuma wanda suka buge ɗin nan kwance baya numfashi ma. Kuma yaron tsohon shugaban ƙasa ne”. “Bugewa kuma? Sai kace wasu ƴan fashi...” “Wlhy ranka ya daɗe abin babba ne fa. Kuma suma can gidansu har mun kira su. Kaga kafin suzo wani abu kuma ya faru gara ku ku fara zuwa. Dan yaran nan gasu nan ko'a jikinsu kamar ma basu aikata komai ba.” Iska Daddy Imran ya ɗan furzar da faɗin, “Okay ba damuwa. Gani nan akan hanya”. Daga haka ya yanke kiran. Dada ya ɗan kalla da faɗin, “Inaga zamu wuce makarantar su Ninah akwai matsala, wlhy yaran nan nakan rasa mike damun kawunansu. Anya ba aljanu ne da su ba na faɗa. Da wahala ga Ruƙayya da Nimrah su cinye sati biyu ba'ace sunyi faɗa a makaranta ba, daga Islamiyya har boko. Idan anyi magana suce yaran ne basu da tarbiyya, shike nan su sun zama malaman koya tarbiyya kai jama'a”. Ko uhumm Dada baice ba, ta aikinsa ma yake hankali kwance. Shima Daddy Imran bai sake magana ba har suka iso makarantar tasu. Sai da ya samu waje yay parking sannan Dada ya bi makarantar da kallo. Imran dake ƙoƙarin fita ya ce, “Ina zuwa”. Daga haka ya maida murfin ya rufe yana barin wajen..........✍️